Showing 81001 words to 84000 words out of 84091 words
baida lafiya ba. Shiru tai taƙi tankawa, sai ma fuska data ɗaure tamau dan kamanin Anam data gani tattare da dattijon ya bata tabbacin shine baban Anam ɗin kuma ƙanin Mamansu da suke uba ɗaya. Duk da cikin taushin murya da sauƙaƙawa yake mata faɗan sai ta murguɗa baki, babu wanda ya lura da abinda tayi sai Abie. Maimakon yaji haushi amma sai yay Murmushi kawai.
Abbah da jin bata amsawa Abie ɗinba ya dubeta shima ransa a ɓace, baida faɗa amma in aka kuresa shima ɗan babu sauki ne. Aiko ya balbaleta da masifa yana zaginta akan shiru dataima Abie ɗin. Haƙuri Abie ya fara bashi amma yaƙi saurarensa, sai da yayi mai isarsa har Fadwa ta fara share hawaye sannan ya ƙyaleta dalilin dawowar Dr Jamal ɗakin.
Cikin ƙanƙanin lokaci rashin lafiyar Shareff ɗin ta shiga kunnen kowa. Waɗan da basu riga sun wuce wajen kamu ba sai suka zarto asibitin dubasa. Babu wanda aka bari ya shiga wajensa dan ba'ason masa hayaniya. Sai Mommy data matsa ita da Gwaggo suka leƙasa. Har dare anata shigowa asibitin duba san, dan wandama sukaje gidan kamu daga can nan suka dinga zartowa. Hakan sai ya tabbatarma da jama'a mara lafiyan ɗan dangi ne. Har sha biyu bai farka ba, anata ma ƙara masa ruwa har lokacin, dole kowa ya tattara ya tafi aka bar Khaleel da Maheer a wajensa duk da Fadwa harda kukanta itace zata zauna da shi. A can gida ma Anam tana kwance rijif da zazzaɓi duk da doctor yazo ya dubata bayan na ido. Haka dai aka kwana zukatan mutane da yawa babu daɗi.
Washe gari aka tashi da shirin ɗaurin aure duk da rashin daɗin da ake ciki akan ciwon Shareff dan na Anam ba kowa ya sani ba. Da sassafe Fadwa ta wuce asibiti ita da Mommy data zillema mutane da ƙyar. Sun samu ya farka har Maheer ya taimaka masa zuwa bayi yayo alwala. Yana cikin yin sallar daya makara ne suka shigo. Sun ɗanji sanyi a ransu. Suna zaune harya idar, suka shiga jera masa sannu yana amsa musu da kai dan sam baya son yin magana. A dai-dai lokacin suma su Abba suka shigo harda Daddy, kamashi su Khaleel sukai ya koma saman gado, cikin magana ƙasa-ƙasa da bata fita da ƙyau ya gaida su. Cikin kulawa duk suke amsa masa da tambayar ƙarfin jikinsa. Ya amsa musu “Da sauƙi” akan laɓɓansa. Abba ya fara masa faɗa akan ya akai ya zauna da ciwo haka babu wanda ya sani? Sai kace wanda baida kowa?.
Ɗan murmushin ƙarfin hali yayi na yaƙe, murya ƙasa-ƙasa yace, “Abba zazzaɓine kawai shiyyasa. Kuma naji sauƙi Alhamdulillahi”.
Abie ya girgiza kansa yana mai dubansa da tausayawa. “Wannan yafi ƙarfin zazzaɓi kawai my son. Kaga kuwa yanda ka rame? Sannan a kwanakin nan gaba ɗaya babu mai ganinka, mu duk mun zata aikine ya maka yawa shiyyasa”.
Ɗan murmushin yake ya kumayi sai dai baice komaiba anan ma. Idanunsa da sukai wani irin kaɗawa jazur ya lumshe da jingina a jikin filon da Khaleel ya saka masa. Ya buɗesu a hankali ya saci kallon Mommy da Fadwa dake zaune kowa ya zuba tagumi. A hankali ya furta “Mommy inajin yunwa”.
