Showing 75001 words to 78000 words out of 84091 words

Chapter 26 - Babu So Book 1 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

267

gudu-gudu dan karma yace zai dakatar da ita. Itama Aysha sauri-sauri tai ta gama ta gudu ta barsu a wajen......

★★★

        Washe gari duk da ta sake tashi da zazzaɓi tana idar da sallar asuba tahau haɗa kayanta da suka rage, dan tun dare ta tattare wasu. Tambayar duniya Aysha ta mata akan miye take haɗa kaya bata tanka mata ba. Har Ayshan taji haushi tai shiru, tamayi kwanciyarta ta juya mata baya. Koda taji ƙarar jan akwati da fitarta bata motsaba tamayi kamar tai barci ne.
    Taji daɗin ganin babu alamar wani ya tashi a gidan, ko mai gadi ma sai da ta ƙwanƙwasa masa ƙofar ɗaki ya fito ya buɗe mata da mamakin ganinta da kaya. Sai dai yanda tai kicin-kicin da fuska bai bashi damar mata tambayar dake a ransa ba. Duk da nauyin akwatin nata ga wata jikkar data ratayo haka taita jansa har titi. Hijjab din Aysha ne har ƙasa jikinta saboda da kayan barci ta fito. Sai da ta iso har babban titi ta samu napep, ALLAH ya sota ma babu nisa zuwa titin. Kai tsaye ta faɗa masa anguwar dazai kaita. Ya faɗa mata kuɗin tace suje kawai.
       Sanda suka iso gidan ba kowama ya tashi ba musamman yara dake hutawa saboda cikin hutu ake. Da mamaki Mom ke dubanta, ta tura baki gaba da faɗin, “Mom bani two hundred zan bama maigadi a wajensa na amsa naba mai napep.” Komai Mom batace ba ta mika mata five hundred. Fita tai ta kaima baba maigadi amma sai yamaƙi amsa. Dawowa tai ta bama Mom kuɗin tare da faɗawa saman three sitters ta kwanta. Mom dai na binta da kallo. “Lafiya da kaya da sassafen nan?”.
       “Ni Mom na gaji dama da zaman gidan can ALLAH. Kawai na taho ne ni tunda Yayan ya dawo ai”.
         “Hummm”.
Kawai Mom ta faɗa ta ɗauke kanta. Anam kuwa barcine ma ya ɗauketa take a wajen dan jiya kasa barcin kirki tayi, haka kawai ta dinga mafarkin abinda ta gani saboda ta saka abin a ranta harda amai tai kusan sau uku a daren jiya dan ƙyanƙyami abin ya dinga bata. Tunda take bata taɓa ganin halittar namiji ba a rayuwarta koda a hoton ma saboda tsayin daka na tarbiyyar iyayyenta a kanta, duk da kuwa ta tashine a wani yanki da yasha banban da nata. Hatta wayarta tanada matakan tsaro kashi-kashi da idon iyayenta ke akai akoda yaushe saboda bata kariya daga faɗawa tarkon musibar zamani na gane-gane dake zama silar watsa tarbiyyar yaranmu da yawa a wannan zamanin ta hanyar waya..
     Ganin barcin nata zaiyi nauyi Mom tace ta tashi ta koma ciki. Batai musu ba ta mike ta shige ciki ta kwanta. Barcin daya gagareta a daren jiya shi ta samu damar ramawa, dan bata farka ba sai kusan sha biyu da rabi. Wanka ta farayi da alwala tai salla ganin one yayi sannan ta fito dan hayaniyar su Fawwaz dake ɗaukar hankalinta..........✍




_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[10/28, 10:41 PM] +234 704 134 7629: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_31_*


