Showing 9001 words to 12000 words out of 41517 words
ba,a wannan tsohon d aren
ina za ki haka Anti? Me ya same ki ki ke kuka haka? Ban
40
iya ba shi amsa ba jikin Baba ne ya tashi? Nayi maza nace mishi "Eh" To ina zaki yanzu sha biyu saura kwata ne fa na dare.
In asibiti kike so a kai shi ga makwabta." Lolkacin nena tuna ashe ma Baba Baidu ya kamata in fara gayawa ba
wani ba, balle Yaya Dijah da ba ma kusa muke ba, tunda
ance makwabcinka na kusa shi ne mutum na farko da ya
Kamata ya taimake ka, in har ka shiga halin bukatar
taimako.
Tare da shi muka je na fara buga kofar gidan Baba
Baidu, sai da ya ji ya bude kofar dakinshi zai fito sannan
ya ce min, Bari in nemo mana motar da za ta kai mu.
Na ce mishi "To, Isyaku na gode." Tamfar dai ba shi
ne Isiyaku da na share ba na ko amsa gaisuwarshi ba.
Ina tsaye a tsakar gida bayan na shiga dakina nayi
shiru na debo duk kudin da nake da su, kuka mai yawa
nake yi saboda yanda nake jin Babana yana magana cikin
jarumtaka da kyar da kyar.
Amanata yake baiwa Baba Baidu da matarshi, ni
Mero sa shiga uku zan rasa uba mahaifi kamar yanda na
rasa mehaifiyata yau ya ya zan yi?
Gare ka nake bauta Allah, gare ka nake neman
taimako ya Ubangiji, abinda kawai nake ta nanatawa
kenan. Ana cikin hakan naji zuciyata tana zargina da
cewar ni da Yaya Dijah muka fara haddasa mishi ciwon
nashi da muka tasa shi a gaba muka yi mishi maganar da baya so.
Ina yin wannan tunanin na sake rushewa da wani
sabon kukan na nadama da bakin ciki. Isyaku ya shigo da sauri.
41
Ga mota Anti na samo." Ya wuce cikin dakin ya
gaya musu. Babana bai iya takowa da Rafafunshi ya fito
ba saboda karfi ya tafi sai da aka rirriko shi aka fito da
shi muna isa asibiti aka ba mu gado.
Dama kuma shi kwastoman asibitin ne, fayil dinshi
aka dauko aka dora bayani akan wanda yake ciki.
Mun kwana muk wuni a asibiti babu alama na
samun sauki a tare da Babana, hankalinmu ya kai matuka
wajen tashi, bar gara nima akan Yaya Dija.
In ban da kuka babu abinda take yi, ni na tayar mishi
da ciwon. Na ce, A'a Yaya Dijah, dama bai da wata
lafiya, ba ki ji bayanin da Anti Safara take fada ba, na
cewar ya dade ba ya bacci da daddare.
A'a amna ai bai tsananta ba sai bayan da nayi mishi
maganar duk kalaman da nake gayawa Yaya Dijah bai sa
ta samu na suwa a tare da ita ba.
Likitoci ne suka yi ta zuwa duba jikin Babana, kusan
duk wanda yazo duba shin kume ya kar tafi ne a yanayi
na tausayawa da fadin kai lalle Mallara Habu yana jin
jiki, Ubangiii yasa kaffara ne.
Wai kuma a wannan lokacin ne da ake cikin wannan
al'ama rin naji Baba Lantana tana yiwa wata mata da in
banda a zuwanmu asibiti ban yi zaton ta taba ganinta ba
tadin Baban da al'amarinsu.
Ai ni don dai kar a ce ban zo ba ne kawai amma 1n
ba haka ba ai ko mutuwa yayi bani da wata asara
mutumin da yake daukan girkinka yana kaiwa kishiyarka
kana ji kana gani ba ka da yanda za ka yi.
Yaje yana yin abin nan da ita. Ni kam ai alhakina ne
ya kama shi yanzu ba sai suje suyi ba in gani? Kin ga tun
42
kafin yayi auren nashi sai ya yi wata biyu wata ku ba
kula ni ba, a hakan...
Ganina da suka yi ya katse hirar tasu ganin da nayi in
sallami Baba Lantana in ce ta koma gida ita kadai ba zai
zamo mai sauki ba, zai kuma kara bayyanar da rashin
adalcinmu mu da Babanmu da ke fama da kanshi.
