Showing 6001 words to 9000 words out of 44561 words

Chapter 3 - Bintu Diyar Bayi Ce 1 Complete Hausa Novel

06 Jan 2025

148

su ba,sai k’asa ta sauka.
Bayan sun shiga aji sun fito hutun cin abunci da azahar, Gimbiya ta hana ta zama cikin d’akin cin abunci,wai ta na sa ta tashin zuciya. Tsaye ta ke bakin d’akin cin abunci, sai had’iyar yawu ta ke dan yunwar yau tafi ta kullum. Rana ko ta take sosai dan kuwa su na sa ran samuwar ruwan sama kwana kusa. Gashi in da ta ke tsaye sam babu inuwa, bini bini sai ta sa tafin hannun ta ta goge zufar da ke faman ketowa bisa kuncin goshin ta. Da ta ga abun ba na k’arau ba ne,ta sanya hannun ta cikin aljihu ta d’auko k'ulin ta da ta d’an k’unso a yar leda. Wata bishiya ta hango,kai tsaye ta nufe shi ta na k’ok’arin kwance ledar k'ulin. Ta gaban d’akin cin abuncin malamai wuce.

Ta taga ya hango ta,lokacin guda ya bar cin abuncin da ya ke hannun sa ruk'e da cokali ya bi ta da kallo. Tin da ya ke be tab’a ganin wacce ta iya tafiya tafiya irin na Bintu ba. Tafiya ce a nutse ko wacce k’afa in aka aje sai an tsagaita kafin ta biyu ta biyo ta. Gashi dai babu alamar tak’ama a tattare da tafiyar amma sai ta zama tak’amar ce ma gaba d’aya. Kuma tsayin ta ya sa haka. Be dene kallan ta ba har ta isa ga bishiyar ta zauna. Ganin ta bud’e wata yar leda ta na fitar da wani abu ta na afawa a bakin ta sannan ya tuna fa yanzu lokacin cin abuncin d’alibai ne,me ta ke yi a waje,ya aje cikoli ya tashi kai tsaye ya fito ya nufo in ta ke zaune.

Bintu ta ba ta hango shi ba,ba ta kuma ga tahowar shi ba,ta ciko hannun ta da kuli kenan ta afa a bakin ta , sai kawai ganin shi ta yi tsaye kan ta,bakin ta cike da k'uli ta d'ago kai su ka had’a ido nan da nan gaban ta ya fad’i,cikin zuciyar ta kuwa ihu ta kurma
‘’wayyo ni Bintu aradu wagga Malami ya takura ni!’’

🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪



©Khadija Sidi.....✍🏼

0⃣4⃣


Cikin sauri ta tashi tsaye ta gaishe shi da harshen (French) faransanci wanda da dama da shi su ka fi amfani a makaranta. Gaba d’aya ta manta da wani kunyar sa da ta ke ji yanzun da ta gan shi tsaye gaban ta dan kwarjinin da ya mata. Kan ta sunkuye tana wasa da ledar k’wilin ta ya amsa mata a takaice fuskar babu walwala ya ce ‘’me ki ke yi waje lokacin cin abunci?’’

‘’Gimbiya Binta na ke jira ta gama cin na ta sai ni ma na ci nawa’’ ta amsa zuciyar ta d’aya ba tare da ta d’aga kai ta kalle shi ba.

Cike da mamakin amsar ta ta ya ke duban ta, ita sam bata lura da kallan na ta da ya ke ba. Kana ya ce "wacece Gimbiya Binta?’’ jin tambayar na sa Bintu ta bud’e baki,cike da mamaki ta ce "laa ba ka san Gimbiya Binta ba? Yar sarkin Sa'ayrasa fa, wata fara tas kamar d’iyar larabawa, ta na da kwarjini matuk’a’’.

Badaban ran sa a 6ace ya ke ba, yanda ta ke kod’a Gimbiyar ta ta sai da ta kusa ba shi dariya. Amma sai dad’a tsuke fuska ya yi kafin ya k’ara da ‘’ban san wakike magana akai ba, amma abunda na ke so na sani shi ne shin dokar makarantar ce sai wata Gimbiya ta gama cin abunci kafin sauran d’aliban su ci ko kuwa?’’

