Showing 15001 words to 18000 words out of 84091 words

Chapter 6 - Babu So Book 1 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

255

jaa ya ɗan bita da su, sai kuma ya janye dayima motar key yay reverse.
Kasancewar anguwace da kakan daɗe bakaga abin hawaba yasa har suka cimmata. Tafiya take tana sharar hawaye. Duk da horn da aketa faman mata baisa ta juya ba. Ransa ya ƙara ɓaci, a fusace yay parking tare da fitowa yasha gabanta, kanta ta ɗauke gefe kamar bata gansa ba zata raɓashi ta wuce.
      Hannayensa ya tura cikin aljihun wandon Jeans ɗinsa. “Idan kika ƙara step ɗaya a wajen nan sai jikinki ya faɗa miki!”. Cak ta tsaya iya taku biyun da tai, wasu irin hawaye masu zafi suka ƙara ciko mata idanu. Motar ya nufa idanunsa tamkar zasuyi aman wuta. Duka kawai take tsoro, dan haka ta share hawayenta dan bata bukatar da ga shi har budurwar tasa su gani, motar ta buɗe ta shiga. Yay ƙaramar ƙwafa da buɗewa shima ya shiga, ya fisgeta da gudu zuwa kan titi batare daya ƙara kallon kowaccensu ba. Sunyi tafiya kusan na minti biyar dai-dai gidan wani abinci Fadwa ta dubesa, “Please Soulmate banyi breakfast ba”. Shiru yay kamar bazai tanka ba, bai kuma da alamar tsayawa, itama kasa ƙara cemasa komai tayi saboda yanda ya haɗe fuska matuka. Harma ta haƙura sai taga ya gangara gefen titi dai-dai wani restaurant da bama tasan da shi ba. Buɗe motar yay ya fita batare da yace musu komaiba, itama Fadwa sai ta fita tana harar Anam data maida hankali ga latsa waya kamar bata a motar.
Suna ƙoƙarin barin wajen yakai dubansa gareta, dai-dai ta ɗago itama suka haɗa ido. Fuska ta sake ɗaurewa tamkar yanda shima ya sake tsuke tasa. A yanayin fusata ta janye nata da ɗan kallar gefen Fadwa. Har suna gab da shiga wajen bata da niyyar fitowa ita, sai da suka shige da kusan minti biyu sannan ta fito dan haka kawai zuciyarta ta raya mata ta bisu koba komai zata ragema Fadwa jin daɗi ai.
Cikin taku a hankali ta shigo wajen, dai-dai yana magana waiter idonsa ya sauka a kanta harta ƙaraso inda suke, kujera taja ta zauna. Idanun nasa ya ɗauke gefe, tare da yin kamar bai ganta ba ya ɗauka wayarsa ya hau dannawa. Kallonsa ta ɗanyi tana tura baki, batare data kalli inda Fadwa take ba itama ta hau latsa tata wayar cikin kwaikwayon salon da yayi.
      Ta gefen ido ya dubeta, numfashi ya ɗan ja a fisge tare da maida hankalinsa ga wayarsa a zuciyarsa yace (azababbiyar yarinya).
      Kamar tasan mi yake ayyanawar ta ƙara ɗaure fuska tana hararsa shi da Fadwa da hankalinta itama gaba ɗaya ke kan wayarta da alama akwai abinda takeyi mai muhimmanci. Isowar waiter ɗauke da tray ya sakasu ɗagowa su duka. Har waiter ɗin ta gama shirya musu abincin tabar wajen idon Anam nakan nasa. Ya ɗau cokali zai fara ci tace, “ALLAH Yaya abincinka yafi nawa nama”.
       Duk yanda yaso basar da ita ya kasa. Ya kafeta da idanu kamar mai harara “Kuɗinki ko kuɗina?”.
  Fuska ta taɓe “Naka ne. Amma kuma ai ina cikin masu cin gadonka idan ka mutu, kaga banda laifi idan nayi magana”.
Wani wawan tsaki Fadwa ta saki tsanar Anam na ƙara faɗi a ranta.
“Shiga shanu ba sharo”Anam ta fada cikin sakin siririyar dariyar data sake kular da Fadwa (*Sharo ba shanu* bahaushiyar malaysia😹😆)
     Tattausan murmushi kawai ya saki a karo na farko da cigaba da cin abincinsa. (Batun yanzuba ya fahimci bata da riƙo. Sai dai ya tabbatar wannan sauyawar tata lokaci guda ba'a banzaba akwai abinda ke ranta).
