Showing 72001 words to 75000 words out of 84091 words

Chapter 25 - Babu So Book 1 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

259

idanunta dake cikin gilashi. A hankali ya lumshe nasa ya sake buɗewa. “Wannan kallo ai sai kisa na gagara faɗar abinda ke raina”.
A yanda yay maganar ya sata sakin siririyar dariya. Hakan yayi dai-dai da buɗe gate da maigadi yayi motar Khaleel ta shigo. Su duka basu maida hankali ba, sai ma dariyar da yake tayata shima yana ɗan duban fuskarta da take kaudawa gefe, yanda yaketa ƙara ƙoƙarin son ganin fuskar tata sai yake ƙara bata dariya harta kasa dainawa....

“Alhamdulillahi lallai yau jama'ar gidan nan zasusha surprise na ganinka Yaya fiye da yanda ƴan can gidan suka sha”. Khaleel ya faɗa yana kashe motar. Bai saurari amsaba ya buɗe gefensa ya fito, zagayawa yay ya buɗe masa fuskarsa ɗauke da murmushi.
Badan glass dake rufe da idanunsa ba babu abinda zai hana aga tsantsar ɓacin ran dake cikinsu. Tuni sun kaɗa sunyi jajur, duk wani annurin dake saman fuskarsa na farin cikin dawowarsa cikin zuri'arsa ya ɓace ɓat. Cike da izzar da fushi ya haddasa ya zuro ƙafafunsa ƙasa ya fito, hakan yayi dai-dai da juyowar Anam dake shirin ɗagama Khaleel hannu.. Hannun nata da numfashinta a tare suka maƙale, ƙirjinta yay wata irin bugawa da batasan dalili ba. A hankali laɓɓanta suka motsa ta ambaci sunansa...
“Yaya Shareff”.
Duk da akan laɓɓa tai maganar hakan bai hana Muzzaffar gane sunan wa ta kira ba, juyawa yay shima a hankali. Cikin dariya Khaleel ya ɗago musu hannu da faɗin, “Surprise”.
Murmushin yaƙe ta saki, mamakinta na sake bayyana akan fuskarta, ta miƙe a hankali kamar wadda ƙwai ya fashema a ciki ta nufesu, hakan yasa shina Muzzaffar miƙewa fuskarsa da murmushi yabi bayanta..........✍




_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[10/26, 6:12 PM] +234 813 060 4664: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_29_*


........“Sannu da zuwa Yaya”. Ta faɗa har yanzu mamaki shimfiɗe akan fuskarta. Idanunsa ya ɗauke daga kanta batare daya amsa ba duk da ba gane hakan ake ba saboda idanun nasa na sakeye a cikin gilashi. Taji haushin yanda yay mata ɗin, sai dai yanayin tsukewar fuskarsa ya sata jin shakka da ƙara ganin kwarjini da fresh daya ƙaro. Muzzaffar ya ƙaraso wajen fuskarsa da murmushi shima yana masa sannu da zuwa. Shima ɗin akan laɓɓa ya amsa masa, koda ya miƙo masa hannu dan suyi musabaha kuma kamar bazai karɓa masa ba, sai kuma ya miƙa nasa shima da ƙyar. Anam ta taɓe baki cikin takaicin shan ƙamshin nasa tana kallon Khaleel da shima yanayin Yayan nasu ya sashi kama kansa, sai dai a ƙasan ransa yana mamakin komawarsa haka dan cikin nishaɗi da farin ciki suka baro gidansu daya fara sauka, kuma da farin cikin ya ɗakkosa a airport.
        Dai-dai suna shigewa ya zare gilashin fuskarsa ya watsa mata wani shegen kallo mai cike da gargaɗi ya wuce. Tai tsamm a waje ɗaya zuciyarta na bugawa da dauri-sauri, amma dan ƙarfin hali sai ta murguɗa masa baki. Muzzaffar kam da kallo ya bisa yana sakin murmushi zuciyarsa na cuɗa masa abubuwa daban-daban duk da ba yaune karon farko daya fahimci wasu abubuwa a idanun Shareff ɗin ba. Numfashi ya sauke a hankali yana nuna mata suje. Itama ajiyar zuciya ta sauke a hankali, jiki a sanyaye ta bisa suka koma wajen zamansu.