...........A haka aka shiga shirye-shiryen bikin Maheer, Anam da Aysha. Yayinda kwanakin dawowar Shareff da ba'a sanar da shi komaiba ke kusantowa. Asabar ɗin daya rage saura sati uku biki Anam da Aysha acan gidan suka yini ana shirye-shirye da tsare-tsare. Anam dai ba shiga sabgar duk wani shirye-shirye take ba, su Fadwa ne dai ƙirjin biki keta kaiwa da kawowa duk da ango Maheer bawai yana ko leƙowa yaji yanda abubuwan ke tafiya ba ne, dan shi ƙiri-ƙiri nunawa yake baya son auren nan. 
        Haka itama Anam Muzzaffar yayi tafiya dan tunda aka fara maganar auren ma bata gansa ba, a wayama sai jefi-jefi dan baya ƙasar yaje wani aiki mai muhimmanci a yankin larabawa.
Washe gari lahadi Khaleel ya dauketa ita da Aysha kamar yanda yay mata alƙawari zuwa wajen tela. Kayanta takai na ɗinki, Mom ce ta bata su takai ɗinki kusan kala goma sha biyar. Kayane masu ƙyau da tsada har tana mamakin miyasa aka banbantata da Aysha, dan telan nata ma na musamman ne saboda Mommy taƙi yarda Aysha ta kawo nata nan. Bayan sun zaɓi ɗinkunan da take so ya gwadata ya faɗa misu bill ɗin kuɗin. Accaunt number ɗinsa Khaleel ya amsa, ya saka masa rabin kuɗin rabi yace sai ya kammala aikinsa. Daga nan gidan wata ƙawar Mom suka nufa ƴar sudan. Har Khaleel ɗin suka shiga ciki, yanda aka tarbesu ya bada tabbacin Khaleel ɗan gida ne. Sun ƙara tabbatar da hakanne lokacin da wata ƴar budurwa ta kawo musu abinsha tana ta faman sinne kai na kunya, yayinda Khaleel ke faman jifanta da wani kallo. Cikin yanayin tuhuma Anam ke kallonsa tana murmushi, yay murmushi kawai da ɗauke kansa gefe.
“Uhm to lallai ALLAH ya sanya albarka Yaya Khaleel, amma auntyn tamu fa tayi dan kun dace”.
Salute ɗinta yayi, hakan ya sakata kwashewa da dariya Aysha na tayata, dan ita ta kasa cewa komai tunda ba wasa yake da su ba. Fitowar matar hamshaƙiya ƴar gayu ya saka Anam haɗiye dariyarta. Suka gaidata cike da girmamawa itama tana amsa musu da kulawa cikin hausarta da bai gama nuna ba. Khaleel dake faman sinne kai ta kalla, “My son wacece a cikinsu?”.
Anam ya nuna, kansa a risine yace, “Itace wannan Mama”.
“Masha ALLAHU, ALLAH ya sanya albarka. Kace mata insha ALLAH bazai gagara ba, nima zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zan shigo dan maybe zuwa laraba mu fara, kaga zamu samu kwana goma sha bakwai kenan”.
“To shikenan insha ALLAHU zan sanar mata”.
Daga Anam har Aysha babu wanda ya fahimci inda zancen ya dosa. Sai dai ganin akan Anam ɗin ake magana ya tsaya musu a zukata. Ƙagara sukai su fita suyi tambaya. Amma sai matar ta tsaresu akan sai sunci wani abu. Su kaɗai suka ɗanci snacks. Shi dai Khaleel ruwa kawai yasha dan kunya. Ganin haka tasa budurwar nan mai suna Suhaima tai musu packaging ɗinsu dan harda gasashshen nama.
“Yaya Khaleel mufa kun samu a duhu.” Anam ta faɗa dai-dai suna shiga mota. Murmushi yayi yanama motar key, cikin basarwa yace, “Akan mi?”.
“Komai ma”.
“To kuyi addu'a ALLAH ya haskaka muku”. Daga haka yaja bakinsa yay shiru. Duk yanda sukaso jin ƙarin bayani bai basu fuska ba har suka iso gida. Kasa haƙuri Anam tayi sai da ta tambayi Mom. Kai tsaye Mom tace mata gyaran jiki na bikin amare za'ai mata dan taga duk tayi duhu. Murmushi kawai tai dan da gaske itama ta fahimci tayi duhun ko dan fitar da take kullum ne oho. Daga haka bata sake bin ta gyaran jiki ba.

