Showing 27001 words to 30000 words out of 41517 words
ga
dangin Inna ta wadanda su ma masu yawa ne babu laifi
ga gaiyar yaya Dija na kawaye da dangin mijinta masu
kara nan gidan su Mubarak ma ba a magana uwargida
kuwa kai kace tamkar da gadara yan uwanta suka zo
don su nuna su din masu yawa ne.
A wancan lokacina marya 6oye kanta take yis aboda
k unya da kawaici ba kamar yanzu ba da amarya ke kai
kawo a tsakanin yan bikinta sai dai hakan abi hanani
tsala ado, wuni nayi ina kwalliya ta burgewa kwalliya
108
kuma mai tsada da kowacce nayi sai kaga kamar kar in
cireta saboda ina tare da gwanayen kwalliyar irinsu
malama Hindu da malama Basma ga uma anti Asiya
wacce ita dama babbar sana'arta kenan gyaran amare ciki
da waje, in nace ciki da waje kema sai ki gane abinda
nake nufi.
A gaba daya sashinmu a wancan lokacin bakina ne
bikin farko da mutanen mu suka sheda video coverage
ana daukar su ana kuma yi musu tambayoyi, me zaku ce
game da wannan aure na Alhaji Mubarak da amaryarshi
Maryam? Wasu su yi magana wasu kuwa kunya da
rashin sabo ya hanasu cewa komai in banda kyalkyalewa
da dariya wasu kuwa da abin yayi matukar burgesu duk
da sun kasa cewa komai fadi sukeyí yau ku zo ku gani
bin mutnae akeyi ana yi musu tambayoyi da irin abin nan
na masu rahoto.
Malama Basma itace tayi magana ta ilimi har ta samu
jan hankulan mutane gaba daya aka koma sauraron
bayanin nata tayi magana ne a kan matsayin aure da
kuma' menene kishi a musulunci, tayi magana sosai ta
kuma karfafa magangnaun nata da ayoyi da hadisai tare
da kawo misalai na manyan mata magabata yanda suka
tafiyar da rayuwarsu tsakaninsu da mazajensu da kuma
kishiyoyin nasu duk da ba wai basa kishin bane ya sa
suka yi hakan a'a sai dai su fahimtarsu a kan kishin
daban mu ma a yau tamu fahimtar daban.
Da ta kawo karshen jawabin nata sai tace ya ku yan
uwanam ata ina kira garemu da mu yi gyara a kan yandaa
muke tafiyar da al'amuran da suka danganci kishinmu a
yau mu daina kishi na jahilci kishi na rashin sanin ya
109
kamata mu koma yin kishi irin na shari'a wanda shi ne
ibada.
Wassalamu alaikum wa rahamatullah, gaba daya
wuri ya kaure da kabbara malama Ubangiji ya saka miki
da alheri abinda kowa ke fadi kenan.
Ana gama wannan aka shiga yin hotuna wai duk
ribibin da kaeyi nayin hotuna da amarya ita Rumasa'u da
kyar ta yarda aka yi mana hoto guda daya ni da ita da
aka kawoni dakinta kuwa kamar yanda aka saba bisa
al'ada na kai amarya wurin iyayen miji da uwargidanta
in har tana da ita yan uwanta basu ji kunyar fadin babu
wata amana tsakanina da ita ba tundai ta din ba wan
girmana tayi ba banda haka kuma ai banbancin dake
tsakainta da ni kadan ne iyaka ita tana ciki ne ni ina waje
ba manyan dattawan da suka kaini ba wadanda
shekarunsu suka kai fassara musu al'ar ari ko da kuwa
da kafa ka iadeshi ba da baki ba ko ni da nake lullube a
gabansu na gane abinda suke uui, to balle kuma su a
haka muka tashi muka fito aka dawo da ni dakina tunda
dama sai d aka kaini wurin Umma kafin a kawo ni
wurinsu mun dawo' daki nuka ci gaba da harkokinmu sai
a wata yar uwarta ta shigo wai ga kudin sayen bakina
marya an manta ba a bayar ba, anti Astya ta ce, aki haba
a1 babu komai mayar masu kawai, ita wannan amaryar ai
ba sai an sayi hakinta ba.
Ana cikin haka aka soma rade-radin ango ya dawo
ango ya dawo kan kace meye wannan har labarin ya bazu
ko ina ango ya dawo, ai kuwa dai dama na san da kyar
ace bai dawo ba yau, kai wannan ango da zumudi yake,
maganganun mutnae daban-daban ne wannan.
