Showing 18001 words to 21000 words out of 41517 words
muna asibiti har kawo dawowarmu
gida bai zo ya gaida babana ba yana ganina ina ganinshi
sai ya yi kamar bani yake kallo ba sannan a hakan wai an
bisu har gida ance in suna so su zo bayan ga wani yana
takai kawo a kaina an san za a bashi ni me yasa ba a
bashi din ba tuntuni tun sanda suke zirga-zirgar aike shi
da mahaifinshi sai a yanzu da suka tattara nmutane suka yi
watsi da su?
Ina alwalar sallar azahar a tsakar gida Rukaiya ta yi
Sallama ta shigo, ran amaryarmu ya dade, ban wani
kulata ba don ana jin kamar ina son wasan nata, anti
Safara tayi ma'a sannu da zuwa ta kuma jagoranceta
Zuwa dakinta hakan ya kara tabbatar min da cewar ba
wurina tazo ba, a cikin zuciyata dai na kasa tunano
yaushe rabonta da shigowa gidanmu? Dakina na wuce na
soma gabatar da nafila kafin in yi farillar har ta bar gidan
kuwa ban san yanda na tashi daga kan salalyar ba don
74
amin amin, dakina ta sbigo ta samen, ke kuma menene
haka kika shige daki kika hau gado kika zauna ba za li
bar gidan ba sai masu kawo kayan sun zo sun sameki?
Na tashi na zauna ina kallont,a kayan me za a kawo?
Harara da dakuwa ta hadamun gaba daya, ba fa na son
rashin kunya, na ce to yaya dija ni ina sanin abinda ake
ciki ne? Kin san irin bakaken maganganun da ya zo ya
dankaramin kuwa? Ni gaskya, ta ce to ba yanzu ne
lokacin fadin gaskiyar taki ba mai gaskiya tashi ki shiga
gidan baba Sumaye don kar su zo su sameki a nan a ce
kin yi rashin kunya tunda ina ganin kamar za su zo da
yawa saboda ya ce min zai hada komai a azo da shi
kayan na gani ina so kayan sa rana, kayan aure da kuma
na sakun lalle don baya so a saka mishi lokaci mai nisa.
Ban iya ce mata komai ba saboda hayaniyar da akeyi
a cikin gidan alamar mutane suna kara shigowa, anti
Safara kuma sai kai kawo take yi tana kokarin ganin
kowa ya sarou abinda zai kai bakinshi.
Duk da kokarin da yaya Dija tayi na ganin na fita
gidan ba tare da an ganni ba sai da wasu suka gannin
basu kuma ja bakunansu sun yi shiru ba sai da suka yi
tambaya, ai dama amaryar tana gidan ne? Sai dai ba su yi
sa'a sun sami mai basu amsa ba muka wuce kofar baba
Lantana a kulle kamar bata nan nayi maza na kalli yaya
Dija na ce mata, tana ciki fa ta kulle kofar ne kawai irin
yanda tayi ranar da aka je jeran anti Safara, bata amsa min ba.
A gidan baba Sumaye dakin da muka saba zama
sanda muke yara na shiga na hau dan gadon bonon da ke
wurin na kwanta, maimakon zuciyata ta tsaya wajen
76
tunanin alamarin dake faruwa a kaina a halin dan ake
cii sai ta koma tunanin da rayuwar kuruciyata tun sanda
nake yar karamata sosai mu'amalata da su Jumare har
kawo ranar da na wayi gari a wannan dakin ina baccin da
ake kira baccin hasara na rasa Innata ban sani ba, hasken
rana ta tashi na fito waje idanuwana suka sheda dimbin
jama'ar dake sallatar wata gawa dake shimfide cikin
makara a ka kuma lullubeta da zanin Innar tawa amma
ban gane itace a kwance a ciki ba, hawaye suka soma
zuba min ganin babu kowa a gidan sai ni kadai ya sa ni
na sake nayi kuka har sai da na gaji nayi shiru don kaina
ban kuma wani dade ba bacci mai nauyi ya daukeni
wanda ban tashi ba sai da naji ana taba ni na bude ido
naga baba Sumaye a firgice na ce mata, magariba har
tayi baba?
