Showing 36001 words to 39000 words out of 41517 words
rabon ta kuma yaî naki zafi baki ga ke
har yanzu baki da komai ba? Ita wate tara babu kwana
biyar tayi ta haihu a gidan nan ina lissafi ban yi magana
bane kawai kina nufin da ya aureki a wancan ba zai
aureta ba'? Zai aure ta domin 'ya'yan dake tare da itan
nashi ne.
Don haka ki yi hakuri, ina share hawayena da bakin
gyalena na ce, to shi kenan ni na hakura ya daina taba ni
bana so bana so na hakura da shi tunda rabon ta ma yafi
140
nawa karfi to na bar mata shi ni ya kyaleni kawai, na ci
gaba da wani kukan.
Mubarak ya sake shigowa bayan ta amsa sallamarshi
bari muje in saukeki sai in wuce don za ni Bauci, to ko
zakaje kawai in na gama sai in tafi? Ya ce a'a uje kawai
ai babu damuwa.
Ta tashi suka tafi amma dai ranta a bacei watakila
saboda ganin kamar zuwan nata bai samar da wata mafita ba.
Ina zaune a falon ni kadai ina tunanin haushina takeji
saboda bata san kishi bà saboda tayi sa'a ita kadai ce a
gun mijinta ba zata iya fahimta ta ba saboda bata taba jin
irin zafi da ciwon da nake ji a cikin zuciyata ba.
Da kyar na iya tashi nayi wanka nayi salla na hau
gado na kwanta ko nemarwa abin da zanci ban yi ba ina
jin Rumasa'u tana ta kyakyacewa da dariya na kuma san
dadi ne ya kamata Mubarak ya yi tafiya a ranar da zan
karbi girki.
Nayi duk abinda na sabayi na al'adata na sa makulli
na kulle kofata na hau gadona na kwanta nufina wai in yi
bacci da wuri sai dai baccin bai daukeni ba wajen karfe
tara da rabi na dare na ji ana kwankwasa kofar tawa, na
tso nazo na bude shi na gani a tsaye fuskarshi a daure
alamar ranshi ya baci da kulle kofar da nayi, ban ma
tsaya a falon ba balle in yi tunanin yi mishi wani abu ina
jin shi ya. yi kaikawon da zaiyi ya gama maimakon ya
shiga dakin da yake kwanciya ya kwanta sai naji shi ya
shigo wurina nayi maza na gyara rufata.
Tashi muje wancan dakin, nayi maza na ce mishi a'a
ni a nan zan kwana.... wani irin cafka ya yi nmin mara
141
dadi kan kace meye wannan sai gani a inda yake nufin
ganin nawa, yi hakuri ki sa hannu ki rage kayan jikin
naki, na sake cwa uh'uh ba zan yi ba bana so kar kuma..
nayi maza na canza maganar saboda ganin abinda ya
soma yi to ai kai kace baka tilasta mace ko sanda kake da
guda daya ma baka yi hakan ba balle yanzu ya ce eh ita
kadai zan rinka yiwa wannan adalcin banda ke tundakin
bari na ganc ki na riga na gane ita daba ke daban, ni
kuma zan iya zama da ku dukanku bisa tsarin da ko
wacce take so banda haka kuma daga yau ba zan sake kai
kararki ba tunda na gane baki da mutunci mara kunya
kawai sokuwa sakarya wacce gata yia hanata fahimtar
abinda take ciki, zagin da ya yi min din zagi ne na
wulakaci bai kuma hanashi yin duk abinda ya shirya yi
ba.
Ance miki tsoro ne ya sa ni, kai traganarki wurinia?
