Showing 45001 words to 48000 words out of 84091 words
Fuska ta sake tsukewa matuƙa, taƙi kuma cewa komai sai harar gefen ido data ballama Shareff daya tsareta da idanu shima alamar bukatar son ji.
“Ina saurarenki ya akai hakan ta faru?”.
Nan ma ƙin cewa komai tai, sai dai ta ɗago yanzu sosai ta kalli Yaya Shareff har suka haɗa ido. Saurin kauda nata tayi da zamewa ta kwanta tana son maida hawayen dake ƙoƙarin zubo mata. Maheer da bai hakura da son jiba yay ƙoƙarin zagayawa inda ta juya fuska Shareff ya dakatar da shi. “Malam ya isa”.
Kamar Maheer zaiyi magana sai kuma ya fasa saboda shigowar Nurse. Sannu tai musu tare da mikama Shareff dake kusa da ƙofa takardar hanunta. “Yallaɓai zaku iya tafiya da ita gida yanzu, ga wannan magungunan sai a saya mata tai amfani da su, ALLAH ya kiyaye gaba”.
Amsar takardar yay da gyaɗa mata kansa kawai. Sai da Nurse ɗin ta fita sannan ya dubi Maheer dake tambayarsa ko can gida zasu wuce kawai?. Bai ce masa komai ba ya fita a ɗakin, shi kuma Maheer ya koma inda ta juyar da fuskarta.
Kallonsa tai da faɗin, “Yaya nidai mu tafi gida kawai, bazan koma gidansa ba, kuma wlhy ta kwana da sanin yanda ta zubarmin da jini sai na rama koba yanzu ba”.
Ɗan zaro ido Maheer yayi da zama a kujerar dake gaban gadon. Kafin ya samu damar cewa wani abu Shareff da wasu Nurse suka shigo ɗakin. Kallonta yake cikin ido saboda yaji abinda take faɗa. Maheer ma kallonta yake sai dai ya kasa cewa komai dan bai fahimceta ba. Da taimakon Nurses ɗin aka kawota wajen mota, tanata mitar ita dai a kaita wajen Mamie. Bai kulata ba, sai Maheer dake lallashinta. Sun tsaya wani pharmacy ya bama Maheer takardar da atm ɗinsa tare da faɗa masa pin......
★★
Tun bayan fitarsu take auna son kiran Mamah (Gwaggo Halima) sai dai gargaɗinsa akan kai ƙararsa ga iyayenta ko nashi na taka mata birki. Sosai ta kasa zaune ta kasa tsaye balle tsaida shawara. Har cikin ranta tsoro ne da shakku ke cizon zuciyarta dake ayyana mata abubuwa masu dama. Ta rasa miyasa yarinyar nan ke yawan shiga mata hanci ne? Kodai akwai alaƙar da suka jima suna jin tsoron ta kasance ne ta ƙullu tsakanin mijin nata da baƙar yarinyar nan? “Kai ina, wlhy zuciyata bazata iya ɗauka ba”. Ta faɗa a zahiri da ƙoƙarin kauda mummunan zaton dake kawoma zuciyarta farmaki. Ba yau ta fara irin wannan tunanin ba, shiyyasa a koda yaushe take ƙara jin tsanar yarinyar bayan wadda mahaifiyarsu ta cusa musu akan iyayenta da ita kanta, bata son ganin wata alaƙa tsakanin Mijinta da Anam, amma abin tsoron a kullum kusanci take gani a tsakaninsun, kusanci irin wanda tafi shiga tashin hankali da shi a yanzu fiye dana baya.. Tabbas lokaci yayi da zata ɗauki mataki, idan tace mataki tana nufin koma wane irine in har zai nisanta tsakanin mijin nata da wadda takema kallon maƙiyya tun a zamanin tsatson kakanni da suka haɗa kishi.....
Harta danna kiran Mahmah ta yanke, dan tasan rashin haƙuri da haɗiye abu irin nata, maida akalar kiran nata tayi ga Mommy, bugu ɗaya kuwa ta daga. Ta gaidata cikin ladabi da kwantar da murya. Itama Mommy sai ta amsa da kulawa sosai. Shiru ya biyo baya, Fadwa na tunanin ta inda zata fara...