Fadwa ta kafesa da kallon mamaki, sai dai shi yaƙi yarda ya kalla inda take. Saurayin dake kusa da su da drama ɗin tasu taja hankalinsa tun ɗazun yay ƴar dariya idonsa akan Anam shi kuma. Juyawa tai taɗan kallesa. Ganin shima ita yake kallo ta ɗauke kanta tana harararsa, abincin Shareff ta ƙara kallo, burinta kawai ta yanda naman kan plate ɗin nasa zai dawo nata, ganin hankalinsa nakan wayarsa tace. “Yaya!”.
      “Uhhyim!”.
Ya amsata batare da ya daina abinda yake ba. “Na faɗa maka wani abu?”.
     “Uhhm”
Nanma ya sake faɗa batare daya ɗago ɗinba. Ɗan shiru tai tana nazari. Bayan kusan sakan talatin ta dubesa sai kuma ta ɗan harari Fadwa ta maida dubanta ga ƙofar shigowa. “Lah Yaya wannan ba Aunty bace?”.
     Kamar bazai ɗagoba sai kuma ya ɗago ɗin jin kamar tayi maganar a serious. Kallonsa ya kai ga ƙofar duk da bai san wace aunty take magana ba akai kamar yanda itama Fadwa da gaba ɗaya takaici ya turniƙe takai kallonta wajen. Wuff ta kwashi kusan rabin naman daya tsole mata ido ta maida a plate ɗinta. Lokacin da yake juyowa fuska a tsuke harta miƙe a table ɗin ta koma na kusa da su da guy ɗin da duk hankalinsa ke kansu yake.
     Plate ɗin abincin nasa ya kalla sai kuma ya kalleta. Kauda kansa yay gefe saboda murmushin dake neman suɓuce masa. Ya ɗan jinjina kansa dayin ƙwafa. Fadwa dai kallonsa kawai take mamakin tsaurin idon yarinyar nan na nema shaƙureta.
       Saurayin da gaba ɗaya komai na Anam ya gama tafiya da imaninsa shima fuskarsa ɗauke da mayataccen murmushi yake kallonta. Ya sake sakin murmushi ganin duk laumar abincin da zata kai sai da yankan nama. Cikin murya ƙasa-ƙasa yanda ita kaɗai zataji yace, “In ƙara siya miki wani gimbiya?”.
        Kai ta ɗago ta kallesa, sai kuma ta saci kallon Shareff. Ido suka haɗa, ya zuba mata hararar da hanjin cikinta suka kaɗa, amma saita fuske cikin dakewa. Ƙasa tai da idanunta Tana ƙoƙarin sake kai abincin bakinta kamar bata gansa ba, saurayin ya sake ɗan matsota cikin ranƙwafowa har tana jin hucin numfashinsa yace, “Queen Please”.
      Wani irin cije baki Shareff yayi da ƙarfi, sai kuma ya miƙe gaba ɗayansa. Gabansu ya iso ya ɗauka wayarta da saurayin ke ƙoƙarin ɗauka. A kausashe yace, “Tashi muje”.
     Kamar bazata ɗago ba sai kuma dai ta ɗago tana kallonsa. “Ni banfa gama ba, ba yanzu muka fara ba, ga budurwarka ma bataci nata ba”.
    “I will slap you in baki tashi ba”.
Miƙewar tayi fuska a kumbure. Ya nuna mata hanyar waje, ko kallon saurayin baiyi ba yayma waiter nuni tazo. Kuɗinsu ya bata, tareda wasu yace ta masa takeaway na naman rago. Fadwa da ko lauma ɗaya bataiba dama ta miƙe tsam da wayarta a hannu ta fice, bayansu yabi, sai dai kafin ya fito Fadwa ta tsaida napep ta shige abunta, Anam ko jikin mota ya sameta ta haɗe fuska tamau. komai baice mata ba ya buɗe ya shiga, a dai-dai nan aka kawo masa takeaway ɗin da ya saka akayo. Jin ya kunna motar tai saurin buɗewa itama ta shiga. Sai lokacin ya lura babu Fadwa, motar ya sake buɗewa ya fito yana dube-dube.
Wata shaƙiyyar dariya Anam ta ƙyalƙyale da ita harda kwanciya, tana ganin zai dawo ta haɗiye kayarta da gyara zama ta fuske...
A dake yace, “Malama dawo nan”.
Ido ta ɗan waro tamkar bata san mike faruwa ba. “Yaya Auntyn kuma fa, ba fitsari taje bane?”.
Kallon banzar daya watso mata ya sata buɗe murfin ta fita tana danne dariya da ƙyar, ƙasa-ƙasa take faɗin, “Ai daga yau daga kai har ita kun shiga uku da ni. Sai tasan ita ƙaramar ƴar iska ce”......