*_Yau litinin_* da tai dai-dai da saura kwanaki goma sha ɗaya biki. A yau ake saka ran saukar su Mamie Nigeria sai dai Anam bata san da hakan ba. Hasalima ta tashi ne da ɗan zazzaɓi. Wajen ƙarfe sha biyu Muzzaffar yay kiranta a waya. Yanda yaji muryartane ya sashi ruɗewa yace zai zo ya kaita asibiti. Amma sai taki acewarta tasha magani. yata lallaɓata amma taƙi yarda dole ya barta dan yasan mutuniyar tasa ƴar tutsu ce. Koda sukai sallama ma sai ta kashe wayar gaba ɗaya ta gyara kwanciya. Wani barcin ne ya sake awon gaba da ita saboda maganin da Aysha ta bata tasha. Bata farka ba sai kusan uku. Alhmdllhi zazzaɓin ya sauka dan hakata samu tai wanka ta ɗanci abinci. Bayan sallar la'asar tana waje zaune ita da Aysha sai ga kiran Muzzaffar, kai tsaye ya sanar mata gashi a ƙofar gida. Murmushi kawai tai ta yanke wayar, dan zuwa yanzu kam Muzzaffar ya samu wani gurbi na musamman a zuciyarta duk da sun jima nesa da juna dan baifi kwana uku da dawowa ƙasar ba. Yau ne ya fara zuwa gidan suyi hira, dan haka sai da Aysha ta fita tayo masa iso, anan inda suke zaune da Aysha saman kujerun roba ya zauna. Aysha ta shige ciki ta kawo musa ruwa ta koma domin basu dama...
“Da alama zazzaɓin nan yaci amanar ango da yawa harfa kin rame dama gaki ba auki ba”.
Veil ɗinta taja ta ƙara rufe fuskarta tana murmushi. Shima ya murmusa cikin ƙara sanyaya murya yace, “ALLAH da gaske nake madam. Kodai aje asibiti?”.
“A'a ni naji sauƙi fa”.
“Kin tabbata?”.
Kanta ta jinjina masa. Murmushi ya sakeyi mai faɗi da shafa sajen fuskarsa. “Alhmdllhi ALLAH ya ƙara lafiya to”
“Amin ya rabbi.”
Shiru sukai na wani ɗan lokaci kafin ta saci kallonsa. Ganin ba ita yake kallo ba ta maida idanunta ƙasa ranta fal mamakinsa, dan babu rawar kan nan tasa, kuma bai kirata Beauty ba ko sau ɗaya. Murmushi yayi da gyara zamansa. “Madam nifa da magana nazo a bakina yau”.
Fuskarta ta ɗan buɗe sai dai bata kallesa ba. Ya cigaba da faɗin, “Juwairiyya gaskiya nima aure nake so”. A karan farko ta ɗago kai ta zuba masa dukan idanunta dake cikin gilashi. A hankali ya lumshe nasa ya sake buɗewa. “Wannan kallo ai sai kisa na gagara faɗar abinda ke raina”.
A yanda yay maganar ya sata sakin siririyar dariya. Hakan yayi dai-dai da buɗe gate da maigadi yayi motar Khaleel ta shigo. Su duka basu maida hankali ba, sai ma dariyar da yake tayata shima yana ɗan duban fuskarta da take kaudawa gefe, yanda yaketa ƙara ƙoƙarin son ganin fuskar tata sai yake ƙara bata dariya harta kasa dainawa....