110
Kan kace meye wannan sai na jiwo muryar tsiyaku a
falo yana gaida jama'a, wani abu kake so ne suna
tambayarshi ya ce a'a yalla6ai ne ya ce in shigo in gani
in mutane sun danyi sauki ya shigo, ata mai iya shege ta
ce mishi, jeka ka gaya mishi bamu yi sauki ba muna nan
cike a wurin. Gaba daya suka kwashe da dariya suna
fadin, ke dai baki da dama, ita kuwa tana dariyar tana
fadin, a'a to haka kawai da rana tsaka ba zai jira abokai
su kawoshi ba? Ba fa saurayi bane ta ce, eh ko ba saurayi
bane ba zai shigo yanzu ba.
Wajen karfe hudu da rabi aka soma walimar maza a
masalacin unguwarmu wanda dama yafi kusa da gidan
Alhaji Muhammadun don shi ya gina shi walima sosai
aka shirya don saniya sukutum aka yanka dominta banda
ciye-ciye da abubuwan sha iri-iri malamai kuma daga
wurare daban-daban aka gaiyatosu.
e Ana cikin haka Isiyaku ya sake shigowa falon, wai
ina anti Asiya, tayi maza ta ce mishi gani nan, wai ince
miki in babu matsala yana so ya shigo.
Ta ce, to to kaje ka ce mishi ya danyi min hakuri
kadan, Isiyaku yana fita ta mkie tace, kai jama'a
surukuta fa ba wasa bane bikin nan ai munyi shi mu dan
ragu mu koa gidan Hadiza, wasu suka ce ka nufi gidanka
ma kai ai yamma ta riga tayi, a can gefe kuma wasu suna
Rorafin wane irin rashin hakuri ne wannan ko bai yi
hakan ba ai za a tafi a bashi wuri.
Isiyaku ya sake shigowa, anti wai gashi duk wacce
zata tafi a bata atamfofi ne wadanda akayi don bakin,
hoton ango da anmarya ne a jiki da hakan ya kashe bakin
mitar da suka soma yi mishi nan da nan aka shiga rabo,
111
bayar kowacce ta karba sai ta wuce ta tafi tana murna da
godiya da fatan karin budi haka a dawo suna ana facin
amin amin, kafin karfe shidan yamam sai ya zama babu
kowa daga ni sai Hasiya Jibrin sai ko ita anti Asiyan
saboda suna kokarin ganin komai yayi tsaf, a haka kuwa
Mubarak ya shigo ina jin gaisuwar da ya tsaya yi da su
nayi maza na jawo gyalena na lullube kaina, yana
shigowa bai tsaya yin komai ba ya durkusa a gabana ya
sa hannu biyu ya yaye lullubin gyalen nawa ya sake sa
hannunshi na dama ya ture dankwalin dake kaina kafin
ya sake sa hannun nashi ya damki gashin da ke gaban
goshina ya iike amma ba damka mai karfi ba, addu'o'i
yayi ta karartawa sai da ya gama ya tofa min a fuskata
sannan ya mike ya fita, yana fita anti Asiya ta shigo tayi
min sallam ta tafi sai muka zama dagı ni sai Hasiya
Jibrin mai ji an mijinta ya zo daukarta ita ce ta kara gara
min komai ko ina ya zama sai kamshi yake yi
kasancewar ilama ta samu wata a gida su ma kuma suna
fafatawa ya a iayi te hapi shawarwarin da take ganin
tamkar za su yi min amtsni na ce kai ai dai Hasiya nafi
son zaman lafiya a kan rikicin nan ni yanzu ba na son
bacin rai na ri za na gaji da shi, ta ce to ai bashi da dadi ni
su din ne gadara ne da su sai su rinka fadin mai mazansu
aka aura, nayi daríya kawai bance mata komai ba. to
Kafin a yi sallar magariba shigowar ango biyu shi ne
ma ya bada mtoar da ta maida Hasiyan gida tare kuma da
yi mata alheri.