       A ciki Aysha da ke kitchen tana girkin dare ita da mai-aiki ce ta fara leƙowa saboda jin sallamar Khaleel, ta wani zaro ido waje da sakin ihun murnar daya saka Fadwa fitowa zumut daga bedroom. Itama idanu ta zaro na mamaki, dan sam bata san da batun dawowar mijin nata ba. Ya ALLAH, ai tama manta da kowa na falon ta fasa ihun murna da kwasowa da gudunta garesa. Baiƙi bata dama ba, dan shima yayi missing ɗinta, ya ware mata hannaye tako shige jikinsa tare da ɗanesa.
     Dariya Khaleel ya saki yana kauda kansa gefe, hakama Aysha da gudu ta koma kitchen tana dariya ita da mai aiki. Acan waje kuwa Muzzaffar ƙoƙarin yima Anam hira yake yi cike da kulawa amma sam sai ya fahimci hankalinta baya tare da shi, yay murmushi da miƙewa yana faɗin, “Bara na barki madam gobe idan ALLAH ya kaimu da dare maybe zan shigo sai mu ƙarasa, ya kamata kije kema ayi murnar dawowar Yayan dake”.
      Murmushin yaƙe ta ɗan masa, dan duk suna jiyo ihun Fadwa. Ya miƙa mata ledar da yazo da shi tare da mata bye-bye. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali lokacin daya fice a gate ɗin baki ɗaya, ta ɗan kalla ledar daya bata sannan ta nufi ciki. Har shigowarta Fadwa na ɗane jikinsa, ya wani rungumesa tsam tana hawaye da faɗin wai tayi missing ɗinsa. Sosai ƙirjinta ya ƙara ƙarfin bugun da yakeyi, tai azamar dafe kujera dan jitai kanta ya fara juya mata kamar maijin hajijiya, amma sai tai matuƙar dakewa fuskarta ƙawace da murmushi. Shi kaɗai da idanunsa ke a ƙofar dama ya ganta, ya sauke sassanyar ajiyar zuciya da har sai da Fadwa taji, cikin jin daɗi ta ƙara maƙalƙalesa tana raɗa masa yanda tai tsananin kewarsa a cikin kunensa. Karon farko tun shigowarsa falon ya saki siririyar dariya, a hankali ya ɗan kaima wiyanta sumbata idanunsa na kallon Anam ƙasa-ƙasa. Sai akai sa'a itama dai-dai ta ɗago nata idanun da hasken cikinsu gaba ɗaya ya kore duk da a cikin gilashi suke. Ɗauke idanunta tai tana taɓe baki da juyasu cikin salon ko'a jikina. Numfashi mai ɗaci ya saki da ƙoƙarin dakatar da Fadwa dake ɗan jan hanunsa.
       “Shiiii!!”
    Ya faɗa cikin wani salo yana ɗaura yatsansa akan bakinta da kashe mata ido ɗaya wanda komai ya ƙara faruwa akan idon Anam data ɗago. Wayarta dake ring ta ɗaga da kaiwa kunenta ta sakin murmushi da ajiye ledar hanunta ta nufi hanyar bedroom ɗinsu cikin ƴar sassarfa.
     Khaleel da sai yanzu ya lura da ita ya ƙara sakin ƴar dariya dan duk zatonsa shi kunyace itama ta sakata yin hakan. Ledar data ajiye a wajen ya ɗauka yana faɗin, “Ƴar ficikar nan mi kika samo mana haka ne?”. Maganar tasa ce ta saka Fadwa saurin juyowa dan itama bataga Anam ɗin ba, a yanzu kuma har ta shige abunta. Ta buɗe baki zatai magana Aysha ta fito daga kitchen ɗauke da tray. Kai tsaye gaban Shareff da yakai zaune cikin kujera ta dire.