★★★★

         A kallo ɗaya zaka fahimci tsananin ɓacin ran dake tattare da ita. Tunda Gwaggo Halima ta kirata ta sanar mata abinda ya faru take kiran wayarsa amma yaƙi shiga. Kasa daurewa tai ta dawo falo tare da tura Hussaina gate zaman jiran shigowarsa. Mintuna goma kuwa ba'aiba cikakku da zaman Hussaina a gate sai ga motarsa ta shigo. Anam ce ta fara fitowa, Hussaina ta bita da kallo harta shige sashen Mom. Shima dake binta da kallon fitowa yay hanunsa ɗauke da ledar takeaway. Hussaina ta taso da sauri tana washe baki dai-dai yana sama motar lock da key ta waje.
      “Yaya sannu da zuwa”.
Batare daya kalleta ba ya amsa mata. Idonta akan ledar hannunsa ta kuma faɗin, “Yaya Dama Mommy ce tace kaje tana nemanka”. A yanzu kam idanunsa ya ɗago yana kallonta. Sai dai baice komaiba tsahon sakkani ya janye. Ganin zai bar wajen takai hannu ga ledar. “Bara na ɗauka maka to”. Harararta yay, babu shiri taja baya tana tura baki gaba. Baibi takantaba ya nufi sashen Mom. Fawwaz kawai ya samu a falon zaune yana kallon cartoon. Yaron ya taso da gudu ya nufosa. Ledar ya ajiye gefe fuskarsa ɗauke da murmushi ya ɗagashi sama. “Oh my Friend ya kake?”.
      “Lafiya lau Yayanmu. Good morning”.
      Kumatunsa ya ɗan ja yana murmushi. Kafin ya ɗan kalla falon. “Gentlemen ina Mom ne?”.
      “Tana ɗaki da aunty Rahma tazo”.
“Okay! To kace ina gaisheta.”
     Kai ya jinjina masa. Sai kuma ya kai bakinsa kusa da kunnen Shareef ɗin, cikin raɗa yace, “Aunty Anam kuma yanzu ta dawo sai fushi takeyi”.
          Idanu ya ɗan waro waje kamar yanda yaron yayi, “Haba dai?”.
   “ALLAH kuwa. Ko kulani ma batayiba ina gaisheta da nuna mata Cartoon ɗina”. “Ayya am sorry my dear, maybe bata da lafiyane. Amsa wannan ka kai mata sai kuci tare”. Duk da ledar ta masa nauyi da ɗan gudunsa ya nufa ɗakin cike da murna yana ƙwala kiran “Aunty Anam! Aunty Anam!!”.
        Idanu yaɗan lumshe a hankali da harɗe hannayensa duk biyu a ƙirji yana murmushi har yaron ya shige ciki. Haka yake shi mutum ne mai tsananin son yara. Bai shirya aure yanzu ba, amma saboda son da yakema yara ya sashi amsar tayin su Mommy dan ta matsu taga yay aure ya rasa dalili?.