Mommy ta katse shirun da faɗin, “Fadwa babu dai wata matsala ko?”. Nan ma shiru kamar bazatace komai ba, sai kuma taja ajiyar zuciya da fara kukan da bata san yana makale a makoshinta ba. “Lafiya Mommy”. “A'a Fadwa, ya zakice lafiya kuma kina kuka. Kinga kar kiji komai faɗamin matsalarki kinji, Shareff ne ko?”.
“Bashi bane Mommy yarinyar nan ce Anam”.
“Anam!!”.
“Eh Mommy”.
Shiru Mommy tayi zuciyarta na tafasa, taja nannauyar ajiyar zuciya tana mikewa. Falon ta fara zagayawa har lokacin wayar na a kunnenta sai dai ta kasa cigaba da cewa komai kamar yanda itama Fadwa tai shiru. Kusan mintuna biyu sannan Fadwa ta katse shirun da faɗin, “Mommy wlhy ni bazan iyaba. Zuciyata bazata iya ɗaukar cigaba da ganin wannan yarinyar mai ƙirar karuwai na shigomin gida ba. Inba hakaba zan iya kasheta na halaka banza.....”
Rai ɓace Mommy ta katseta da faɗin, “Shi Shareff ɗinne ya kawota gidan?”.
“A'a tare da Yaya Maheer sukazo. Yanzu haka daga ta ɗanji ciwon da tana akan sani tayisa dukansu sun kwasheta zuwa asibiti a ruɗe. Kusan awa huɗu kenan har yanzu basu dawo ba. Wlhy Mommy na tsaneta, dan ALLAH nidai ta daina zuwa min gida”.
Katse wayar Mommy tayi, ranta a matuƙar jagule ta fara laluben number Maheer, harta katse ba'a ɗauka ba, ta sake kira nan ma ba'a ɗagaba. Ranta ya sake ɓaci ta maida akalar kiran ga Shareff. Tana gab da tsinkewa ya ɗaga, cikin girmamawa a gareta da tausasa harshe na ɗa nagari ga iyaye yay mata sallama da faɗin, “Mommy barka da yamma”.
“Kuna ina?”
Ta jeho masa tambaya batare data amsa gaisuwar tasa ba. Ɗan jimm yay alamar tunani, sai kuma ya kalli Anam dake kwance cikin kujera idanunta a lumshe. Kamar mai raɗa ko tsoron tada jariri a barci yace, “Pharmacy”.
“Kai da wa?”.
Kallon Anam ɗin ya sakeyi suka haɗa idanu, a marairaice ta janye tana kauda kanta gefe. Numfashi ya ƙara saukewa, cikin sake tausasa harshe yace, “Ni da Maheer ne....”
“Dawa kuma?”.
Ta tare numfashinsa tun kan ya ƙarasa. Bai iya karya ba, shi mutumne kai tsaye koda ace gaskiyarsa zata ja masa laifi ko matsala zai faɗa ya amsa hukuncin daga baya. Dan haka yace, “Mommy da Juwairiyya ne da taji ciwo”.
A fusace tace, “Waye Juwairiyya kuma?”.
A hankali yace, “Anam”.
“Kusameni kai da Maheer”.
Ta faɗa tana yanke wayar. Tsirawa wayar ido yayi kamar mai son ganin Mommyn a ciki, sai kuma ya ɗan girgiza kansa ya ƙara kallonta ya ɗauke kansa yanama motar key saboda hango Maheer na fitowa. Baicema Maheer ɗin komaiba ya canja hanyar zuwa gidansa zuwa amsa kiran Mommy. Shima Maheer ɗin baiyi magana ba a tunaninsa mitar Anam ce ta sashi canja shawara.
Gidan su Anam ɗin ya fara tsayawa, sai dai bai shiga da motar ba yay parking a ƙofar gate. Kusan atare suka fito shi da Maheer. Maheer ɗinne ya buɗe mata murfin yana faɗin, “Kefa yau kin zama gimbiya sai dai a ɗaukeki ko?”.
Kanta ta jinjina masa tana murmushi duk da hango mugun kallon da Shareff ya watso mata. Tana ƙoƙarin miƙa masa hannu duk da tsokanarsa dama tai niyyar yi su Abie suka fito shi da baƙon abokinsa da suka jima basu haɗu ba. Hannun Maheer ya janye ya nufi su Abie ɗin kamar yanda Shareff yayi. Abie dake kallonsu fuska ɗauke da murmushi ya riƙo hanunsu su duka yana kallon abokin nasa. “Waɗan nan yarana ne, Babana Al-Mustapha muna kiransa Shareff. Architect kuma Shugaba mai mallakin companyn da nake maka bayani, sai Barrister Maheer”.