Tana da girma ne a wurina da kika barta har ta fita baki
bata hakuri kan bacin ran da ta gmu da shi ba a
dalilinki, sannan duk maganar da kikayin naji wani abin
da baku i. himta b ke da Rumasıi'u shi ne ni din babu
wacce za 1a sa ni n yi abinda banyi niyya ba, sannan baa
zan saki wata a cikinku wani kato yaje ya auran min
mata ba, ba kuma zan yarda in karkata karkatar da zata
cutar da ri ba, dukkanku ing ennku ina kuma son
dorewar zamana da ku don haka zan zauna da kowacce
ne a bisa tsarin da ta nemi mu yi zaman ni da ita wacce ta
nemi zaman lafiya mu yi wacce ta nemi sabanin haka ma
ina shirye in wani zai yi min laifi in kyaleshi kuma ina
tabbatar miki in kikayi min ba zan kyaleki ba, ba zan
yarda ki bata min rai ki ga kamar kin ci bulus ba za ki
142
rinka tuna wane da kikayi min kaza nima nayi miki kaza
ba kalau kik kwashe ba, don haka admision din da na
saman miki na karanta Is!amic law a jami'a na janye shi
na fasa ba za ki yi karatun ba. Na soma kuka ina bashi
hakuri ya ce ai sai ki yi ai ba hauka nake yi ba saboda
kishi sai ki hanani taba jikinki tsawon wata guda? Kina
so ne ki rinka tirsasani da hakan? Ai itama ban barta ta ci
nasara a kaina da hakan ba balel ke, zuciyata ta kara
kutata zafin da ke cikinta ya kara karuwa kwoacce
magana zai yi sai ya hadani da ita kowacce magana zai
yi sai ya nuna min ta fini, za ki rinka tuna sanda kika
hanani kanki na hanaki, karatu saboda na gane wanda
kakayi a baya bai yi miki amfani ba don bakya aiki da shi
nan gabe in kika koyi sanya iliminki a cikin aya kanki sai
mu san abin da muke ciki.
Babana a shirya zuwa Gaidan wurin danginshi karo
na farko cikin shekaru talatin dabiyu shi da anti Safara da
jaririnta da su yaya Dija yaya Ibrahim nema zai kaisu a
cikin sabewar motar da tace min Mubarak din ya bashi
banje musu sallama ba banje musu sannu da zuwa ba
saboda bai ga dama ba, na rame na zube haskena ya ragu
saboda abubuwan da na samu kaina a ciki, a hakan kuma
na soma girkin gidan gaba daya saboda yace in karba ko
dama can kuwa tund awowar da' mukayi daga Jaji na
soma yiwa baba abincinshi na safe da na dare saboda
kasancewarshi mai lalurar suga.
Banje ko ina da fara yin girkin ba naji hirar
Rumas'au da kawarta tana gaya mata cewar a'a
abubuwan sunyi sauki sun kuma lafa daman ashe doki ne
kawai ya firgitata har ya nemi sata ta gudu ta bar ladanta
143
ai yanzu wayar gari take yi tana kwance tana hutawarta a
dakinta nike tashi da sassafe in yiwa yara wanka in
shiryasu in basu abinci su ci su tafi makaranta dole kuma
in yi ko don in zauna da shi lafiya tunda shi a kan
ya'yanshi babu abinda ba zai yi ba ko ita da ta haifesu
lallabashi take yi in dai a kansu ne.
Raina ya baci na samu kaina cikin wani al'amari nayi
kamar in daure in ci gaba kawai da abinda nakeyi sai
kuma naga ba zan iya in dai hidimar yuran zai iya zama
sanadin zarnana to ina ganin gara kawai ya zama ko na
samu in huta da 6acin ran da nake gamuwa da shi gashi
ko bacci bana iyawa matukar yana dakinta to ni kuma
bana iya bacci da daddare gashi tsakanina da shi abin ya
ki dadi.
Na kar6i girki ina cikin dakina a wkance da safe ban
fito ba balle in yi abincin karyawa ball in yiwa yaran
wanka, Ummulkairi ta shigo falon ina jinta ana gaya
mishi baba wai inji mamauau wai zamuyi lattin
makarant, to menene? Wai anti tazo tayi mana wanka ta
shiryamu.
Ina jira i ji kiraná zaiyi ko me zai yi Sai naji ya ce
mata ke tafi bani wuri ba a dade ba naji isowar
uwartata na ce Ummu tazo ta gaya maka za su yi lattin
makaranta, ya ce to menene? Ta danvi shiru kafin ta ce,
nace. wai wankan ba zata fito ba ne? Wacece mai
wankan? Ke kuturwa ce da ba za ki yiwa 'ya'yanki
wanka ki shiryasu ba, sai wata tayi musu?