Kai Mommy ta jinjina masa, tare da taɓa Fadwa datai zurfi a duniyar tunani. Numfashi ta kawo mai haɗe da ajiyar zuciya ta kalli Mommyn. “Kira su Bintu muji wai ba'a kammala abincin bane gashi yace yunwa yake ji”. Da to ta amsa. Tana shirin kiran waya sai ga sallamar Mom da Mamie. Su Abba ne kawai suka amsa da Khaleel. Suka shigo Maheer biye da su ɗauke da basket, sai Mubarak da carton na ruwa. Daga Mom har Mamie fuskokinsu sun kasa ɓoye damuwarsu akan yanayin Shareff ɗin, suka shiga masa sannu da jera masa addu'a su Daddy na amsawa da amin. Mommy da Fadwa dai sunyi kamarma basu san da zuwansu ba. Abba ne ya bada umarnin Maheer ya zuba masa abincin dasu Mom ɗin suka kawo tunda yace yunwa yakeji daman...
Shigowar Doctor ta sakasu duk suka fito, Daddy ya dubi agogo, ganin lokaci yaja gashi yau juma'a ga ɗaurin aure yace su ai gara su wuce gida ma Khaleel da Fadwa sai su zauna a waje sa, dan dama acan gida sune suka hana kowa zuwa har Gwaggo. Cema mutane akai kawai an ma sallamesa dan haka kowa ya dakata da yunƙurin zuwa aka maida hankali ga shagalin biki. Fadwa da Khaleel aka bar masa, su kuma gaba ɗayansu suka wuce gida, sai dai Maheer bai so hakaba, soyay shima a barsa anan basai yaje ɗaurin auren ba. Amma babu yanda zaiyi su Abba suka korashi, ga Mommy sai zabga masa harara takeyi.....
★★
Gidajen biyu duk sun gama cika da jama'a, bakajin komai sai hayaniya da al'ada irin ta biki. Maza duk sun wuce massallaci domin halartar sallar juma'a da ɗaurin aure. Yayinda amarya Anam ke ƙudundune har yanzu taci kuka harta godema ALLAH, zazzaɓi ne mai tsananin zafi tattare da ita. Haushin kowa takeji a gidan, har shi Muzzaffar ɗin da rabonta da shi a zahiri tun randa Shareff ya dawo, saita waya jefi-jefi yake kiranta daga gaisuwa kuma sai yace mata yana da uzuri. badan bata son sa ba take jin haushinsa, kauce-kaucen da yake mata ne yafi komai mata zafi, musamman a kwanakin matsowar bikin. Su Abie sun isa da itane shiyyasa take danne komai saboda farin cikinsu, ko sai bayan sun ɗaura mata aure suka gaya mata bazata taɓa jayayya da su ba saboda matuƙar girma da darajar da suke da shi a gareta. Amma shi mizaisa ya dinga mata kauce-kauce kamar dole akai masa ya aureta bashi yazo yace yana sonta ba?, ya kuma ɗauke ƙafa da zuwa inda take ma sai kace zasuyi auren ƙiyayya?. Hawaye ne suka cigaba da silalo mata a hankali dan bata da ƙarfin yin kuka, a wannan yanayin barci ya saceta saboda allurar barci da doctor ya mata.
★Tun bayan barin su Daddy asibitin yaƙi ya sake magana da kowa, Fadwa da Khaleel ma cayay su bashi waje yana buƙatar kaɗaici. Ran Fadwa ya ɓaci sosai har ta kasa shanyewa ta dubesa zatai magana Dr Jamal ya ɗan girgiza mata kai da mata alamar roƙo kar tace komai. Harara ta watsama Shareff tai fitowarta. Shiko Khaleel biyota yay fuskarsa ɗauke da murmushi, yayi tunanin ma asibitin zata bari gaba ɗaya, amma sai ya sameta a waje zaune tana danna waya alamar kira take ƙoƙarin yi. Baice mata komai ba ya kai zaune a kujerar dake kallonta, waya ya ɗauka shima, yana jinta tana faman jan tsaki da alama wanda take kiran bai ɗauka ba. Suna a wajen zaune Dr Jamal ya fito, Fadwa ya kalla dake cika tana batsewa. Yay murmushi da girgiza kansa. “Madam kiyi haƙuri kar kiji zafinsa da yawa, shi mai ciwo haƙuri ake da shi dan bakomai ake masa yaga an masa daidai ba. Zaki iya komaa yanzun ya samu barci, amma ba'a buƙatar motsi mai ƙarfi dan barcin nasa bazaiyi nauyi sosai ba”.