“Masha ALLAH yaran albarka”.
Murmushi duk sukayi suna mai rissinawa da gaishesa. Ya amsa cike da kulawa yana riƙo hannayensu shima. Albarka ya dinga saka musu kafin ya juya ga motarsa dake fake a gefe yana faɗin, “Ato ga ɗan uwanku ma ai tare muke da shi sai ku gaisa ko”.
A tare duk suka kalli motar, dai-dai da fitowar Anam daga mota itama cikin matuƙar son nuna dauriya sai dai ta kasa taka ƙafar ta nema zubewa. Da sauri Shareff ya nufeta saboda ratsa kunuwansu da siririyar ƙararta tayi, ya riƙota dai-dai ta kusa kaiwa ƙasa.
“Ance ki fitone?”.
“Nifa na gajine ga zafi a motar”.
Kamar zaiyi magana sai ya fasa saboda idanun su Abie dake kansu, yayinda kunnuwansu ke jiye musu bayanin da Maheer ke musu na cewar ciwo taji a ƙafa.
Ƙoƙarin ɗaukarta Shareff ɗin yake yi tai saurin ja da baya cikin zare idanu da bugawar ƙirji sakamakon ganin wanda batai zaton gani ba.
“W...waya kawoka gidanmu?”.
Ta faɗa idonta kar a kansa kamar yanda shima ita ɗin yake kallo. Su kuma su Abie su dukan suke kallo. Tattausan murmushi ya saki yana mai janye idanunsa cikin na Shareff da yay wani irin mugun kicin-kicin da fuska, akan fuskarta ya maida cikin ɗaga kafaɗa yace, “Ina tare da Daddyna ne. Amma badan nasan nanne gidanku ba Beauty ”.
Sau ɗaya ta kalli abokin Abie ɗin ta maida kanta ta duƙar. Cikin sake faɗaɗa murmushi Alhaji Abu kalla ya dubi ɗan nasa da ƙyau. Kansa ya shafa yana mai kauda kai da sakin ƙaramar dariya. Alhaji Abu Kalla yay ƙaramar dariyar shima da ɗauke idonsa ga ɗan nasa ya maida ga Abie da shima dai murmushin yake da sonjin ƙarin bayani..........✍
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
0913484810_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107 ko
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽
[10/20, 12:59 PM] Mariyamah: *_Typing📲_*
*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_16_*
.........“Ita kuma f...”
Bai karasaba Abie ya bashi amsa da faɗin, “Mamana Juwairiyya (Anam)”.
“Woow masha ALLAH! Masha ALLAH. kace ɗiyar tawa ma ta girma ashe. Damma ƙaramin jiki ya ɓoye shekarun”.
Gaidashi Anam tayi batare data sake yarda ta kallesu ba, ya sanya mata albarka itama da mata sannu akan ciwonta tare da addu'ar samun sauki. Su Maheer suka amsa da amin, banda Shareff dake ƙoƙarin ciro wayarsa a aljihun wandon jeans ɗin jikinsa da kira ke shigowa. Saurayin ya karaso gabanta idonsa ƙyam a kanta ko ƙyafatawa bayayi. Ɗagowa tai itama ta kallesa. Ya kashe mata ido ɗaya yana sake faɗaɗa murmushinsa. Cikin ɗan rankwafowa da murya can ƙasa yace “Kona ɗaukeki da kaina”.
Kanta ta girgiza masa tana satar kallon su Abie da Shareff dake waya duk da idonsa baya kansu, amma abinda bata sani ba kunnensa sarai yaji masa abinda saurayin ya faɗa. Shima ɗan janyewa yay daga kusa da ita ya mikama Shareff daya gama wayar hannu. Fuska ɗauke da murmushi yace, “I'm Muzzaffar Abu Kalla”.
Cikin ido ya kallesa da ƙyau. Ganin su Abie a wajen ya sashi yarda ya mika masa nasa hanun kamar mai ciwon baki yace, “Al-Mustapha Muhammad Shareff”.
“Nice name and nice to meet you”.
“Same”.
