Showing 33001 words to 36000 words out of 41517 words

Chapter 12 - Halin Rayuwa Book 4 Hausa Novel Complete

Sodangi   

28 Jan 2025

254

ta hakura da shi tunda shi
kadai ne.
Cikin natsuwa na ce mishi, ko kuma don kunyar kai
din dan fari ne ba'? lyayenmu ai masu kunya ne, yayi
shiru ya bar maganar.
Muna isa Jaji na sha mamaki gidan da aka tsaida
motar da muka yi tafiyar a ciki gida ne ginin kasa ko ince
block din kasa ginin mutanen karkara sai dai babba ne so
sai cikin zaure gidan muka shiga muka fada tsakar
gidan mai matukar girma, Isiyaku ne yake jagoranta ta
den daga hirar da nayi ma sai nags kamar yafi yallabai
din yawan zuwa garin a'a ahah kar dai amarye ce yau a
gidan namu? Na daga ido a yanayi na girmamawa ina
sauraron kalamanta cikin zuciyata na tabbatarwa kaina
da cewar itace dattijuwar da ban gane ba a Gaidan ashe
daga nan taje can din.
A'a wuce mansa wuce ki karasa ina uan shigowa, na
bi umarmin da ta bani naci gaba da bin bayan Isiyaku ban
karasa inda zanin ba naji tana cewa sannu da zuwa Alhaji
kun zo ba? To hannurkn da zuwa hannunku da zuwa.
Wata kofa na shiga wacce na dade ina hange saboda
nisanta wani tabkeken gida na gani a cikin wata
kanmalalliyar katanga ginin block, sannunku da zuwa ta
yi min sannu da zuwa cikin matsananciyar fra'ar da ta
baiyanarda jajayen hakoran makkanta guda biyu dan
kamannin da ke tsakainta da shi kacna ne sai dai kuma
hakan ba zai hanaka sheda cewar ita din mahaifiyarsa ce
ba shi dogo ne ita. kuwa bata da tsayi shi ingarma ne ita
mai dan jiki, ita fara shi wankan tarwada a bakcan kuma
130
su na da dan wani abinda ya hadasu da ya danyi shigenta
kadan sai dai ban gane menene ba?
Har kun fito? Cikin ladabi na ce mata, ah to sannu da
Zuwa shiga mana na shiga falon na ta na samu daya daga
cikin luntsuma-luntsumarn kujerun da ke wurin na zauna
a cikin ina mamakin wurin nata yafi kama da na sabbin
amare saboda irin kawatuwar da akayi mishi, sannu da
Zuwa ta sake fadi daidai ta zauna a kan kofar shiga daya
dakin nima ra sauko kasa na zauna muna gaisawa tana
tambayata yaya gida? Yaya manyan duka? Ina amsa m
ata da na ji ta danyi shiru sai na tambayeta Inna ina
Izzatu, tayi dariyar jin dadin tambayar yar autar ta ta da
na yi ta ce, ai kuwa dai yanzu na aiketa wurin yayarta
dake nan bayanmu.
Mubarak ya yi sallama ya shigo ya koma can gefe
sannu Inna daga yanayin maganar tasu na kara gane
gaskiyar abinda ya gaya min, baba baya nan ne? Ya yi
tambayar bayan surn gaisa ta ce eh ya zaga baya can
kasan sunf ara sharar gona saboda ana ganin kamar
damuna tana gab da zata fara zube ya ce haka ne.
Isiyaku ya yi ta shigo da tsaraba yana jibgewa a wani
daki na daban wanda yawanci kayan amfani ne ya gama
ya miko min jakunkunan guda biyu na dauki daya na
mika mishi daya na ce a amyar min da ita ta ce a'a haba
jaka tayi ta zama a cikin mota a sa miki su a dak mana.
Mubarak ya ce ai ba dadewa ma zamu yi ba Inna
Kaduna zamu uce gidan abokina, ta ce a'a ai dai ku ku
wuce amma ita wannan ai nan ta zo za ta zauna ta ga
yan uwanka su ganta ta sansu su santa in ya so in kuka
juyo sai ku biyo ku dauketa.
131