“Amma Doctor dan mutum na ciwo sai ya dinga dizga mutane kuma. Shi baya ganin ƙoƙarin mu ne?”. “Bawai baya gani bane, yanayin da yake ciki ɗinne sai anyi haƙuri da shi Please. Ki ƙara haƙuri ki koma ciki mu zamuje massallaci ne”. Bata sake cewa komai ba ta tashi ta shiga, su kuma suka fice shi da Khaleel da yaƙi saka baki a maganar tasu dan ƴan miskilancin na kusa..........✍
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[11/1, 1:27 PM] +234 813 060 4664: *_Typing📲_*
*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718
*_34_*
...........A wajen ƴan biki kuwa dawowar ƴan ɗaurin aure ya sake ruɗa gidajen biyu, bakajin komai sai guɗa da kirarin maroƙa tako'ina. Bakin su Daddy ya kasa rufuwa saboda tsananin farin cikin da suke ciki na sake samun damar aurar da yaransu a karo na uku. Hakama Mommy tana a cikin tsananin farin cikin cikar burinta na sake aurar da Maheer ɗinta a ganinta ta raba ƴaƴanta biyu da ƙaya. Shiko ango Maheer ko walwala baka gani a fuskarsa, dauriya kawai yake na amsa gaisuwar jama'a da taya murna a garesa saboda baya son su Daddy suga kamar bai ɗauka shawararsu ba......
A ɓangaren Mamie da Abie ma duk da wannan rana ta tilon ƴarsu tazo musu a yanayin da basu gama shiryata yanda suke so ba hakan bai hanasu kasancewa cikin ɗunbin farin ciki ba, dan albarkar auren suke nema mata ba wai tsarabe-tsaraben cikinsa ba. Fatansu ALLAH ya bata zaman kafiya da zuri'a masu albarka ita da mijinta. Suna zaune a ɗakin Abie da take barci suna kallonta fuskikinsu murmushi ya kasa sauka, ga ɗunbin tausayinta da ƙaunarta na ratsasu. Abie ya kauda kai gefe yana murmushi ganin Mamie na sharar hawaye, cikin son danne nasa dake ƙoƙarin sakkowa ya miƙe yana kai waya kunnensa tamkar zaiyi kira ya gudu a ɗakin......
Ƙananun maganar da suka fara fitowa a bakunan mutane saboda jin yanda ɗaurin aure ya kasance suka fara yawaita a gidan har wasu a dangin Mommy ya fara isa kunnuwansu. Da yawansu mamaki suke nunawa jin yanda al'amari ya kasance dan su dai basu san da wannan aure ba. A cikin ƙanen Mommy da abin ta jisa tamkar saukar aradu ta kasa haƙurin shanyewa kamar kowa ta shiga neman Mommy. Da ƙyar ta samota a sashen gwaggo wajen tsoffi na ƴan uwa da ƙawayen ta da suka taru acan.
“Ke ko lafiyarki kuwa Samira kika shigo mana kamar wadda take a rikice”. Gwaggo ta faɗa ganin yanda aunty Samiran ta shigo har tana cin tuntuɓe. “Gwaggo dole kike ganina a haka, wani mummunan labari nake jiyowa yana tashi a gidan nan dana gaza gaskatawa, Aunty dama akwai auren wata bayan Fadwa akan Shareff?”.
“Samira ban son takale-takalen masifa ina cikin farin cikina wane aure kuma?”.
“Humm aunty kenan, aure nawane aka ɗaura a gidan nan yau, kidai bincika dan yanzu naji anata ƙus-ƙus wlhy wai dama matarsa ce sai dai yau aka sanar.” A rikice Mommy ta kalli gwaggo, itama gwaggon kallonta takeyi baki buɗe. Cikin ƙarfin hali gwaggo tace, “Nifa sam bamma gane wannan soki burutsun nakiba wlhy Samira”.
“Nima da nake faɗa mukun na kasa ganewar, inaga bincikawar dai kamar ya kamata kuyi”.