Shareff ya faɗa a takaice yana janye hanunsa. Muzzaffar ya mikama Maheer shima suka gaisa. Hakan yayi daidai da fitowar Aysha. Itama gaidasu tai su duka cikin girmamawa. Shareff yace ta kama Anam su shiga ciki. Sai da yaga shigewarsu sannan shima yayma abokin Abie sallama ya shige batare daya sake kallon sashen da Muzzaffar yake ba. Ganin haka shima Maheer yay musu sallam yabi bayansa.
Kai tsaye sashen Mommy suka nufa saboda kiranta dake ta faman shigo masa a waya, duk da kuwa ya ɗaga na farko ya tabbatar mata suna ƙofar gida zasu shigo yanzun. Amma ta kasa haƙuri da tunanin suna raina mata wayone kawai. Da sallama suka shigo falon, har yanzu tana tsaye sai faman kai kawo take kamar an bata gadin kayan falon. Babu zato babu tsammani ƙarar lafiyayyen mari ya shiga bada ƙarar amsa kuwwa a illahirin falon. Maheer ya dafe kuncinsa wata azaba na ratsashi, wani ta sake kifa masa a ɗayan kuncin nasa. Cikin huci mai nuna tsananin ɓacin rai take nunasa da yatsa. “Wannan kaɗanne namaka daga cikin abubuwan dana tanada maka inhar rayuwarka bata nisanta da jinin Usman da Maryam ba anan gidan wlhy wlhy Maheer.....”
“A wane dalili rayuwarsa zata nisanta da jininsa data kasance dolensa kenan Nafisa?”.
Muryar Daddy da basuyi zato ko sanin yana biye da su ba ta karaɗe kunnunwansu, ya dakatar da Mommy dake ƙoƙarin juyawa ga Shareff da mutuwar tsaye ta samesa sakamakon marin da Mahaifiyarsu ta sakarma ɗan uwansa na bazata
“Nafisa! Wai miyasa akoda yaushe kike son nuna ƙarfin iko akan ƴaƴanki wajen wargazamin zuri'ata? To bara kiji, na rantse da ALLAH, daga ranar da tunanin ƴaƴanki ya fara sauyawa zuwa shiga hurumin zumincina da ɗan uwana ko iyalinsa kamar yanda kike ƙoƙarin yi, zan tabbatar da shigarki nadama irin wadda bakiyi tsammani ba daga gareni. Idan kuma kinaga bazan iyaba saboda ɗaga miki kafa danai na tsahon shekaru ku ku gwada aikatawa ku gani”. Ya ƙare maganar da nuna su Shareff cikin tsananin ɓacin rai tare da juyawa ya fice batare da ya jira cewar waninsu ba.
Daga ita har su da kallo suka bishi. Wani irin ɓacin rai na nuna kansa a fuskar Mommy. Ta watsama su Maheer wani mugun kallo batare data sake cewa komaiba itama tabar falon. Da kallon dai itama suka bita harta shige, Yaya Shareff ya sauke nannauyan numfashi da maida kallonsa ga Maheer, kafaɗarsa ya ɗan bubbuga alamar lallashi, dan fuskarsa duk tayi sayin yatsun Mummy.
Cikin ɗacin murya Maheer dake kallon yayan nasa ya ce, “Amma Yaya Mommy......”
Kai ya jinjina masa alamar baya son jin komai, ya ɗan ƙara bubbuga kafaɗarsa tare da ɗan hugging nashi ta gefe sannan ya fice. Maheer ya bisa da kallo....
Mommy da duk ke tsaye a bakin ƙofarta tana kallonsu tai ƙwafa. A ranta kuwa babu abinda take ƙullawa sai tabbatarma Daddy bataji maganarsa ba. Dan kuwa ko ana ha maza ha mata sai ta tabbatar da ƙiyayyar maƙiyanta a zuciyar ƴaƴanta ya jima baiyi abibda ya ɗauka alwashin ba. Iyaka dai yace ya saketa ko! To sai me, ko rabuwa tai da shi ta san yanzu Shareff da Maheer sun taka matsayin da zasu iya riƙe rayuwarta fiye da shi. Hussaina dake daga ɗakinsu tana sauraren komai itama ta ƙwalama kira, da sauri ta iso tana faɗin, “Gani Mommy”.
“Ki bimun Yayanku kiga ya tafine ko ya koma can gidan”.
“Okay Mommy”.
