Showing 3001 words to 6000 words out of 84091 words
duk da halin uwarsa bazaka taɓa ganinsa ya nuna banbanci akan yaran gidan ba, matan kuma yana girmama kowa yanda ya kamata duk ɗa nagari yayi........✍
KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE.
DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL
IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)
BIYU (400)
UKU (500)
HUDU (700)
KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
HAFSAT UMAR KABIR
ZENITH BANK
2270637070
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
07040727902
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09134848107
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
[10/16, 7:26 AM] Mariyamah: *_Typing📲_*
*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_04_*
..........Kallon juna sukai cikin ido, tai saurin janye nata saboda wani irin harbawa da ƙirjinta yayi......
“Please Beauty ko details ɗinki ki bani mana”. Saurayin ya faɗa a marairaice. Ai kafimma ta bashi amsa mai gayya mai aiki ya fisgi motar da ƙarfi. Da sauri saurayin ya saki murfin yana mai yin tsalle gefe dan saura kaɗan ya takashi. Sosai yanzu kam Anam ta firgita, dan har hannunsa ta riƙo batare data sani ba. Tureta yay a jikinsa tare da mika hannu ya rufo ƙofar gefen da take ɗin. Sai kawai ta fashe masa da kuka tana kiran sunan Mamie da Abie. Bai nuna yama san tanaiba, saima hankalinsa daya maida ga motar dake bin bayansu, sai da suka hau titi sosai hasken solar ya bashi damar ganin fuskar guy ɗin da suka baro ne. Lip ɗinsa ya ciza da ƙarfi yana wani fici-fici da idanunsa, sai ya koma tafiya a slow-slow harya zam saurayin ya ɗan gota su. Gefen titi ya gangara, sai da yaga saurayin na ƙoƙarin dai-daita nasa gudun danya sauka gefe titi shima saboda ganin sun tsaya sai kawai yay warming motar da wani irin karsashi ya sake harbata saman titi tamkar shikaɗaine a kansa. Tabbas da ace akwai ƙasa babu abinda zai hanashi bulama saurayin ita.
Wani irin duka saurayin ya kaima steering ɗin a ƙulle da kufcewar damar daya samu. Ya kife kansa yana furzar da huci mai zafin gaske, dan harga ALLAH yarinyar ta matuƙar tafiya da dukkan imaninsa.
Kamar yanda ya fita a fusace haka ya dawo a fusace, ko parking bai gama daidaitawaba da ƙyau ta ɓalle murfin motar ta fice da sauri. Wani irin mugun kallo yabi bayanta da shi, sai kuma ya janye yanayin ƙwafa ya kashe motar ya fito. Zaune ya sameta kusa da Abbah tana zuba surutu, dan har yanzu suna a falon suna hira. Sosai takaici ya riƙe masa maƙoshi, ya harareta yana ɗauke kai da zube ledojin hanunsa gabanta. Fuskarta ɗauke da murmushi kamar ba itace ta gama kuka a hanyaba yanzu tace, “Jazakallahu khairan Yaya Shareff”. Ta ƙare maganar da masa gwalo yanda su Abba basu luraba sai shi.
Yi yay tamkar baima gantaba duk da tsaurin idonta na bashi mamaki, sosai ƙanensa ke shakkarsa a gidan, amma sam babu irin wannan tsoron da yake gani a idon ƙanensa tattare da ita. Kai tsaye take abunta garesa, abunda ya fuskanta dukane kawai bata so, dan tun dukan da ya taɓa mata ita da Aysha ta shiga hankalinta a lokacin har tana wasan ɓuya da shi. Sallama yayma su Abie dake saka masa albarka ya fita fuskarsa ɗauke da murmushin daya saka Anam sakin baki tana kallonsa da mamaki. Dan inba Abie ɗin ba da wahala kaga murmushi a fuskarsa, kullum fuska a ɗaure kamar ɗan raka gawa....