Suɓucewa plates dake a hanun Mommy sukayi, ƙirjinta na matuƙar bugawa da sauri-sauri. Fitt ta fito ɗakin Gwaggo na ƙwala mata kira amma bata juyo ba. A yanda ta fito ɗin yaja hankalin mutane da yawa suka shiga binta da kallo. Kai tsaye sashen Daddy ta nufa, sai dai koda ta shigo bata samu kowa ba sai kwanikan abinci dake barbaje alamar anci. Har bedroom ta leƙa, nan ma babu kowa a ciki. Da sauri ta shiga laluben wayarta dake cikin handbag ɗin hanunta da take tara kuɗin yinin bikinta dan yau takeyi, hannunta ma rawa yake, tadai samu da ƙyar ta lalubo number Daddy tai dailing. Sai da ta kusan tsinkewa ya ɗauka, babu ko sallama tace, “Daddyn Shareff wani shirme nakeji yanzun, nazo sashenka kuma baka nan?”.
Kai tsaye ya gano abinda taji ɗin, dan haka a dake yace “Ina waje tare da mutane, idan na shigo sai muyi magana...” ƙitt ya yanke wayarsa tana ƙoƙarin dakatar da shi. Tsananin tsoro ne da firgici ya ƙara saukar mata. Tabi wayar da kallo kamar zata gano Daddy ɗin a ciki. Kai ina bazata iya haƙuri ba sam, akalar kiran nata ta maida ga wani yayansu data tabbatar Daddy baya ɓoye masa komai dan abokinsa ne shaƙiƙi tun ƙuruciya. Bugu biyu ya ɗauka, tai ƙoƙarin shanye tashin hankalinta dan tasan saita lalama Yaya Awwalu zai faɗa mata abinda take bukatar. Bayan ta gaishesa yake cemata tayi haƙuri bai shigo ya mata an ɗaura aure ba wani uzirine ya taso masa amma zuwa anjima zai dawo gidan.
“A'a babu komai Yaya ai kai mai yine, yanzuma na kiraka ne saboda inji ko kana tare da abokin naka dan zuwa anjima ina son ka ɗan ƙarama Maheer faɗa kasan yaran nan da taurin kai, Shareff ya fisa haƙuri da biyayya tunda kaga shi duk aurarrakin nan zaɓinmu ne amma ko yau bai tada hankalinsa ba akai”.
Yaya Awwal yay ƴar garan murya irin ta manya da ɗan murmushi, “A'a karki damu shima zai kwantar da hankalinsa ai, kuma hankalinsa aiba ɗaya dashi Mustapha ba. Amma zan shigo ɗin insha ALLAH, yaya jikin shi Mustapha ɗin ma? Dan ina tambayar bangansa ba akace yana asibiti babu lafiya”.
“Eh wlhy zazzaɓine ya kadashi amma da sauƙi, inagama yau za'a sallamosa tunda ba'a kai amarya babu ango ba”.
A karon farko yay ƴar dariya mai sauti da faɗin, “Wannan gaskiya ne, ALLAH dai ya basu zaman lafiya da haƙuri da juna tunda duk gidane, sai dai dan ALLAH kiyita ƙara nusar dashi da tausarsa tunda su duka ƴan uwansa ne kar zuminci ya samu matsala azo ana hai hai babu daɗi. Gaba ɗayansu ɗaya suke a wajensa babu wadda tafi wata.......”
Tunda ya fara jawabin nasa na ƙarshe jikin Mommy ya hau rawa, bazata iya jin ƙarshen zancem ba dan haka ta yanke wayar. Hajijiya taji tana neman ɗibarta, a dai-dai nan Gwaggo da taga shiru bata dawoba ta biyota ta shigo. Salati ta saka da riƙeta da sauri. “Ke ko kina lafiya zaki kashe kanki Nafisa?”.
Kuka Mommy ta fashe da shi, “Gwaggo sun kasheni, wlhy sunyi a banza, har abada jinina dana Usman bazasu zauna a inuwa gudaba. Gwaggo na rantse yau duk masifar da za'ai a gidan nan sai dai ayi sai Shareff ya saketa, ni Muhammad zai cima amana, ni Muhammad zai yaudara ya zalunta.....”