Tuni Bintu ta fara shan jinin jikin ta dan kuwa tabbas idan hukumar makarantar ta ji wannan maganar matsala zai zame mata. Kana ta ce "iye! Na’am? Dama wai,dama ai..........’’.
"dama me?” ya katse ta ya na mai duban ta. Nan fa Bintu ta shiga cikwikwiya ledar hannun ta, ta rasa amsar da za ta ba shi.
"dokar makarantar ce sai wata Gimbiya ta gama cin abunci kafin sauran d’aliban su ci ko kuwa?’’ ya dad’a maimai ta mata tambayar cikin k’aguwa. Ganin ba ta da niyar amsawa rai 6ace ya furta "menene dangantakar ki da wannan da ki ke kira gimbiya ?ya sunan ki?’’

Cike da tsoro Bintu ta amsa ma sa "sunana Bintu, Bintu Bala Mahuta, ni d’iyar bayi ce, ni ce baiwar da ke kula da Gimbiya Binta ta masarautar Sa’ayrasa.....’’
‘’wannan ne ya bata damar hana ki abunci? Haka ake gudanar da lamarin wannan makarantar? Saboda zalinci? Toh daga yau ya k’are ni Aisar ba na san zalinci kuma ba zan juri ganin zalinci ba’’ ya na gama magana ya juya a fusace ya fara tafiya, ganin haka Bintu da tun da ya fara magana ta gama firgita, ba ta san sanda ta saki ledar k'wilin ta ba, ta bi shi da sauri tare da shan gaban sa, sai ga ta ta zube gwiwowi biyu a kasa. Da sauri ya ja ya tsaya ya na mai duban ta cike da mamaki ganin duk zafin ranar be hana ta saka tafukan hannayen ta biyu k’asa ba ta mai duk’ar da kai kamar wacce ta ke shirin shigewa k’ark’ashin k’asa.

Hankali tashe ta shiga jero masa magiya ta na mai fad’in "tuba na ke, ka gafarce ni, na tuba, ka yiwa Allah da manzon sa kar ka had’a ni da Gimbiya, aradu idan ta ji wannan maganar na kad’e har ganye na,ka min rai, na tuba....’’ ta k’arasa maganar na ta cikin kuka. Aisar kuwa kasa magana yayi ya na mai duban ta cike da tausayawa kana daga bisani ya ce ‘’tashi....."

maimakon ta tashi sai ta dad’a kask’antar da kai ta yi kasa ta na kuka, jin kukan na ta ya ke har ran sa. Idanun sa runtse ya ce ‘’ya salam wannan wata irin yarinya ce mai shegen taurin kai! ki-ta-shi-na-ce’’ a hankali yayi maganar kamar mai koyan magana. Sai a sannan ta tashi, amma har lokacin hawayen ta ke.

Kallan ta yayi na wasu dan dak’ikai, kafin ya mata nuni da inuwar da ya tadda ta zaune ya ce koma can ki zauna ina zuwa. Baki ta bud’e da niyar yi masa musu, amma ko da su ka had’a ido sai ta tsinci kan ta ta na mai fad’in ‘’toh’’ ta yi sauri ta koma k’ark’ashin bishiyar in da ta jingina jikin ta, ta na mai mayar da ajiyar zuciya ganin Aisar shi ma ya juya ya tafi.

Ta na mai addu’ar Allah ya sa ya hakura kar ya dawo har ta samu ta shiga d’akin cin abunci. Sai a sannan ta lura da ledar k’ulin ta a k’asa ta yi sauri ta d’auko ta ka6e dattin da ya mak'ale jikin ledar kafin ta tura cikin aljihun ta dan kuwa shi ma ya fita ran ta. Jim kad’an Aisar ya dawo d’auke da wata yar bakar leda, ya mik’a mata ledar tare da fad’in "gashi maza ki je ki sami waje ki ci’’ ledar ta bi da kallo, wani irin kamshi ke ziyarta hancin ta daga cikin ledar, tuni ta mayar da mugun yawu, ta na mai girgiza kai ta ce "ah ah na gode ai ba na jin yunwa dama’’ "ba kya jin yunwa?’’ ya maimaita cikin sigar tambaya. Kai ta gyad’a masa alamar eh. Amma mai za su ji? ‘’kulululu’’ sautin da ya fito daga cikin ta kenan wanda ya ke gasgata zargin Aisar na Batun Bintu ba ta jin yunwa yasasshen zance ne.