Washe gari da ƙyar Aysha ta iya tashinta danta shirya. Haka tai wanka tanata mitar ita barci bai ishetaba. Shiri tai cikin wando da riga, sai dai anan babu maganar fita a haka duk da zafi da ranar da akeyi a Nigeria, dole ta ɗaura abaya, Sosai tayi ƙyau kamar ka saceta ka gudu. ɓata fuska taketa faman yi dan bada son ranta tasa abayar ba, sai dai yanda Mamie ta gargaɗeta ta dingayi tunda tasan kayan nata duk ba irin na sawar Nigeria ba ne. Shiyyasa ta zubo mata abayoyi kusan goma tanata mita bata kulata ba. Kasancewar akwai sanyin safiya sai bata damu da saka abayar ba sosai.
Sashen Mommy suka nufa ita da Aysha, sai dai daka kalleta kasan ba'a san ranta bane. To amma kodan Aysha da kunya tace bazataje ba. Mai aiki kawai suka samu a falon tanata aikin gyarawa, suka gaisa Anam na amsasu cike da fara'a, dan haka kawai ita dai Ladi ke birgeta. Bedroom ɗin Mommy suka nufa daga nan, bayan sallama aka basu iznin shiga. Zaune suka sameta a kujerar mirror tana murza ɗauri, ganin aysha ta rissina tana gaisheta itama saita ɗan rissina batare data yarda sun haɗa ido ba. Bata amsa na Anam ɗin ba, sai Aysha data watsama harara... “A ina kika kwana?”.
“A sashen Mom ne”.
Aysha ta bata amsa cikin ɗari-ɗari dan tasan faɗa zata sha. Aiko kamar jira Mom ta rufeta da faɗa, ta inda take shiga batanan take fitaba. Itadai Aysha haƙuri kawai take bata. A tsawace tace. “Ɓacemin da gani shashasha da bata san ciwon kanta ba”.. Kafinma aysha tai yunƙurin fitowa tuni Anam tai waje ranta fal ƙarin mamakin masifar Mommy ɗin...
Da sauri tai baya jin suna neman yin karo da mutum. Ta tura baki gaba tare da ɗan matsawa gefe saboda hararar da yake watsa mata. Yana ƙoƙarin raɓata da nufin wucewarsa tai tunanin bugeta zaiyi, kamar ƙiftawar ido yaga ta zura da gudu ta fice. Idanunsa ya ɗan lumshe tare da girgiza kansa kawai. Anan ɗin ma yana ƙoƙarin shiga ɗakin Mommy Aysha ta fito tana sharar hawaye, rissinawa tai ta gaishesa, maimakon amsa mata sai ya jeho mata tambaya idonsa kafe a kanta, “Mike damunki?”.
Kanta ta girgiza masa. “Ba komai Yaya Mom ce, dan naje sashen Mom na kwana shine taketa faman faɗa, ni kuma saboda naga Anam ne tunda nasan idan mukazo nan bazata barta ta kwana ba”. Shiru yay yana cigaba da kallonta kawai, batare da yace komaiba kuma sai ya raɓata ya wuce ɗakin Mommy ɗin.
Anam kam sai da ta tabbatar tabar sashen sannan ta ƙara kumbura baki, sashen Gwaggo ma da tun jiya batako kallaba sai da Abie ya korata sannan ta tafi fuska a haɗe kamar zatai kuka. Bata son kakar tasu dan itama tasan ba sonta take ba. Koda ta shigo sashen tsohuwar a ciccije take. Tamkar bama tasan Anam ɗin ba take kallonta, hakan yasa itama Anam ɗin tsumewa tai kamar bama wajenta tazo ba. Cikin ƙunar rai Gwaggo ta ture ƙaton kofin shayin da take sha gefe tana kallon Anam cike da tsana,
“Fitsararriya cokalin banza. K ko kunyar kanki bakijiba sai yau kike zuwa gaisheni? Da yake baki da mutunci. to in bakizoba k ai ubanki shi yazo dan uwarki”.
Shiru tai taƙi cewa komai, hakan sai ya sake tunzura Gwaggo ta fara bala'i ta inda take shiga bata nan take fita ba. Ko motsi Anam bataiba ballema tai mata gaisuwar da akace tazo tayi, sai da ta tabbatar mintunan da Abie bazai zargi komai ba sun cika sannan ta gaida Gwaggo dake yayyafa ruwan bala'i da zage mata iyaye tai ficewarta batare da ta jira amsa ba. Biyota Gwaggo tayi tana ƙwala mata kira.