Ta ce eh, nayi maza na ce ban fa yi la'asar ba, ta ce to
ai sai ki tashi ki yi, na idar da sallar magariba ina addu'a
ita kuwa baba Sumaye sai fadi take yi, kai uh-uh uhhh, ta
gyada kai jimawa kadan ta sake nisawa ta ce, mu mata
muna da aiki shi namiji a kan matar da yake so ai
maganin shi hakuri ne kawai in kayi hakuri komai sai ya
wuce amma in ba haka ba ai abin da wahala wannan irin
kaya da Alhaji Mubarak ya yi miki dame sukayi kama ni
Sumaye? Ta kama baki ta rike tana fadin, kinga ni ko
Kayan auren ban gama gani ba na tashi balle kuma sauran
komai fa a ciki sha biyu ne dozin sai bayani baba
Sumaye take yi min tamkar dai ta mance ni ce amaryar a
wancan lokacin namu kuma ba a hirar aure ko kayan
aure da wacce za a yiwa aure.
77
Ban samu ganin kayan auren da baba Sumaye ta bani
labari ba saboda gaba daya kayan babana ya ce yaya Dija
ta tafi da su can gidanta ta adanasu.
Kwana uku da kawo kayan auren Mubarak ya zo a
zauren gidanmu na sameshi da ganinshi nasan zuciyarshi
a soshe take saboda yanayin da na gani a tare da shi,
daga wurin yaya D:ja nake naje wajenta ne don ina so in
yi muku adalci dake har ita da na so da sai kawai in samu
malam Ibrahim in nemi alfarimar lokacin da nake so a
sanya main na biki to banyi hakan ba sai naje na sameta
don in baku damar ku me kika gaya mata da yasa ta ce
min wai zaia shiga wannan maganar ne kawai in mun
warware mas'alar da ke tsakaninmu? Menene a tsakanina
da ke? Me bayi miki? Me yasa ke baki da sassauci kan
abinda ya sihafeni? Daga shekaru biyar zuwa yau za ki
iya tunaw da wani abin da kika yi min guda daya da
niyyar ki i in ji dadi? Kina tsammanin in banda wani
al'amarin 1e na daban a tsakaninmu da ke zan lamunci
irin wadar nan abubuwan ne? Ai bana son 6acin rai Mero
abinda ya kenan ya tsare mutum ya yi ta gaya mishi
maganganu in banda hzka bai iya komai ba gaba daya
samarin da nayi ban taba ganin wanda baya zama ya
gaya min irin son da yake yi min ba sai shi tsawon
rayuwata da shi bai san ya vabi kwalliyata ba sai dai ya
saya min kayan adon kawai dana kai munzali na 'yan
matanci gaba daya burina ya yabi kwalliyata ne don inji
dadi bai yi ba ko ince baya yi na kai wani matsayi na
bukatar ace ana sona bai yi ba wasu suka yi ta furta min
hakan na kasa jin dadin kalmar a bakunan su saboda ba a
wurinsu nake son jinta ba, bai buda baki ya gaya min irin
78
son da yake yi min ba sai a loakcin da al'amura tsakanina
da shi suka rikice ko ince suka lalace ya fadeta a sanda
fadin nata bai amfanar mana da komai ba tunda wannan
lokacin kuma bai sake gaya min wata magana
makamanciyarta ba da zata sani in ji sanyi ko inji dan
wani sassauci a zuciyata, ban san yanda aka yi ba naji
nakina ya ce mishi, nifa nafi son auren mutumin da zai
rinka furta min kalmomi masu dadi yana gaya min irin
son da yake yi min.
Maimakon da ya ji hakan ya gaya min wata magana
mai dadi sai na ji ya ce min, to ya ya za ki yi da kaddarar
rayuwarki Mero? Ko wace mace ai da irin kaddararta ke
taki kaddarar ita ce ta ba za ki auri saurayi ba mijin wata
za ki aura ba kuma za ki auri wanda zai zauna yana yi
miki irin wadannan kalmomin ba don bai iya ba.
Na 6ata rai na ce ko kuma a kaina ba? Eh to watakila
a kankin ne kawai nake hakan da kuma za ki yarda da
shawarar da zan baki da kin daina kawo zancen wata a
tsakanina da ke.