“Alhamdulillahi lallai yau jama'ar gidan nan zasusha surprise na ganinka Yaya fiye da yanda ƴan can gidan suka sha”. Khaleel ya faɗa yana kashe motar. Bai saurari amsaba ya buɗe gefensa ya fito, zagayawa yay ya buɗe masa fuskarsa ɗauke da murmushi.
Badan glass dake rufe da idanunsa ba babu abinda zai hana aga tsantsar ɓacin ran dake cikinsu. Tuni sun kaɗa sunyi jajur, duk wani annurin dake saman fuskarsa na farin cikin dawowarsa cikin zuri'arsa ya ɓace ɓat. Cike da izzar da fushi ya haddasa ya zuro ƙafafunsa ƙasa ya fito, hakan yayi dai-dai da juyowar Anam dake shirin ɗagama Khaleel hannu.. Hannun nata da numfashinta a tare suka maƙale, ƙirjinta yay wata irin bugawa da batasan dalili ba. A hankali laɓɓanta suka motsa ta ambaci sunansa...
“Yaya Shareff”.
Duk da akan laɓɓa tai maganar hakan bai hana Muzzaffar gane sunan wa ta kira ba, juyawa yay shima a hankali. Cikin dariya Khaleel ya ɗago musu hannu da faɗin, “Surprise”.
Murmushin yaƙe ta saki, mamakinta na sake bayyana akan fuskarta, ta miƙe a hankali kamar wadda ƙwai ya fashema a ciki ta nufesu, hakan yasa shina Muzzaffar miƙewa fuskarsa da murmushi yabi bayanta..........✍




_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[10/31, 1:43 PM] +234 813 060 4664: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_31_*