Wanda ita take kokarin baiyanawa koya ya zama
sheda akai, bisa haka sai na hada ta ita da Anti Safara
nayi musu magana akan su koma gida wanda da kyar
suka yarda hakan.
In na tsaya cewa mun shiga wani hali ni da Yaya
Dijah dama duk wani, wanda yake tare da mu a
tausayawa to na tsaya bata bakina kawai nake yi.
Ina zaune kan kujerar roba ina tashe da Babana bayan
tafiyar Yaya Dijah da mijinta, in banda kuka babu abinda
nake yi na roke ka ka yafe min abinda nayi maka.
Baba abinda kawai nake iya fadi kenan ban ji lokacin
da ya shigo ba saboda shagalar da nayi da abinda ke
gabana sai ganinshi kawai nayi a tsaya ta daya gefen
kusa da Babana.
A daga ido na kalle shi Mubarak ne yana cikin
natsuwa mai yawa yanayin da ke fuskarshi ce ta kara
bayyanar da hakan.
"Ubangiji ya baka lafiya Baba, yasa kaffara ce. Shi
ciwo ai rangwame ne, domin kaffara ce ga zunubai
sannan jikin naka ma da sauki ba haka nayi zaton
ganinka ba."
Babana ya dan daga ido ya kalle shi saboda jin
kalamin nashi, ya sake yi mishi sannu kafin ya sake
43
daidaita tsayuwarshi, ya karanto addu'ar da ake yi wa
mara lafiya.
Kafin yayi mishi sallama ya juya da nufin tafiya. To
zo mana, ban iya yi mishi musu ba duk da mun dade
kwarai ba mu ga juna ba ban da haka ma mun dade da
fita hanyar juna.
Tun bayan abind ya faru a tsakaninmu, sai muka
shiga kiyayyar juna, ai ba nisa za ki yi ba, ya gaya min
hakan don kara karfafa min in zo din.
Ke haka ake yin jinya ne? Nayi maza na kalle shi don
in ji ta inda kuskuren nawa yake in gyara, kin tasa shi a
gaba sai kuka ki ke yi, kina rokonshi gafara?
To a kan me ki ke yin hakan, ki, Rara kashe mishi jiki
ko ki kara-tsoratar da shi, ki karya mishi zuciya?
Shi majinyaci karafa shi ake yi da kalamai na karfafa
zuciya, ba yi tayi mishi kuka ba, shi ciwo ma da ki ke
ganinshi be shi ne mutuwa ba fa.
An yi yafi a kirga mai laifiya ya mutu ya bar mara
lafiya a kwance, kin gane? Nayi maza nace mishi eh.
Yanzu ke menene damuwarki da ki ke wannan
kukan? Ban iya boye mishi ba ko in ce zanja mishi aji
saboda halin da nake ciki, sai kawai na gaya mishi
Babana bai da lafiya.
Gashi an kawo mu wurin da kowa ya zo ya ganmu
sai ya ce uh' uh hh lalle Mallam Habu yana jin jikı, a
dakin da yake din ma na gobe da nisa ne kusan kullum
sai an yi mutuwa a dakin dazu ma an yi wata mutuwar.
A hankali ya ce min, to kiyi hakuri ba ni in yi
magana a canza muku dakin a kaiku inda za ki dan samu
natsuwa shima Baban ya samu kulawa ta musanmman.
44
Koma wajen shi ina zuwa, ban ce mishi komai ba na
tashi na tafi na dawo na samu Babana a yanayi na canji.
Nan take na tuna da addu'ar da Mubarak yayi mishi
wacce na taba ganin bayanin da Manzon rahama yayi a
kanta cewar duk sanda mai duba mara lafiya ya
karantawa mara lafiya ita, Ubangiji zai saukar mishi da
wani rangwame a halin da yake ciki, ko da kuwa cutar ta ajali ce.
Nayi maza na matsa kusa da shi.
"Sannu Baba."
Ya amsa a hankali "Sannu Yachuwuna, kina ta
wahala da ni, Ubangiji ya yi muku albarka."
Na dauko kofi na tsiyayo kunun gyada na zauna kusa
da shi ina gauraya kunun da cokali don ya yi sanyi.