Shiru yayi ni kuwa naji dadin hakan da ta fada tunda
ni kam asalin niyyata dama ai ta zuwa wurina ne ya ce
sai mu karasa Kaduna na ce to.
Ashe kuma baki sun zo ta amsa a yanayi na kunya,
saboda hada jam'in maganar da akayi sai naji ta ce ni fa
amarya ta fito na ce wannan tafiya mai nisa da tayi gashi
ba ta gama hutawa ba ta sake yin wata ko da yake dai
wannan tai bada ce muka gaisa da matar da na wuto a
tsakar gida tajuya ta tafi cikin natsuwa na ce mata, Inna
ban san da mutane a gidan ba ni su Izzátu kadai na yiwa
tsaraba na tura mata jakar da tsarabar ke ciki, wannan
duka su Izzatu? Ai kuwa dai su suka kwashe kayan jakar
taki, to Ubangiji ya yi mulu aibarka ya rufa m uku asiri
ya zaunarmuku da wannar aure na lau lafiya ya kuma
kareku daga sharrin mahassada.
Mubarak dake can gefe ya ce anin ni kawa nayi shiru.
Ta mike ta fi ta ta kallei, ni fa zan wuce na ce mishi
a'a mu kwana tare, da sauri ya kalleni a ina? Na nuna
mishi ga dakuna in ma ba zaka kwana anan ba ai ba za
ka rasa dakin kwana a gidan ba duk yanda za su kai da
jin dadin ganin ai bai kai su ganmu tare ba, ta daure
fuska mai don kar in ga yana wasa nima nayi kamar ban
ganshi ba na kau da kaina gefe ta sake shigowa zata
wuce, cikin natsuwa ta ce min wai so nake in yi sauri don
mijinki ya danci wani abu kafi ya tafi, ban kalleshi ba na
ce mata ai kwana zai yi, da sauri ta ce au haba? Lalle yau
da bak a gidan to a zo a gyara muku wancan daki
mana, ta fita tana kiran Izzatu mai yawon nunawa
kawaye tsarabar da aka kawo mata.
132

Amma ba kina shirin turani wancan dakn ne ke ki
dawo nan ki kwana ba ko? Na yi maza nace mishi
share dakin tasa aka yi ta canza labule ta fitar da katifar
dake ciki ta sa aka kai wata akayi shimfida yana dawowa
daga sallar magariba na ce mishi kO zamuje can ne in kai
mana abinci? Bai yi musu ba daki ne har da bayan gida
a ciki ya fita sallar isha'i ya dan tsaya wajen mai gadin
suka gaisa wanda shima ya jid adin ganinshi don har nan
ya biyoni wai mu gaisa Innan ce ta ce mishi ai nima
zanzo in gaisheshi ya ce to ba yanzu ba a barni sai da
safe saboda duhu.
Nayi hira yar kadan wurin Inna saboda sanin da nayi
mijina yana can shi daya a dakin, sai da safe Inna, ta ce
min to sai da safe 'yar nan dauki wannan kwanon ki tafi
muku da shi na ce mata to, a dakin kwanciyar namu
Mubarak ya yi kwanciyarshi iritn ashi bako ne ni kuwa
na mike na zauna kan shimfidar na soma zare kayan da
ke jikina daidai da daidai ina yin wurgi da su ba tare da
ina lura da inda suke faduwa.
Da sauri ya dago kai ya kalleni a hankali cikin murya
kasa-kasa da ke kare baiyanar da bakuntrshi a urin ya
ce min, "Ke Maryam a gidan mutane kike irin wannan
tubewar?"
Ban kula shi ba, ya yi maza ya jawo gefen babbar
rigarshi ya rufe fuska, wai ma ba zai bari ya ga abin da
nake yi ba, ban daina ba bar na kai ga babu abinda ya
saura min sai r brazier da ke jikina na mika hannu
daya da nufin in karasata itama sai na ji caraf ya rike
hannun nawa.
133