Na yi shirn shima ya tayani yin shirun na dan wami
lokacin kafin ya kawar da shirun da tambayata, da ma
damuwar kenan? Ban kula shi ba, sai na ji ya kara
sassauta muryarshi a hankali, cikin nutsuwa a soma
cewa, ban yarda na koyi irin wannan rayuwar ba ne
Maryam saboda nafi so da sha'awar rayuwa irin wacce
na samu iyaye da kakannina a kai ina irin rayuwa ta
kunya da kawaici kan abindą kake so musamman mace
kin gane? Shiru nayi ban ce mishi komai ba har ya yi
min sallama ya tafi a kan gobe zai yi sammakon tafiya
79
Legos nace to Ubangiji ya kiyaye hanya, ya ce to amin
na gode.
Kwana hudu bayan tafiyar Mubarak aka yi bakon
wani dattijo a gidanmu ganin shi da zanen barebari irin
na babama da nayi da kuma sanin da nayi cewar babana
yana mutunta duk wani mutumin da ya gani da irin
wannan zanen a fuskarshi ya sa nima na mutunta wannan
dattijon ta hanyar shinida mishi tabarma a cikin zaure
na,kawo mishi ruwan sanyi tare da butar alwala da kuma
abincin da aka girka wanda bai yarda ya taba komai a
ciki ba in banda butar da ya dauka ya je ya taba ruwa ya
sake daura alwalarshi da ta kárye a sanadin taba ruwan
da ya yi sannan ya dawo kan tabariar ya sake zama ya
zubamin ido yana kallona cikin natsuwa ya tambayeni a
daidai lokacin da ya ci gaba da jan dogon carbinshi yana
kos kos kos, to ina malam Bukar din da tace nan din
gidanta ne tace babanta ne? Kai tsaye na fahimci inda
yake nufi tunda shiua baban nawa shigen irin hausar da
yake yi kenan na ce msihi e maiam shi ne babana, ya
gyada kai ya ci gaba da abinda akeyi, ni kuma na mike
na shiga gidi na dauko gyaiena bayan na shedawa anti
Safara cewar zanje kiran babana saboda wani bako mai
irin zanen shi ya zo wai yana son ganinshi ta ce to yi
maza ki kira mishi shi nace mata to na fita.
Bako da irin zanena ya zo nema? Ya yi min tambaya
cikin yanayin murmushi na yi maza na ce mishi ci baba,
ya ce to muje gani nan zuwa, na ce mishi to na dawo na
cewa bakon gashi nan zuwa na Wuce ciki bayan ya amsa
min ta yanayin gyada kai saboda ya riga ya shagala da
mu'amalar da yakeyi da carbinshi.
80
Ina daga cikin dacina a zaune na ji isowar babana
ssboda kaurewa da yayi da wani irin barbarci na sha jin
shi yana furta lcalmomi har da hira cikin harshen nasu
idan yaga abolkan harshen nashi amma ba irin na yau ba aa
hankali na sake fiitowa daga dakin nawa cikin sanda na
leka zauren don in ga melke faruwea mutumin na ganii a
tsaye ya saba gorarshi ta ruwa da tun sanda na kai mishi
buts ya sake cikata da ruwa alamar tafiya zai yi yayin da
shi kuma babana ya bajea kasa yasa hannu biyu yana
rike da kafafuwanshi cikin yanayi na bada hakuri. s A
Ka yi hakuri Abba Gana ka yi hakuri kar kace zaka
tafi nasan nayi maka laifi amma tunda har ka iya nemana
to layi halkuri ka zauna.
To tayi hakuri ta zauna tayi menene? Ba ta riga ta
ganta ba ba shi kenan magana ta kare ba, ai ta ganta taji
dadi ta gofe tasan tana raye itace kawai bata je wajenta ba.
Gabana ya fadi kar dai dan uwanka ne wannan ga
zatona a zuci nake yin maganar ashe ban sani ba ta fito
sai kawai naji babana ya ce min, eh Yacuwuna babanki
ne wana ne uwarmu daya ubanmu daya, ban san sanda
na kama ihu ina buga tsalle tamkar wata zararriya da
sauri anti Safara ta fito tana tambayata menene? Ban iya
bata amsa ba kartawa kawai nayi da gudu na nufi gidan
yaya Dija don in kai mata labarin, gaba daya muka dawo
har da yaya Ibrahim da yaran ya kwaso mu a motarshi
saboda na sameshi a gidan.
