Showing 54001 words to 57000 words out of 84091 words
bata gama yarda da cewar har yanzu kewar tasu bace. Amma sai ta barta a hakan dan tasan Anam da rashin ɓoye-ɓoye koma miye wataran da kanta zata sanar musu. Sai da suka tabbatar sun sakata farin ciki tana ƙyalƙyala dariya kamar ba ita ba sannan sukai mata sallama Mamie na faɗin ta gaida mata Yaseer. Farin cikin waya da iyayenta ya taushe abinda Shareff yay mata ta shiga wajen aikinta da walwala kamar yanda ta saba ko yaushe.
*_MALAYSIA_*
“Humairah waye naji kina faɗin Mamana ta gaida miki?”.
Cikin rashin damuwa Mamie tace sirikinka ne duk da dai naga ɗiyar taka bata son a gane hakan.....”
Cikin sauri ya ɗago yana kallonta, har ya kasa dannewa sai da ya ambaci “Suruki kuma?”.
Ƴar dariya Mamie tai, “Eh bashi kake fatan ganiba daman?, bayan shi ma ai akwai wasu. Yaron nan Muzzaffar da kuma wani abokin Shareff Jamal. Amma naga hankalinsu yafi zuwa ɗaya da Yaseer ɗin nan kamar”.
Jin shiru baice komaiba ta ɗago ta kallesa, kallonta yake kamar mai nazari ko tunani, ta ɗan taɓashi, ajiyar zuciya ya sauke. “Abien Anam akwai matsala ne?”.
Kai ya ɗan jinjina mata yana gyara zamansa, “Babbama kuwa Humairah, miyasa tun muna Nigeria baki sanar min hakan ba.”
Sosai maganar tasa ta sakata kafesa da ido dan mamaki, amma ta kasa cewa komai. Fahimtar hakan ya sashi jinjina mata kai, “Basai kin tambayeni komai ba Humairah, amma idan lokaci yayi ko baki tambayeni ba zan baki amsa da kaina”.
Gaba ɗaya kanta ya ƙara ɗaurewa ita kam, sai dai rashin sabo dayi masa dagiya yasa ta kasa cewa komai ta bisa da kallo kawai ganin ya miƙe yana kai waya kunensa. Yana gab da shigewa ɗakinsa taji ya ambaci sunan Yaya (tasan Daddyn Shareff yake kira da hakan). Jitai kamar ta tashi ta bisa amma sai ta dake kawai, zata bisa a sannu dan tasan dalilinsa na son hana Anaam ɗin tsayawa da samari bayan kuma duk fatansu kenan ita da shi tunkan ta wuce Nigeria.....
★★★★
Sauraren sakatariyarsa kawai yake batare da yana fahintar abinda take faɗa masa ba, idanunsa ma gaba ɗaya nakan kula ɗin daya shigo dashi, wadda baya raba ɗayan biyu Anam ce ta manta ta...
“Kinga jeki zan nemeki”.
Ya faɗa cikin katse sakatariyar da ke faman zuba bayani cike da yanga da kwarkwasa. Bataso hakan ba, sai dai sanin shi sam baya wasa yasata bin umarninsa. Sai da ta fice da kusan minti ɗaya ya sauke kakkauran numfashi tare da furzar da shi, yakai bayansa kwance jikin kujerarsa yana mai lumshe idanu. kusan mintuna uku ya ɗauka a hakan kafin ya bude idanun, kular ya ɗauka ya buɗe. Ya tsirama abinda ke ciki idanu tamkar mai irgawa ko lissafa abinda aka sarrafashi da shi. Abincine irin na ƴan ƙasar malaysia, shima yana bala'in son sa a lokacin da ya rayu acan, ko yanzu kuma da yake a Nigeria yakan je takanas ya siya a inda yasan zai samu. Hannu yakai ya ɗauka spoon ɗin dake ciki ya ɗiba dan tabbas wannan ɗin da gani an masa haɗi da girki na musamman ne. Sosai ya lumshe ido lokacin da yake taunawa, koda ya haɗiye sai ya sake ɗiba yakai baki, kamar da wasa sai gashi ya cinyesa tas dan dama bai karyaba ya fito gidan, shayi kawai ya sha, shima sai da Fadwa ta ɓata rai dayin korafin ganin saurin da yake faman yi duk da ta fahimci shi mai fitar wuri ne office sannan ya sha a tsaitsaye ya barota tana tura baki gaba.......