“Zuwairah!! Zuwairah!! yanzu nan ni kikema wannan ɗibar albarkan? To ko ubanki ai bai isaba, ke ko kakarki ma data haifi uban naki balle ke yarin....”
“Ki cinye kanki fitinanniyar tsohuwa”. Anam ta faɗa a hankali tana ƙara sauri dan ko muryarta bata buƙatar ji. Taji daɗin samun Abie harya shiga mota, dan haka ta buɗe wuf ta shige duk da bataji daɗin yin tafiyar da wanda ta gani zai jasu ba. Sai da suka fita a gidan gaba ɗaya Abie daya lura bata gaida Shareff ɗin ba ya dubeta ta mirror.....
“Anam!”.
“Na'am Abie ”.
“Kin gaida Yayanki kuwa?”.
Ido suka haɗa da shi ta mirror, ita ta fara ɗauke nata idon ganin kallon banzar daya jefa mata. “Abie na gaishesa tun ɗazun ma ai da muka haɗu a sashen Mommy”. Idanunsa da basu gama bajewar kumburin barci ba ya sake ɗagowa ya dubeta. Itako ta ɗauke kanta cike da basarwa. Abie kam daya yarda sai kawai yay murmushi da maida hankalinsa ga lap-top ɗin dake a cinyarsa yana dubawa, ta Shareff ɗince yake nuna masa ayyukan company duk da dama can komai za'ayi yana sanar masa. Sai dai a kullum cikin ƙara bashi wuƙa da nama yake da nuna masa duk yanda yayi dai-dai ne kawai. Koda suka iso inda zatai daidaita komai daya shafi hidimar ƙasar nata bata yarda tako kalla Ya Shareff ba, shima bai shiga sabgartaba dan koba komai yana jin nauyin Abie sannan shi sam baya wasa da yara dama can, itacema kawai za'ace ta ciri tuta a wajensa tana ƙarama.
Komai da taimakonsa shi da Abie ya kammalu, basu sami nutsuwa ba sai kusan azhar. Maimakon gida sai suka wuce company. Tunda akai
Companyn Anam batazo Nigeria ba, dan haka ta ɗan nutsu a kallon tsarin wajen da yanda ma'aikata keta kaikawo na daidaita kansu tun shigowar motar tasa. Koda suka fitoma sai gaisuwa ake miƙa musu cike da girmamawa da mutuntawa har suka isa katafare kuma haɗaɗɗen office da yaji komai na more rayuwa da saka nutsuwa ga mazaunin cikinta. Abayar jikinta ta shiga ƙoƙarin cirewa. “Wayyo Abie zafi”.
Yanda tai maganar ya sashi ɗan juyowa ya dubeta, ai da sauri ya ɗauke kansa ganin kayan dake a jikinta. Wando ne dayay matuƙar fidda surar jikinta da ƴar riga da itama bata ɓoye komai ba. Sun mata ƙyau sosai kuma dai-dai da halittarta ta masu ƙaramin jiki. Har veil ɗin data naɗa bata bari ba sai da ta yaye, ɗaurarren gashinta da yasha gyara ya bayyana, sai dai tuna gargaɗin Mamie yasata warware veil ɗin duk da ba wani girmane da shiba sosai taɗan yafa tana duban sashen da yake....
“Yaya Shareff Please kasa ac zafi”. Tayi maganar ne tamkar zata fasa kuka, dan da gaske zafine ya taso mata lokaci guda, har wani dimm kanta ke mata. Ta ƙasan ido ya harareta, sai dai baice komaiba ya ɗauka remote ɗin ac dake a desk ɗin office ɗin nasa ya kunna ɗin. Ajiyar zuciya ta sauke cike da jin daɗin jin yanda sanyin ya wani buso mata da faɗin, “Alhmdllhi, Abie ALLAH da kamar ana dafamin fatar jikina fa”.