     “Yayanmu sannu da zuwa kazo lafiya? Ya hanya?”.
   Kanta ya shafa kawai batare da yace komai ba. Hakan ya sakata sakin murmushin jin daɗi, ruwan data tsiyaya a kofi ta miƙa masa. Ya karɓa idonsa akan Fadwa da ita sam bata da niyyar hakan ma a garesa... Khaleel daya fahimci kallon da Shareff ɗin yay mata ya dubeta shima. “Madam kina tsaye Aysha ta kwashe ladan daya kamata ki samu, anya kuwa bazamu ƙaro amarya ba a gidan nan dan ba'ai mana tarbar data dace ba”.
      Har ƙasan zuciya maganar Khaleel ta soki Fadwa, ta kalli Shareff dake shan ruwansa tamkar baya jinsu dan hankalinsa na kan tv ne, kallonta ta maida ga Khaleel cikin haɗe fuska. “Yaya Khaleel wane fatan tsiyane wannan dan ALLAH da yammacin nan?”.
         Zama yay yana faɗin, “Naga kamar haka ya kamata muyi ne ai hajjaju, idan kuma baki son amarya sai ki gyara kurenki da wuri”. Da gaske magana ya faɗa mata a kaikaice, amma kuma cikin wasa da murmushi Aysha na tayasa da dariya. Hararar Khaleel ɗin tayi, a karo na farko taji tsanarsa, sai dai batace komai ba taje kusa da mijinta ta zauna fuska a ɗaure. Kofin hanunsa ya ajiye yana miƙewa, bedroom ɗinta ya nufa yana faɗin, “Haɗamin ruwan wanka, ke kuma Aysha kuje ku gyaramin side ɗina”.
      “To Yaya”.
Aysha ta amsa cike da girmamawa. Matar gidan kam takaicin Khaleel ya hanata amsawar, sai dai ta miƙe cike da isa tana gallama Khaleel ɗin harara tabi bayansa. Daga Aysha har Khaleel sunga harar, tana shigewa Aysha tai dariya. “Yaya Khaleel ka sakama Aunty Fadwa jin haushin maganarka fa”. Cikin halin ko'in kula ya ɗage kafaɗa da taɓe bakinsa irin I don't care ɗin nan. Ƴar dariya Aysha ta ƙara saki da mikewa zata nufi waje dan kiran Anam ya sanar mata tana ciki ta shigo...
        “Tabbas na kusa fara shukama Khaleel rashin mutunci a gidan nan in har yana min wannan maganar banzar”. Ta faɗa a fusace tana shigowa ɗakin, dai-dai Shareff na ajiye agogonsa daya cire saman mirror ɗinta idonsa akan wayarta dake maƙale a ɗan sama. Video take ɗauka zatai posting a tiktok ihun Aysha ya sakata fita, ALLAH yasota wayar ta gaji ta rufe kanta. Jin bai tanka mata ba ta ƙara maimaita abinda ta faɗa tana kallonsa. Yanzu dai ya juyo ya kalleta sai dai baice komai ba ya ɗauke kansa yana ƙoƙarin jan necktie ɗin wuyansa.
      “Soulmate kanaji fa ina magana”. Ta faɗa a shagwaɓe da rungumesa ta baya. Kamar bazai tanka mata ba, sai kuma a taƙaice yace, “Miye nawa, maganarku ce”.
      “Hakama zakace?”.
   Ta faɗa tana juyowa gabansa. Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe akan lips ɗinta, sai kuma yay ƙoƙarin kaudawa amma ta riƙo fuskar tasa, bai samu damar cewa wani abuba ya haɗe bakinsu.....