"Tun da dai abin da kike so kenan to barni kawai zan
karasa wannan din."
Ban sani ba ko bakuntar da yake ji a zuciyarshi ne ya
hanashi makara duk da abubuwa masu dadi da suka
kasance a daren wadanda suka hanashi samun baccinshi,
kiran sallar farko naji ya tashi ya kammala abubuwan da
zai ya yi nufin fita masallaci ina jinshi yana tashina ban
ayrda na tashin ba.
Mubarak da dole dole ce ta sanyashi kwana a gidan
nan sai gashi shi da kanshi ya cewa Inna zai bar tafiyar
sai gobe saboda ganin yanda yan uwa ke ta isowa suna
fadin sun zo ganin babban yaya da amaryarshi, ita kuwa
Inna duk wanda ya shigo mace ko namiji dan uwa ne ko
abokan zama abokan mutunci sai ta dauko wani abu
cikin tsarabar da mukazo mata da ita ta mika mishi a yi
ta godiya ana sa albarka, shi ma Mubarak rannan ya yi
kyauta har na rinka tsorn kar dai kudin nashi su kare sai
dai kuma anyi sa'a basu karen ba, bai yiwuwa in tsaya
cewa Ina tayi farin ciki sai dai kawai in ja bakina in yi
shiru.
Washegari da hantsi ina zauze a gabanta yayin da
Mubarak yake waje wajen mai gidan don yin sallama da
shi saboda tafiya za mu yi sai ta kalleni ta ce min
"Ubangiji ya yi miki albarka ya rufa miki asiri ya baki
zuriya mai albarka, ya jikan mahaifiyarki da rahamarsa,
in kunje gida kuma ki sa hannu ki kar6i girkin gidan
mijinki da yace min baki soma ba ki rinka girki kina
baiwa uban mijinki yana cin abincinki, itama matar gidan
uwar taku kar ki yarda ki samu mas'ala da ita don tana
da tasiri mai karfi a kan al'amarin mijinki sannan
134

ya'yanshi ki sa hannu biyu ki rikeiSu babu ruwanki da
uwarsu kin ji ko baki ji ba ko?
Na ce "Naji Inna na gode Ubangiji ya kara girma.
Izzatu ta shigo dakin kuka takeyi wai zata bini na ce
"To Inna inje da ita mana ai itama 'yar yata da na goya
haka take kamarta.
Ta yi maza ta ce "A'a ba yanzu ba in kin haihu dai za
ta zo ta tayaki jego." Shiru nayi ban amsa ba.
Inna ta ban tsaraba kashi biyu tace daya namu daya
kuwa na yaya Dija, muna barin Jaji Kaduna muka karasa
gidan Abdulhamid muka sauka shima mata biyu ne da
shi sai dai shi amaryarshi har ta haihu nan din ma fafatak
ishi mai zafi akeyi a tsakaninsu.
Mun dawo da kwana uku anti Safara ta haifi da
namiji zuwa ginin yaron da nayi shi ne shigata gidanmu
na farko tun taifiyata Gaidan shi ma barka kawai naje bai
yarda naje sunan ba wai ban kai zuwa suna ba don haka
Rumas'au ya tura taje a madadina duk da ba wani shiri
muke yi ba.
A wannan lokacin ne akayi gagarunin zama tsakanin
Rumasau da Mubarak da kuma iyayensu gaba daye ashe
duk wani iya shege da takeyi da nunannin ita da miji kut
da kut suke a mane dajuna ita kishi ne kawai ya sa take
yin hakan tsakanin nasu ba mai dadi bane.
Wurin yan tsegumi masu kai kawo tsakanin jama'a
na samu labari don a bakin Mubarak dai ba zan ji ba
saboda baya yin maganar wata a wurin wata musamman
ace ba ta nan.
Ashe wai tun sanda babana ya zo ya yiwa Alhaji
Muhammadu maganar nan cewar in har Mubarak yana