Tuni har zaurenmu ya fara cika da jama'a makwabta
baba Bairu da baba Hodijo da ma wasu makwabtan sun
hadu sai taya babana bashi hakurin ya zauna suke yi, shi
81
kuwa yaja ya tsaya sai nanata kalmominshi yake yi ta
riga ta ganta ai ta gode ta ganta da ranta da lafiyarta to
inta zauna me zata mata?
Ka yi hakuri malam ka yi hakuri ka zauna na rokeka
ka yi hakuri, cikin yanayi na natsuwa da girmamawa
yaya Ibrahim yake bashi hakurin baba Baidu ya kaelshi
ya ce mishi, kayi mana malam wannan mai rokon naka ai
surukinka ne shi ne mijin babbar yar taka? Abba Gana
yana jin haka jikinshi ya yi sanyi alamar surukuta tana da
karfi da muhimmanci a wurinshi, a hankali ya koma kan
tabarmar ya zauna sai dai kuma yana zaman sai ya daso
ido ya kali mutanen da ke wurin cikin wani irin yanayi
ya tambayesu to da da saa ta zauna ta hanata tafiyan nan
kam me zata yiwa Bukar ne bayan ta tafi ta barta shekara
talatin da daya? Yana fadin hakan ya soma shisshikar
kuka shima baban nawa haka, nayi maza na karasa cikin
gida da gudu ban tsaya gurin ganin abinda ya ci gaba da
faruwa ba.
Kafin magariba dai har makwabtas unf ara zirga-
zirga a gidanmu kowa ya ji dan uwan malam Habu mai
timatir ya zo sai yazo wai ya zo gaisheshi, kowa ya zo ya
fita kuma da abinda zakaji ya zo fadi, wanshi aka ce ne
ko kaninshi? Abokin magana ya ce a'a wanshi dai sai ace
a'a to ai ma yafi malam Habun karfi da kuruciya, a'a ba
zai fishi ba barijn gida da dangi wasa ne? Sannan shi
malam. Habu wannan ja'irar mata da ya gamu da ita ai
sa'a ma akayi da aka sam eshi a haka kasan ba karamin
amfani auren nan yayi mishi ba don ma yayi jinya kanan
nan ai duk sanadin ta ne duk masifar ta ce ta jawa
mutumin nan wannan Wahalar.
82
Wasu kuma suka ce oh ka ji wani abin mamaki wai
yana da 'yan uwan shi har da shakikai amma shekara
talatin da daya bai nemesu ba ko me suka yi mishi haka
oho? Kai koma me suka yi mishi bai kyautawa kanshi ba
ko da yake dai ance wai in ka ga bera ya rugo da gudu ya
fada wuta to binda ya koro shin ya fi wutar zafi.
Daya mutumin ya ce uhun ai gara da kai da kanka ka
fadi hakan don ni yanzu babu abinda ke kadani ya
razanani in tsorata irin inga yanda mutnae suke wasa ko
suke cin mutuncin zumuncinsu sai ince oh oh anya a irin
wannan hali da muke
zumunci dake kan siratsi kuwa da akace zai rinka fisgo
mutanen da suka tozartar da shi a rayuwarsu ta duniya ya
rinka jefasu cikin wuta a ranar alkiyama? Rabbi sallim
sallim gaba dayansu suka ce amin amin nima nayi maza
ciki zamu tsallake makatan
na tayasu fadin amin din.
Ban taba ganin babana a yanayi na farin ciki
kwatankwacin wanda na ganshi a ciki ba rannan cikin
zuciyata na ce oh ashe dai yana son 'yan uwan nashi in
da suke ne kawai bai son zuwa, ita kuwa baba Lantana
wacce itace mai abincin gidan nan nan taki ta tsaya ta yi
wani abin arziki sai tsaki takeyi tana fadin, uhun malam
wai shi ma nan yana da wayo yaga ya samu zai cusa
yarshi gidan masu kudi yaje ya nemo dattijon babarbare
wai shi ne wanshi don ya wanketa daga gorin rashin
dangi da asalin da kishiya zata rinka yi mata to dadin
abin shi ne babu abinda ban sani ba.
