Showing 39001 words to 41517 words out of 41517 words
don tsoron abin da take
shirin yi don kuwa damkar da naga ta yiwa kwankwason
nata irin wanda na rinka yiwa nawa kwankwason ne a
ranar da nayi gwagwarmaya da nakuda waiyo-waiyo
kwankwasona, Umma ina jin dai yau din nan za a yi
abinda ba a taba yi ba don gani nake tamkar
kwankwason nan nawa zai tarwatse ne ya ratattake ya
zube a kas,a me rake kai yara ku kira min mai rake.
Mubarak dai tunda ya yi mata kallo guda daya bai
sake ba balle ya nuna ya ji ko ya ga abinda take yi, hannu
biyu kwai ya saka ya dauke danshi ya wuce ya yi
tafiyarshi da shi ya barni nan wurin a tsaye ina kallon
busasshen wulakancin da Rumasa'u take yi min, ni ba
abin in sureta in fyadeta da kasa ba damben tsiya za mu
yi kafin in kaita kasa don itama karfi ne da ita to balle a
halin da nake ciki yanzu na jego danye.
151
Humhum hum waiyo waiyoo bayana in dai kuka
raken yakema to ba zan sake shanshi ba, ta kwashe da
dariya ai kuwa dai an bar dadi.
Na shigeta nayi tafiyata na shiga daki na zauna ina
jirani zuwan Mubarak don ya san da ni takeyi amma ya
ja bakinshi yayi shiru.
Yana shigowa na soma magana yanzu nan haka
matar nan za ta yi tayi min irin wannan wulakancin a
gidan nan ba za ka tsawatar mata ba? A fusace kwarai ya
ce min an ki a tsawatar din sanda kikeyi ban yi miki
kashedi ba? Bance miki za ki yi abin da za ta zo tana yi
miki iya shege da shi ba don ita bata kukan haihuwa
kikace tayi din, sai kuma yanzu da kika jawa kanki abin
magana inje ina tare miki? Ba zanyi ba in taji kin yi shiru
ba ki tanka mata ba za ta gaji ta bari ai babu abin da ya
tabbata kar ki kulata kin ji? A kan dole na ce mishi to
don na gane ba zai yi komai a kai ba.
Ta tasoni a gaba abin har ba a magana, kyakkyawar
dariya in taji nayi sai ta shiga kwalawa mai rake kira.
Rannan kawai nayi sa'a tana cikin tsala tsiyarta a
tsakar gida tana murde-murde da iface-ifacen a rike mata
kwankwaso zai ratattake ya zube a kasa sai kawai na ji
muryar baba yana kwalawa Ummana kira, ina
Ummulkhairi ta ke? Da sauri Umman ta fito tana rike da
dankwalinta a hannunta, gani Alhaji lafiya dai ko? Bai
amsa mata ba ya soma jero mata tambayoyi, yanzun nan
kina nan a gidan nan ake yin wannan iya shegen baki
hana ba? Ko kina jira ne sai abin ya zama tashin hankali
a tsakaninsu? A kidime Umma ta ce mishi, nayi magana
Alhaji.. Da sauri ya sake tambayarta ba ta ji ba kenan
152
saboda kema ta raunaki? To ai kuma shi kenan na riga na
gano kan al'amari na gane dalilin da ya sa fitina taki
karewaa tsakaninsu shi ne na kina da bangaren da kike
marawa da kinja kin tsaya a matsayiniki na uwar danki
kawai wanda ya yi ba daidaiba ki tsawatar mishi da abin
nasu bai yi tsanani haka ba don haka zanyi maganin abin
in kuma na sake jin sunyi fada to na san mai laifin tunda
na gane ita din fitinanniyar yerinya ce.
Tu daga nan jikin Rumasa'u ya yi sanyi ta shiga
tsoron kar wani abu ya hadani da ita baba ya ce itace mai
laifin, ni kuwa sai nayi arnfani da wannan darmar nima
muna hada ido da ita sai in mata gwalo, rannan ina
falona a kan kujera shirya Muhammad nakeyi sai ga
Mubarak ya shigo zuwa ya yi ya zauna kusa da ni ko
ince manne de i tamkar dai a ce maida mu cikinshi zai
yi dagan i har yaron, rike yake da kafarshi yayin da shi
kuma yake ta faman modar nono.