"Bari in kurkure maka baki ka dan sha kunu Baba, ka
dade ba ka ci komai ba." Ya dan sha kunun kadan kafin
ya daina kar6a nima na kyale shi ban matsa ba tunda dai ya dan sha
Na gyara zama a kan kujerar da nake zama tare da
jingina a jikin gadon nashi ban san yanda aka yi ba, sai ji kawai nayi ana ta shina.
Nayi maza na bude idona da gaske ashe bacci nayi,
ga dukkan alamu kuma yayi nauyi, don na dan ji canji a tare da ni.
Na kalli Nos din da ta tashenin bisa zaton ko lokacin
shan maganinshi ne yazo, sai naji ta ce min "Bari mu
canza muku dakin ko?"
Nayi maza na kalleta duk da bayanin da Mubarak
yayi min akan canjin dakin ban dauka da sauri ne haka
ba.
45
Yayanki ya ce a maida sBaba privater ward. " Na ce
mata To. Aka dauke mu aka maida mu private ward.
Mu kadai nea wurinbga tsafta ga kulawai ta
musamman sai dai maimakon saukin das Babana ya dan
samu ya dore sai kuma jikinya: kara táshi, kasancewar
likitoci baba tsinkewa a wurin sai sukal yi ta: kai kawo
suna bincike kan oalanarine nashi, ina daga gefe ina
kallonsu cikin natsuwa yayin da zuciyata take ta faman
karanto addu'o'i iri-iri, kafin gari yawaye har an canza
mishi magungunan da yake sha gaba daya.
Ganin haka ne ya sani matsawa kusa da shi sosai
lokacin da wani lokaci ya sake shigowa don duba
yanayin jikin nashi da safe, sanmu da aiki doctor. Ya juyo
ya kalleni, yauwa sannu ko? Ya ya jikin nashi? Na yi
màza nace da sauki, yanayin da na gani a tare da shi ya
karamin kumarin yi mishi tambayar da nake son yi mishi,
Dr. An ganw wani abu ne a tare da shi da yasa aka canza
mishi magu agunan nan? Sai dai ya daga ido ya kalleni
kafin ya maida kallonshi ga aune-aunen da yake yi, mara
lafiyan mene ne dinki? Na yi maza na ce mishi, babana
ne mahaifi, to me za ki yi in kin sani? A hankali na ce
babu komai, nayi shiru ban sake ce mishi komai ba, ya ci
gaba da abinda yake yi har sai da ya gama zai fita sai ya
sake kallona ya ce min, me sunanki, na ce mishi
Maryam, har ya yi kamar zai juya ya tafi sai naji ya ce
min, menene aikin zuciya a jiki? Cikin nutsuwa na ce
mishi harba jini zuwa sassan jiki, to daya ko biyu daga
cikin jijiyoyin da sukeyi mishi wannan aikin ne ya samu
matsala. Jikina ya yi sanyi sosai da jin bayanin nashi
amma da yace min kin gane? Sai na yi karfin halin ce
46
mishi eh kamar in sake yi mishi wata tambayar sai naga
to kar ya ce na dameshi don halka na hakura nace mishi,
na gode, ban san tunanin da ya yi ba wanda ya sashi ci
gaba da yi min bayani, bangaren hagu na zuciyarshi ne ta
samu matsala har ya dan kumbura kadan saboda jjiyoyin
wurin basa aiki sosai shi yasa numfashi yake yi mishi
wahala.
Bayanin da ya yi min ya sani tambayar shi, to yanzzu
menene abin yi Dr? Za mu yi mishi ailki nę mu gyara
Jjiyoyin.... bai gama yi min bayanin ba sai ga Mubarak
ya shigo duk da sanin likita. ne ko kallonshi ban yi ba
balle ya ce bari ya gaisheshi na juyo da kallona gareshi
da nufi gaisheshi saboda mutuncin da nalke ganin yayi
min na kulawar da nake -ganin ya nuna a kan rashin
lafiyar babana, wani irin lalataccen kallo naga ya yi min,
jkina ya kara yin sanyi cikin zuciyata ina tunanin laifin
me nayi mishi, sai kawai na ji ya ce min, shi. ma wannan
din saurayinki ne? Gabana ya yi mummunan faduwa nan
take kuma na ji mummunan bacin rai a zuciyata, wacce
irin mummunan magana ce wannan, ina fama da jikin
babana ya kalleni ya ce, wai ina samartakan, me ya
maidani? Nayimaza na kawar da maganar tashi daga
cikin zuciyata na dai kudunawa raina kamewa in daure
mishi fuska sosai watakila don yaga na dan sakar mishi
ne yasa yake so ya yi min wulakanci irin wanda ya saba.