135


da muradin aurena bai fasa ba to su zo su karbi auren ya
basu, ya ce eh basu fasa ba, da ta ji maganar ta rokeshi
va yi mata alfarnmar neman wata ya aura in yaso ma kar
ya auri guda daya ta yarda za kuma ta zauna da su lafiya
in har ni zai hakura da ni ya ce mata a'a wannan bai
shafe ta ba in tana da wani abin dai ta fada, ta ce ita
kadai ce ya ce to a'a ba huruminta bane don ba itace zata
zabar mishi matar da zai aura ba, tund aga nan in yazo
gareta da bukatarshi bata sauraronshi ba ta yarda da shi,
haka suka yi ta zama har akayi bikina watanni uku don
haka da na zo gidan shi kuma sai bai salke komawa ta
kanta ba shiga dakin yake yi ya yi baccnishi in gari ay
waye ya tashi ya fita, ba ki ga yande ta kare ba, na cewaa
mai bani albarin ai bana kallonta, ta ci gaba da bayani, ai
yanzu ba ta fi rabin da ba don irin wannan wulakancin
ciwo ne da shi to yanzu shi ne ta gayswa kakar ta ta irin
zaman da sukeyi shi ne akayi zaman to yanzu wai an
sasantaus shi aayi mishi fada an gaya mishi laifinshi ya
ce a yi hakuri zai gyara itama anyi mata na ta fadan ta
rokeshi gafara ya ce ya yafe.
Hausawa suka ce wai kishi kumallon mata gashi dai
dama can ban san irin zamand a sukeyi a tsakaninsu ba
amma da akayi min wannan bayanin sai na dan ji nauyi a
zuciyata nan take kuma sai ta fara tunano min to wato
abinda ya faru kenan shi yasa jiya na ganshi ya makara a
dakinta bai kuma iya fitowa mun karya da safe ba har na
gaji na karya a wurina ni da Inna wai yana bacci kan
kace meye wannan sai zuciyata ta soma nunawa
idanuwana irin bare-bare. da zumudin da Mubarak din
136

yake yi a kan daidaitawar tasu nan da nan sai naji na
kullace shi a cikin raina.
Kusan sati biyu ay kasa gane al'amarina tun yana
kallon abin a wani irin yanayi har dai ya gaji ya
tambayem Kina da damuwa ne? Na ce babu, to meke
faruwa ne? Na ce ba komai, a'a yaya za ki ce min babu
komai, na mike na tafi na barshi wuri bai sake ce min
komai ba muka ci gaba a haka. Rannan mun kai sati
hudu a wannan lokacin ko yarda mu hau gado daya da
shi bana yi cikin dare ya taso ya zo ya sameni a kan
katifar da nake kwance na yi zumbur na tashi na zauna,
wani irin lalataccen kallo ya yi min, ke kar ki maidani
sakarai mana kina ganin kamar wai zan tilastaki ne? To a
kan me? Ai ba haka nake ba ko sanda nake da mace daya
bana wannan shirmen bale yanzu.
Maganar tashi ta soki zuciyata naji zafin ta ba kadan
a raina na ce ai kuwa dai sai dai mu yi ta zama a halka in
don ka ga ana kai kararka ne, ya katsemin tunanin nawa
a dalilin maganar da ya yi, so nake in tambaye ki wane
laifi nayi miki? Na tabe baki tare da girgiza kai don in
nuna mishi bai yi min komai ba, ya zubamin ido yana
kallona haka kawai kike nishadin ki ka ga bari ki yi min
wulakanci? A zuciyata nayi nufin ce mishi eh sai dai ina
dagowa da nufin yin maganar idanuwanmu suka hadu sai
naji ba zan iya ba nayi maza na sunkuyar da kaina kasa,
ba kya ganin kamar in na gaji da hakurin da nakeyi zan
iya ramawa don kema ki ji inda dadi? Cikin natsuwa na
ce mishi ai gara ka raman, ya ce to shi kenan ya mike ya
koma in dai ya fito ya yi kwanciyarshi.
137

Washegari da muka tashi ko gaisheshi ban yi ba na ci
gaba da harkokina na kuma zuba ido cikin sauraronta ina
ramakon nashi zai faro.
Ina cikin dakina a kwance sai kawai naji sallamar
yaya Dija da sauri na taso ina rike da dankwalina a
hannuna kai yaya Dija bakya ko jin tausayina, sai ki ki
zuwa in yi ta jin marmarinki har in gaji in hakura, bata
amsa ba ta nemi wuri ta zauna na wuce naje na kawo
mata abubuwanci citrus wrapes, perrz da arapers ciko
farantin nayi nazo na ajiye mata na sake komawa naje na
kawo mata soyaiyan naman rago na sake komawa na
kawo niata kindirmo na sake juyawa na dauko wani
kwanon tayi maza ta dago ido ta lkalleni, ke bana soon
rashin bankali ina zan kai wadannan abubuwan da kike
taramin? Zo ki kwashe su duka 'ya'yan itace kawai nake
bukata yanzu nace mata to.
Wani abu ya faru ne? Tayi min tabmayar bayan mun
gama gaisawa a hankali na tambayeta me kika gani? Idonta
yana kaina ta soma yi min magana cikin natsuwa, Alhaji
Amadu ne ya aika a gayawa babansu wai in babu
damuwa yana son ganina yanzu, na taba baki tare da
girgiza kai, fuskarta tayi saurin canzawa alamar ba ta ji
dadin yanayin amsar da na bata ba kan atce min komai
sai gashi ya shigo adonshi yayi kyau gashi sai kanshi
yake yi.
Ki yi hakuri na tasoki, ta ce a'a babu mas'ala ina fata
dai babu damuwa, ya ce eh babu a hankali ya soma
magana, ba ina nufin kawo kararta ba ne don gaskiya ba
dabi' ata ba ce ma yin hakan amma ina so in rokeki a yi
mata magana saboda bana son fitina a tsakanina da 1ta,
138