        Shigowarsa falon yasa Hussaina saurin yin shiru ta haɗiye sauran gulmar da take faɗama Mommy. Sai dai kuma yama riga yajita, kallon daya watsa mata yasa tai saurin barin falon tana tura baki gaba.
     “Shareff kai dawa kaje gidan Halima!!”. Mommy ta faɗa a fusace tunkan yace mata komai. Ɗan jimm yayi na wasu sakanni, sai kuma ya ɗago yaɗan dubeta. “Mommy ni ban shiga gidanba ma balle naje da wani”. Harara ta watsa masa. “Wlhy Al-Mustapha ka kiyayeni a gidannan. Idan kace zamu saka ƙafar wando ɗaya da kai bazakajita da daɗi ba! Yanzu na kiraka nace kasata a napep ta dawo shine danka rainani ka ɗauketa kukaje wajen wadda ke shirin zama matarka har kana mata walaƙanci a gabanta ko?! Ita kuma shegiyan yarinyar mai kama da ifiritin aljanu haihuwar bakwaini tana mata rashin kunya, to idanma wani abune a ranta tun wuri ta fiddashi dan har abada bazan haɗa zuri'a da Usman ba, sunga ta rasa miji a can shine zasu kwasota su kawo nan talla......”. Murmushin yay da tasowa ya dawo kusa da ita, sai dai a ƙasan carpet ya zauna ya ɗora kansa jikin ƙafarta, hanunta ya riƙo cikin nasa murya a sanyaye, “First-luv Please cool down, yaronki bashi da wata mata bayan zaɓinki, idan ma hakane a ransu ai bani kaɗai bane ɗa a gidan ko?!.....”
        “Ko kai kaɗaine bazaka aureta ba, kuma ko yanzu dan kayi aure idanma hakane a ransu Maheer ma yafi ƙarfin nan sai dai suje can su nema mata miji dan ko Khaleel saina hana uwarsa yarda”.
       Murmushi ya saki mai faɗi da lumshe idanunsa. Yayinda kunensa ke cigaba da sauraren banbamin masifar Mommy. A haka su Aysha suka shigo suka samesu. Gaisuwar da suke masa ce ta sashi buɗe ido da tashi daga jikin Mommy yana kallonsu. Kafinma yace wani abu Hassan yay saurin faɗin, “Yaya daga aikan Gwaggo muke fa”. Komai baiceba ya miƙe ya fita a falon.

___________________

        A yau da Anam ke cika kwanaki biyar a gidan ya kamata ta fara shirin fita aiki, amma mutuniyarku barcinta take sharɓa saboda jin daɗin ɗan sanyi-sanyin safiyar dan bata isashen barcin dare daboda zafi. Da zarar an ɗauke wuta bazata sake rintsawaba. Dan ƴar fan ɗin da Mom ta bata Fawwaz ya joganeta jiya taƙi ɗaukar caji. Gaba ɗaya Mom ta shafa'a da batun fara fitar Anam ɗin yau itama, shiyyasa batai tunanin tadata ba tanata ƙoƙarin shirya su Fawwaz karsu makara tafiya makaranta suma. Sai daga baya ta tuna taje ta kakkaɓeta da ƙyar..

        Kamar kullum cikin shirin fita office ya fito. Shareff mutum ne mai himma, bashi da wasa akan aikinsa shiyyasa a kullum cikin haɓaka kamfani yake. Zamansa tsayayyen mutum yasa ma'aikatan ke tsananin shakkarsa da kiyaye dokokin kamfani, dan shi babu ruwansa yana ganin baka serious zai sallameka ne acewarsa a kwai dubu masu buƙatar gurbinka zaune a gida. Sashen Mommy ya fara shiga, ƙanensa nata ƙoƙarin karyawa suma. Cikin girmamawa duk suka gaidashi. Amsawa yay yana ƙoƙarin kaiwa zaune a ɗaya daga kujerun falon dan bazaka taɓa ganinsa cikinsu yana cin abinciba. Mommy dake tsaye itama a dining ɗin tana haɗa masa tea ta ƙaraso garesa. Tunkan ta ƙaraso ya miƙe fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa mug ɗin. “Good morning First-luv”.
      “Morning dear, how are you?”.
“Alhamdulillahi”.
     “Haka ake so ai. A saka maka Irish ɗin?”.
    “No Mommy wannan ɗin ma is ok for me. Yau na makara gashi inada meeting eight thirty”.
        “To aiko gara ka hanzarta tunda gashi eight ɗin gab yake dayi”.

