Showing 21001 words to 24000 words out of 41517 words
abin
mamaki yanda ya iya tsallake yan uwa da dangi masu
yawa haka yayi tafiyarshi ba tare da ya taba waiwayarsu ba.
Sai dai banfi kwana uku da zuwa garin ba na soma
jin labarai iri iri na abinda ya yi dalilin da ya sa babana
ya tsallakesu ya yi tafiyarsu, labaran dai iri-iri ne kowa
kuma da irin abinda yake fada sai dai wanda nafi
kamawa shine wanda matar baba Abba Gana ta bani da
kanta wato Kabudi sunan da na ji suna kiranta kenan ita
ce ta shedamin cewar su su babana su biyu ne wurin
uwarsu daga shi sai Abba Gana saboda ita uwar tasu ta
rasu da wuri hasalima bayan haihuwar baban nawa da
kadna ne ta rasu, sun fara maraicin mahaifiyarsu baa
wani dade ba sai na uba ma ya samesu don haka sai
rikon nasu ya koma hannun kanin mahaifinsu wanda ko
kadan bai kula ya tsare zumuncin dake tsakaninshi da
dan uwanshi da ya rasa ba banda gadonsu da ya cinye
tun basu isa komai ba sai kuma suka taso a hannun nashi
cikin wahala mai yawa shekara da shekaru dai su ne
masu noma mishi gonakinshi da suka taso kuma yaga
sun isa munalin aure har wani tsohon aminin babansu da
ya rike zumunci ya baiwa Baba Abba Gana auren 'yarshi
shi sai ya nuna yarshi da ta soma tasowa yace in ta isa
aure ta babana ne tana isa auren kuma sai dan mai kudin
87
garin ya zo ya ce yana sonta sai kawai ya dauketa ya
bashi ya ce babana ya yi hakuri ga kanwarta nan in ta isa
auren zai bashi itama da ta isa auren sai ya dauketa ya
sake baiwa wani da ya zo daga waje ya bashi kudi bai
lura da cewar shekara da shekaru babana ke nomoe mishi
gonakinshi ba, ana cikin haka ne ya sake cewa an satar
mishi kudinshi da yake binnewa a gonarshi a gindin
bishiya babu kuma wanda zai yi mishi wannan satar in
banda babana don yafi kowa sanin gonar a dalilin haka
ne ya yi mishi wulakanci a bainar jama'a, tare da fadin
wai tuni dama shi ya gane duk sace-sacen da ake yi a nan
gidan dama makwabta ba kowa ba ne ila shi kam haka ya
kwace mishi 'yan kadarorin shi da ya yi aikin kodago ya
dan adana kwanaki biyu ne kawai da faruwar hakan da
safe ya dauki garmarshi ya fi ta kamar yanda ya sabayi
kullum sai aka ga shiru bai dawo ba aka bishi gonar ba a
sameshi ba sai garmar tashi aka gani a ajiye a kan
daukota aka dawo da ita gidan tund aga ranar babu
wanda ya sake sa Bukar a idonshi sai ko wannan ganinn
da dan uwanshi yaje ya yi mishi, sunyi nema sun yi
nema har suka gaji 'yan kwanaki kadan da tafiyar tashi
sai ya baiyana kowa ya gane ba shi ne mai yin dauke
dauken nan ba dan kanin baban nasu ne da suke kai daya
da shi don ko da ya bar gidan ba a daina ba banda haka
ma sai kawai aka kama shi da akuyar mutane ya yanka ta
ya durata a buhu, hankalin babban nasa bai yi
mummunar tashi ba sai da ya ga damuna tazo ya rasa mai
nome mishi gonarshi ga kuma dan nashi da surkayen
nashi suna kallo lokacin ne ya yi nadama mai tsanani ya
yi kuka har ya gaji ya nemi Bukar har ya zama abin
88
tausayi a kan neman nashi ko zuwa akayi aka bashi
labarin cewar anga wani mai kama da shi a wuri kaza sai
ya debo kudin mota ya ce a tafi a gani ko shi ne sai aje a
dawo a ce mishi ba shi bane, sula yi nema har suka debe
tsammani, suka hakura sai a 'yan shekarun nan da yan
uwan Malam suka yi ta rasuwa sai hankalinshi ya sake
tashi ya sake yin niyayr zai sake neman Bukar ko zaiyi
dace in har yana raye su ga juna kafin rai ya yi halinsa
shekaru biyar kenan yanzu tunda ya koma bai da wani
aiki sai na rokon Ubangiji ya sadashi da dan uwanshi in
har yana raye in kuwa baya raye to ya nuna mishi wata
alama da zai gane hakan don ya samu natsuwar da zai
hakura to a cikin hakan ne ya samu labarin anga wani
mai kama da shi a can kasar kudu ya shirya ya tafi ya yi
iyakar neman da zai yi har ya gaji ya dawo bai sameshi
ba wannan fitar da ya yi dai na wannan karon shi ne fita
ta uku ko hudu da ya yi sai kuma gashi ya dawo cikin
nasara.