na tambayeta in wani abu akayi mata ta fada ko ba ni ba
in wani ya yi mata tana da yancin gaya min domin
zamana take yi taki ta yi magana nace zAn rama abinda
take yin don itama tai in da dadi ta ce wai gara inr ama,
kinga kenan tana sane da abinda take yi tana yi ne kuma
da wata manufa shi yasa na nemeki me akayi mata? To
in an yi mata sai ta nemeka da fitina wane irin al'amari
ne wannan? Me akayi miki? Nayi shiru kenan gobe ko ya
ganki kina yina binda kika ga dama kar ya nemeni don
ban isa ki gaya min damuwarki ba? Ya mike ya fita ya
barmu ni da ita, tana ganin yaf itant a soma yi min fada
mai tsanani ni kuma na soma yi mata kuka dont ayi shiru
taki yarda ta yi shirun.
Ke ba za ki gane abubuwan ba ne, a halin da ake ciki
fa ni babu mai sona a gidan nan nice bare, su kansu a
hade yake in banda kwarata babu abinda ake son gani.
Me suke yi miki na kwarar? Nayi shiru na rasa ta inda
zan bullo mata, to a soka a gidama ai halinka ke ja maka
kuma yaushe kika zo gidan har kika soma wadannan
maganganun? Kenan har kin fara samun mas'ala da
mijinki Maryam in banda mummunan tarbiya da kika
samu? To kin girma gaban mai cewa miji ya kunshe baki
kamar masai ai ni dama gabana yana faduwa ina tunanin
wane irin zaman aure za ki yi? Kuka sosai ta soma yi har
tana fyace majina da zaninta, wace irin magana kike so
kija mana? Yanzu a irin yanda akayi auren nan naku da
irin dawainiyar da mutumin nan yayi babu abinda ba a
fada ba babu wahalar da baiyi ba ga 6acin rai a kan aurenn
ne fa mnatar tayi ta tsalle tana cewa gara mata kishiyoyi
hudu da ke ke kadai bata sani ba ma ashe sakarya za a
139

kawo mata, kai ba a kyautar zuciya Maryam da na samo
Wacce tafi dacewa dake na baki.
Ganin 6acin ranta da ambaton matarshi da tayi ya sa
ni ce mata, to ai yafi sonta da ni kinga bare-baren da
yake yi ne... ban karasa ba ta katseni, ba dole yafi sonta
dake ba ita sulhu take nema a tsakaninta da shi ke kuwa
kina nemanshi da fitizaa, haba in banda namiji bai gajiya
da abinda yake so wane dadi yaji ne a tare da ke kuma
karya kike yi mishi wane bare-bare zai yi a kanta da ya
wuce wanda ya rayu yanayi a kanki? Kurna sai me in ya
yi ba matar shi ba ce, ba da ita kika sameshi ba, na kara
tsaranta kukan da nakeyi saboda tsananin bacin ran da
kalaman anta suka kara min gaba daya yaya Dija ba zata
fahimceni ba ban san yanda akayi ba sai naji bakina yana
ce mata kwacemin shi akayi aka bata, kwace min shi
akayi saboda ita tana da gata ai ba nata bane ni ba mijinta
na aura ba ia ta auran min.
To yan ya ya za ki yi Maryau? Tambayar da ta yi
ta fito a lafazi na baiyanar da canjin da zuciyarta ta samu,
ki yi hakuri ai kaddarace ta yi miki hakan ba wani ba ne,
itama matarshi ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login