Yaya Ibrahim ya iso tare da yaya Dija kamar yanda
suka saba yi kullum ta zo ta tayani mu yi mishi abinda ya
dace sai su tafi sai lkuma ta gama abinda zatayi sai ta zo
mana da abincin rana daga gida kuma Anti Safana take
zuwa mana da kunun gyada da baba yake sha sai da
47
daddare Yakumbo Halima ta kawo mana abincin dare ita
kam baba Lantana ko tazo da wani abu bana yarda ta
baiwa babana saboda na riga na jita tana fadin alhakinta
ne ya kamashi banda wannan ma na ji ta tana fadin' ko ya
mutu bata da asara, ashe Alhajit Mubarak ya zo? Nayi
shiru ban amsa mata ba to me ya sa kika yarda yad awo
da mu nan? Ban tsaya yi mata wani bayani ba na ce mata
ki yi hakuri mu ne zamu biya, bata sake yin maganar ba
sai ta tambayeni, to yaya kuka kwana da jikin nashi? Ban
boye mata ba sai nayi mata gaba daya bayanin da likita
ya yi min, dama ana yin irin wannan aikin ne? Ta yi min
tambayar cikin wani irin yanayi, na ce nima ban sani ba
tana jinnace ban sani ba ta soma kuka, ban iya bata
hakuri ba kukan nima na shiga yí muka hadu muka yi sai
da muka gaji muka yi shiru don kanmu.
A sallameshi kawai, nayi maza na kalleta a
sallameshi" yaya Dija mu yi yaya da shi da wannan
numfashi nashi? Ai ba gida zamu maidashi ba wani
asibitin zamu sake mishi in da za a bashi magani ya ji
sauki ba tare da an yi mishi aiki ba, kin taba ganin wanda
aka yiwa irii wannan aikin dą sukace za su yi mishi ná
gyara jijiyoyin zuciya? Nayi miaza maca mata uh-uh ta ce to.
Gaba daya muka sake tsundurma cikin wani hali na
kunci da danuwa. Mubarak ya sake dawowa shi da
abokinshi Amiru kulawarshi da tsayawarshi kan
al'amarin babana abin sha'awa ne don kuwa gaba däya
ma'aikatan wurin sun dauka shima dan babana ne komái
yake yi baya sauraron kowa duk abinda aka ce za a yi sai
ya ce a yi sau biyu ina zuwa wajen sayen maganin da aka
48
rubuta sai su ce kudinku da kuka ajiye bai kare ba na
luma san shi ne ya ajiye kudin amma a kame kwarai
nake da shi in ba shi ne ya tambayeni wani abu ba bana
tanka mishi, shima kuma ba sosai yake shiga harkar tawa
ba sai ta kama ina dai kaffa-kafia da sh saboda na riga na
sanshi na kuma kara ganeshi shi mutum ne mai iya
wulakanci a ko ina kuma a kuma ko da yaushe a shiryc
yake ya yi min in ba haka ba banga dalilin da zaisa ya
kalleni a halin da nake ciki na rashin lafiyar babana ya ce
wai a asibitin ma samari nakeyi.
Cikin natsuwa da girmamawa na gaida Amiru, yaya
mai jikin? Na ce mishi da sauki, ashe aiki za a yi mishi
ko? Na dean yi jim kadan cikin tunani kafin na ce mishi,
anya? Anya wane iri? Ya yi min tambayar cikin wani irin
yanayi na tsatsuwa mai yawa, na sunkuyar da kainaa
saboda yanayin da yake kallcna a ciki sai naji ya ci gaba
da yin magana, ba yanzu muka fito daga wurin likitocin
da za su yi aikin ba ni da Alhaji Ahmad? Ai ya riga ya
gama maganar da su har ya yi setting din bill din da suka
bayar baki san komai bane a kai? Ban iya cewa komai in
banda sa hannun da nayi na soma share hawayen da suka
Soma zubo min.