        Aysha ko koda ta shiga ɗaki sai ta samu Anam duƙunƙune cikin bargo, tana taɓata taji zafi sosai a jikin nata zazzaɓinta ya dawo. Sannu tai mata, ta maida mata bargon ta lulluɓa mata. Ita kaɗai taje tai gyaran, hakan ya sata jan lokaci bata gama ba duk da babu datti sosai saboda sukan gyara lokaci-lokaci. Tana cikin saka turare Shareff ya shigo sanye cikin jallabiya fara tas. Sannu ta masa, ya amsa mata da kai yana bin falon da kallo. Baiyi magana ba dan komai ya masa yanda yake so, ya wuce bedroom ɗinsa baifi mintuna uku ba ya fito ya sake ficewa. Itama kammalawa tai a gurguje ta fito dan kiraye-kirayen salla aketayi.
     Ita ta tada Anam sukai salla, suna idarwa ta koma gado ta kwanta. Kyaleta Aysha tai sai da aka ƙara kiran sallar isha'i sannan ta sake tadata. Koda suka kammala babu yanda batai da itaba akan suje falo taci abinci tasha magani amma taƙi. Dole Ayshan ta barta ita ta fito.  Fitowar tata kusan dai-dai ta fitowar Fadwa daga kitchen tare da mai-aiki. Sannu tai musu dan suna faman shirya abincine a dining, itama tayasu tayi, suna tsaka da shirya abincin ya shigo falon yana waya. Kai tsaye dining ɗin ya nufo dan yana son ya ɗanci abincin yaje ya kwanta da wuri a gajiye yake matuka. Mai-aiki tabar wajen da sauri saboda hararar da Fadwa ta zuba mata. Aysha dai kujera taja masa baya. Zama yay idonsa akan matarsa dan sabuwar kwalliyar tata ta masa ƙyau sosai. Ta ɗan duƙo ta sumbaci gefen fuskarsa. Hannu yakai ya ɗan shafi tata fuskar ya cigaba da wayarsa. Aysha dai ta ɗauke idonta a kansu tun sanda Fadwa takai masa kiss........✍🏻