Ta ce ahh hakama zaka ce? To su bar zuwa
makarnatar mana ya' ya na ne? Ai dama na sani tunda ka
samu kwana biyu...: ya yi maza ya katseta, in kika
144
gayamin magana a gaban yara, bata tsaya ba ta juya ta
fita, ban san yanda akayi ba sai naji an tafi kaisu
makarantar bai kuma dai fita ba balle ince ko shi ya yi
musu girki biyu a jere ban yi ba. Rannan ya zaunar da ni
yana tambayata, kina da mas'ala da shirya yara da safe
ne Maryam? Na ce mishi ch, menene mas'alar? Na ce a
canzamin wani aikin kawai ba wannan ba, bai ja ba ya
ce, to ki rinka yi m usu lesson, na ce to, za ki yi? Na ce
eh zan yi, ay ce to shi kenan na tashi nayi tafiyata ba tare
dan a tsaya gaya mishi wani dalili ba balle aje ana kace
nace, da na samu zarafin gaya mata magana kuma sai na
gaya mata cewar ni din zama kaina nake yi a wurin
mijina ba zamanw ani ba duk wata kunatawa da zan yiwa
wani to zan yi ne don in kara gyara auren nawa amma ba
don ina tsoron kar ya zamo mishi wani sanadi ba.
Rannan ya dawo daga tafiya ya shigo dakina ya
sameni Inna da Izzatu suna gaisheki da sauri na
tambayeshi kaje ne? Ya ce min eh, na ce amma baka
gaya min zaka ba'? Ya ce e ban yi niyyar cewa najen ba
sakon da ta bani in baki ne ya sa na gaya miki, tana ta
tambayata wani har yanzu haka kike babu komai? Nace
mata eh shi ne ta bani wani ita ce tace ni kawo miki
wannan amma na gaya mata cewar ke din maganin hana
haihuwa kike sha, ban yi mamakin jin maganar a akinshi
ba don naji irinta ko makamanciyarta a bakin Umam
bance mishi komai ba na sa hannu biyu kawai na karbi
Itacen na ce mishi na gode na kai daki na adana.
To a haka abin yake jifa-jifa zan danji wasu kalamai
Suna fitowa daga bakinshi wanda nasan ba ganin abin
yayi ba gaya mishi aka yi kamar in tambayeshi ta inda
145
maganganun suke zuwa msihi sai na fasa na ja bakina
kawai na yi shiru.
Ni da Rumasa'u kuma a wannan lokacin wani irin
zama m ukeyi na kai da gindi iyaka dai naki yarda mu yi
zaman gaba zaman da babu wata mu'amala a tsakaninmu
ko bata kulani ba gaisheta nakeyi sai dai hakan ba yana
ufin zata yi min in kyaleta ba ne ina kuma mu'amala da
yara in musu lesson in yi musu alheri gawargwadon
iyawata in kuma sukayi min ba daidai ba in hukuntasu
tun ina yi m usu hukuncin a ce su jira babansu in ya zo
Su gaya mishi har abin ya zama rikici tsakanina da ita
ban daina ba shima ukam ban taba ji ya yi min magana
ba.
Rannan Mubarak yana dakin ban san yanda akayi ba
dasawamukeyi tuns afe dai nasan yake tattalina yake
tarairayata watakila saboda yana bukatar daren ya zamo
mai cike da kwanciyar hankali, to dansa hannu ki rage
kayan jikin nan naki mana Maryam yaushe rabon da ki yi
min irin wannan mututnawar? Ba fa najin dadin irin
wadannan abubuwan na tashi zaune na soma cire kayan
jikin nawa saboda nima ba jin dadin karfin da yake
gwada min nake yi ba, dadi ya kamashi, yanzu in duniya
tana da gaskiya Maryam ni ace tsakanina da ke zaki iya
hanani jikinki? Wannan jikin dai to na wane ne? Ban
kalelshi ba nace naka ne, to me nayi miki ya sa kike
gayawa mutane ba za ki yi a zama da ni ba? Wa ya gaya
maka? Ya ce uh'uh kar ki tabmayen wanda ya gaya min
kin fada ko baki fada ba? Cikin natsuwa na ce mishi, na
taba gayawa yaya Dija banda ita ban taba gayawa wani
ba itama kuma nasan ba zata fada ba, ya yi maza ya ce
146
haka ne me nayi miki? Bance mishi komai ba sai naji ya
ce min, kishi ne ya yi miki yawa Maryam ni kuma bakya
barina inji tausayinki sai kice zaki tirsasani, ba zan iya ba
ba zan iya yarda da hakan ba saboda ina gani na cancanci
abubuwa guda uku daga wurinki saboda dalili guda daya,
na cancanci kulawa tausayawa da kuma rangwame, ki
kula da ni ki kyautatamin saboda kasancewata a
tsakaninku a tsakanin naku kuma ina cikin zargi, dole
kuma in yi adalci saboda shari'a bata barni in yi abinda
naga dama ba ta kewayeni da dokoki in nayi miki
kuskure kuma ki yi min rangwame saboda kin san
kuskure nayi kin sani sarai ba zan 6ata miki da gangan
ba ai ina gudun 6acin ran naki bakya ganewa na
wadannan abubuwan kuma don kin yi min su ba komai
bane saboda ina sonki ba dabi'ata bace fadin hakan
amman kin sani na koya karfi da yaji a hakan kuma ban tsira ba.