Ƴar dariya Abie yay yana mai girgiza kansa da kallon Shareff dake ƙoƙarin buɗe wajen da yake gudanar da duk ayyukansa na zane. Babu mai shiga wajen sai shi kaɗai, sai ko Fharhan da Khaleel da yakan bama dama a wasu lokutan su kuma Engineers ne, dan company ɗin nasu aikinsa kenan, mai buƙatar zane amasa, idan da gini duk a haɗa, kai dai kawai ka ajiye kuɗi ne kaga biyan buƙata.
“Babana kaji fa wani shirme, dama zafi na dafa fata ne?”.
Murmushi ya ɗanyi cikin sanyin muryarsa da shafa kansa yace, “Abie akwai zafinne ai”.
“Oh ka goya bayanta kenan dai kawai”.
Murmushi ya sake saki mai faɗi fiye dana ɗazun. Sai dai baice komaiba, saima ɗan hararan Anam data saki baki tana kallonsa ganin murmushi a fuskarsa yayi. Itako ko gezau kallonsa take kamar ta samu hoton bango. Fuska ya ɗan tsuke da ɗauke kansa daga saitinta. Itama sai ta janye tana taɓe baki.
Tare da Abie suka shiga, yayinda gaba ɗaya hankalin Anam ke ga littafin data ɗauka mai tambarin company ɗin nasu da alama samples ɗin ayyukan sune a wajen. Koda taji shigewar tasu bata maida hankali kansu ba, ta jima tana kalle-kalle, wasu su birgeta wasu ta taɓe baki harta fara hamma. Sai kawai ta zame ta kwanta a kujerar.........✍
KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE.
DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL
IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)
BIYU (400)
UKU (500)
HUDU (700)
KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
HAFSAT UMAR KABIR
ZENITH BANK
2270637070
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
07040727902
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09134848107
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽
[10/16, 7:26 AM] Mariyamah: *_Typing📲_*
*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_02_*
.........Alhaji Mustapha Ɗaher wanda akafi sani da (MD Shareff) shine asalin mai gidan. Tsohon soja ne dan kuwa suna sahun farko na sojojin da sukaima ƙasar Nigeria hidima tun a farkon ƙarni. Matansa uku. Uwargida Hannatu bata taɓa haihuwa ba har yanzu da tsufa ya risketa, sai dai ta riƙe ɗan matarsa ta biyu tamkar itace ta haifesa saboda zaman lafiya da sukai baka taɓa cewa kishiyoyine ba. Matarsa ta biyu itace Hajarah haihuwarta huɗu da shi. Muhammad shine babba wanda tun bayan yayensa ya koma hanun Hannatu da suke kira da (Gwaggo). Sai Halimatu itace ta biyu, sai Abubakar, sai auta Umar. Sai kuma amarya Juwairiyya nada biyu. Usman da Maryam. Rayuwar gidan MD Shareff rayuwace bahaguwa, dan kuwa dai Uwargidansa da matarsa ta tsakkiya kansu a haɗe yake, bazaka taɓa ganinsu ka ɗauka kishiyoyi bane. Amma Amaryarsa Juwairiyya a ware take a cikinsu, dan kuwa sam batajin daɗin zama da su sai ma ɗan karen azaba da ta dinga fuskanta daga garesu kasancewarta kurmiya. Juwairiyya nada matuƙar haƙuri da kawaici, duk da wahalar da take sha a hanun kishiyiyinta bata taɓa ko nunawaba a fuska balle ga wani sai dai idanunka ya gane maka. MD Shareff yayi iya bakin ƙoƙarinsa na ganin matansa biyu sun daina gallaza rayuwar amaryarsa amma hakan bai faruba har yabar duniya ya barta da sabuwar gwagwarmayar rayuwa a cikinsu.
