Showing 3001 words to 6000 words out of 41517 words

Chapter 2 - Halin Rayuwa Book 4 Hausa Novel Complete

Sodangi   

28 Jan 2025

244

natsuwa ya ce min "To, tunda
haka ne Mero, in rinka kwana a zauren gidan nan
mana kawai, ai shima wani babban dalki ne, in na rufe
kofar waje na rufe ta ciki ba shi kenan ba?"
Nayi maza na ce "Kwarai kuwa Sallau, to ai ma shi
kenan tunda ka samarwa kenka wata dabara. "
A haka al'amura suka ci gaba har na kai ga fita
daga dakina na koma na Sallau na kira mai gyara ya y
wa dakin gyaran da ya dace kafin mai fenti ya zo ya yi.
Ita bata yi tunanin ba dom a ranar da ake aikin ma
wuni tayi tana fadin, To tunda babu tsayayyen da zai
tsaya ya kwasa ya kai gidanshi, can inda ake ta harin
kuma uwar yarinya taja tayi damara ba dai a shiga ba,
sai dai a kare a titi.

16

Ai sai kiyi ta gyara kina fenti don ki ji dadin zama
tunda ba ki da ranar tashi." Ban kalleta ba ma balle
tasan naji abinda take fadi.
Da daddare ma da Babana ya dawo naji shi yana
tambayarta ni ina butar nan ne? Sai naji ta ce mishi, Ni
fa Mallam na wanke butocina na tura su a Rarkashin
gado, don na fara gajiya da wannan auren na zuba
ruwa a buta.
Kai baka da wani aiki sai na a baka ruwa a buta,
don haka rinka yi da na roba kawai ga su nan a bakin
famfo suma a wanke suke nayi maza na tashi na fito na
ba shi butar da nake amfani da ita, na koma dakina can ciki na zauna.
Ina jin ta tana cewa, To, ni in ban da na san in ta
kasance a kanka dolensu su bani ciki da falon da nake
ciki zan yi wannan susutaccen zaman ne? To dadin
abin duk tsiyarsu su din mata ne, mata kuma ba wani
Rarfi ne da su ba da dai suna da namiji a cikinsu ne ai
da anga tsiya to babu shi."
Ranar Laraba da sassafe bayan an idar da sallar
Asuba aka daura auren Babana da amaryarshi Safara a
Masallacin unguwar su Baba Baidu ne yaje ya karbar
mishi auren.
Yana dawowa daga daurin auren Baba Sumaye ta
rinka rangada guda tana fadin, "Kai, wannan ya da
jaruntaka take, to ashe ma tana da irin wannan kokarin
ta bar ubanta yayi ta rayuwa a cikin wannan fitinar?
Ubangiji ka yi wa Hadiza albarka."
17

Da yake Baba Lantana bata tunanin koma1 game da
Babana musamman kuma da yake tasan mu'amalah
tayi matukar ja baya tsakaninshi da Baba Baidu balle
iyalinshi, bata kawowa ranta komai ba sai kawai ta
rinka jan tsaki tana fadin "Munafukan unguwa, ko ina
ta samo wata Hadiza kuma oho."
Sai tayi maza ta sake jan wani tsakin don ta tsani
Baba Sumaye, ta tsani kuma ta jiwo muryarta tana
wata magana sai tayi tsaki tayi ashar ko ta ce
munafukan unguwa.
Tsohuwar aminiyar aminiyarta Delu, ita ce tayi
sallama ta shigo gidan, rabon da in ganta kuwa an dan
kwana da yawa, ina jin tun lokacin da ta shirya aurena
da surukinta Alhaji Muhammadu Nalami, ta gaiyaci
tsofaffin abokai don su tayata sheda isowar ta da
mallakarta shekaru hudu kenan da suka wuce.
Delu ce yau a gidan? Tayi mata tambayar cikin
wani irin yanayi na wulakanci da shirin tozartawa,
"Kun gama zagaye-zagayen gulmarmakun naku ne
kuma ki ka gaji ki ka zo wurina? To ai babu abinda
bana ji, duk maganganun da ku ke fada suna dawo
min, musamman ma ke.
Tunda ke kam ai butuluci ne yake sa ki fadar
magana a kaina, ko ma menene a tsakanina da Nalami
ai aure ne tsakaninsu da Asabe ga shi nan kuma tana
zaune tana ta haihuwa 'ya'yanta. Delu tayi murmushi
ta ce, tana ta yawo dai wannan haihuwar tata ta ukun
ina ce-a unguwa ta yi ta? Ko menene ba a sani ba?
18