Ban sani ba ko ganin hawayen nawa ne ya sashi
saurin juyawa wajen Mubarak din, kai baka yi mata
bayanin komai ne? Ya ya za ka tsaya kan yiwa
mahaifinta aiki irin wannan ba tare da ka yi shawara da
ita ba? Kuma. mcke tsakaninka da ita tunda dai ka
hadiycshi ka zo ai sai ka bar komai ka fuskanci maganar
rashin lafiyar kawai in ya koma gida sai ku dora daga
inda kuka tsaya.
49
Har a mu'amalar da takeyi da samari sai in yi hakan
dai ta? Gabana ya fadi saboda jin mu'amala da samarin
da ya ke ikirari, ba sha'anin gabanta take yi ba ba sai in
kyaleta nima in yi nawa ba?
Wani irin mummunan tsaki Amiru ya ja kafin ya ce
mishi, kaif halinka kenan a ko ina a ko wane hali a kuma
kowane irin yanayi wai kana iya yin kishi. Ran Mubarak
ya soma baci da jin maganar tashi a fusaceya soma ce
mishi, a'a kai Amru kar kaja ta raina ni fa wane irin
magana ne wannan? Ni kishi nakeyi a kanta? Yanzu kai
baka ga irim abinda suke yi ita da wannan likitan da muka
samu a nan ba tana yi msihi magana una wani yauki tana
wani kakkashe mishi murya shi kuma sai zirga-zirga
yake yi yana kaiwa da kawowa don ya gane abinda take nufi.
Amiru ya ja tsaki kafin ya saki wani lallausan
murmushi ya ce, ban ga komai ba Alhaji kai ne kaga
hakan ni dai na san a halin da Maryam take ciki a yanzu
in ma kaga tayi wani abu makamancin hakan to sai dai
tayi don ya zama dabi'arta amma ba don ta burge wani
ba don haka kayi hakuri ka rage sa mata ido ku fuskanci
juna kai dai ta don ku f jin dadin mu'amala a
tsakaninku.
Kai kam ai dama baka son laifinta ban taba kawo
maka zancenta kan abinda take yi min ka goyi bayana ba
sai ka ce wai sa ido nane ya yi yawa.
Bai sake tanka mishi ba sai ya juyo gareni, ke rabu da
shi kin ji Maryam daina kuka ki share hawayenki kin ji?
Ni zan tafi. Nayi naza ma share hawayen nawa kamar
50
yanda ya bani umarni na kuma yi mishi godiya, Mubarak
yabi bayanshi nayi maza na koma wurin babana. ai n
sBa a wani dade da yin hakan ba sai na hango shi
yana dawowa alamar rakyar ba mai yawa ya yi mishi ba
don haka na yi maza na sake fitowa daga dakin na tare
shi a dan dogon falon da kofofin dakunan ke ciki a
hankali cikin natuswa ta yanda babu mai jin abinda nake
fada na ce mishi, ko zaka daina zuwa ne don kar mu zo
muna batawa juna rai? A yanayin da nayi mishi maganar
a irin shi ya bani amsa, ranki ya zo yana baci dai amma
ni me zai 6ata min rai? Aiina ganin so mi somin hakan
na daga wurinki zan yi maza in yi maganin abin don
gaba daya zan hanalki zuwa asibitin kamar yanda kika
hana matan gidanku zuwa. Gabana ya yi mummunan
faduwa na yi amza na daga ido don in kalleshi saboda
mamakin maganar tashi in ga irin karfin halin da ke
gareshi da zai yi min irin wannan hukuncin alhalin ni da
mahaifina ne, wani irin lalataccen kallo naga yana yi
min, kina nufin kinfi kowa kusa da shi ne ko kinfi kowa
sonshi ne? Ki yarda in ga wani abinda bai yi min ba ki
gani? In gani in zan hanaki zuwan ki zo ki ga wulakancin
da zan yi miki baki iya rashin kunya ba? Kar ki dauka
kuma wai kishinki nake yi kamar yanda Amiru yake fada
ko daya.
Rasa abinda zance mishi nayi na soma yi mishi kuka
saboda sanin da nayi cewar zai iya aikata abinda ya ce din.
Sakarya kawai sokuwa wacce ko ciwon kanta bata
sani ba sai rashin kunyar tsiya.
51
Ya wuceni zai tafi nayi maza na ce mishi, to bana son
aikin da kake son sawa a yi msihi. Maimakon ya ce min
to kamar yanda nayi zaton ji daga gareshi sai naji ya ce
min to ai bake ke da shi ba yana kuma