A hankali na ce mishi, to ka yi hakuri, ya ji dadi
sosai, a hankali ya sake ce min, to yi min wani alkawari
bayan hakurin da kika bani don in kara samun natsuwa a
raina, ba zan sake hanaka jikina ba, ya sa hannu
juyar da ni ta yanda muka fuskanci juna, ba za ki sake
ganin bacin raina ba kenan ai ko laifi kikayi nasiha kawai
zan rinka yi miki ba fada ba, ai da wata ce tayi min
yanda kika yin sai in bata wata shida to amma ke da yake
kin san ba zan... na katseshi ta hanyar tambayarshi,
ya cem aka ina hana kaina haihuwa? Ya ce uh'uh ai nace
kar ki tambayen amma ba ga magani nan Inna ta ce ta
kawo miki ba ki sha ba me yasa? Yaya Dija ce ta ce in
ajiyeshi tukunna, ya danyi shiru kadan kafin jimawa ya
147
sake tambayata, da ma ita antint asan da wani abu ne?
Nayi shiru to shi nę ni ba za ki gaya min in sani ba, Inna
ma in gaya mata hankalinta ya kwanta, kinga yanda ta
kosa taji kina da wani abu kuwa sai kace bata taba ganin
jika ba.
Tun daga ranar muka koma zama mai dadi tsakanina
da shi sai dan abinda ba za a rasa ba ban sake yarda wani
abu ya faru tsakanina da shi da ya zama dalilin da nayi
mishi rowar kaina ba, hakan kuma sai ya zama sanadin
raguwar bacin rai a tsakaninmu.
Ana cikin hakanc ikina ya kai watanni bakwai yaya
Dija ta soma yi min aiken magugunan zaki da saukin
nakuda sai dai bana sha don basa yi min dadi rannan ta
zo dubani muna hira sai ta ce min bakya shan
magungunan saboda bakinki ya saba da zaki bari zan
Rara tambayar baba Lami inji rake ne yake maganin zaki
ko zuma ne? Wadannan kam ai za ki sha ko? Nayi maza
na ce garama dai ace raken ne, to ki dai bari in kara
bincike tukunna nace to.
Tun daga washegarin ranar na soma shan rake a
matsayin maganin zaki da kuma saukin nakuda, sai in
wuni ina sha ina gyatsarshi ina karawa in naga ya kusa
ya kare mi ince Isiyaku a kawo min rake ya ce to ya
kawoshi cikin wheelbarrow, ke Maryam kin tabbatar
raken nan da kike sha haka maganin zakin ne ko? Ince
mishi eh baba Lamin gidan su yaya Dija ce fa ta fada ita
kuwa ka san babba ce haihuwarta goma sha hudu sai
Mubarak ya ce min to babu laifi.
Rannan na wayi gari bani da lafiya nayi maza na
yiwa baba abincinshi na safe da na dare na aike mishi da
148
shi saboda tun daga jin cabkar farko da nakudar nan ta
fara yi min na gane uh lalle da magana ba karamin artabu
za a yi da ita ba. Kafin hantsi har na fara gundura da ita
na fara gurnani ina mita tafdijan yanzu duk uban raken
nan da nayi ta sha dama haka zamuyi da nakudar nan?