Dadin abin shi ne babu ta inda abinci bai yi ta
shigowa ba daga gidansu Mubarak ma katuwar kula aka
kawo cike da farfesun kayan ciki ga kuma tuwo miyar
83
kuka nima a cikin gidanmu nayi mishi burabuskon gero
da miyar kuka da naman kaji a ciki na kuma zubawa
kowa har da baba Lantana da ta k tsayawa ta yi girkin,
Anyi sallari sha'i sanda naji zuwan Alhaji
Muhammadu ya zo yiwa wan babana barka da zuwa va
kuma dade a wurin suna hira kafin ya yi musu sallama ya tafi.
Gaba daya 'yan hira suka watse aka bar babana da
dan uwanshi saboda kafafuwa sun fara daukewa alamar
dare ya fara nisa gashi kuma lokaci ne na sanyi amma
duk da haka baba Abba Gana ya shiga gida ya ki shiga
wai shi zauren ma ya isheshi don haka a nan sukaci gaba
da zamansu nima nayi maza na hura wuta cikin kasko na
kai musu.
A haka suka kwana suna hira ba na zaton sun samu
runtsawa don sau biyu ina farkawa cikin dare ina jin
zancensu sai dai bana gane me suke fadi saboda
barbarcinsu suke yi.
Washegari da safe daga gidan yaya Dija aka kawo
lafiyayyen abin karyawa wanda basu da cikin gidanmu
ba kawai har gidan su baba Sumaye sai da aka kai musu.
Ina zaune a gefe sai taya babana murmushin da
yakeyi nakeyi saboda jin dadin ganin dan uwa da yayi a
zuciyata kuma ina tunanin yanda muke ni da yaya Dija
haka su ma suke uwa daya uba daya sai dai kawai su
maza ne mu kuma mata, ina wannan tunanin ina kuma
kwatanta girman al'amarin da ke tsakaninsu sai na ji
yaya Ibrahim yana ce mishi, baba ai sai kawai ka tsaya a
yi daurin aure kafin ka tafi tunda ita Yacuwunan ai
kwanan nan ne za a daura auren nata.
84
Da sauri ya ce a'a a'a a'a ba za ta tsaya a nan ta
daura aurenta ba zata kai ta can gida dangi ma ta ganta
mijinta tana sonta ta bita can gida ma zata bata in bata
Sonta ta zauna ta bata miji a cen shi kenan miji kam tana
karewa ne?
Duk da irin yanayin da yayi maganar a ciki kowa ya
gane abinda yake nuff gaba daya sukayi tsuru tsuru ana
kallonshi an rasa mai karfin halin da zai musu maganar
tashi ni kuwa ko a jikina ban damu ba don ya ce zai tafi
da ni tunda dai babana ya yarda wanshi ne uwa daya uba
daya kowa ya gansu tare kuma sai ya yi magana a kan
kamanninsu dan uwan babana ne ban damu ba duk yanda
yaga dama ya yi dani musamman ma kuma da yace zai
kaiwa dangi ni don su kara yarda da cewar shi din ya ga
Abubakar yana nan a raye har ga sheda nan ya zo da ita
na yarda mai kama da shi karo na farko da na ji wani ya
ce wai ina kama da babana.
Yaya Ibrahim ya shiga yi mishi kalamai da bayanai
na nuna mishi wai ai tunda ya riga ya zo sun ganshi sunji
bayanin komai to yana tafiya za su je don haka ba sai ya
tafi da ni ba daga zarar an gama bikin zai gayawa angno
ya kawo musu ni ko ma mu taho tare dukanmu ai kaga
uban angon baba shi baya nan ne ya yi tafiya.
Baba Abba Gana ya kalli yaya Ibrahim cikin natsuwa
ya tambayeshi, a'a Ibrahimu zata hanata tafiya da abinta
ne? Yayi maza ya ce a'a baba ba haka bane. Ya gyada
kai tare da fadin, to insha Allahu zata je da 'yan uwana.
Ya sake bude baki cikin natsuwa ya ce mishi, to ko
zaka daga tafiyar daga gobe ka kai jibi don mu yi shiri
mu maida kai gidan.
85
Haka nan ba yanda nayi zaton ganin Gaidan din na
ganta ba gari ne babba da ya ci gaba a kan al'amura da
yawa musamman ma masarautarsu haka nan
zamantaaekwar garin akwai sha'awa a ciki mutane ne
masu kula da lamuran addini.
Babana yan uwa ne da shi sosai abin har