_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_30_*


..........Ganin tanata bubbuɗe abincin tana nuna masa ta kurma yay mata nuni da fruit salad kawai. Ta nuna masa abinci, yay mata alamar 1spoon kawai. Yanda ya buƙata haka tai masa, sai dai tasa masa haɗin salad a gefen shinkafar da ɗan yawa saboda tasan yafi buƙatar hakan. Da idanu yay mata alamar ‘thanks’ ta sakar masa murmushi.
         Sun fara cin abincin yay sallama da wanda suke wayar ya ajiye. Harya maida hankali ga abincinsa ya ɗago ya kalla Aysha. “Ina Anam?”. Ya faɗa a taƙaice. “Yaya tana ɗaki bata da lafiya, nayi-nayi ta taso taci abinci amma taƙi kuma ko magani bata sha ba”. Idanu kawai ya zubama Ayshar, sai abincin dake bakinsa da yake taunawa a hankali. Sai kuma ya janye kamar baiso yace, “Kiramin ita”. Mikewa Aysha tai da faɗin to.
      Da ƙyar ta taso Anam, amma da tace bazataje ba ita abarta. Sai da Ayshan tace, “Kin san dai zai iya zuwa har ɗakin nan ya ɓata miki rai ko”. Kamar bazata tashin ba sai kuma ta tashi tana ɓata fuska ga idanunta jazur. Ya ɗan juya musu baya, dan haka har suka ƙaraso wajen bai ɗago kansa ba. Sai da Fadwa tai magana idonta akan Anam datai gefe da fuska sannan ya ɗago. Kallonta yay da ƙyau ya janye idanunsa. Hakan yasa Fadwa sake yin magana cike da kissa. “Baki da lafiya kuma sai kije ki kwanta da ciwo a ɗaki Anam?”.
    “Uhhm”.
Kawai Anam ɗin tace a taƙaice, amma ko kallonsu taƙi yi daga ita har mijin nata. Murmushi Fadwa ta sake saki a zahiri, sai dai a ranta daɗin damar data samu takeyi, cikin sake sakin fuskarta tace, “Kije ɗakina saman mirror cikin First aid box akwai maganin zazzaɓi sai ki duba wanda zaki iya sha”.
        Yanzu kam sosai ta juyo ta zuba mata idanu, mamakin kissa da sabon salon Fadwan fes a kan fuskarta, sai dai kafin tace wani abu Shareff da yay kamar bayajinsu ya katseta. “Ki wuce ki ɗakko kizo kici abinci kisha”. Baki ta buɗe zatai magana sai kuma ta fasa, ta jefama Fadwa dake murmushi har yanzu wani kallon banza ta wuce zuwa bedroom ɗin nata da yau ne karon farko da zata shigesa. Sai da ta gama ƙarema ɗakin kallo tana taɓe baki sannan ta nufi mirror zuciyarta na ƙoƙarin danne abinda ke taso mata saboda kayansu data gani a watse a ƙasa da saman gado alamar ansha bidiri dai. Magunguna ta samu zube akan mirror ɗin wanda har ta ɗauke kanta ta kasa sai da ta sake kallonsu.
     Wani irin mummunar bugawa ƙirjinta yayi lokacin da idonta ya sauka akan sticker ɗin ɗaya daga cikin magungunan. Batama san sanda tai wurgi da maganinba ta fasa ƙara dayin tsalle gefe jikinta na maƙyarkyata. Aysha da Fadwa har rige-rigen isowa ɗakin suke. Yayinda uban gayyar ya shigo a ƙarshe fuskarsa a haɗe. Aysha dai dama kanta tayi, Fadwa kam dariya ta fara sai dai shigowarsa ya sata gimtsewa da sauri itama ta nufi Anam ɗin. Da robar maganin data cillar yaci karo, ya ɗauke kansa da maida dubansa gareta saboda abinda take faɗa tafukan hanunta rufe da fuskarta taƙi yarda Aysha ta buɗe.
      “ALLAH ya isa! ALLAH ya isa ƴar iska wayyo Mamie na ban yafe ba ban yafe ba.....”
    “Ikon ALLAH badai mu bane ƴan iskan ko Anam?!”. Fadwa ta faɗa cikin tafa hannaye da nuna damuwa na makirci saboda ganin ya shigo. Shi kuma ɗakin yabi da kallo har idonsa ya dawo kan robar data cillar ɗin, baima san sanda yakai hannu ya ɗauka ba yawun bakinsa na ƙoƙarin kamewa. Idanunsa ya rumtse da ƙarfi ya buɗe akan Fadwa ransa a ɓace. Sai da gabanta ya faɗi ganin yanda idonsa ya kaɗa yay jazur cikin lokaci ƙanƙani.
      “Kamata ku fita!”.
Ya faɗa cikin bada umarni ga Aysha. Hanun Anam daketa faman jera ALLAH ya isa har yanzu ta kama suka fice. Sai da suka fice ya tako ya zauna a bakin gadon ya dafe kansa bayan ya ajiye maganin gefensa. Ƙoƙarin danne tsoron dake faɗi a ranta tai ta nufesa, cike da kissa takai hannu kan kafaɗarsa. “Soulmate wlhy na man....”
      “You're vary stupid da zaki faɗamin kin manta. Kinsan suna shigo miki ɗaki zaki ajiye waɗan nan abubuwan a inda idonsu zai gani. Koke da kika saka kanki ajiyewar dole ne sai kin bar stickers nasu a jikinsu saboda baki da hankali!!”.
         Yanda yake masifa ba ƙaramin bugu zuciyarta ke mata ba. Ta shiga girgiza masa kai dan yana yine kamar zai mareta. Ta matso da nufin rungumesa ta basa haƙuri ya tureta ya fice. A falo ya sami su Anam har yanzu tana faman kwarara ALLAH ya isa, Aysha na tambayarta wai miya faru ta kasa bata amsa.
     “Shut up!! stupid!”.
Ya faɗa a tsawacen daya tilasta Anam gimtse bakinta da janye hanunta dake akan fuskarta har yanzun. Da sauri ta sake maidawa ta rufe ganinsa tsaye a gabansu. “Idan kika ƙara wani magana anan saina mareki, dalla kuwuce kuci abinci”. Kusan a tare duk suka miƙe zuwa dining ɗin, yabi bayansu yana jan tsaki mai ƙarfi. Aysha ta zuba mata abincin, jin yanda yaketa faman jan tsaki a jajjere ya sata cin abincin badan taso hakan ba. Laumarta baifi uku ba tai yunƙurin mikewa ya watsa mata harara. Da sauri ta koma ta zauna kamar zatai kuka.
        A daidai nan Fadwa ta fito jiki a saɓule, sai dai daka kalleta zaka san tayi kuka. paracetamol ta ajiye gaban Anam tana satar kallonsa, fruit ɗinsa yake sha sai dai fuskar tamkar zatai aman wuta. Kujera taja ta zauna. shiru wajen ya ɗauka babu mai ko tari sai ƙarar cokula. Anam ce ta fara turo nata dan da gaske zazzaɓin nata neman dawowa sabo yake. Aysha ta ɓalla mata magani ta bata. Amsa tai tasha babu musu, tana kammalawa tabar wajen da ɗan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login