“K wai miya farune kin sani a duhu?!”.
“Gwaggo aure fa suka ɗaurama Shareff da ɗiyar maƙiyana, wai ƴar gidan Usman. Kuma tabbas batun yau ba ma.”
“Ƴar gidan Usman?!!”.
Gwaggo ta faɗa a razane, Mommy bata amsa mataba ta mike fuu ta fito hanunta dafe da kanta dake juya mata. Gwaggo na ƙoƙarin tsaidata yanzu ma bata saurareta ba. kai tsaye hanyar gate tayi, Samira ta biyita da sauri. “Yaya! Yaya miya faru ne? Da gaske ne ko?”.
Bata iya bama Samira amsaba ta fisgi gyalenta tai waje, kasancewar anata ɗaukar ƴan biki da kawosu ta samu a napep. Daddy daya hangota da yake suna zaune a ƙofar gidan cikin runfa ya miƙe, sai dai kafin yazo har napep ɗin tabar wajen.......
★Tun ɗazun ya farka saboda zuwan gayyar abokansa da sukaje ɗaurin aure. Shidai kallon mamaki yake musu, dan baiyi tsamanin ganinsu haka da yawa ba a waje ɗaurin auren ƙanin nasa. Suko sai faman washe baki suke da tsokanarsa a sigar daya kasa ganewa dan kowa ya kasa fitowa fili yace wani abu saboda ganin Fadwa tare da shi. Ga kuma dama Dr Jamal ya rokesu kar suce komai anan Please. Basu wani jima sosai ba suka fita acewarsu zasuje cin abinci zuwa anjima zasu dawo duk da Doctor yace maybe ma zuwa dare su sallamesa. Bayan fitarsu Fadwa ta dawo kusa da shi. Ganin yanda tai kicin-kicin da fuska sai yaji wani iri, hannu ya miƙa mata alamar tazo, tai kamar zata noƙe sai kuma ta nufesa ganin yay mata alamar roƙo. Jikinsa ya jawota ya rungume, ya sakar mata sumba a gefen wuyanta tare da ɗaura kansa a kafaɗarta yay shiru. A hankali ta lumshe idanunta da haɗiye kukan dake neman ƙwace mata.
“Shii!!”.
Ya faɗa a hankali cikin kunnenta yana kai hannu ya tallafo fuskarta ya juyo da ita...... Burumm ta faɗo ɗakin kamar an jehota. Su dukansu sukai saurin kallon ƙofar, ganin Mommy ya sashi janye jikinsa cikin jin tsananin kunya, Fadwa kam wani irin takaici ne ya tsargi ranta kamar ta dannama Mommy zagi. Mommy kam da sam hankalinta bama yakai kan yanda suke ɗin ba ta jefa masa takarda da biro saman jiki......
“Rubuta mata saki uku yanzu-yanzun nan da manyan baƙi yanda iyayenta zasu gani da ƙyau bama ƙanana ba...”
Cikin tsananin mamaki da rashin fahimta yake duban mahaifiyar tasa. Yayinda ƙirjin Fadwa yay wani irin mahaukacin dokawa tamkar gagarumar aradu ta bada sautin fashewa. Ita dai tasan ita kaɗaice matarsa ai........
Takarda da biron ya tattara ya ɗauka, a hankali cikin muryar mara lafiya ya dubi Mommy. “First luv ban gane ba. Wazan saka?”.
“Shegiyar yarinyar da aka ɗaura maka aure da ita a ɓoye mana, inba hakaba zan tsine maka Al-Mustapha, tsinuwa mai muni kuwa da a duniya ko kai bazaka ƙara morar kanka ba balle waninka!!”.
A kusan tare zuciyarsa data Fadwa ta nema wantsalowa waje. Cikin rawar lips shi yay ƙarfin halin faɗin, “A...Aure kuma? First luv n... Ni aka ɗaurama aure??”.
Sake fusata ta tambayar tayi, cikin tsananin kaushin murya ta sake bashi umarni batare data amsa masa tambayarsa ba. “Bani da lokacin maka wani bayani anan, dan wlhy zan iya tsine maka Al-Mustapha. Da manyan baƙi cikin