Showing 15001 words to 18000 words out of 41517 words
ko dama can kuwa mafi yawancin zuwan nashi kan
62
zamo cikin dare ne lokacin da zirga-zirgar dubiya tayi
sauki in dai ba wani dalii mai karfi ne ya kame na yazo
da ranar ba.
Rannan da safe ni da yaya Dija ne kawai a tara da shi
bayan mun goggoge mishi jiki mun gyarashi mun
tsabtace komai na dakin sai kamshi yake yi yaya Dija ce
a kusa da shi tana bashi ruwan tataccen kabeji da karas
yana sha a hankali yayin da ni kuma na gama tattara
kayan wanke-wanken mu na mikawa Inna nace taje ta
wanke sai kawai mukaji an turo kofar dakin a hankali
tare da yin sallama, gaba daya muke amsa sallamar tare
da maida hankalinmu wajen kofar.
Gabana yayi mummunar faduwa saboda ganin mai
sallamar, Umma ce ko ince Umman Mubarak tare da
Rumasa'u da Rukaiya, kadan ya rage in dibibice in rude
saboda rabon da muyi gaba da gaba da su haka an dade
ko ince tun daga ranar da abinda ya faru tsakanina da
Mubarak na samuna da akayi a dakinshi da al'amuran da
suka biyo baya wa ta mu'amala bata sake hadani da wani
daga cikin mutanen gidan ba, wacce tayi dalilin
haduwarmu a wuri daya kamar hakan ba dan gara-gara
Rukaiya in ta kure mana a makaranta mukan gaisa
saboda munyi karatu tare.
Sannu da zuwa Umma yaya Dija ce ta fara yin
gaisuwar daidai tana mikawa Umman kujerar zama, na
mika hannu don karbar yarinyar da take hannun
Rumasa'u duk da yanayin dake fuskarta tamkar dai ace
mu din ba wasa tare muke yi ba, gaba daya aurenta da
Mubarak ya canza al'amuran dake tsakaninmu ni da ita
kowa ya fi jin zafin wani oho?. Ko da yake dai nikam can
63
cikin zuciyata na sani bana jin zafin Rumasa'u kamar
yanda nake jin zafin Mubarak da wadanda suka sashi
aurenta.
Gaba dayansu na bisu na gaishesu kamar yanda naga
yaya Dija tayi, yaya jikin na malam? Yaya Dija ta sake
amsawa Umma zancensu ni kuma na dawo da hankalina
wajen sauraron abinda Rukaiya ke gaya min naga Hasiya
jibirin shekaran jiya ta tabaye ni ke na gaya mata tace in
gaisheki itama zata zo, nayi murmushi na ce mata ai jiya
tazo nan ta kusa wuni muna zancenmu ban sake Juyawa
na kaili Rumasa'u ba saboda bata bani fuskar da zan iya
fuskantarta in kakalo wata naganar da zanyi da ita don
haka na ci gaba da wasa da 'yarta da kuma hira da
Rukaiya, kc kadan dai banji dadin sammakon da sukayi
mana ba an saukin abiıma sun zo sun samu babana da
kuma dakin da muke ciki cikin tsabta.
Bayan tafiyarsu yaya Dija ta kalleni tayi murmusbi ta
ce, kai kishi babu kyau mata suna kokari, ban tanka mata
ba balle zancen ya yi nisa na kalli knna na ce mata, jeki
ki yi mana wanke-wanke kin ji? Ta ce to ta tashi ta fita
ba fa zuwansu bane ina jin Alhaji Mubarak ne ya turosu.
Na sake kin amsawa don kuwa ban san dalili ba sai naji
bani da ra'ayi a kan zancen nasu.
Sati biyu da aikin babana aka sallatmo mu muka dawo
gida bisa dokoki da aka jaddada mana binsu. Ranar wuni
nayi ina aiken Inna gidajen mutanen da sukayi ta zirga-
zirga suna ta dawainiya da mu irinsu Jumare gidan baba
Hodije Yakubo Halina, Hasiya Jibrin, malamaina ua
Markas irin su Malama Basma da Hindu abokan
karatuna na makarantar mu ta ilimi addini mai zurfi
64
musamman wadanda mukayi aji daya da su wadanda har
karo-karon kui suka yi suka kawo min don taimakawa
Zumunci irin wanda mutane suka nuna mana a wannan.
lokacin babu abin da zamuce musu sai dai addu'ar
Ubangiji ya sakawa kowwa da alherinsa amin summa
amin.