Shigowar Fharhan ta sashi ture kular gefe yana goge bakinsa da tissue. Fharhan dake kallon kular da murmushi ya kai zaune yana faɗin, “Ɗan gatan madam, abincin ma sai an baka kazo office kuma ba gayyatar masu tayaka ci ka kulle office kai kaɗai”.
Murmushi kawai yay yana miƙa masa hannu sukai musabaha. “Kai ka cika sa ido wlhy, ka hucema kanka takaici kai auren kaima sai a ringa baka kana zuwa da shi kana hanamu”.
“A'a karka damu alhaji, ai abun bana gori bane muna hanya da iznin ALLAH”.
“Haka muke so ai muma. dan kun ishemu a tituna”.
Dariya sosai Fharhan yake da maganar ta Shareff, yace, “Kaima yaushe kabar titin. Ba komai zan rama”.
Shima ƴar dariyar yayi. Cikin komawa serious yace, “Yanzu nake duba saƙonka ta email ai. Mutanen nan ya zasu mana haka kuma?”.
“Wlhy nima abin ya ɗauren kai, jiya badan karna takurakaba da a daren zanzo na sameka gida tun shigowar saƙonsu, na kira wayoyinka kuma duka switch up”.
“Mtsoww! Kabari kawai, wlhy ban san madam ta kashesu ba sai da asuba na gani. Amma gaskiya abun nan nasu yayi tsauri, anya kuwa bazamuce mun janye ba”.
“Amma janyewar sai nake gani kamar akwai matsala Musty. Sakamakon company na buƙatar babban aiki irin wannan a halin yanzun, na biyu mun riga munyi zama da su har munyi signing akan agreement ɗin, kasan kuma turawan nan dai musamman chines ɗin nan da basa wasa da damarsu”.
Huci ya ɗan furzar yana mai komawa jikin kujera ya kwanta. Har ga ALLAH abubuwa masu yawa ne ke masa kaikawo a cikin rai. Amma duk sai ya haɗiye abunsa yana sake fuskantar Fharhan dake kallonsa. “Ni gaskiya da tafiyar ta zama nine dole zanyi shine matsalata Fharhan”.
“Oh saboda amarya?”.
Hararsa Shareff yayi, “Ko saboda ita ma ɗin ai inada hujja”.
“hhhh hakane ango kafa ɗan ɗana. To mizai hana kaje da ita kawai”.
“Zan so hakan nima, sai dai bazai yuwu ba”.
“Mi yasa?”.
Shiru kamar bazai amsa ba, sai kuma ya girgiza kansa da furzar da iska ya sake komawa jikin kukera ya kwanta yana ɗan juyata. “Ina hasashen Fadwa nada shigar ciki, sai dai ko ita kanta bana jin ta sani. Yin tafiya da ita a irin wannan gaɓar zai iya zama haɗari”.
“Masha ALLAH! Alhmdllhi. Lallai wannan angon da gaske sharp shooter ne. ALLAH ya inganta mana”.
Shareff ya ɗan murmusa da faɗin “Amin” akan laɓɓa. Cigaba da tattaunawa sukai, daga ƙarshe dai shawara ta zauna akan shi zaiyi tafiyar tunda dai wata uku ne kawai insha ALLAH.
Bayan fitar Fharhan ya buƙaci shigowar sakatariyarsa, daga haka ya cigaba da ayyukansa har zuwa lokacin break....
★★★★
Duk da bata ɗauki gargaɗinsa da muhimmanci ba sai ta kasa sakewa da Yaseer gaba ɗaya yau. Kullum shike fita da ita su ciyo abinci a inda yasan za'a samu abinda take iya ci. Amma yau saita ɓoyema ganinsa. Daga salla ta maƙale a massallaci taƙi fita. Sai ma ta ɗauka alkur'ani tahau karantawa.