Ita. kam Asabe ai abin tausayi ce ita don kuwa
mugun abin ki ne ya shafeta, ni tausayinta nake ji
tunda ko jiya tazo wurina."
Bakin Baba Lantana ya dan rusuna a dalilin cewar
da Delu tayi ko jiya Asabe taje wurin ta watakila taso
1ne yanda ta yanke ta share tsofaffin aminan nata, itama yar tata tayi haka.
Delu tayi amfani da damar da ta samu na shirun da
Baba Lantana tayi ta ce mata "Kinga ni fa ba fada ma
ya kawo ni wurinki ba, zuwa nayi in ji dalilin da yasa
hidima irin wannan ta taso miki, ba ki neme mu ba.
Cikin natsuwa Baba Lantana ta tambaye ta hidimar
me kuma nake yi yanzu in banda ta fama da tsohon
mijin da bai iya hassala komai.
Delu ta ce, Kai haba bai iya hassala komai aka
daura mishi aure? Ko kuwa dai don ya yi aurenne yasa
ki ke fadin haka akan shi don ki bata shi?
"Aure?" Tayi tambayar a wani irin yanayi, "Wane
aure kuma? Wace mata ce zata yarda ta auri Mallam a
yanda yake din nan?"
Baba Sumaye da ke cikin gidanta tana jiwo hirar
tasu, kasancewar a tsakar gida suke, don ko dakinta
bata kaita ba,s ai ta takarkare ta rangada wata irin
matsiyaciyar guda mai ratsa kunne da jiki.
Kafin ta ce "Ubangiji na gode maka, na kuma roke
ka ka yi wa Hadiza albarka da ta raba ubanta da
wannan musiba da ya dade yana rayuwa a ciki.
19
Kar dai dama da ni wannan matsiyaciyar matar
take yi? Aure? Wane irin aure kuma. Mallam zai yi?
Wace mata ce zata yarda ta aure shi? Ai kuwa da
taci.."
Baba Sumaye ta kwashe da dariya tare da fadin
Yau fa za a ga hauka tunda an yi wa mahaukaciya
kishiya, aiyururururii." Sai ta sake rangada guda.4
Gaba daya Baba Lantana ta birkice, Delu kuwa ta
yi maza ta suri takalmanta ta kama hanyar fita, tana
fadin Ke ni fa ban san ba ki ji ba da ban zo na gaya
miki ba, alhalin maganar take yi fuskarta cike da
murmushi alamar bukatarta ta biya.
BoBaba Lantana ta kama fadin maganganu tamfar
wata zararriya, "To Mallam ma har wani namiji ne da
za a yi kishi a kanshi, sullutu a cikin maza, shi in ana
kiran maza har zai buda baki ya amsa?
Ai karyarsu ta kai karya, ace ya yi mata biyu bai
isa ba, Baba Sumayc tayi maza ta ce to na náwa? Wai
an tambayi tsuntsuwa sunanshi? Ya ce na nawa? Ta
bar wannan ta koma durawa Baba Sumayen ashar, ita
kuwa ba ta amsa ba.
Tayi ta gaji ta koma kan Babana da ba ya nan
zuwanta runfarshi biyu bata samun shi ta dawo tazo ta
zauna ta zagi Innata ta hada da Yaya Dija da ni da
makwabta ta gaji rushe da kuka ita kadai.
Ana cikin haka sai ga Asabe ta shigo gidan, rabe-
rabe da 'ya'yanta uku biyu suna biye da ita, daya tana
20

goye ganin uwar tata a yanayin da take ciki yasa
ikinta yayi sanyi kiyi hakuri Mama.
Tanfar tuna mata zaman nata tayi ta juya kanta da
zagi da tsinuwa ba dai kin ce ke wurin makiyana za ki
rinka zuwa ba? To ki daina zuwa wurina na yafe musu
ke kije can ku karata na bar musu ke. Ta ufe mata
ya'ya da duka gaba daya gida ya kaure da koke-koke.
A A zuciyata na ce, "Kun gamu da mahaukaciyar
Kaka, säi ga Yaya Dijah ta shigo ita da Aminanta, Anti
Kubra da Anti Asiya. Nayi zaton zata rufe Yaya Dijah
da duka, sai naga ba haka ba, sai da Yaya Dijan ma ta
mika mata 'yan kayan da tazo mata da su a matsayin
kayan fadin kishiya, shi ne naji ta ce mata je ki ki
k2iwa Ramatu kin ji ko ba ki ji ba? Munafukai ke da
yar uwarki."
Ta ci gaba da zage-zagenta tana watsi da kayan. Ba
su ce mata komai ba, sai lekowan da Anti Asiya tayi
dakina ta ce min "Ke je ki ki karbo mana kayan cefane
a wurin Baba, aiki muka zo yi don yanzu 'yan jere za
su iso, na ce mata to.
Ban dawo na samu Baba Lantana ba, kofarta a
kulle itama Asabe ta tasa 'ya'yanta sun yi gaba sai
kawai muka sake a gida muka yi ta hidimarmu, 'yan
jere suka iso suka yi ta jerensu, makwabta ma suka yi
ta shigowa suna yiwa Yaya Dijah murnar auren da ta
yi wa Babanmu, sai hira ake yi ana aikin ana bada
labarin haukar Baba Lantana ana kwashewa da dariya.
21

