Showing 21001 words to 24000 words out of 44561 words

Chapter 8 - Bintu Diyar Bayi Ce 1 Complete Hausa Novel

06 Jan 2025

152

buhu gefe in da Bintu ke aje kayan sawa. Ko tabarma babu a d'akin, sai siminti da ya bi ya faffashe rugu rugu. Gefe guda Habibu ya aje akwatin sannan ya fice ya bar Bintu ta na mai zubewa bisa gadan ta a gajiye. Lalle kuwa kowa fa ya bar gida gida ya bar shi. Daga waje ta jiyo Inna na fad’in ‘’Ki hito ki watsa ruwa fa ‘yar nan’’
Bintu ta amsa ‘’Gani nan hitowa(fitowa) Inna’’

🐪🐫🐪🐫🐪🐫
®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪



©Khadija Sidi.....✍🏼

1⃣2⃣



Ganinsu gabanta nan da nan ta zube k’asa ta na mai fad’in "Rangwame salamun, masu duniya ku na shagalinku, babban bijimi babban Yerima, hadari malafar duniya, barka da siddi!’’

Yerima Nuhu wanda ya ke kyakkyawan saurayi, musammam idan ya sha rawani da shiga irin ta saraki, ya tsinci kan shi ya na mai murmusawa, yayin da abokansa su ka amsawa Bintu da ‘’An gaishe ki yarinya’’ Shi kuwa kallonta ya ke cike da shauki, ya ce ‘’Mu na lahiya Bintu arziki?’’ Dama da sunan da ya ke kiranta kenan.

Cike da nuna ladabi ta ce ‘’Lahiya lumi ran Yerima Nuhu ya d’ade." Kai ya gyad’a kafin ya zunguri dokin shi yayi gaba, haka sauran abokan na sa su ka rufa masa baya. Sai da ta tabbatar sun yi nisa sannan ta tashi ta na mai ajiyar zuciya, ita dai har ga Allah ba ta san irin kallan da Yerima ya ke mata ba tun yau ba, shiyasa ma duk inda ya ke ta ke gudun shi, ko da yake k’awarta wacce su ke kira Cangwai ta ce ina ma ita yake yi wa haka da sauran bayi ‘yan uwanta sun shiga uku da tak’ama. Da wannan tunanin Cangwai ta fad’o mata, ta na mai tunanin ko me ya hana ta zo tun jiya ta ganta yanda ta saba oho, bayan kiran Gimbiya za ta je ta duba ko lafiya, idan kuma sun had’u a babban gida shikenan.

Cikin wannan tunanin ta k’arasa soran da zai sada ta da cikin gidan sarki, wanda su ke kira babban gida. Ginin k’asa ne wanda aka gina tin tale-tele mai cike da kayan ado na al'ada. Sauro shida ne reras, wanda kowanne d’auke ya ke da shimfid’u da ado, biyu daga cikin su da d'akuna, wasu kuma tsuntsaye ne fal ciki musammam jemagu su ka mamaye saman ginin. Haka Bintu tai ta shiga ta na fita, wani ta tadda dogarai, wasu kuma bayi haka ta na gaishe su har ta fito sarari, sai ga ta farfajiyar gidan sarki. Duk da shi ginin bulo ne, amma komai na gidan tsarin al’ada da kuma tambarin sarauta ke gare shi. Wato tsayawa fasalta irin kyawun gidan sai na cika shafi be k’are, dan kuwa tsari dai na al’ada da sarauta gida ya tsaru.

Inna Salti Bintu ta fara cin karo da kasancewar 6angaran ta ne na farko cikin jerin matan gidan. Ta fito daga 6angaran na ta kenan sanye cikin shiga ta alfarma, abin ku da bafulatanar mace Allah ya bata kyau, gashi sam ba ta tsufa. hannun ta rik'e da na Yerima Nadir, sai baiwar ta wacce ta ke biye da ita. Ganinta nan ma Bintu ta zube domin d’ibar gaisuwa ta na mai fad’in ‘’Barka da safiya uwa ma ba da mama, farar aniya alkhairin duniya, jikinki fari, tufar ki fara, zuciyarki fara wane balbela.....’’
Murmushi ta saki ta na mai mamakin yanda karamar yarinya ta iya zaro magana har haka, ko da yake zama da mad’aukin kanwa shi ke kawo farin kai. Shi kuwa Yerima ganin Bintu tuni ya saki hannun Inna Salti ya na mai fad’in ‘’Inna Salti Bintu ce!’’ Har da tsallansa sai gashi jikin Bintu ya na mai rungumota. Ita ma Bintu dariya ta ke saboda farin cikin ganin Yerima Nadir. Inna Salti kuwa kallansu ta ke, ta na mai mamakin wannan soyayya da ke tsakanin Bintu da autan nata, dan kuwa duk cikin bayi babu wacce ya ke sakarwa fuska, amma idan ka ganshi da Bintu ko ciki d’aya su ka fito sai haka. Cikin fara’a Inna Salti ta ce ‘’Brkan ki dai Bintu, an dawo lahiya?”
‘’Lahiya lumi ranki shi dad’e’’ Cewar Bintu.
‘’Toh ja66ama.’’
Yerima Nadir ya dubi Inna Sallati ya ce ‘’Inna Salti zan yi wasa da Bintu’’
Inna Salti na mai murmushi ta ja hannun Yerima Nadir ’’Tunda ka ga ta yi sammako haka, ko shakka babu aiki ke gare ta, ko Bintu?’’