Sai da ta daidaici lokaci yaja sosai sannan ta fito. Kamar jira tana fitowar wani abokin aikinta yazo ya sanar mata tana da baƙo. Da mamaki take kallonsa dan bata tunanin wani zai iya zuwa wajenta a yanzu. Daga Muzzaffar har Dr Jamal bata tunanin ganin wani anan, garama Muzzaffar yakan zo idan ya daidaici sun tashi yace zai ɗauketa sai dai bata taɓa yarda ba. Kamar bazata je ba sai kuma taga gara taje dai taga wanene.
Turus tayi lokacin data iso taga mai kiran nata, zaune yake a cikin mota sai dai ƙafarsa ɗaya na waje dan ƙofar a buɗe yake..........✍🏻
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
0913484810_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107 ko
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽
[10/21, 3:14 PM] +234 813 060 4664: *_Typing📲_*
*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718
*_19_*
.......... Ɗagowa yay daga latsa wayar da yake yana kallonta, dan ƙamshin turarenta da takunta ya sanar masa da zuwanta duk da ta kasa magana. Idanunta ta ɗauke daga kallonsa tana faɗin “Good Afternoon”.
“Ni kike ma gaisuwa kina juyar da fuska?!”.
Juyowa tai Idanu cike da ƙwalla tana kallonsa. “Ni wlhy Yaya ban san mina maka ba duk kabi ka tsaneni ka takura ni. Komai nayi a duniyar nan a wajenka ban iyaba”. Ta ƙare maganar da sakin siraran hawaye.
Kallonta kawai yakeyi ko ƙyaftawa babu. Ji tai kallon ya sake saka mata jin haushinsa, juyawa tai da nufin barin wajen.....
“Kika bar wajen nan sai ranki ya ɓaci”.
Idanunta ta rumtse tana jin wasu zafafan hawaye da sukafi na farƙo na neman kufce mata. Ita kam ta rasa mita tsarema bawan ALLAHn nan a duniya, tana fatan watanin nan bakwai da suka rage mata su maza suzo ta kammala abinda ya kawota tabar ƙasar nan, dama tun farko abinda ta gujemawa kenan amma su Mamie suka kasa fahimtarta. Haɗiye hawayen tai batare data barsu sun zubo ba sannan ta juyo garesa, yana a yanda yake har yanzu, sai dai idanunsa masu kwarjini da kaifin dake hana ƙarfin halinta tasiri na nan tsaye kanta ƙyam har yanzu. Kasa jurar kallonsa tai, tai ƙasa da nata, shima sai ya janye nasan, juyawa yay kujerar gefensa ya ɗakko ledar dake ajiye. Miƙa mata yay kansa tsaye.
Ledar ta fara kalla tare da hanunsa dake ɗaure da agogo da zoben azurfarsa da ya jima yana birgeta, har addu'ar damar sace zoben ta taɓa yi a zuwa na karshe da tai kafin wannan.... Saurin ɗagowa tai tana kallonsa jin ya kamo hanunta cikin nasa, ya wani sake ƙanƙance idanu cike da salon kallon da a duk sanda ya jefeta da shi yake firgitata, ta fara son zame hanun a hankali dan gaba ɗaya lakar jikinta neman daina aiki takeyi, kanta ta fara juya masa tamkar mai ciwon wuya, tana son zare idanunta daga cikin nasa amma yaƙi bata damar hakan nan ma, sai kawai ta sakar masa kukan karya.
Hanun nata ya saki a hankali bayan ya saka mata ledar, kamar wadda ake control da remote fitt ta ɓace a wajen. Tsabar sauri har tintiɓe tayi ALLAH dai ya taimaketa bata faɗi ba ta dafe gate.
Murmushi ya saki mai ɗan sauti daga ƙirjinsa yana kauda kansa. Ya maida ƙafafunsa cikin motar tare da rufeta yabar wajen.