Da yamma yan biki suka tafi, bayan sun gama
kintsa komai a kan sai da daddare masu kawo. Amarya
za su kawo ta. Suna barin gidan sai kawai naga Baba
Lantana ta balle kofar dakinta, ta fito, ashe wai duk
abin nan da ake yi tana ciki ta kulle kanta, tana jin duk
abinda ake fada.
Muna hada ido da ita, ita ce ta ce min "Dukkanku
kuma za ku ci ubanku, har da shi uban naku zan ga
yanda za a yi ya yi mata biyu a cikin gidannan da ni ku ke yi."
Tun kafin Baba Lantana tayi min wannan bayanin
a tsorace nake da ita, balle kuma da ta gaya min hakan,
ko dama can kuwa mafi girman tsoron nawa ya ii
tafiya ne ga tunanin yanda za a yi Babana ya shigo
dakin wata mata a gabanta, tana kallonshi, to halle
kuma yanzu da tayi maganar da bakinta.
Magriba kawai aka idar sai kawai jama'ar amarya
suka dawo wai har sun kawo ta, nan da nan gida ya
gauraya da kamshi, ba su wani dade ba kuma sai süka
watse suka yi tafiyarsu.
A ka bar amarya ita kadai a dakinta, nima ina nawaa
dakin, ina fama da faduwar gaba saboda tsoron abinda
zai faru tsakanin Babana da Baba Lantana in ya shigo
gidan nan yau, tunda ta ji maganar ba u yi ido hudu ba.
Kan turmi ta fito ta zo ta zauna da damara a
kugunta, tana fadin "To duk wani iya shegen mutum
ni kam ai kallonshi kawai nake yi, ni kam ai iyaka ce
ai ni nafi tsumma lalacewa, yau zanga yanda za a yi
22

Mallam ya zo ya ce min yayi aure a gidannan zai shiga,
wani daki, ai sai dai kowacce ta aura mishi ke din taz
tayi gadinshi, in har ta matsu sai yayi abinda take so
yayin da ke, munafukan banza munafukan wofi."
Tana cikin wannan sambatun sai ga shi ya shigo da
gyaran muryarshi da ya saba, da kuma sallama. Da
sauri ta taso ta tare shi tana fadin Munafuki, na ce
maka munafuki.
Ina lekensu ta jikin kofa, na ganshi a tsaye yana
kallonta, ai babu inda za ka je zan ga yanda za a yi ka
ahiga wani wuri ba nawa ba, kai nan ma har wani
namiji ne? nayi kamar in tashi in fita in taya Babana,
sai kuma naga kai bari dai kawai in zuba ido in yi ta
kallo, in har ta bana shi shiga dakin amaryar tashi shi
kenan in gari ya waye in taga zata zauna ta zauna, in
taga zata tafi ta tafi.
Wane dadi ne ya kwaso Baba Lantana? Oho. Sai
kawai na ganta tasa hannu biyu ta cukume wuyan rigar
Bahana tana fadin "Kai din me? Me kuma aka yi..."
Bata gama ba sai kawai naga tanfar an dagata sama ne
kafin aka yi firo da ita ta tafi can nesa ta fadi.
Mamaki yayi matukar kama ni, na ganin abinda
yayin, nan take kuma sai na tuna ai duk iya shegen da
Baba Lantanan ta rinka tsulawa a gidanmu bata taba
gwada sa hannu ta shake wuyan Babana ba sai yau.
Kafin ta taso tuni har ya gyara zaman rigarshi ta
daidaita a jikinshi, yayi sallama kofar dakin Amarya ta
amsa, ya shige ciki.
23