Mun dawo gida da babani a dalilin saukin da ya
samu kowa murna yake yi muna farin ciki musamman
da yake a yanzu yana da mata mai kula da tattali da
kokari ganin asirin gidanta ya rufu sai dai kuma hakan
bai hana hankalina da zuciyata tafiya wajen tunanin
abitda ya hana Mubarek zuwa yiwa babana muriar
dawowa gida ba rabonshi da zuwa asibiti tun kwana biyu
ko uku da yin aikin bai sake takawa ba to yanzu kuma
mun dawo gida ga mu ga shi ba zai shigo ya gaisheshi ya
karasa ladanshi ba bayan duk irin hidima, dawainiya da
ya yi da rashin lafiyar tashi, to ko dai matarshi ce ta
hanashi zuwa? Tanbayar da ta zo cikin zuciyata kenan,
nayi kokarin in kawar da hakan ta hanyar tambayar kaina
anya Mubarak yana yiwa matarshi irin wannan tsoron
kuwa? To amma me akayi mishi? Da dai naga damun
kaina kawai zanyi sai nayi maza na cire wannan tunanin
daga cikin zuciyata na maida hankalina kawai wajen lura
da halin dà babana ke ciki ina kuma rama bacci da
gajiyar zaman asibiti tinda muka dawo matarshi ke kula
da shi ga anti Safina ga baba Lantana ba a je ko ina cikii
kulawar ba na soma jin maganarshi daga dakin baba
Lantanar yäna cewa uh'uh ba fa zan iya irin wadannan
abubuwan ba a yanzu in kin ga da matsawa kawai jeki ni
bani da wata damuwa a yanzu.
65
Mamakin babana ya kamani cikin zuciyata nace kar
dai ace babana zai fara yin magana ne.
Ba a dauki wani lokaci ba baba Lantana ta fito da
halayenta da akafi saninta da su na kin yin girki da
sauransu saukin abin kawai anti Safana tana nan tana
kuma tsaye kan al'amuran mijint adama ni kaina da take
matukar ji da ni batama ko kiran sunana a yanzu wai sai
maman baba wani irin ji da ni takeyi ban sani ba ko gani
take tamkar don ita da abinda ke cikinta na yi jinyar
baban nawa.
Rannan da sassafe na idar da sallar asuba na shafa
fatiha na shiga dakin anti Safara inda nasan ya kwanaa
don in gaisheshi in kuma bashi magungunanshi da naki
yarda wani ya bashi, yana shan magungunan muna yar
hira magana kadan kadan.
Baba kana cin zaitun din an kuwa? Magani ne fa ba
kadanka. Kafin ya bani amsa sai kawai naji muryar yaya
Ibrahim yana sallama tare da shigowa cikin gidan, shigo
mana Ibrahim, baba ya yi mishi umarni don haka ya
shiga har cikin falon.
Kan maganar zuwan mutumin nan ne ikita na ce a
kira min kai inji kayi binciken a kan nashi ne? Na mike
na fita saboda ganewar da nayi maganar a kaina ne tunda
na ji ana ambaton likita wato Dr. Bello wanda ya biyo
mu gida da kai kawo da hidimomi iri-iri.
Ni fa baba binciken da'nayi kan mutumin nan ba
wani mai yawa banc saboda ga Alhaji Ahmad a kusa da
mu wanda aka dade ana tare yaushe za a je ana bincike
kan wani sabo kuma? Gabana ya fadi jin da nayi ya
ambaci sunan Mubarak, babana yayi maza ya ce,
66
Mubarak kuma? Cikin zuciya na ce, a to ai gara dai da ko
tambayeshi.
Cikin natsuwa va ce mishi, eh baba i ni a wurina
banga wani wanda ya fishi ba, babu ma wanda ya kaishi
cancanta in dai har za a bada auren ne bisa cancanta da
dacewa babu wanda ye fishi dadewa a cikin
nemankullurn kuna a tsaye yake a kan al'amarinta ga
zaman tare da makwabtakar dake tsakani, don haka in
har ba shi ne ya ce bai da bukatar auren ba to babu wani
dalili da zaisa mu je muna binciken shi ikita, to yaushe
ma muka sanshi?
Cikin natsuwa da yanayi na rage murya naji babana
ya ce mishi, to ai banga kamar har yanzu yana kan
naganar nan ba tun yaushe rabon da ka ji sun turo kan
maganar? Sannan tunda akayi aikin nan da kwana biyu
har zuwa yanzu ban sake ganinshi ba.