Cikin natsuwa nace mata, shi kanin baban nasu ya
dade da rasuwar ne ya kabidi? Bana shekararshi tara
kenan, cikin shekaru taran nan kuwa ba karamin zuba
akayi ba a gidan kin ga wancan dakin da wanene da
wance a ciki wannan ma da su wanene in takaice miki
dai a yanzu daga babanki ne sai dan uwanshi goni su ne
manya a gidan shi kuwa goni shi ne dan karami baban
nasu kanin wancan da suka taso tare da Bukar.
Tausayin al'amarin ya kamani can cikin zuciyata na
yi tunanin duk yanda abu ya kai da zai tsakaninka da
dan uwanka to yafiya ituce maganin al'amarin tunda in
ma baka yi hakan ba watarana sai a wayi agri ba wani a
89
cikinku, sannu a hankali kuma sai dukkan ku ma ku kai
ga karewa.
Babana dangi ne da shi masu yawa ku san kullum sai
baba Abba Gana ya bada umarnin a kaini wajen wasu da
ya dace su ganni duk da na gane abu mai zati aka yiwa
babana wanda ya yi dalilin barinshi gida babu ma dai
irin satar da aka dala mishi don kuws na sah jm manya
su na fadin wai ita satar dan halal ma baya yinta to amma
duk da baka sai na rinka ganin tamkar da bai yi fushi mai
tsanani ba haka da yayi ya tafin ya samu kamar wasu
shekaru da basu tsananta ba da sai ya waiwayi dangi
musamman ma da yake a can in da ya tafin shima ya
samu rubonshi na aure.
Baba Goni shima mutumin kirk ne amma da ganin
tsarin zarman nasa da baba Abba Gana kasan ba karanmin
hakuri yakeyi da shi ba.
Wata irin kulawa baba Abba yake yi min amman duk
da haka bai hana sanda na kwana bakwai a gari naji
hankalina ya kona gida ba kewar mutacn da us baro ta
fara damuna babana, yaya Dija da iyalanta sannn a
hankali sai naji shima Mubarak ina som ganinshi ban
kuma ji hankalina ya tashi na gane har a vanzu da kulım
nake kin auren Mubarak ba kararmin son shi nake yi ba
don kuwa a ranar da na ji kishin kishin wurin Yatakabudi
cewar baba Abba Gana ya ce ba zai sake barina in koma
gida ba zai rike ni ne kawai ya aurar da ni a nan don da
hakan ne kawai yake ganin zai karfafa zumunci
tsakaninmu da yan uwanmu da mu da su ba wan
shakuwa muka yi ba tunda in ya aurar da ni a nan to ko
Su basu raye zumunci zai dore a tsakaninsu yaya Dija
90
zasu rinka zuwa ko ba don kowa ba don ni su ma nasu
ya'yan tunda gani a cikinsu zasu kula da zumuncin dake
tsakaninmu da su yaya Dija, kasa bacci nayi kwana nayi
rannan ina tunanin duk da tunanin nashi unari ne mai
kyau ama anya zan iya zama da wani mijin kuwa
matukar ba Mubarak ba ne? Duk wani mutumin da ya
taba zuwa wurina kan maganar aurena na amince wani
dalili yana hana auren nake mancewa da shi inji garama
da ba a yi auren ba ya fiye min in gamu da shima ban yi
komai ba saboda bani da wata danuwa gamne da
game
al'amarin shi amma banda Mubarak, Mubarak ne mutum
daya da zuciyata ta kasa daina kishinshi na kasa daina jin
zafinshi na kasa fita cikin harkokinshi in daina son jin
abinda yake ciki, na kan dai daure in kawar da kai game
da shi har in bude baki ince mishi ya fita harkata amma a
zahiri ne kawai hakan yake faruwa yana gwada zai fita
harkar tawa sai inji nayi matukar takura, dan sa'an da
nayi ma shi ne shi din ba wani jarumi bane kan lamarin
fita harkar tawa da ban san yanda na rinka ji ba a raina.