Ka fito Malam tun muna shaida juna da kai, tun
tun muna girma da arziki da kai tun ban shigo nan din
na same ka ba. Ta zabura wai zata shiga dakin
Amarya, ban san yanda aka yi ba na dai ji Amaryar
tana cewa.
A'a haba wannan kuma ai neman wuce iyaka ne,
koma dai daga can wurin zaman naki kawai in yana
son ganin naki zai zo inda ki ke ya same ki."
Ke har wata iyaka ce da ke? Ta soma zage-zage
sai dai kuma ta kasa shiga dakin ta same shin, ana
cikin haka naji an turo kofa an rufe girif an kuma sa
sakata an kulle ta ciki.
Buga kofar yayi matukar razana Baba Lantana, nan
take ta kurma ihu mai karfi, ni kuwa nayi maza nima
na sawa tawa kofar sakata, don kar ta fado min dakina,
na hau gadona nayi kwanciyata aka barta a tsakar gida
ita kadai tana ta faman sambatunta.
Washegari kuwa farkawa nayi a dalilin an
kwankwasa min kofa saboda makarar da nayi, saboda
Baba Lantana bata bar ni na samu natsuwar da nayi
bacci da wuri ba, shiga da fita ta rinka yi tana buga
kofa kamar zata ballata, ban sani ba ko ni kadai ce kai
kawon nata ya hana bacci.
Ina bude kofar dakin nawa naga Amarya tsaye da
murmushinta ga kamshinta na amarci a tare da ita, kai
Yaya Dijah ba karamin ladan Babanmu ta samu ba,
abinda zuciyata ta fada kenan sanda na karewa
amaryar kallo.
24

Gajiye ce ta saki makara ko? Na tayata 1nurmushin
da take yi nin, to in kin idar da sallar sai ki zo, na ce
mate to. Ina shaia fatiha na shige dakin nata don kuwa
dama na kosa inga Babana in ga yanayin da yake ciki.
Yana zaune kan wata shimfidaddiyar darduma, kai
da ka ganshi ka san yana cikin farin cikı, an tasa mishi
abin karyawa a gabanshi.
Na tsuguna na gaishe shi, farin cikinshi a bayyane
yake, me ki ke so ki karya da shi? Tayi min tambayar
bayan ta gana anmsa gaisuwar da nayi mata. Akwai tea
skwai kunu, ge kuma farfesun kayan ciki.
Na zuba musu ido ina kallo, can cikin zuciyata
kuwa nasan da abinta tazo, ga kuma kayan tsarabar
bikinki zan. Na ce, Na gode, a bar min & nan sai Za ni
makaranta zan karba in kaiwa 'yar ajinmu.
Babana ya ce, "A'a kar6i kici abinli in za ki je
makeranta ki diba a nawe." Na ce, To.
Hu'un, lalle namiji sai a bar shi, na kuma yarda
lalle Mallam ba karamin algungumi ba ac, ashe duk
halin naza shima ya iya, ina kallonshi sumu-sumu
abin tausayi, ashe ba abin tausayin ba ne, ai inda nasan
haka ne da ba karamin gasa shi nayi ba. Ashe dama
lafiyarshi kalau?
A zuciyata na ce da kin kashe shi dai ba gasawa ba
in dai gasewa ne kawai ai dukanmu mun gasu. Ni da
kain ba karemin mamakin Babana nayi ba, gaba daya
kwanaki ukun nan na dakin Amarya ko rumfarshi ba
ye budewa, yana nan a gida a kuma cikin dakinta,
25

yana kishingide akan darduma duk lekawan da zan yi
kuma zan hango shi an tasa mishi wani dan abin motsa baki a gaba.
In kuma ya fito don yin alwala zuwa Masallaci, sai
kaga tana biye da shi tana rike mishi da butar tanfar
dai ace gadinshi take yi.
A wannan lokacin ba ka iya kwatanta yanayin da
Baba Lantana take ciki, in ban da uhun maza? Babu
abinda za ka ji ta tana fadi. Namiji? Kai lalle sei a bar
su, ashe dai babu wani dan kankani a cikinsu.
A haka aka koma dakin Baba Lantana ina daga
dakina ina jiwota, "Oh, Mallam ashe lafiyarka kalau
ka ke yi min irin wannan abin? Gaba daya ikwanan nan
uku ba ka yi fahsi ba ko daya, ina kallonka yau din me
ba za ka yi wani motsi ba ne ina yi maka magara kayi
shiru ka lullube kai de bergo.
Ko kana nufin a kaina ne ba ka da lafiy, amma in
a can ne lafiyarka kalau? To i ba zai taba yiwuwa ba,
nayi maza nasa yan yatsuna shabbaba na toshe
kunnuwana da su don in samu in daina jin
maganganun nasu, ko zan samu in yi bacci.
Komai na Safara a tsare yake, kullum girkinta yazo
zata ba mu lafiyayyan abinci da irin kudin da ake
baiwa Baba Lantana tana rainawa, tana kin yin girkin.
Ga ta gwanar iya abincin gargajiya ce iri-iri.
Su burabusko, su gwate, su dan wake su danbu su
gauda su gurasa, su sunasir su wasa-wasa, balle ayi
26