Itama koda ta shiga sai da ta samu jikin wata mota ta huta tare da share hawayen ƙaryarta sannan ta buɗe ledar. Shawarma ce da ice-creem sai yogurt da robar ruwa. Haka kawai sai kuma ta samu kanta da sakin murmushi. A fili tace, “Ga rashin mutunci ga kirki idan yaso”. Dariya ta sake ƙyalƙyalewa da shi dan haka kawai drama ɗin tasu ta yanzu take maimaita kanta a zuciyarta tana saka mata nishaɗi.
Yau kam tayi aniyar kozai daketa bazata yarda tabi motarsa ba, dan haka kawai ragwantakar data nuna ɗazun a gabansa ke hanata sukuni, sai dai murmushi ya kasa barin fuskarta har Yaseer sai da ya kasa haƙuri ya tambaya. Ƴar dariya kawai ta masa batace komai ba. Ana tashi itace farkon fitowa, bata son bin Yaseer ɗin badan tana jin tsoron tabbatar hukuncin Yaya Shareff ba, ba kuma ta buƙatar shiga tasa motar shima gara ta hau napep. Sai dai kuma cikin rashin sa'a tana fitowa taci karo da motar tasa a wajen gate, kuka kawai ya rage ta fasa ta huta, tai tsaye ta kasa matsawa ga motar har tsahon wasu sakani. Sauke glass ɗin da dariyar Khaleel ta sata sakin ajiyar zuciya, dan tunda ta fito idonsa a kanta. “Ai ba mai motar bane sai ki taho mu tafi farar kura kawai”.
“Humm ALLAH Yaya bazaka ganeba. Shi Yaya Shareff ɗinne ya cika takura da hana mutane sukuni suji daɗin rayuwa”.
“Maybe yana tsare mutuncin kayansa ne kar kiga laifinsa”.
Bata wani gane mi Khaleel ɗin ke nufi ba, saboda da hausa yay maganar ta buɗe ta shiga tana dariya kawai. Shima yasan bata gane ɗin ba dan haka ya dara.
____________________________
Tun daga waccan ranar Anam ta sake kafa wasan ɓuya da Yaya Shareff, motar Khaleel ta samu matsala, sai kawai ta koma bin school bus na yaran gidan. Kasancewar suna fitar sassafe kafin Shareff daya tsiri zuwa gidan da safe ya iso har sun wuce. Ana tashi kuma zatai wuff ta fito ta tari napep. Motar Yaseer ma dai ta daina shiga duk da yata bibiyarta da son jin ba'asi tana tabbatar masa babu komai.
Samarinta biyu da sukafi takurama rayuwarta taga sun rage manne mata. Dr Jamal da Muzzaffar. Kowannesu kuma yanada gurbi na musamman data ajiyesa dan koba komai suna sakata nishaɗi a wasu ɓangatorin na rayuwa. Sai dai ta gagara neman jin dalilin kowannensu akan ɗan janye mata da yayi, garama Muzzaffar sukan ɗanyi waya jefi-jefi ko chart wasu ranakun.
A gidan nasu kuwa bata da wata damuwa sai su Hussaina wataran, dan idan rashin kunyarsu ya tashi sukan mata sai dai bakinsu nashan bugu dan bata ɗaga musu ƙafa. Ta daina zuwa gaida Mommy da Gwaggo sai in ta ritsa sun haɗu a hanya taita sinne kai wajen gaishesu. Ko kallonta basayi, dan a ganinsu ma ƙin zuwa gaishesun ta taimakesu koba komai sukan manta da wanzuwarta a gidan. Hakan baya damunta, takan wataya tsakanin sashen aunty amarya da Mom abinta. Ita da Aysha da sauran yaran gidan kuwa sai sambarka. Hakama Daddy da Abbah a koda yaushe cikin bama rayuwarta kulawa suke fiyema da yaransu, dan kullum da tsarabar da waninsu zai kawo mata gidan da kuma mata nasihar tsare mutuncinta suke.