.........Sai ƙarfe goma da wani abu Fadwa ta baro sashen Shareff, dan tun a daren jiya ta lallashi abunta ya sakko duk da dai yaƙi sakin fuska har yanzun. Amma da yake maza su babu ta ido wani lokacin duk da tsuke-tsuken fuskar tasa hakan bai hanashi ya biye mata ba ya sake murjeta san ransa a daren da safiya ma. Duk kewar kwanakin da sukai ba tare da juna ba sai da ya fanshe kayansa da fatan ALLAH yasa ya samar da madadin abinda ya rasa na tayin cikinsa. A gefe kuma magungunan mata da tasha su Mamah suka ɗura mata sumane suka sake susutar da shi ya kasa kauda mata ido.
       Ta samu mai-aikinta harta kammaa gyara ko'ina, almajirin ma dake zuwa ya share tsakar gidan har yayi ya gama abinsa ya tafi, dama da sassafe yake zuwa shi. Ɗan motsin da taji a kitchen ya sakata leƙawa. Mai aiki ce keta gyaran kitchen ɗin. Cikin girmamawa ta gaisheta, ta amsa mata sama-sama da tambayarta mita musu na kalaci.
       “Hajiya ai baki faɗi komi za'ayiba, shiyyasa sai na dafa shayi kawai na soya ƙwai”.
   Tsaki taja da buɗe kular da ƙwan ke ciki. Sai kuma ta juyo tana kallon mai aiki. “Wannan ai shirme ne, Soulmate bazaici ƙwai kawai ba. Ita Ayshan yau wani saban salo ne ya hanata fitowa kuyi breakfast ɗin tare?”.
        “Wlhy hajiya ban saniba, badai ta fito ba har yanzu. Itama waccan ɗin yau banga fitowarta ba”.
   Ɗan tsaki taja ta wuce store. Ta ƙwala mata kira da sauri ta sameta, “Ki soya Irish, kuma ban san shirme karki cika masa gishiri. Sai ki ɗumama farfesun jiya dabai ciba zanje nayi wanka”.
     “To hajiya”.
Fita tai batare data tanka mata ba. Itako ta bita da harara tana ƙunƙuni duk da kuwa ta girmi Fadwa nesa ba kusa ba. Shigewarta babu jimawa Aysha ta fito, kitchen ta nufa kanta tsaye mamakin da gaske Anam ta wuce gida na cinta, dan yanzu tai kiran wayarta Husnah ta ɗaga tace barci takeyi. Suka gaisa da iya cikin girmama juna.
      “Maman Abu yau duk mun makara kenan ba'ai breakfast da wuri ba ko?”.
    “A'a tun ɗazun na dafa shayi aka soya ƙwai, amma hajiya tace a sauyawa Alhaji bazaici ba”. Cikin ɗan waro ido waje Aysha tace, “Kina nufin Yaya bai karyaba har yanzu? Sha ɗaya saura fa”.
    “Eh ai yanzu hajiyar ta dawo daga wajensa ma”.     
   “Lallai ma Aunty Fadwa, shine ita bazata zauna ta haɗa masaba kuma ta bar miki. Na kula har yanzu bata gama sanin wanene Yaya ba.”
          “Maman Abu dai batace komai ba, dan ita kanta yau ta jinjina wautar Fadwa ɗin duk da tun jiya take mamaki akan duk abinda ya faru. A yanda ta santa da soyayyar Shareff tun suna gida batai zaton zatazo gidan aure tai sakaci haka ba, tunda dai komai na mace Fadwa ta iya nan kuma mahaifiyarsu (Gwaggo Halima) batai sakaciba gaskiya musamman ma akan Fadwa data kasance mace babba. Fatan dai ba raye-raye a wayar nan dake ɗauke mata hankali tazo ta cigaba dayi anan ɗin ba, dan tara ƙawayen data saba tun acan taga har anan kullum cikin zarya suke.
        Da taimakon Aysha aikin ya kammala yanda tasan Shareff zaici a kwanciyar hankali. Suka ɗiba nasu ta shirya na Shareff ɗin da Fadwa. Tana ƙoƙarin fita Fadwa ta fito cikin kwalliya sai zabga ƙamshi takeyi. Gaisheta Aysha tayi. Ta amsa cikin raba hankalinta biyu tana buɗe abincin. Da murmushi ta kalli Aysha. Aysha ta mayar mata batare da tace komai ba. “ALLAH ya kaini ran aurenki shatu. Dama inata zullumi nakai abincin nan ya gane banice nayi ba”. Ita dai Aysha dariya tayi kawai. Fadwa zata ɗauka tray ta amsa da cewa. “Bara na ɗauka sai na gaishesa daga nan”.
       A tare suka nufi sashen nasa, sun samesa a falo zaune yana waya. Aysha da tasan bai cika damuwa da zaman dining cin abinci ba sai ta dire tray ɗin saman centre table. Fadwa kam gefensa takai zaune dan haka ya ɗan kalleta idanu ƙasa-ƙasa dan kwalliya na ɗaukar hankalinsa matuƙa ga mace, Fadwa kuwa gwanace wajen iya tsarawa nan ɓangaren ta ciri tuta dan batajin ganda kamar girki da sauran ayyuka da latsa waya ke hanata nutsuwar yinsu yanda ya dace. Ya ajiye wayar daya kammala yana kallonta da ƙyau, sai kuma ya ɗauke kansa ya maida ga Aysha dake gaishesa.
       “Kin tashi lfy?”.
    “Lafiya lau Yaya, ya gajiyar tafiya?”.
“Alhmdllhi”.
Ya faɗa a taƙaice. Harta yunƙura zata tashi ya dakatar da ita. “Ku har kun karya ne?”.
      “Yanzu zanje na karya Yaya”.
Ɗan jimm yay kamar bazaice komai ba. Dan har ya ɗauke idonsa a kanta sai kuma ya sake juyowa.
“Har yanzu tana kwance ne?”.
     Ta fahimci Anam yake nufi. Dan haka ta girgiza kanta. “Tun ɗazun ta tashi ta wuce gida”.
     Fadwa da sai yanzu ta saka musu baki, tace, “Gida kuma? Rijiyar zaki wai?”.
   “Eh aunty, tana idar da sallar asuba kusan 6:30 nama zata da wasa take na shareta sai dana tashi naga da gaske ta tafi shine na kirata Husna tace min tanama barci”.
       Daɗine ya sauka har cikin ƙasan zuciyar Fadwa, ko banza shirinta na jiya yayi aiki tunda Anam ta bar mata gida a kan gaɓa. Amma saboda mazuran da yay jiya sai ta nuna rashin jin daɗinta a yanzu har hakan ya bama Aysha mamaki dan tasan dai ba shiri suke da Anam ba. Zaman nan da akai tare dan ya zama dolene kawai. Shiko mai gayya komai bai ce ba. Sai ma umarni ya bata akan ta tashi ta bashi abinci. Cikin shauƙin farin cikin tafiyar Anam ta miƙe ta fara haɗa masa tea. Aysha kuma ta miƙe ta fice ta basu waje.
     Kusan itace ma ta basa abincin a baki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login