Yana idar da salar magariba ya sake shigowa, kin yi
salla ne? Yana daga tsaye ya yi mint ambayar na ce
112
mishi eh, ya ce to bari in koma wajen wa'azin nan kar su
Abdulhamid su sani a gaba don ba wani kirki ne da su ba
ga sa ido, na yi murmushi na ce mishi to, amma ai kin
san in anyi sallar ish'ai zamu shigo tare da su ko, zasu
rakoni sayen bakin amarya, ban ce mishi komai ba ya
sake juyawa ya fita, ni da kaina tunani nake yi cikin
zuciyata ina tambayar kaina kot a ina yake biyowa yake
wannan zirga-zirgar oho?
Ko da yake Mubarak bai bar kawaen da na zo da su
daga Gaidan sunz auna ba sai ya ce aje da su in gari ya
waye zaije ya yi sallama da bakin gaba daya zai hada har
da su ni kadai din sai nayi shiri na tunda ashekaru baya
can na taba yin kawancen su Jumare su Hasiya Jibrin, na
kara gyara kaina ko da dai dama akwai kwalliya mai
kyau nake wacce kuma ban dade da yinta ba ga kuma
kanshi mai dadi a tare da ni.
Ina jin sanda suka shigo falon saboda sallamar da
suka yi sai dai ban yi musu amsawar da zasu ji ba daga
falon suka zauna a kan kujerun dake wurin, to ina
amaryar take? Kai Alhaji Ahmad to ka kori 'yan matan
amarya yaya za a yi a sayi bakin amaryar? Maimakon ka
barsu in munzo mu maidasu? Ai sai ka fito mana da ita.
Mubarak ya leko dakin da nake a takure cikin lullu6i
zo ki basu ko ruwa ne Maryam in kuma da wani abu ki
hado musu, ban yi musu ba na tashi na shiga kicin na
shirya musu 'ya'yan itace a plate daya sai da na cikasu
da nau'o'insu kala daban-daban sannan na cika wani
plate din da kayan tsarabar amarya na zuba soyayyan
naman rago da yaya Dija ta sa a kawomin a wani plate
din na hadasu kan wani madaidaicin tirem ai kyau na
113
kawo musu, maimakon in yi shiru kawai in ajiye musu
sai na manta na kara gaishesu, Mubarak ya ce, shi kenan
ta hutar da ku sayen baki, Abdulhamid ya ce, a'a a'a kai
kayi mata wayo ka korar mata kawaye ka kuma sanyata
aikin da yayi dalilin da ta yi magana don haka ga kayan
sayen balkinta nan turarurruka ne akwati guda muka
kawo mata ta yi ta fesawa tana yin kanshi.
Sunkuyar da kaina kasa nayi nayi shiru tare da kasa
rufe fuskata da gyalen dake hannuna saboda kunya,
Ubangiji ya zaunar da wannan aure naku lafiya Maryam
ya kuma sanya albarka mai yawa a rayuwarku, gaba
dayan maganar Amiru kenan yayin da Abdulhamid ke
fadin, amin amin.
Kawo ledoji in akwai ki juye musu kayan su je da shi
can, ban yi magana ba na tashi naje na kawo ya juye
musu suka yi min addu'a suka tafi, shima ya bi bayansu
don rakiya da kuma zama wurin wa'azin da akeyi, ina jin
duk karatunad akeyi har aka kai ga gamawa malamai
suka yi addu'o'i ga kasa, jama'ar kasar, al'umarm
usulmi da kuma ango da amarya, ina jin hakan na
tabbatar ya kusa shigowa don haka nayi maza na jawo
gyalena na kudundune a kasa na rufu da shi na daddanne
ko ina ina jinshi ya shigo yanakiran sunana Maryam,
Maryam, to wai-ke ya ce miki amarya tana yin bacci ne
tun kafin angonta ya shigo, ban motsa ba shima bai
tsananta ba sai ya juya ya fita, motsin ruwan da naji ya saa
na gane wanka yake yi, ya sake shigowa dakin Maryam,
sau daya kawai ya kira sunan nawa sai kawai ya sunkuya
ya sa hannu biyu ya sureni ya nufi falo da ni, ke ance
miki amarya irin ki tana da wani lokaci ne na yin bacci a
114
darenta na farko? Muje ki biyamin karatunki in ji,
doguwar kujera ya nufa ya zauna ya mike kafarshi guda
daya a kanta ya zunar da ni a kan cinyarshi ya sake
dauko daya kafar tashi ya dora a jikina nayi matukar
takura da hakan da ya yi min saboda kunya da rashin
sabo bana zaton a tsawon dadewar da nayi da shi ya taba
taba jikina da nufin shi in dai ba a kan wani dalili mai
karfi ba shima a wancan lokacin ne nan baya ba a
wannan karon ba, a yau din kuma da ya dorani a hakan
rigar baccin da ke jikinshi mai igiyoyi ce ko tsayawa
daureta bai yi ba sai dan gajeran wando kirjinshi gaba
daya a bude yake har zuwa kan cibiyarshi hannu biyu na
saka na rufe fuskata yayin da jikina ke ta faman bari.