Mubarak ya kalleni ya kawar da kai, to rake da kika yi ta
sha ba dadi kika sha ba? Na soma kuka, yayi maza ya
dakatar da ni, ke Maryam tsaya in gaya milki mata fa
basa kuka in zasu haihu har ki yarda ki yi abinda
Rumasa'u za ta zo tana yi miki gori don ita ba ta kukan
haihuwa.
Hankalina a tashe na ce to kar tayi din mana ni ina
ruwana? Ya mike ya kama hanyar fita tare da fadin, bari
in kira su Umma su zo su kaiki asibiti da wuri tun baki
jawa kanki wani abin magana ba a gidan.
Sy Ynna syja sgugi daudau uba cewa uh uh uhh tafi
can lalle yau za a yi ta, ba za a yi komai ba, lafiya yau za
ki haihu ai duk wanda kika gani da danshi abinda ya ji
kenan kafin dan ya kai ga zuwa hannu.
Waiyo waiyo kwankwasona ai yau kam ina jin gaba
daya zai ratattake ya zube a kasa da dai ace na san haka
ne da ban bata lokaci ba ma wajen shan raken nan.
Rumasa'u ta kyalkyale da dariya har tana neman
wurin zama a dalilin dariyar ta tsananta lalel yau mata
zasu haihu tafdijan.
Takaici ya kama Mubarak ya rasa yanda zaiyi dani to
wai ke babu dama ki rufe bakinki ki yi shiru ne? Umma
ta ce a'a to wai kai ina ruwanka da ita ne? Nace uhun
kyaleshi kawai bai san yanda abin yake ba ne waiyo
waiyo kwankwasona.
149
Sannu Maryam, Umma ce mai yi min sannun sai in
ce mata yauwa Umma na gode.
A haka mukaje asibiti muka samu yaya Dija don an
gaya mata za a kaini asibiti, ita kam saboda takaici ji ta
rinka yi tamkar tayi amai don bakin ciki, to wai ke ba
dama ki yi shiru ne? Sai ince uh uh yaya Dija ba ki fa san
abinda nake ji ba kin san ke naki masu saukin kikeyi da
rakin da magana, ganin da kukan da ihun kiran likitan
gaba daya basu sa haihuwar tazo ba sai da lokacinta yayi
wajen karfe goma da rabi na dare gabjejen yaro kato ga
girma ga nauyi tubarkalla gashi mai kyau sai raba
idanuwa yake yit amkar dai ace kallon mutane yake yi.
Suna Mubarak ya yi irin wanda Rumasa'u da yan
uwanta sukace wai bai taba yi ba ya kuma sanyawa
yaron suna Muhammad ya kara yiwa babanshi takwara
bayan da ya yi mishi da danshi na biyu wanda yake
namiji 'yan uwan Mubarak na Jaji sunzo sunan ba kadan
ba sun kuma zo min da alheri mai yawa, Inna ma ta cika
alkawarin da ta yi na turo min Izzatu ita da Inna ne da
kuma tsohuwar da aka daukar mun suke tayani hidimar
jegon.
Duk kokarin Mubarak na ya boye ya barwa
zuciyarshi al'amuranshi don ya samu tsaida adalci
tsakanin iyalinshi ya kasa kawar da kai a kan
al'amarinshi yana ganinshi yake sakin lallausan murmshi
na kuma san da wuya in har ya san sanda yake yin hakan.
Wani irin lafiyayyan jego nayi ni da yaron muka
zama tubarkalla in banda ina aka saka damu babu abinda
Mubarak yake yi da mu.
150
Rannan ya shiga dakina ya fito a lokacin nan kuwa
satina uku ne da haihuwa na tsala wata irin kwalliya da
in ka ganni sai kayi zaton ranar ne zan karbi hidimar mai
gidan, biyosyi nayi tsakar gida ina rungume da yaron a
kafadata, karbeshi mana to ba ka ce wurin baba zaka ba?
Kaje mishi da shi mana, maganata nakeyi ba tare da na
damu da zaman Rumasa'u a tsakar gidan ba.
Mubarak ya juyo ya karbeshi yana kara lillibeshi atre
da fadin, ki fa rinkayin hankali da shi girman jiki ne
kawai... bai karasa ba sai kawai muka jiwo Rumasa'u ta
kwallara ihu da sauri muka juya don ganin abin da ya
sameta kwankwaso naga ta rike da iyakacin karfinta
gabana ya yi mummunan faduwa