Jin haka Bintu ta san me Inna Salti ta ke nufi, kana ta ce ‘’Dama Gimbiya Binta ce ta yi kira na."
‘’Ka ji ko Nadir? Didi ta yi kiranta’’ Cewar Inna Salti. Ba dai haka ya so ba, amma be fasa tambayar ko anjima Bintu za ta yi wasa da shi ba, in da ta amsa masa da eh, da haka su ka yi sallama, sai da ta tabbatar sun wuce sannan ta tashi daga sunkuyen da ta yi, kai tsaye 6angaran su Gimbiya ta nufa ta na mai fad’uwar gaba.

K’atan falo ne mai d’auke da ado irin na gidan sarauta, haka kuma ya na d'auke da d’akuna biyu, kowanne da b’and’aki ciki, wanda na fari shi ne na Gimbiya K’amariyya, sai kuma na Gimbiya Binta daga can 6angaran.

Bayi ne guda hud’u ke ta kai kawo. Kai tsaye d’akin Gimbiya Binta ta nufa, ganin babu kowa bakin k’ofar d'akin ya sa Bintu kwankwasawa a hankali. Sai da ta kai wajan minti goma tsaye bakin k’ofa sannan ta ji muryar Gimbiya Binta ta na fad’in ‘’Gide wata maratarbiyar na samu a nan?’

Cikin rawar murya Bintu ta ce ‘’Ran gimbiya ya dad'e Bintu ce....’’ Shiru sai bayan wasu d’an dakik’ai ta sake furta ‘’D’iyar bayi ki ke kowa? Kya iya shigowa’’

A hankali ta murd’a hannun k’ofar, tuni wani ni’imantaccen kamshi ya daki hancin Bintu, sa k’afarta, ta ji ya lume cikin lallausar kafet(carpet), ga wani rab'a mai ratsa jiki da ya kama d'akin. Babu shakka d’akin Gimbiya Binta yana da fasalin d’akin d’iyar turawa. Komai na d’akin fari ne fat.
Lullu6e cikin bargo, idanu lumshe ta ce ‘’sai yanzu ki ga damar zuwa?’’ kofar ta mayar ta rufe sannan ta zube k’asa ta na fad’in ‘’Tuba na ke Gimbiya, barka da asuba.’’

Ba tare da ta bud’e idanunta ba ta yi nuni da d’an yatsa zuwa akwatinan da aka jibge gefe guda, sannan ta ja bargo ta rufe fuskar ta. Ko da ba ta yi magana ba, Bintu ta gane umarnin da aka ba ta. Dan haka tashi ta yi ta na mai bin akwatinan da kallo, su goma sha biyu ne cif. Himma ta d'aura, ta bi akwatinan d’aya bayan d'aya ta na fito da kayan ta na jera su cikin durowar Gimbiya.

Wasa wasa aikin nan sai gashi ya d'auke ta awa d’aya. Ta na kan akwati na k’arshe ne Gimbiya K'amariya ta shigo cikin shiga na alfarma. Kallo d’aya za ka mata ka tabbatar da farin cikin da ke tattare da ita. Gimbiya K'amariyya fara ce kamar Gimbiya Binta, doguwa ce siririya, dan kuwa sam ba ta garin jiki, ba ba'a ba, irin wannan matan ne da ake yiwa lak'ani da "Muciya da zani" Tsabar rashin jiki. Ta na da kyawun fuska daidai gwargwado dan har ta fi Gimbiya Binta.