sWai ina kike kokarin zuwa ne? Da kike mutsu
mutsun kwacewa, ya sa hannayenshi duka biyu ya cire
nawa da na rufe fuskata da su ban yarda na bude ido ba
balle in ga yanayin da yake ciki sai kawai naji ya dora
bakinshi a kan nawa, gaba daya ya kidimani ya sanyani
na shiga wani hali da ban ma san yanda zanyi in
kwatantashi ba sai dai kuma nasan babu mamaki ya samu
kanshi a yanayin da ya wuce wannan don sau biyu zuwa
uku yana cewa me za ki ci Maryam, ga abubuwanci na
kawo mkiki kin san bai kamataki kwanta baki ci komai
ba, sai dai ya kasa sakina balle in iya ganin abin da yake
cewa ya zo da shi din bale har in iya samun zarafin da na
iya kai wani abin bakina, yanda ya fito da ni falon
adauke haka ya mike ya sake maidani dakin a dauke ya
dorani a kan shimfidar,a jiyar da na bari wurinki za ki
bani, kyautarda kika dade da yi min nake so in karba a
yau, a kankame nake a jikinshi yake wadannan kalaman
115
ina jinshi ban tanka ba ban kuma motsa daga yanayin da
nake ciki ba sai na ji shi ya soma cewa.
Yi min wani alheri guda daya mana Maryao so nake
ki martaba min irin martabawar da kika yi min a wancan
ranar da wancan lokacin tashi ki sa hannuki rage min
wadannan kayan na jikinki da kanki karki barni ki ce sai
dai ni inyi yi min wannan alfarmar don in kara jind adi in
kara farinciki zuciyata ta kara gamsuwa kuzarina kuma
ya karu saboda na san zan karbi ajiyar tawa ne in. karbi
kyautar tawa cikin yarda da gamsuwa da amincewarki ba
tilastaki zanyi ba.
Yana gama fadin hakan na mike na zauna na sa
hannu na soma cire kayan da ke jikina da kaina yana
karbar su yana yin jifa da su ba tare da yana lura da inda
suke tafiya ba, sannu a hankali har na cire duk wani abin
da nake sanye da shi saura rigar nono na maida
hannayena baya da nufin in balleta itama kowa ya huta,
sai naji ya ce min uh'uh Maryam bar min wannan in
karasata da kaina, ai ko a wancan ban barki kin cire ta
ba, yana daga kwancen ya miko hannayenshi ya balleta
itama ya yi wurgi da ita komai naki yana nan tsaf
Maryam kamar yanda na fara ganinshi sai dai ma kyau
da kwarjini da suka kara.
Zai yi wuya rannan in har akwai wani wuri a jikina
rannan da Mubarak bai yi mishi irin abinda yake ganin
shi ne ya kamaceshi ba saboda wani irin yanayi da ya
samu kanshi a ciki na kidima tamkar dai ace bai taba
sanin wata mace a tube a gabanshi ba tsawon rayuwarshi
sai a wannan ranar.
116
Gyara ki ji dan tsaya ki ji abinda zan gaya mia
taimakeni ki karantamin wannan addu'ar don mu
karantata tare da ke.... ya soma karantota ni kuma nayi
maza na sake maida tafukan hannuna a kan fuskata na
rufe saboda tsananin kunya da nauyin da ambatonta a
bakina ya yi min, sai dai nayi dabara na karantata cikin zuciyata...
Waiyo Maryam, waiyo Maryamu, Wayyo Mairona,
bani da nake wahala da hakuri da juriya a dalilin shi ce
nake furta kalmomin ba shi da yake yin yanda yake so ne
kuma yake furta kalmomin da yake so ban iya ce mishi komai ba...