Kwana biyu bayan maganar da Yakabudi tayi min
naje dakin baba Abba Gana da safe don gaisheshi kamar
yanda da ma kullum nake yi tun zuwana gidan sai ya
zaunar da ni yana yi min bayani game da muhimnmancin
yin auren zumunci a wurina ga dan Uwanki nan da na
yiwa Bukar takwara da shi don shi ne dan da Kabudi ta
fara haifa bayan barin shi gidan sai in hadaki da shi dan
uwanki ne amma ba zan yi hakan ba sai na baiwa
mutumin da aka gaya min cewar yana sonki lokaci na
kwanaki ashirin da dayu in har ya biyoki kafin cikar
wadannan kwanakin to shi kenan ke din rabon shi ce in
91
kuwa bai zo ba sai bayan cikarsu ko da da karin kwana
biyu ne to ba zai saurareshi ba.
Hankalina a kwance na ce mishi to baba saboda ni da
kaina na gamsu da adalcin da ya yi na bada wa'adin
kwanaki ashirin da daya duk da dai a lokacin ina da waje
kwanaki tare ne a gidan.
Yan uwan babana sun nuna min gata na zumunci
sun martaba zamaa a cikinsu sun kamama bakuntata irin
karramawar da har na rinka yin mamaki sai dai duk da
haka zuciyata tafi son in koma gida kusa da babana da
yar uwata yaya Dija da iyalinta in so kuma shi ne samu
to zanso ace na wayi gari a gidan Mubarak a matsayin ni
din matrshi don haka sai nayi ta addu'a ya iso Gaidan
kafin cilar kwanakin da baba Abba Gana ya dibar mishi
na kwanaki ashirin da daya.
Ranar da na cika kwana goma sha hudu wato sati
biyu cif da zuwB garin Gaidan sai ga Mugaram ya iso
babu wanda ya yi zaton ganinshi a lokacin har nima farin
ciki irin wanda nayi bai raisaltuwa sai dai ban bari an
gane ba.
Sub iyu ne suka zo abinda naji ana gayawa Yakabudi
kenan sai nayi zaton ko shi da Amiru ne, sai da na shigga
dakin da aka saukesu na gansu eai naga ashe ba Amiru
bane, rana marya ya dade, inji abokin nashi.
Mubarak ya harareshi, kai nan har wani kulata
zakayi? Ya yi dariya to ba zan kulata ba me ya kawoni?
lta amaryar ma ance maka ta na yin laifi ne? To ai shi
kenan tunda a wurinku bata.yin laifi.
Na gaida abokin nashi cikin mutunci da girmamawa
a hankali Mubarak ya tambayeni, kin ganeshi kuwa? Na
92
gyada kai muna alamar eh, ya sake kallona a ina kika
sanshi da kikace kin ganeshi, na yi murmushi kawai nayi
shiru, gayamin sunanshi in har kin gane shin da gaske,
ban fadi sunan ba saboda in girmamashi sai na ce mishi
na taba ganinku tare da salla ka ce min daga Kaduna
yake.
Ya yi murmshi ya ce, a to ai tace maka ta ganeni kai
Icafi so sai ta ambeci sunana ga tsal ita kuma mai kunya
ce, to ni shikenan yi ta zugata.
Na matsa kusa da kwanukan abincin da na samu an
kai musu na soma budewa yallabai ai baku ci abincin ba,
bai kalleni ba ya ce, to abinci muka z0 ci sunje sun
dauko min mata ba da sanina ba sun kawo min ita nan ni
banyi musu muzurai kan abin da suka yi min ba sai su ne
kuma wai za su yi min? Cikin natsuwa na ce mishi, too
kayi hakuri si kasan iyaye ne.