maganar tuwo, sai tayi sati biyu tana girki bata
maimaita abinda ta girka ba.
Haka nan abin karyawa tuni muka daina sanmakon
fito nemanshi, ganin da tayi inä ita nemo mane ranar
girkin Baba Lantana, yasa ta kirani ta ce min rinka
zuwa nan kullum da safe muna karyawa kin ji, shi dai
da ya ajiyeta ranar girkin nata su san wanda suke ciki,
na ce mata to.
Baba Lantana ta tsunduma. cikin wani irin abu.da
bata taba zaton zata tsunduma cikinshi ba, a zamanta
da Babara, ga kishiya te kwatsam wacce kuma ta haife
ta ga shi tasa hannu ta kalallame shi, in ban da Beban
nawa ba dan gayu ba ne, don su wanka da shafa man
nan da duk sai tayi mishi, to ba zai yaria ba.
Ga ehi tana ganin wadansı irin al'amura a wurinshi
wadsnda bata taba tsammanin yana da su ba, sai ta
zama kemar wata zareriya, babu abinda take so irin ta
samu abokin hirar da zata yi zance da shi don ta rage
damuvarta babu.
Saboda babu mai zuwa wur inta duk ta kore su
sanda ta samu daular gidan miji ita kuwa Amarya sai
kai-kawo take yi da 'yan uwa da abokan zama, dan
muguntan da take yi mana na kin yin girki muyi takai
kawon neman abinda zamu ci yanzu duk ta kau.
Ko kadan Safara bata kallon abincinta in ta gama
ta ce su zo su ci ta ce to, tunda tare suke ci in bata
gama ba ma oho. Za ta ci wani abu nima zata ba ni.
27

Bakin ciki ne ya ishi Baba Lantana, taga kamar in
ta tayar da wuta zata iya korar Amaryar nan saboda
taga komai take yi ba ta ce mata komai.
Ta karbi kudin cefane ta ki yin. girki, ko taga
shanyarta a igiya ta zube. Rannan an tashi da safe naji
Anti Safaran na cewa Yaya ina kwana? Ko dama a
lalace take amsa raata gaisuwar, amma bata daina ba.
Yaya ina kwana? Ta sake maimaitawa, sai naji ta
ce mata, ke raba ni da wani yaya, yayan mnunafurci, ki
kira ni yaya a bayan idona kina yi min munafurci, rike
yayarki bana so tunda ai ni ban ma ga wani abinda na
girme ki da shi ba.
Ta ce, To kiyi hakuri. Taja bakinta tayi sbiru bata.
kiranta Yayan oa ta kuma kian sunanta, ana cikia
haka ta sake cewa kicin nata ne a ranar girkitita bata
yarda wani ya shiga ba. Nan ma ta ce, To sai ta fito de
risho dinta in zata dan yi wani abu ta tura a baya
kofarta tayi.
Ba a gama da wannan ba sai kuma ta fito da wani
salon in Safara ta gama abinci ta kawo ta kira ta ba za
ta ce ba za ta ci ba, sai ta dauko kujerarta tazo ta zauna
tasa hannu ta gutsuri lomar tuwon ta kai bakinta, sai ta
fara tauna shi.
Sai tayi wuf ta dawo da shi ta tofar tare da fadin,
kai tir, wannan tuwon ai danye ne ke ba ki iya komai
ba ne a tayuwarki sai jarabar bin miji? Ba ta ce mata.
komai ba, rannan dai sai ta gaji ta ce mata da dai kin
28

daina irin wannan abin, tunda kema kin san baida
amfani, shi hatsi ai be a yi mishi haka.
Sai kuwa Baba Lantana ta zabura ta sake gutsurar
weci lcmen te ka: bakinte, tayi mishi tauna daya te
maido shi kan asalin tuwon da ke cikin kwanon wanda
ite take ci, anyi din an yi wa hatsin rama mishi.
Haka kawai sai ki rinka yiwa mutane danyen
abinci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login