To in baya cikin neman saboda wa yake hidimar da
yakeyin'? In ana tunanin ko makwabtaka ne shi yafi kowa
sanin hakkin makwabtaka baba? Ai ya gaji da turowar
ne yasa ya hakura ya zuba ido yaga iya kar al'amarin.
To tunda ya nuna ya gaji yanzu sai a yi yaya da shi
Tbrahim? Ba shi kenan ba sai a yi da wanda bai gaji ba
yake ta kai kawo. Cikin zuciyata na sake cewa a to.
A'a baba a basu hakkinsu tukunna sai in sunce basa
so shi kenan sai a yi da wannan din, a ra'ayina ina ganin
a yi musu aike a gaya musu in suna so su zo in suka ce
basa so shi kenan.
Hannu biyu na saka na dafe kirjina saboda tsananin
harbawar da yake yi cikin tsananin karfi saboda tsoratar
67
da nayi da maganar tashi, ban taba jin muguwar shawara
ba irin wacce ya baiwa babana a yau.
A tambayi Mubarak da iyayenshi sai in sunce basa so
na ne za a aurar da ni ga wani wannan wane irin zace
ne? Tambayar da nake yiwa kaina kenan sai naji ya ci
gaba da bayani yin hakan ba komai ba ne baba ba kuma
wulakanta kai bane aure ne shi kuma auren darajarshi ta
wuce duk yanda ake zato, in wasu sunyi mana
mummunar fassara ma to mu kam ai babu ruwanmu
tunda mun san alheri muke nufi ba kuma don wani abin
hannunsu ba. Bayani sosai ya yiwa babana har dai ya
gamsar da shi ya yarda da shawarar tashi.
Cikin zuciyata na ce, na shiga uku yanzu bayan duk
abinda na wuce a baya kuma bai isa bah er sai an sake
jawo min wani wulakancin mai salo na dabna.
Yaya Ibrahim yana barin gidan naje.na samu anti
Safara wai in yi mata magana ko zanyi sa'a ta yarda ta
yiwa babana magana kan rashin dacewar abinda suke
shiryawa sai kawai naga ta kalleni cikin natsuwa ta ce
min, to ai yana jin maganarki kema ki sameshi mana
kawai ki gaya mishi. Yanayin da íayi mnaganar a ciki yasa
na gane abinda take nufi don ahka na wuceta nayi
tafiyata.
Ina jin baba Lantana daga dakinta tana fadin ina ma
dai in anje su koro wanda yaje din kwadayi mabudin
wahala, in da kwadayi da wulakanci, kuda wajen
kwadayi yake mutuwa, yaron nan da iyayenshi ba tun
yau ba sunce basa so basa so ba sa so amma kun ki yarda
ku hakura kun manne sai dole sun kar6i kai tir.
68
Duk da irin wadannan kalamai da baba Lantana ta
wuni tana yi basu sa babana ya canza daga abinda suka shirya ba.
Washegati da safe naji yana cewa anti Safara, yau fa
za ni sallar juma'a da wuri kuma zan tati don sai naje
gidan Alhaji Muhammadu nayi mishi maganar nan kafin
in wuce masalllacin.
Da kanka kenan zaka? Ya yi maza ya ce, ei ai gara
inje kawai da kan nawa babu komai ai 1aganar aure ne
ya yi magana da dan shi ne in suna so shi kenan su zo in
kuma basa so shi kenan mun fita hakkinsu sai a yi da
wannan da yake tsayen, ta ce haka ne Ubangiji ya zaba
mana mafi alleri, ya ce to amin.
Hankaline ya yi matukar tashi ben taba ganin yariyar
da aka yiwa irin wannan tallan ba sai ni dama dai inyi
sa'a suce basa so shima Dr. Bellon ya ji labari ya ce baya
so na ya fasa in ga yanda babana da yaya Ibrahim za su
yi da ni tun da dai na lura gajiyar da sukayi da ni ne ya sa
suka yanke hukuncin yi min irin wannan wulakancin.
Ban san abinda ya faru tsakanin babana da Alhaji
Muhammadu mahaifin Mubarak ba illa iyaka dai da
daddare Isiyaku yayi sallama a zanren gidanmu da anti
Safara ta amsa mishi kuma ya slhigo har dakina ya
sameni cikin fara'a ya soma gaisheni ina amsawa a natse
sai da muka gama gaisuwar sai ya kalleni cikin
murmushi yana susar eyarshi ni da yaliaba: ranki ya dai
ya dade ne yana zaure yana son ganinki, nace to madalla.