A hankaii ya dago ya kalleni har da shi ma wannan
gorin a cilkin iyayen ya kare? Jin yanda yayi maganar a
kanshi ya sani yin maza na ce msihi, shima fa kanin
babana ne. Ya yi kamar bai sani ba, au haba? Ai na
dauka shima yana cikin maneman naki ne? Abdulhamid
ya yi murmushi tare sdaa fadin, kai kam Ahamad
Ubangiji ya shiryeka surikin naka kake cewa yama cilkin manema.
Mubarak ya murtuke fuska ya ce, to menene don ya
nema ba 'ya'ya maza suke da babanta ba ta haramta ne a
wajenshi? Ai ni wannan mutumin ban yarda da shi ba
don bai yi min kama da wanda zan yi surkuta da shi ba
baka ga ko kadan bai yi murnar zuwan namu ba?
93
Na kau da kai daga zancen nashi saboda ganewar da
nayi bai san komai maganganunshi ne dai kawai na'zato
da kishi da ya saba da su na soma zuba abincin da aka
kawo musun na mika mishi ya karba ya ajiye a gaban
Abdulhamid kafin ya sake karbar wanda na sake zubawa
ya ajiye a gabanshi.
Suna gama cina bincin Abdulhamid ya mike, kai nifa
zan sha iska a waje daga nan inga yanayin wurin, bai jira
amsar da Mubarak din zai bashi ba ya ficewarshi.
cikin nutsuwa na kalli Mubarak na ce mishi, ashe ka
dawo? Ya ji dadin irin karbar da nayi musu ha watakila
bai zaci hakan don haka cikin murmushi ya ce min, na
dawo na zo ban sameki ba na ce darma ana yin haka ne
mace tayi tafiya mai tsawo irin wannan babu izinitn
mijinta ba a gaya musu an riga an bani ke ba ne? Gashi
anzo suna cewa wai ba za ki bini ba ni kuna na zo ne da
niyyar tafiya da ke ban gane abinda suke ba fa ko kin san
da wani abu ne? Na ce mishi a'a sai dai a'a da nace bai
hanani gaya mishi bayanin da baba Abba Goni ya yi min
na ce to amma ai kazo kafin cikar lokacin da ya diban.
Ya kalleni cikin nutsuwa ya ce, ke dai kawai ki danyi
gaban ki jiramu a kan hanayr can ta shigowa unguwar in
muka fito sai kawai mu daukeki mu yi tatiyarmu don in
ba haka ina ganin wadannan ba rabuwa da su lafiya zan
yi ba.
Na yi murmushi na ce, haba yallabai ranka ya dade ai
kaima ba zaka so in yi irin wannan salamar da su ba in ka
bisu a hankali sai ku daidaita shi baba Abba Gana ai
al'amuranshi masu sauki ne gashi kuma mutumin kirki
ne sosai.
94
Hira sosai mukayi da Mubarak irin wanda ko da
bamu taba yin irinshi ba ko kuma mun dade har na
mance rabon da mu yi irinshi, nayi mishi kalamai masu
8aua ya samu natsuwaa tare da shi.
In dai sake komawa wuinshi kenan da maganar?
Nace mishi eh, to babu laifi bari in kira Abdulhamid
muje inda tuntuni haka kikeyi min Meor ai da babu
dalilin da zaisa in yi ta sakin baki ina daddankara miki
bakaken maganganu, to in nazo da damuwa sai kice sai
kin karamin to in ban gaya miki bakin ki ji kema inda
dadi ba yaya zanyi? Ban tanka mishi ba na wuce na tafi
don su samu damar sake ganin baba Abba Gana.
Sai bayan sallar la'asar ya sake aikowa a kirani a
jikin motar da suka zo a ciki na sameshi, to mun daidaita
da su Maryam duk da dai ba haka naso ba to amma tunda
mun ajiye matsayar da muka yarda da ita shi kenan
magana ta kare, ya ce a nan zan yi daurin aure a nan zai
yi biki saboda ba zai yiwu a ce za a dibi jama'a a je can
ba lokacin biki kuma da kyar ya yarda da kwanaki talatin
da biyar nan gaba sati biyar kenan sannan wai a nan za a
bariki.
Na ce to ai kamar yanzu ne sai kaga lokacin yazo, ya
ce to yi min wata magana komai kankantarta da zai sa in
ji damuwar da ke zuciyata tayi min sauki don bana son
tafiyar da zanyi in barki.