Nace in sonki Maryam nace ina sonki kin ji abinda
na fada ko ba ki ji ba? Ba dai ke burinki ince ina sonki
ba? To sau nawa yau kike jina ina furta miki wannan
kalmar? Maganar yake yi cikin yanayi na jaruntaka
saboda gajiyar da ke tare da' shi da dai ace so shi ne samu
da shiru ya yi ya yi baccinshi don jikinshi ya samu
hutund a yake bukata, ni kuwa ina jinshi bance mishi yi
shiru ka huta ba saboda gani nake nima tamkar bai yiwa
nawa jikin irin adalcin da ya dace ya yi mishi ba.
Washegari da safe ni kan farkawa nayi a makare
saboda bude ido nayi na kalli agogo hannunshi dana gani
kusa da ni na ga karfe shida ne har da mintoci guda biyar
na mike na shiga bandaki nayi wanka sosai na yiwa
jikina duk wani abinda nake ganin zai taimake shi nayi
alwala na fito ina cikin yin salla ne na ganshi ya shigo
dakin ya koma gefen gado ya zauna sai da na idar na
shafa addu'ar da nayi sannan ya mika hannu ya sake
kamoni ya dorani a kan cinyarshi kamar yanda yayi min
117
Jita, saukin abin kawai babu irin mas'alolin jiyaa tare da
shi banda haka kuma a yanzu yana sanye da sabuwar
jallabiya ne da ta saukar mishi har idon sawunshi.
Kin yi min addu'a kuwa? Na gyada kai a hankali
nuna alamar eh, don kuwa ban tashi a wurin ba sai da na
yi mishi, ya ji dadin amsar da na bashin, cikin natsuwa
ya ce min addu'o'i masu yawa nayi miki Maryam na
kuma yiwa Inna. Muka dan yi shiru kafin ya kawar da
shirunda tambayata me kike so ki ci yanzu nasan kina jin
yunwa musamman ma da yake kin kwanta ba ki ci komai
ba, ban yarda mun hada ido ba na ce mishi nafi so in yi bacci.
Ya yi maza ya mike na kwanta ya tayani gyara
kwanciyar sai da na ce mishi ya yi sannan ya fita ya ja
kofar dakin wai don in kara samun nutsuwa.
Na farka ne ina tunanin lalle nayi bacci saboda yanda
naji yanayin jikina ya canza ban dade da farkawa ba na
soma jiwo muryar Mubarak a falo yana magana da wata
da nake zaton Umminshi ce.
To ko Maryam ce kadai a gidan yau kam ai ab za ta
yi girk ba, 8in ta ga dama tayi in bata gani ba ta bari duk
abinda take ganin kamar in tayi ita ta yiwa ta bari ba ita
na yiwa aurena ba.
Ban ji maganar Umman ba saboda muryarta ba mai
karfi ba ce kamar tashi sai na ji shi yana cewa, eh Umma
dukansu nawa ne na kuma yi alkawarin yin adalci a
tsakaninsu, to amma yana daga cikin adalcin ne ace don
na kwana a dakina marya jiya ace yau ta fito ta yiwa
mutanen gida girki? Banji abinda tace ba na sake jinshi
ya ce, a'a Umma ku yi hakuri kar ku roketa na gaji da
118
rokon da ake yi mata in dai alfarmar yiwa Maryam girki
ne kar ta yi bana so.
Assalanmu alaikum, wata sassanyar murya ce na ji
tayi sallama na kuma ji dadi saboda na gane mai ita, a'a
Ramatu ce Umman ce ta fadi hakan ta amsa eh ta soma
gaisheta kafin naji tana cewa Mubarak sannu kawu, ya
amsa tare da amsa gaisuwar da take yi mishi, yaya su
babanki da antin, tace sunce a gaisheku.
Ban san me ya gani ba naji yana ce mata, ai tana
bacci ne, cikin ladabi ta ce msihi ba dakin zan shiga ba
zan shiga kicin ne in ajiye kayan da nazo da shi ya ce
mata to.
Tana shiga kicin din naji motsin ruwa ya fara zuba a
fanfo na tabbatar zata gyara wurin ne tayi wanke wanke,
Inna yarinya ce da yaya Dija ta yiwa tarbiya iyawar
iyawarta aka kuma yi dace ita din mai daukar tarbiyya ce.
Tashi nayi na shiga bandaki na sake watsa ruwa a
jikina an fito na zauna nayi shafa nayi kwalliya da wani
lallausan