Cike da jin kunya ta sunkuyar da kai k’asa, duk 6acin ran sa sai da ya tsinci kan sa ya na mai murmusawa. ‘’kar6a ki ci maza kafin a koma aji’’ sai da ta d’an yi jim, kafin daga bisani ta sa hannu biyu ta karb’a ta na mai godiya, fad’i ta ke ‘’Godiya na ke, madallah, Allah ya saka ma da alkairi’’ ba ta jira jin amsar shi ba tayi gaba, hannu na rawa ta ke k’ok’arin bud’e ledar dan ganin abun da ya ke, ganin lafiyayya abuncin da ke cikin ledar tuni ta fara k’ok’arin fara kaiwa baki dan ta ma manta da Malam Aysar da ya bi ta da kallo cike da tausayawa har ta k’ure masa. Kai ya jinjina ya na mai shan alwashin maganin wannan zalincin da Gimbiya ta ke yiwa Bintu na hana ta cin abunci cikin d’alibai yan uwan ta. Shin dama har yanzu ana irin wannan zalinci? wannnan wani irin sakaci ne daga hukumar makarantar, da ga alama dai ba banza ta kawo shi makarantar ba, babu mamaki watan rufe makarantar ce ta tashi muddin ana irin wannan zalincin da sanin hukumar makarantar. Da wannan tunanin ya nufi ofishin Malam Hamisu. Yayi rashin sa’a ba ya nan dan haka dole ya hakura ya koma ofishin zaman malamai da k’udirin cikin ran sa.

Yanda Bintu ke cin abunci kamar wacce ta shekara ba ta ci ba ya sa ta saurin gamawa kafin su koma aji. Suna komawa kuwa lokacin koyarwar Aisar ne. Da shigowar sa ba tare da 6ata lokaci ba ya fara abunda ya kawo shi, wato koyarwa. Darasin na sa yau akan "Gaba" ne. Aisar ya fara da tambayar misalan yankuna ko masarauta masu tarihin gaba tsakanin su, ba jamhuriyar Nijar kad’ai ba har mok’otan su. D'aya daga cikin d’aliban ce ta d’aga hannu, in da Aysar ya bata damar amsa tambayar, ta ce "kamar gabar da ke tsakanin masarautar Sa’ayrasa da masarautar Fabarusa’’ Aisar na mai jinjina kai ya ce "haka ne ku tafa mata’’ aji aka d’auki tafi "raf raf raf"

Bayan haka ya k’ara tambayar "su waye ‘yan masarautar Faburasa cikin ajin nan?’’ wajan mutum uku ne su ka d’aga hannu, bayan wani d'an sakanni ya ce su sauke, masarautar Sa’ayrasa ma su d’aga hannu. D’alibai shida ne su ka d’aga hannu, ciki har da Gimbiya. Bintu kuwa ta na can ta na tunanin duniya, gaba d’aya hankalin ta ba ya ajin. Hannun su d'age be ba su izinin saukewa ba dan shi hankalin sa kan Bintu ya ke, suma kuma ‘yan ajin sun lura da hakan dan su ma d’in Bintu da ta doka uban tagumi su ke kallo.

Kamar daga sama ta ji ya ce ‘’Bintu hankalin ki ba ya aji na!’’ ta yi firgit ta dawo cikin hankalin ta ta na mai cire hannun ta daga tagumin da ta yi. Ganin idanun kowa kan ta, ga hannun wasu daga cikin yan ajin har da Gimbiya d’age ya sa Bintu kai duban ta ga Aisar, in da shi kuma ya maimaita mata umarnin da ya ba su. Da saurin ta ta d’aga na ta hannun sama sannan ya ce su aje hannun na su. Wata har da fad’in "wash hanuna" a hankali yanda Aisar ba zai jiyo ta ba.