Ta faɗa tana ƙoƙarin ficewa. Maheer ma yabar falon, dan haka ta fita da saurinta sai dai kuma dole tayo baya ta ɓuya dan hango yayun nata a tare. Yaya Shareff na waya ne, sai Maheer tsaye a gefensa alamar jira yake ya kammala.
Wayar ya sauke bayan yayi sallama da Dr Jamal. “Miya faru kuma?”. Ya faɗa cikin kafe Maheer da idanunsa da launinsu ya canja gaba ɗaya. Shima Maheer ɗin kallonsa yake rai ɓace. “Ni zanje na ƙara duba Anam yanzu, dan bazan iya ƙinyin hakanba gaskiya”.
Wani irin murmushi da Maheer ya kasa bama fassara Shareff ya saki, sai kuma ya ɗago yana dubansa cikin ido “Brother be careful!”. Ya faɗa murmushin fuskar tasa na ɓacewa.
Da kallo mai ƙara harzuƙa zuciya Maheer ya bi Yayan nasa, dan tuni harya bar wajen ya nufi gate. Cikin dakewa itama Hussaina tazo ta wuce sa kamar aikenta akai, a mota ta samu Shareff, yana kwance cikin kujera idanunsa a lumshe, a can gefe ta ɓuya tana kallonsa, ya kai kusan mintuna goma a wajen kafin yayma motar key yabar anguwar. Juyawa tai ta koma gida, bata samu Maheer a inda ta barsa ba, dan haka takaima Mommy bayanan data aiketa. Jin Shareff bai shiga gidan su Anam ba yasa Mommy sauke nannauyar ajiyar zuciya, sai dai acan ƙasan ranta ta gama shirya makaman yaƙar su Mamie ta yanda inhar suka tashi tafiya sai sun wuce da ƴarsu wucewar da har abada bazata sake leƙo Nigeria ba balle ta raɓu mata ƴaƴa.
★★★
Duk da ta faɗama Mommy damuwarta hankalinta bai kwanta ba. Sai faman kaikawo take na neman mafita. Zuciyarta ce ta bata shawarar kiran biyu daga cikin ƙawayenta da tafi aminta da su. Cikin sa'a kuwa dukta samesu, umarnin suzo gareta ta bada kai tsaye kai kace itaɗin haihuwarsu tai. Babu ko wanda ya musa mata saima tabbatarwa kafin mintuna shafiyar data basu zasu iso.
Hakan kuwa akai, dan mintuna goma sha biyu bai gama cika cif ba Sima da Amal suka iso. Amal da Sima ƴaƴan talakawane fitik, sun haɗune da Fadwa a media. Komai tayi a shafinta na istagram cikin yabonta da mata Comments suke, idan wani ya zageta zasu haƙiƙice wajen kareta koda kuwa akan gaskiya aka zagetan. Waɗan nan garkuwa da suka dinga bata yasa ta fara kulasu har takai da sun haɗu a zahirin rayuwa. Da farko ganin su ba ƴaƴan kowa bane yaso sakata ja baya da su, sai kuma hakan ya gagara dan suna taka rawar gani a duniyarta ta yanar gizo sosai. Dole ta buɗe bakin aljihu wajen gyara su Sima ɗin ta hanyar siya musu kayayyakin sawa da kaisu wajejen gyaran jiki na manyan yara. Maimakon ƙananun man bleaching da suke shafawa saita ɗaurasu akan manyan harka masu tsada, dan ita Amal ma allura akai mata. Cikin ƙanƙanin lokaci ta canja musu rayuwa suka fara karo da manyan yara. Fadwa nada wasu ƙawayen bayan su Sima dan ita macece mai yawan kwashe-kwashen ƙawaye, ita da mafi yawan ƙawayenta sunyi matuƙar suna a media musamman tiktok a yanzu dake taka rawar gani a rayuwar yaranmu. Komai na rayuwar Fadwa da ƙawayenta a bayyane yake, duk inda zasu samo location ko baground ayi vedio bai musu wahalar zuwa koda a wajen kano ne. A ɓangaren lalacewa bazamuce dukansu a lalace suke ba, dan kuwa akwai wanda a cikinsu da yawa babu ruwansu da mazan inba a ɗan ɗauka vedio ba ko abota shikenan. Fadwa na ɗaya daga cikinsu, dan tunda ta tashi Shareff kawai