Da sauri Bintu ta zube ta na mai fad’in ‘’barka da safiya Gimbiya’’
Da fara’ar ta ta masa da ‘’Barka dai, kya iya cigaba da aikinki’’
Bintu ta koma ga aikinta, inda Gimbiya K’amariyya ta zauna gefan gadon Gimbiya Binta. A hankali Gimbiya Binta ta yaye bargon daga fuskarta tana mai murmushi ga yar uwarta, ashe duk lokacin nan idanun ta biyu.

‘’A kwana a hantse sai d’iyar sarakai.’’ Cewar Gimbiya K’amariyya tana mai dafa kafad’ar Gimbiya Binta. Tashi ta yi zaune kana ta ce ‘’Gidai ban fa gane wanga farin ciki na ki ba, hallo ana fama da fari gidai ki na fama da farin ciki? me an surrin?(kin gan ki ban gane wannan farin ciki da ki ke ciki ba, muna fama da fari ke ki na ta farin ciki? Menene sirrin?’)’

Kwanciya Gimbiya K’amariyya ta yi gami da runtse idanu, sannan ta furta ‘’Barde ne’’
Cikin nuna rashin fahimta Gimbiya Binta ta maimata ‘’Barde ne?’’
Idanunta ta bud’e ta na mai duban Gimbiya Binta ta ce ‘’Soyayya na ke da Yerima Barde na Fabarusa!’’

Wato ba Gimbiya Binta ba, hatta Bintu da ke can gefe sai da ta tsaya cak ta na fidda idanu jin batun na Gimbiya K’amariyya cikin ran ta tana mai maimaita ‘’Yerima Barde mai kyawun duniya? Kai ba k’aramin baiwa Allah yayiwa Gimbiya K'amariyya ba’’
Cikin k’aguwa Gimbiya Binta ta ce "Didi ina ku ka had’u? Takawa(sarki) ya sani? Da gaske kyawunshi ya wuce na kowa a duniya?’’

‘’Wanga tambayoyi haka kauna(kanwa) ta? Kimin d’aya bayan d’aya’’
Kana Gimbiya Binta ta ce ‘’Toh, ina kuka had’u?’’
‘’A k’asa mai tsarki mu ka had’u, kin san mun je ki na makaranta’’
‘’Ya san ke wacece kuwa?’’

Gimbiya K’amariyya na mai d’aga mata hannu ta ce ‘’Tsaya dai ki ji komai, bayan had’uwar mu, jinin mu ya had’u, hallo mu ka kulla soyayya mai k’arfi, kullum cikin waya mu ke ta sabuwar wayar tafi da gidanka da ya shigo k’asar ga, mun yi alk’awarin amre(aure) da kuma kawo k’arshen gaba da ke tsakanin masarautar nan ta mu guda biyu, hallo hakan ne ma ya sa Allah ya had’a mu’’

Gaba d’aya Bintu ta manta da aikin da aka saka ta, ta saki baki da hanci ta na jin lamarin ubangiji, ‘’Ashe dai da rabon za ta ga Yerima Barde a rayuwarta’’ Farin cikin da ya mamaye ranta kenan. Kamar daga sama ta ji an daka mata tsawa
‘’Yallah can (dalla can) makira fita ki ba mu wuri! Ki ga yanda ta saki baki da hanci ta na jin mutane, wato ki sami wanda za ki d’auka ki watsa rariya(waje) ko?’’
A firgice Bintu ta dawo cikin hayyacin ta ta na mai raba idanu kamar 6era cikin tarko yayin da ta zube k’asa.

Gimbiya Binta bata gushe ba ta k’ara da ‘’Idan na ji wanga magana ta hita rariya(idan na ji wannan maganar ta fita waje) sai dai uwar ki ta haifi wata! Aradu ma kuwa!’’

‘’Lalle ma kuwa, yo to ai na manta tana nanniya’’ Cewar K’amariyya ta na duban Bintu. Jikin Bintu na rawa ta ce ‘’Tuba na ke! Aradun Allah na tuba, in na kara kada rabbi ya gafirce ni!’’

‘’Hita yallah(fita dallah) jaka kawai!’’ Gimbiya Binta ta daka mata tsawa. Tuni Bintu ta tashi jiki na rawa ta fita.

Bayan fitarta Gimbiya Binta ta ce "Wai har wanga d’iyar bayin ni za ta yiwa alherin maye ramuwa da mugunta? Har ta isa had’a samrayi(saurayi) da ni?’’
Baki bud’e Gimbiya K'amariyya ta ce ‘’Kwarainiya mota a randa! Shi ko wanene wanga samrayi?’’
Gimbya Binta na mai murmushi ta ce ‘’Aisar Gaddafi Nur."