Bintu ba ta tsorata ba sai da ta ga Gimbiya ta juyo ta watsa mata harara. Wani mugun yawu ta had’iya tuni hantar cikin ta ta kad’a. Malam Aisar kuwa be gushe ba ya cigaba da "shin wa zai fad’a min lokacin da gabar ta samo asali?’’ d’aya daga cikin su ta amsa da "gabar ta samo asali ne tun kaka da kakanni amma anfi dangan ta shi da lokacin mulkin sarki Abdulrahaman III na masarautar Faburusa’’ Malam Aisar ya ce a tafa mata sannan ya sake tambayar hanyoyin da ya dace a bi domin kawo karshen gaba tsakanin k’asa da k’asa ko masarauta da masarauta. Dalibai da yawa su ka d’aga hannu, amma ga mamakin kowa sai ji su ka yi ya ambaci sunan "Bintu’’

‘’Wayyo shi dai sai ya fad’awa kowa ya san sunana ko menene haka?’’ ihun da Bintu ta kurma cikin ran ta kenan. Gaba d’aya ajin idanu su ka zubo mata yayinda ta tashi a hankali murya kamar ba nata ta ba, ta furta abun da ya fara zuwa bakin ta "auratayya tsakanin masarautar’’ nan fa aji aka kwashe da dariya, Zahira ta ce "auratayya tsakanin bayi, d’iyar bayi ta auri dan bayi.....’’ aka dad’a sa dariya.

Kunya ta rufe Bintu kamar ta shige k’ark’ashin kujera ta 6uya. "shiru!’’ Aisar ya daka musu tsawa. Aji yayi shiru kamar wanda ruwa ya shanye, ran malam ya 6aci. ‘’wata mara tarbiya ce ta yi wannan maganar?’’ ya tambaya a fusace. Aka rasa mai bashi amsa, har sai da ya sake maimaitawa sannan Zahira ta tashi tsaye gwiwa a sanyaye. Bintu ya duba ya umarce ta da ta zauna kafin ya koma ga Zahira. Ya ce da yan aji kowa ya dube ta, shin ita yar wata yanki ce. Ta na zumb’ure zumb’ure ta amsa da ‘’Niamey’’ kai ya girgiza kan ya ce ‘’Niamey na alawadar da masu hali da kalimi irin na ki, kalamai ne irin na marasa tarbiya wanda su ka tashi a watse, lalle idan har Jamhuriyar Nijar na da yan k’asa irin gaba tsakanin yankuna ba zai tab’a yankewa ba, fitar min daga aji kuma kar ki sake shigowa in har ni ne cikin ajin’’ Zahira ta wuce fuuuu za ta fita ya ce ‘’dube ta k’azama kawai’’ kunya ya rufe ta ta fice da sauri.

Jikin kowa yayi sanyi, tin ba ma Bintu ba. Aisar kuwa be sake cikakken minti goma ba ya fice da ga ajin,dan kuwa tabbas d’aliban makarantar na fama da rashin tarbiya na gaske. Surutai kuwa ta sha wajan yan aji, daga mai fad’in "kun ji yanda ya ke kiran sunan ta kuwa?’’ sai mai fad’in ‘’ta yaya ya san sunan ta bayan be ta6a tambayar sunayen mu ba?’’ ita kuwa Bintu kai ta kifa bisa teburi dan Allah kad’ai ya san masifun da ke gudana cikin zuciyar Gimbiya, ta san yau kam sai yanda aka yi da ita wai d'an daudu a kabari.

🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪



©Khadija Sidi.....✍🏼


0⃣5⃣



Bayan an tashi daga makaranta, ko kallan ta Gimbiya Binta ba ta yi ba ta ta wuce gaba ita da Ruqayya, Bintu na rawar jiki rik’e da jakar Gimbiya ta bi bayan su. Ba su zame koina ba sai d’akin su in da su ka tadda Zahira na jiran su dan gasawa Bintu gurasa danya a hannu.

Zagaye Bintu su ka yi tsakiyar d’aki, sai ta fad’a musu yanda aka yi Aisar ya san ta yasan sunanta da har ya ci mutuncin Zahira saboda ita. Bintu na raba idanu ta ce ‘’Dan Allah Gimbiya ki min afuwa, aradu shi da kan sa ya tambayi sunana........’’