Duk da tsana da tsangwama da su Gwaggo kema Juwairiyya da ware ƴaƴanta hakan bai hana yaran gidan tashi da ƙaunar juna ba, sai dai kuma Halimatu ta fita zakka a cikinsu, dan akwai shegen baƙin hali, sam bata yarda Maryam ta raɓeta duk da itace kanwarta mace tilo. Ahaka dai aka gungura har yara suka tasa Juwairiyya bata huta ba, ga shi babu miji, ƴan uwanta kuma sunƙi janta a jiki balle ta koma garesu taji sanyi, wanda ke ɗan tausaya matan yana ƙasar Malaysia yana karatun daya samu tafiya ta hanyar scholarship. Shima yayantane dan shi take bimawa. Haka tacigaba da haƙuri har ALLAH ya kawo Yayanta ƙasar Nigeria ganin gida tare da matar da yake aure wadda ya aura acan ƙasar Malaysia ɗin, amma ƴar Nigeria ce karatu take a hanun yayanta acan. Kowa ya nuna ƙin matar tasa itako ta nuna soyayyarta gareta dan bataga aibunta ba tunda musulma ce. Daɗin abinda tayi yasa Yayan nata da matarsa shiga suka fita wajen ɗauke mata Usman dake gab da kammala secondary school. Ita kuma ya saya mata gida tabar cikin su Gwaggo.
Wannan abu ya musu matuƙar ciwo, dan ƙiri-ƙiri suka nuna ƙiyayyarsu da kishinsu akan hakan, tare da dagewa wajen cusa tsanar Usman da Maryam a zuciyar sauran ƴaƴansu, ita dai tai musu sallama harda kukan sabon zama ta ɗauka diyarta Maryam da Usman ke kira Mimi suka koma sabon gidansu.
Rayuwa ta shuɗa, komai ya canja yara duk sun girma. Tafiya da Usman yasa Gwaggo da Mama jajircewa wajen ganin su Muhammad sunyi karatu mai zurfi dan kar Usman yafi ƴaƴansu. Sai dai shi UBANGIJI ba'ai masa dole, dan kuwa shike bama wanda yaso a kuma lokacin da yaso. Sun sami nasara sosai ta rayuwa saboda zukatansu cike suke da son ganin ɗan uwansu bai zartasu ba kamar yanda iyayensu kullum ke kwaɗaita musu, dan zuwa yanzu da gaske ƙiyayyar Usaman da nuna masa ƴan ubanci tai tasiri a zukatansu saboda huɗubar mahaifiyarsu da abokiyar zamanta. Sun buge gidansu na gado kasancewar babba ne sosai tare da siyen na maƙwafta dake son tashi suka ware ma Usman da Maryam nasu gefe su suka gina nasu a tare su huɗu tare da kason ƴar uwarsu Halima da tuni tayi aure, koda Usman yazo Nigeria yaga ɗan abinda aka rage musu baice komaiba, saima ƙoƙarin ganin ya samu kusanci da shaƙuwa da ƴan uwansa yake kamar da. Hakan bata samu ba, dan babu abinda suke masa sai ɗagawa da fariyyar sunada kuɗi yanzu, koda aka kaisa turai bai fisu da komai ba. Murmushi kawai yayi, dan al-amarin nasu yanzu dariya kawai yake bashi. Watansa kusan uku a Nigeria ya tattara mahaifiyarsa da ƙanwarsa Mimi suka wuce Malaysia, wannan ma ya sake ɗaga hankalin su Gwaggo, suka cigaba da tunzura su Muhammad.
Tsahon shekara huɗu bai sake waiwayarsu ba sai da aurensa da ɗiyar kawunsa tilo da suka haifa ya tashi, dan kawun nasa da matarsa mai suna Asiya haihuwarsu ɗaya mace Aysha Humaira, shaƙuwar dake tsakanin Usman da Humaira ta ɓaci dan kusan shine yay rainonta, Hakan yasa soyayya mai tsanani shiga tsakaninsu. A Nigeria sukazo akai bikin duk da ƴan uwansa nata masa wulaƙanci, shidai baibi takansu ba sai fatan shiriya yake musu.
Haka rayuwa ta cigaba da shuɗawa shi da Humaira ALLAH bai basu haihuwa da wuriba har ALLAH yayma mahaifiyarsu Juwairiyya da Asiya rasuwa a ƙasar