Ya dan saurara ko zaiji na sake yin wata magana bai
ji ba ya gaji ya sake tambayata, me zance mishi? Ban
69
kalleshi ba na ce mishi abinda kaga ya N maka, ya gaji
da tsugunno ya tashi ya tafi ban san yaya saka, kare ba.
Kwana biyu a jere ko leken kofar gida bapyi ba
saboda bakin ciki da takaicin yanda yaya lbrahim da
babana suka hadu suka zubar min da 'yancina, ban salke
jin wani motsi ko wata magana. daga wurin kwoab a sai
kawai na gane Mubarak da iyayenshi sun karbi tallan
aurena da su babana suka kai musu a daliin wasu yan
al'amura da na lura da su shiryawa nayi da, safe cikin.
kwalliya mai sauki mai kuma ban sha'awa riga da-siket
din atanfa ce a jikina ni'na yiwa kaina dinkin don haka
ba sai na tsaya cewa sun dace da jikin nawa ba pa sanya.
takalmi silifas dan Italy tare da 'yar faramar jaka ta pos
a hannuna, maimakon in yi tafiyaa-a haka- ko, in yi
damara kamar yanda 'yan mata a loacin sukeyi sai ya
jawo wani dan madaidaicin gyale na yane jilkin, pawa sai
dai bai hana kwalliyar tawa baiyana ba'ta fto.tsalcar gida
ina gayawa anti Safara zanje wajen yaya Dija yanza zan
dawo.
Ta tsaya tana kallona nuna alamar bata gamsu, da
yanda nayi mata bayanin ba, sanarwa kenan ba neman
izini ba, na yi maza na ce mata yi hakuri anti ba sanarwa
ba ne neman izini ba zan dade ba.
Ta yi murmushi ta ce, to ki gaisheta, nace mata to za
ta ji, na kamo hanya na fitod aga gida ina jin baba
Lantana tana fadin, anyi jiran anyi jirani abin ya gagara
har an koma yin talla, ban kulata ba çikin zuciyata dai na
shirya zuwa wurin yaya Dija ne don in san menene ake
ciki, in kuma gaya mata ra'ayina kan hakan da aka shirya
don ta sani.
70
Yar tafiya 'yar kankanuwa na fara nir tina in kara
ba bakin hanya inda zan samu abin hawa sai kawai ga
Isiyaku ya biyoni da sauri har yana haki, wai lki dawo in ji shi.
Na ja na tsaya ina kallon Isiyaku cikin takaici, kai
Isiyaku kafin in gaya mishi abinda nake nufin gaya mishi
sai naga ya saki wani lallausan murmushi, ai ba dagani
bane ya hacla da rantsuwa kafin ya ce shi yallabai ranka
ya dade din ne ya ce in zo in gaya miki kar ki tafi ko ina
gashi can suna tsaye shi de bakinshi.
Ban san dlaili ba bana iya karya dokar Mubarak ko
da dai a lolkacin zuciyata tana raya min ne wai zanbi
umanin nashi in komá gidan ne in bar tafiyar saboda kar
in kunyatasbi a gaban bakin nashi amma can cikin raina
ni da kaina na sani ba haka bane ba don su ba ne
maganar guca daya ce a duk hali ko yanayin da muka
samu kanmu a ciki ni da shi bana iya sabawa ko bijirewa umarninshi.
Na juyo da baya na korna na nui gida a makogarona
ina fadin don dai kana da baki ne kawai a zuciyata nasan
ya zama min tilas in koyi jaruntakar da zan koyi bijirewa
irin wadannar dokokin nashi ba komai ya ce min shi
kenan ba.
Ina tsaye a kofar dakina ina kokarin bude kofar tare
da yiwa anti Safara bayanin sai an jina za ni sai na jiyo
sallamarshi a cikin zauren gidanmu da kanshi ya yi
sallama alamar bai zo da dan aike ba nayi kamar kar inje
sai kuma naga to ai baba Lantana tana kallona ni kuma
bana so ta sheda wani al'amari a tsakanina da shi don
haka na juya na koma zauren tuni har kanshinshi ya
71
mamaye ko ina a wurin kwalliyar kananan lkaya ya yi,
sun kuma yi matukar karbarshi.
Ina zaki da safen nan kikayi wanna kwalliyar haka?