Kusan kwanaki goma kenan basu haɗu da Shareff ba, sai a yau da akai sa ranar auran Maheer da sam bata san da zancen auren ba sai da taga akwatina a sashen Mom akace na auren Maheer ne yau za'a saka rana da kai akwatinan. Tayi mamaki sai dai batace komai ba, sai daga baya Aysha ke bata labarin ai Maheer ɗin baya son auren Mommy ce ta takura kamar yanda ta takurama Shareff shima. Auren zumincine da ɗiyar ƙanwarta. Sosai Anam taita mamakin hali irin na Mommy, a ganinta ta cika takurama ƴaƴanta a gidan, musamman Yaya Shareff da Yaya Maheer ɗin. Gashi suna mata matuƙar biyayya fiye da duk sauran yaranta, dan tasha ganin Mommy nama Aysha da su Hussaina faɗa suna ƙunƙuni. Itace ma kema Aysha faɗa da nuna mata illar hakan ga iyaye. Sai kuma gashi masu mata biyayyar sunfi shan wahala a hanunta fiye da su Ayshan da sai abinda suke so sukeyi.
Batabi takan duk hayaniyar da ake a gidan ba, kasancewar ma a sashen Mom baƙin da zasuje kai kayan suke isowa, saita fito domin wucewarta sashen aunty amarya ta huta dan asabar ne. Kamar ta juya taji, lokacin dataga motarsa na ƙoƙarin yin fakin gab da sashen Mom ɗin, amma sai ta dake ta fuske zata wuce abinta.
Siririn tsakin da taji anyi dai-dai zata gitta ya tilasta ta juyowa, dan sam baiyi kama da tsakin Yaya Shareff ba. Fadwa ce a tsaye cikin shigar madam getzner shadda da taci uban aiki sai walwali take, tabbas tayi ƙyau sosai. Anam ta sakar mata wani murmushin ƙularwa da kashe mata ido ɗaya ta cigaba da tafiyarta. Kusan ɗan cin karo sukai da Shareff daya zagayo waya manne a kunensa yana magana. Shima dai sanye yake cikin shaddar fara tas datai masa ƙyau da fiddosa a asalin bahaushensa ɗan arewa dan harda hula. Ta ɗan ja baya yayinda shi kuma ya tsaya cak dan gaba ɗaya hankalinsa akan waya yake baima san wainar da suke toyawa da Fadwa ba. Kallonsa tai tana wani ƙyaƙyƙyafta idanu, sai kuma ta tunzura baki gaba ganin kallon nata da yakeyi shima tamkar idanunsa zasu cinyeta. “Good morning”. Ta faɗa tana gittasa da ƴar sassarfa.
Cikin basarwa ya cigaba da wayarsa, hakan sai yayma Fadwa data tsaresu da idanu daɗi harda matsowa zata rungumesa ya kauce mata yana nuna mata sashen Mom. Cikin shagwaɓa tace, “Ni dai ka gama mu shiga tare ALLAH kunya nake ji”.
Sarai yasan ƙarya takeyi, amma sai baice mata komai ba har ya kammala. Gaba yay ta bisa a baya....
Bata buƙatar zaman tunanin abinda ya shafi waninsu, dan haka tai connecting bluetooth ɗinta ta manna a kunne. A hankali takai kwance bisa grass carpet dake a ɗan ƙaramin garden ɗin dake bayan ɗakin aunty amarya tana lumshe idanunta cike da nishaɗi, dan waƙar da take saurare tana matuƙar sonta, mawaƙin ɗan ƙasar malaysia ne, waƙar ma anyitane da yaren malay sai dai an cakuɗa da turanci. Tayi nisa sosai wajen sauraren waƙar fuskarta shimfiɗe da murmushi, ga idanunta a lumshe sanyin inuwar wajen na ƙara girmama nishaɗinta, bakinta sai motsawa yake a hankali alamar bin waƙar takeyi....
Jin ƙamshinsa ya ƙara ƙarfi cikin hancinta ya sata kasa cigaba da jurewa ta buɗe ido a hankali batare da tabbacin mai ƙamshin bane a wajen. Sai dai kuma cin karo da