Ji ka kake tas! Gimbiya ta kwashe ta da marin da sai da Bintu ta ga wuta a idonta, a gigice ta sa hannu bisa kuncin ta na mai fashewa da kuka. Gimbiya ba ta gushe ba ta ce " Yar iska! A shekarun ki har kin iya karuwanci?!!!’’ Ta sa k'afa ta shure Bintu. "Yo dama ana raba bayi da karuwanci ne Gimbiya?’’ Rukayya ce ta ara ta yafa. Zahira ta k’ara da, "Wallahi tunda ki ka sa mutum kamar Aisar ya ci mutuncina sai kin yabawa aya zak’inta."

Ita dai Bintu ta kasa magana, kanta durk’ushe, sautin kuka kad’ai ke iya fita daga bakinta. Gimbiya ta ce ko dai ta fad’a mu su yanda aka yi ya san ta har ya tambayi sunan ta ko ta kira waya fada a zo a mayar da ita Sa’ayrasa. Jin haka haka nan da nan Bintu ta shaida musu komai. Duka da mari babu wanda ba ta sha ba. A fad’ar Gimbiya don tasan tana da k’udirin auren Aisar ya sa ta ke masa shisshigi dan ta 6ata ta wajan shi, toh wallahi ta yi kad’an, duk randa ta yarda wani abu ya k’ara shiga tsakanin su ta tabbatar ranar zaman ta a wannan makarantar ya k’are. "Godiya nake Gimbiya’’ a
Abinda ke fita daga bakin Bintu kenan har su ka k’araci masifar su, su ka tafi d’akin Zahira.

Bintu na zaune inda suka bar ta, ta had’e kai da gwiwa in ban da ajiyar zuciya babu abun da ta ke, sai ga Iya Dije ta shigo da sallamar ta. Ganinta Bintu ta yi saurin gyara zama ta na mai k’ok’arin goge hawayen da ke fuskar ta gudan kar Iye Dije ta gani. Cike da mamaki Iye Dije ta ce "Bintu lafiya? Me ya sa ki kuka haka? Ya na ga idonki d’aya ya kumbura?’’ "Ba na jin dad’i ne Iya Dije, ciwon kai da ido na ke’’ Bintu ta yiwa Iya Dije k’arya gudun abun da zai je ya dawo. Cikin nuna tausayawa Iya Dije ta ce " Ayya Allah ya sauwake, na ce dai kin je kilinik (clinique, karamin asibitin makarantar) an duba ki ko?’’ Kai Bintu ta girgiza alamar ah ah, sannan ta k’ara da ‘’Ba sai na je ba, ina da magani, idan na sha shikenan."

Kallan ta Iya Dije ta ke kamar mai nazarin wani abu, kafin daga bisani ta ce ‘’Toh Allah ya sauke.’’ Ta ja wata yar kujera ta zauna sai a sannan Bintu ta lura da ledar hannunta, a gaban Bintu ta aje ledar kan ta tambaya "Shin al’adar ta ki ta d’auke ne?’’ Cikin nuna jin kunya Bintu ta girgiza kai alamar ah ah. Iya Dije ta ce "Ai bakomai, dama daga kwana d’aya har zuwa kwanaki goma sha biyar yakan iya kai wa. Dama batun turaren ne, Malam Aisar ya ba ni kud’i, sanin ba a bari dalibai su fita daga makaranta yasa na yi karambani na siyo miki’’ Ta sa hannu cikin ledar sai gashi ta fito da kwalaban turare har guda uku, ta aje gaban Bintu ta na fad’in ‘’Kinga wannan Danduwala ne, ga kuma Kafin-kafin, ga Binta Sudan duka na ki ne." Ta k’arasa maganar tana mai washe hak'ora don tasan ba k'aramin gwanin ta ta yiwa Bintu ba, duk da dai rabin kud’in da Aisar ya bata a aljihun ta ya k'are.

Bud’ar bakin Bintu sai cewa ta yi "Iye Dije na gode amma dan Allah ki mayar masa, aradu ba zan iya karb'a ba, ba na so’’ ‘’La'ilaha illallahu!" Fad’in Iye Dije ta na mai tafa hannu "Ku ga yarinya za ta watsan k'asa a ido! Ba kya so a na wani dalili? Iyye?!!!’’ Ta yi tambayar ta na mai fidda idanu ganin Bintu na shirin kwance mata zani a kasuwa, don kuwa karya da gaskiya ta had’a ta fad’awa Aisar kan buk’atun Bintu, haka ya bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login