Cikin natsuwa na sunkuyar da kaina kasa don in
tabbatar bai taf ida wata damuwa ba sai na ce mishi, ai
ko ka tafi ka barni a nan din ba wani abu bane babu wani
abin da zai faru a bayan naka sai alheri, ya ce to babu
laifi.
95
Sai bayan tafiyar su Mubarak din ne na gane banda
dinbin tsarabar da ya kawo musu har da kyautar manyan
kudi ya yi musu ga kuma lissafe-lissafen da Yakabudi
tayi mishi nasu a wurinsu ans bada kudin yin lalle da
kuma na turare ya tambayi yewan su ta fada suma ya
bayar.
Sallama mukayi da Mubarak ba tare da ya gaya min
cewar zai dawo ba amma sati biya bayan tafiyar tasu sai
gashi ya zo shi da Amiru wani sati biyun mns beym
nan ya sake dawowa a lokacin nan kawa baifi kwanaki
biyar sulkz saura a fara bikin ba.
A Ciki wadannan kwanakin kuwa babu abin da
Yalkubudi bata yi min ba wanda suke yi wa amarensu ko
da yake ma kamar karasawa ne don tafi kwanaki talatin
tana min jike-jike, hayake-hayake, tsime-tsimw, gogo
goge, gyare gyare, kuilum kuma ta kan yi ne tare da yi
min bayami wannan uban zirga-zirga da wamuiea yro
yake yi ai gara a kara gyara mishi ke ya sameki.. kin san
ance wai ko kana da kyau to ka kara da wanka kar ki
yarda ki zauna bakya gyaran jikinki don shi namiji da
kike kallonshi.... ta danyi shiru kada katin ta ce, uhuyy
ke yanzu yarinya ce ba za ki gane yanda alamarin yake ba tukunna.
Ana cikin haka kwanakin biki suka iso jama'a suka
yi ta haduwa fiye da duk yanda ake ko daga gida
mutanan da sulka zo bikin ko kadan banyi zaton ganinsu
haka ba Umman Mubarak, Yakumbo Halima, baba
Sumaye, baba Lami, manyan dattawa wannan yan
matasa yaran mata kuwa akwai anti Asiya aminiyar yaya
Dija da malamata malama Basma akwai yar anti Safara
96
ga wasu mata su uku da suka gabatar min da kansu a
matsayinsu ne angwaye alamar ko dai kanne ko kuma
abokan wasan Mubarak sai dai ban san ta ina ba maza
kam babu adadi don kuwa naji ana ta maganar yawan
nasu abokan Mubarak da yawa sun zo daurin auren ga
samarin unguwa irin Isiyaku su ma ba a barsu a baya ba
don kuwa shi mai mu'amala da na kasa da shi ne abokan
babana irinsu baba Baidu da baba Hodijo kasuwar
timatir su ma ance mota guda suka zo abin dai gwanin
dadi gwanin sha'awa.
Ina kwance a dakin da nake zaman lalle ina lullube
da kaina na ji an shigo an zo an durkusa a jikina a
hankali na bude ido don ganin waye hakan? Inna na gani
da sauri na saki wani lallausan murmushi yaya Dija ta zo
ne? Ta ce a'a babanmu ne ya zo da mu ni da Abba,
sannunku da zuwa na mike na zauna ina nunam ata
kwanukan da na san akwai abinci a ciki don taci ta
girgiza kai nuna alamar ta koshi.
Buki baba Abba Gana ya yi irin wanda yake yiwa
ya'yan da ya haifa a cikin shi kona ince fiye da haka
dno kuwa yayi hidima ya ciyar da jarna'a abin ba a
magana, bayan san kowa daga jama'a ne aka yi daurin
auren bai yarda an dauki amarya kamar yanda abokan
Mubarak suka so su yi ba sai ya ce tafiyar tayi nisa baza
a dibi mutane masu yawaa yi irin wanan tafiyar da su
ba a cikin dare.
Don haka aka bari sai washegari a waunan lokacin
ango baya zuwa wurin daurin aurenshi don haka
Mubarak bai zo Gaidan ba yana Kaduna wurin
harkokinshi.
97
Washe gari ana gama karyawa akayi ta shiri ana fita don shiga motocinda