Ban san yanda akayi ba naji bakina ya bashi amsa, gidan
yaya Dija, to yaya za ki fita baki gaya min ba? Ba ki ji
maganar da babu yaje ya gayawa baba bane? Nace ban ji
ba na fadi hakan a daidai lokacin da zuciyata ke nanata
maganar tashi, ba ki ji maganar da baba ya je ya gayawa
baba ba ne? Wato babana ne ya je ya gayawa babanshi
cewar da nayi banjin ba da yanayin da nayi maganar a
ciki ya sashi zuba min ido yana kallona, ba ki ji bane ko
kina da wata magana ne, tsakanina da ke ai babu wani
6oye-6oye ko kin yi nufin 6uyan ma ba zai yiwu ba don
babu wani al'amarinki da ban sani ba, don haka fadi
gaskiyarki kawai in kina da wata magana ne kuma kiyi.
Na daure fuska sosai kafin nace, ina da ita, da sauri cikin
natsuwa ya ce, ai kinga hakan yafi fadeta inji.
To ni gaskiya ba da yàrdata aka yi miin hakan ba a ma.
shawaceni ba don haka bana so karma ka dauki hakan da
wani muhimmanci da har zaisa ka rinka neman ka shiga
harkokin rayuwata bana so.
Ya dan gyara tsayuwarshi kadan kafin ya tambayeni
bakya son me? Na yi shiru bakya so kamar yaya? Ai
magana za k yi don in gane abinda lkike mufi.
Na sunkuyar da kaina don kaucewa kallon da yake yi
min in kuma ji dadin gaya mishi abinda nake son gaya
mishi. Nace bana son auren da ake shiryawar saboda
bakai nake son aura ba ina son auren saurayi ne dan
uwana kamar yanda nake budurwa ba inje ina auren
mijin wata ba.
72
Hankalinshi a kwance ya tambayeni, to yanzu yaya
kike so a yi? Na ce rokonka zanyi ka fita hanyata ka
daina kulani ka daina shiga harkokin da suka shafi
gidanmu.
Wani irin lalataccen kallo ya yi min kafin ya
tmabayeni, kenan har kina da wata harka taki da ake
shiga, yaushe rabon da kika ga daga ido na kalleki.
Kirana aka yi kirjina ya bada wani irin sauti na dum,
a dalilin jin kirana aka yi nan da ya ambata na shiga uku
ni yasu tawa ta sameni, yaya Ibrahim ne ya yi min
sanadin wanman wulakancin gashi tun ba a je ko ina ba
an soma gorantamin ban iya daurewa na soma kuka ban
iya tsayawa ba na juya da nufin in shiga gida sai ya yi
maza ya tura kofar zauren dake wurin ya rufe ya hanani
shiga ban daina kukan da nake yi ba.
Kin shiga ulu ke 'yasu taki ta samehi yaya Ibrahim
ne ya yi miki sanadin wulakanci gashi tun ba a je ko ina
ba an soma goranta miki, to da akayi miki me? Kina so
ki gaggantsaramin maganganu ina kallonki inja bakina in
yi shiru? Ya soma yin magana kamar yana nufin yin
rarrashi, nayi naza na bijire mishi gaba daya tunda gori
ay shiga cikin maganar ai kuma shi kenan magana ta
kare ban shiga ba ma kenan ina kuma ga na shiga
gaskiya ba zan iya ba da wanne zan rinka ji da gorin da
zaka rinka yi min ko da wnada matarka da 'yan...
Kinga Maryam kinga, nayi maza na bar maganar
saboda jin kinga-kingan da ya fara ambatawa don haka
na koma yin kukan kawai ina fyace majinata da bakin
gyalena.
73
Nace in kina da magana mai ma'ana ki yi ina jin ki
na tsaida kukan da nakeyi cikin natsuwa na ce mishi a
fita hanyata kawai, ban sake yin wata magana ba ya juya
ya fita yayi tafiyarshi na dawo cikin gida na zauna ina
tunanin al'amurana úa Mubarak babu wani alherinshi ko
taimakonshi a kaina da ban tuna ba ko ince na manta a'a
komai irin sa ne dashi sai dai yanda zuciyata take rike da
wannan lissafin hakakuma take rike da abubuwan da
suka faru tsakaninmu da gidansu, da baubuwan da
mutanen unguwas uka yi ta fadi tuni dama mutane da
yawa suke fadin wai babana yaki aurar da i ne yana
jiran Mubara din saboda kwadayin dukiyar gidansu ba
wannan ne abinda yafi komai damuna ba irin dauke
kafar da ya yi fun