      Koda ya fito sashen Mommy wajen aunty Amarya ya shiga suka gaisa kamar yanda ya saba duk safiyar duniya zai shiga ya gaida kowa na gidan. Daga nan kuma babu mai sake ganinsa sai wata safiyar, sai dai duk ranakun juma'a da laraba zai sayo fruit bayan ya tashi aiki ya shiga kowane sashe yakai musu, hakama duk ƙarshen wata zai sayi kayan tea dasu sabulai omo MacLean kayan dai buƙata kananu yakai kowane sashe. Tun Mommy najin haushi da masa faɗa har dai ta tattara ta zuba masa ido amma hakan na damunta da ɓata ranta saboda zugar Gwaggo. Sashen Gwaggo ya nufa itama ya gaisheta dan itace a tsakiyar Mom da aunty amarya. Yasanta da son su zauna hira dan haka ya maƙale daga ƙofa suka gaisa duk da tayin kunun gyaɗa da take masa kuma ransa naso.
      “Gwaggo na makara, amma zubamin zanje da shi office nasha. Bara na gaida  Mom a kaimin mota”.
    Kafinma tace wani abu ya fice da sauri zuwa sashen Mom idonsa akan agogon dake a tsintsiyar hanunsa. Gaisuwar su Fawwaz ya fara amsawa dake fita da gudu zuwa school bus ɗinsu. Kafin ya ƙarasa cikin falon su gaisa da Mom. Itama nan koda tai masa tayin abinci cayay Alhmdllhi ya fito da hanzari. A jikin motarsa ya samu Ladi mai aikin Gwaggo ɗauke da ƙaramin basket. Tunkafin ya ƙaraso ya buɗe motar da key tai ƴar ƙara. “Ranka ya daɗe gashi inji Gwaggo”. Baice komaiba ya amsa basket ya ajiye a gefen mai zaman banza, fitowar Daddy ta dakatar da shi daga yunƙurin shiga motar da yay niyya ya nufi Daddyn ɗin duk da sun gaisa bayan fitowarsu massalaci da asuba, tare kuma suka fita motsa jiki....
       “Babana har an fito?”.
   “Eh Daddy nama so makara dan inada meeting”.
    “To ai yau da gobe sai ALLAH ko”. Daddy ya faɗa dai-dai da fitowar Anam daga sashen Mom. Tsaf take shirya cikin kayan NYSE da sukaima jikinta cif kamar ka saceta ka gudu. Ta naɗa yololon veil ɗinta tare da ɗora p-cap ɗin samansa, saita goya bag ɗinta mai suffar teddy data zuba komai a ciki. Tayi ƙyau sosai sai zuba ƙamshi take mai daɗi. Fuskarta ƙawace da murmushi ta nufo inda suke, sai da ta sauke hular daga kanta tace, “Good Morning Daddy”.
     “Good Morning Maman Daddy. how are you?”.
    “I'm fine Daddy, sai dai zafi da dare barci babu daɗi”.
         “Ayya mamana ba'akwai fan a ɗakin naku ba?”.
  “Akwai Daddy, idan suka ɗauke nepa ɗinne fa, fan ɗin da Mom ta bani yaƙi ɗaukan cagi jiya”.
     Kanta ya ɗan shafa da faɗin, “Am sorry insha ALLAH za'a saya miki wata to koda an ɗauke wutan, koma ac za'a sayo dai?”.
      Ƴar dariya tayi da satar kallon  Shareff da tun zuwanta wajen ya haɗe fuska yana danna waya kamar bai san da zuwan nata ba. Shima Daddyn dariya yay da duban Shareff ɗin, “Kun gaisa da Yayan naki ko?”.
        Baki taɗan tura gaba da ɓata fuska, sannan tace, “Good morning”.
      Duk da sarai yajita bai amsaba, sai duban Daddy yay yana tura wayarsa a aljihu da faɗin, “Daddy bara na wuce ina ƙara makara”.
    Daddy yace, “Ato shikenan sai kije ya saukeki tunda hanyarsa ce”.
       Idanu ta waro da ƙyau tana ƙyaƙyƙyafta su. “Daddy Abie yace driver zai dinga kaini”.
     “No na dakatar da shi ai. Duk motocin gidan nan ace sai an ɗauka miki wani driver. Idan Shareff zai fita sai ya dinga tafiya dake, idan ya tashi aiki kuma ya ɗakkoki ba shike nan ba”.
         Zatai magana ya girgiza mata kai alamar kartace komai. Shirun kuwa tai, sai dai kamar zatai kuka takeji. Sam bata buƙatar haɗa sabgarta da shi. Duk miskilancin Khaleel tafi jin daɗin zama da shi, shiko Maheer dama mutum ne mai sauƙin kai da faran-faran, shiyyasa da akace mata bayanan taji duk babu daɗi.
      Ganin shima baice komai ba Daddy ya dubesa “To ALLAH ya bada sa'a. Sai ka wuce da Mamana ko”.  Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya ɗan rissinar da kansa ƙasa da fadin. “Mu yini lafiya”. Jinjina masa kai shima Daddyn yayi. “ALLAH yasa. Mamana bishi ALLAH ya bada sa'a”. “Amin Daddy” ta faɗa dabin bayan Shareff da tuni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login