Cike da mamaki Gimbiya K'amariyya ta ce ‘’Kai haba dan Allah, Aisar dan shugaban k'asa gide?"

Gimbiya Binta ta gyad'a mata kai.
"Yo to in ban da abun ki ina tusa zata hure wuta? Ina d’iyar bayi ina dan mulki? Ai komai tsiyar 6arawo ya bar wuta a murhu’’ Cewar Gimbiya K'amariyya.


🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

©Khadija Sidi.....✍🏼

1⃣3⃣

Kai Gimbiya Binta ta girgiza, tana mai fad’in ‘’Ba ki san makircin wanga d’iya ba ne Didi, bari dai na baki labarin kad’an daga cikin halin ta.’’ Nan fa ta saka Bintu a faifai, k’arya da gaskiya haka ta had’a ta shedawa Gimbiya K’amariyya, ba don komai ba ko don ta samu mai taya ta saka baki a hana Bintu komawa makaranta.

Jiki na kyarma Bintu ta fito, Allah ya sa shigowar Inna kenan su ka had’u a rariya. Inna na ganin Bintu ta san akwai abin da ke damunta, tambayar duniyar nan Inna ta yi mata, amma ta k’i fad’a mata, sai k’arya ba ta jin dad’i ta yi mata. Ta na mai mata Allah ya sauwake ta ja ta gefe ta bata fatan dusan da ta taho mata da shi dan karin kumallo kafin ta yi na ta wajan, tabar Bintu ta na zabga loma.

              ***      ***      ***

Da yammaci, sati guda kenan da dawowa su Bintu.
Bintu kwance tare da Inna da Habibu zaune bisa tabarma a tsakar gida su na shan iska dan kuwa zafi ake na gaske ma kuwa. Inna da ya Habibu ke hirar halin da ake ciki na fari a yanki, su na muhawarar yanda za a sami mafita, in da Bintu ta yi kwance can gefe, gaba d’aya tunanin Aisar ne ya addabi rayuwar ta, dan ko yanzu ma tunanin na shi ta ke yayinda ta ke murza zobensa da ke sanye cikin yatsunta.

Baba ne ya shigo kamar an jefoshi, fad’i ya ke ‘’An dai wad’i(fad’i) ba nauyi!'’ Tashi su ka yi tsaye a tare, Inna na mai tambayar ‘’Malam lafiya kuwa?’’ 
Baba ya ce ‘’Yo to tunda aka fara fari ina mu ka ga lafiya? Yau fa kur’ia aka doka a fada, kuma sakamakon shi ne za mu nemi sulhu da kuma taimako daga wajan mak’iya abokan gaba, eh masarautar Fabarusa!’’

Babu wanda bai girgiza ba jin kalamin na Baba. Habibu ne ya ce "Gide a rasa in da za a k’ask’antar da kai sai wajan abokan gaba?’’ Baba na mai d’aga kafad’a ya ce "Ta dai faru ta k’are an yiwa mai damo d’aya sata, don kuwa magatakarda ya tura wasik’a zuwa Fabarusa, idan an amsa gobe da sassahe za a d’auki hanya  tare da Uban Gabasawa(Sarki) da kansa zuwa wajan abokan gaba nema sulhu’’

Ya na gama fad’in haka ya shige ciki Inna na mai bin bayansa. Shi kuwa Habibu silifa d’insa ya ja ya saka sannan ya fice, wato ya fita yad’a zancen kenan. Bintu kuwa komawa ta yi zaune abin ta, duk da dai itama ta yi tunanin neman taimako daga Fabarusa, jin za a je d’in da gaske sai ta tsinci kanta tana mai fad’uwar gaba.

********
Washegari da sassafe Mai Martaba da tawagarsa su ka d’auki hanyar Faburusa. Babban gida sam babu armashi kowa cikin fargaba ya ke. Gimbiya K’amariyya tafi kowa shiga tashin hankali, gashi tun jiya ta ke kiran wayar Yerima Barde amma wayar ba ta shiga. Gani ta ke kamar alakarsu ce ta zo k’arshe. Ita kuwa Gimbiya Binta damuwarta daban ne, tun dawowar su ta ke ta sak’e-sak’e akan abinda za ta ce da Takawa(sarki) ya canza mata baiwa, dan ita aradu ba za ta koma makaranta da Bintu ba.

Ranar Allah ya taimaki Bintu ta yi aiki da hidimarta cikin Babban gida ba tare da ta sami matsala daga wajan Gimbiya Binta ba. Da yammacin ranar ta raka Yerima Nadir Lambu, nan su ka ta tad’in su kamar ta sami babban mutum. Labarin makarantar su ya ce ta bashi, nan fa Bintu tai ta bashi, har da labarin Aisar. Bata san ta na kewan sa sosai ba sai da take maganar sa a zahiri ba a zuci ba, wata k’ila ma ya manta da wata Bintu, abun da take fad’awa kan ta kenan. Shi kuwa Yerima Nadir kallon ta kawai ya ke ba tare da ya fahimci in da ta dosa ba, ballantana ya gane halin da ta ke ciki.

******
Bayan magrib ta koma gida, shiru har lokacin sarki be dawo ba. Bayan sun ci abinci suna kwance a falo ita da Inna, sun ci sa’a akwai wutar lantakarki, fanka ke kad’awa ta na mai fitar da k’ara alamar ta fara gazawa.Akwatin radiyon Inna su ke sauraro in da ake labaran duniya.

Jin mai karanto labarai ya ce ‘’Jikin shugaban k’asa Gaddafi Nur ya tashi, za'a fitar da shi zuwa k’asar waje domin ba shi taimako’’ Ya sa Bintu tashi zaune da sauri ta na mai tambayar ‘’Inna daman shugaban K’asa be da lafiya?’’
‘’Eh Allah sarki ai be da lafiya, yo to da k’alau ya ke ai da tuni ya magance wanga fari da mu ke ciki, dan ba kya sauraran labarai ne shi ya sa ba ki ji ba’’ Inna ta amsa mata.

Bintu na mai dafe kai ta ce  "innalillahi wa innailaihirrajiun, Allah sarki Monsieur Aisar, suna cikin tashin hankali’’ 
Inna ta dubeta, ‘’Waye shi kuma Bintu?’’

Nan Bintu ta kwashe labarin Aisar ta fad’awa Innar ta. Fuskarta na nuna rashin jin dad’in labarin, Inna ta had’e fuska. ‘’Ai da walakin goro a miya, shi ya sa mana na ga kin dawo wata wuri wuri da ke, d’an shugaban k’asa Bintu?’’

Bintu na mai tura baki ta ce ‘’Yo to Inna minene ciki? Ba fa wani abu ba ne taimako gareshi kawai........’’

‘’Wani taimako? Chiim zanne la nya bangin! (rufa min baki ko na buge ki)’’ Inna ta katse ta, ta k’ara da ‘’Taimako ne har da siya miki turare ma su tsada haka Bintu? Binta sudan? Kafin kafin? Danduala? Turaren da sai Saraki kad’ai ke sawa? Kuma ki na dai ganin yanda Gimbiya ta yi mi ki saboda shi? ngoy awo gulgin d3! (ai ga abinda nake fada), yanzu ba za ta bari ko koma maranta (makaranta) da ke ba!"

Komawa Bintu ta yi ta kwanta, ta na mai lumshe idanu. Kana ta ce ‘’Allah ya ba shi lafiya’’
"Wa fa?’’ Inna ta tambaya. Bintu na mai bud’e idanunta ta ce ‘’Mahaifin Monsieur’’

Tsaki Inna ta ja, kafin ta amsa da ‘’Yo to amin, amma kanki ya kamata ki yiwa addu’a fero (yarinya) a halin da ki ke ciki, ki ma cire wannan mutumin daga ranki, can ga su gada zomo ya ji kid’an farau ta’’

‘’Inna Allah na sa a raina." Cewar Bintu. Kamar daga sama su ka jiyo Habibu daga tsakar gida ya ce 
"Kin gama komai kauna(kanwa) ta?''

Ashe duk maganar da su ke ya na can zaune tsakar gida ya na jiyo su ba su sani ba. Murmushi Bintu ta saka, ita kuwa Inna cewa ta yi ‘’Ala sakaa (Allah ya kare)"

Washegari da asubar fari Bintu na tashi daga barci Baba ne ya fad’o ranta, don kuwa har su ka yi bacci be dawo ba. A tsakar gida ta tadda Inna ta na alwala, ka na ta ce ‘’Inna barka da asuba’’

‘’Barka dai Bintu, kin tashi k’alau?’’ Inna ta amsa mata.

"Lafiya lumi, shin Baba kuwa an dawo?’’ Bintu ta sake tambayarta, inda Inna ta amsa mata da sun dawo lafiya lumi kan ta shige d’akin ta bayan ta gama alwala, ita ma Bintun buta ta d’auka ta shige band’aki.

Babban gida kuwa a yau rashin armashin sa ya fi na kullum,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login