Ban taba ganin mai son da ba irinki gyara dai gyara
dai kowane lokaci balkya gajiya da gyarashi ke duk
kokarinki wai ki nunamin kin fini sonshi ne ko? Da sauri
na ce mishi wace ni yallabai? Baba ne ya ce alkai mishi
shi shi ne nake kara kintsashi. Ya kara baiyanar da jin
dadinshi ya ce min, kin san abinda yasa baba yake son
yaron nan, nayi maza nace mishi uh'uh, to tunawa yake
yi da irin wahaloli da kai kawon bacin ran da nayi ta
gamuwa da su a kanki Maryam domin shi din shi ne
takuici na duk wani abinda kika sani a tsakanina da ke na
bada yaron aka fita da shi ya knkameni a jikinshi na
tsawon lokacin da yaga hakan ya isheshi sai da ya sake ni
don kanshi sai kuma ya kalleni ya ce min, na ganki kina
153
yiwa Rumasa'u gwalo dazu kar ki sake don ba zai zamo
min komai ba inje in sameshi in gaya mishi cewar ba ita
kadai ce fitinanniyar ba ku dukanku biyun mutane ne daa
baku da kirki don baku damu da son zaman lafiya ba, too
kawai nace mishi na ja bakina nayi shiru ban dai sake ba.
Rannan sai ga Asabe ta zo wurina a wan1 irin yanayi
da ba zai kwatantu ba na rashin kyan gani ga kazanta na
tuna tsabta da kwalliya irin ta Asabe wai ta zama
kazamar da karnintama kawai ya isa ga 'ya ya uku su ne
biye da ita daya kuma a bayanta hudu gaba dayansu
callo duya zaka yi musu ka kawar da kai, aka ce min kin
haihu shi ae nace bari inzo in ga yaron daga nan in yi
miki barka, na ce ai na gode bari in kawo miki shi ki
ganshi, ne shiga daki don dauko mata shi.
Mubarak dake wurin ya kalleni, ke kada ki rinka yi
min rashin hankali kin ji ko? Na ce mishi to na dawo na
sameta muka dan soma hira har ta kaima na tambayeta
ina baba Lantana'? Ta tabe baki ta ce tana can Enugu tana
jin dadinta mu tayi banza da mu a nan ta barmu tamkar
ba itace tayi mana sanadin wannan wahalar ba, ai ko
rannan da naje wajen yaya Salau da sauri na ce a'a
Sallau yana ina ne Asabe, ta ce yana can wani gari nan
baya yana ta sana'arshi ta gwari, na c kai madalla kowa
Ubangiji ya bashi yanda zai yi, maimakon tace amin sai
ta ce uhun kai kam ai uwa ta riga ta lalata maka komai
sai dai sakaiyar Ubangiji kawai don ta ciceka, zuba mata
ido nayi ina kallonta cikin zuciyata na ce, me wannan
haihuwar ta amfanar? Iyayen da akace mu yi musu
addu'a ita sakaiya take nema a kanta uwar uba kuwa
dama ba a maganarshi na sake yin wani tunanin na tuna
154
rayuwar dá baba Lantana ta so inyi kenan a gidan Nalami
sai kuma reshe ya juye da mujiya da hannunta ta kai
yarta.
Kinga baya bamu sabulun wanka bare na wanki balle
man shafawa balle zani abincima na dare kawai yake
bayarwa in nayi magana ya ce wai shi yana ganin
kokarin kanshi in nace zan yi sana'a matarshi ta hana in
wasu sukayi tausayina suka bani abu tace satar mata nayi
shi kuma yana kallo bai cewa komai don tsoronta yake ji
tafi karfinshi.
Mama ga kudin cizo a jikinki tayi maza ta kai wa
yarinyar duka wannam ne kudin cizo? Kyankyaso ne, na
mike na shiga daki na debo turare guda biyu na kawowa
Asabe tare da kudi masu dan aiki don na Mubarak ne na
gani a ajiye tayi ta godiya ta tafi ta bani ina tunanin
rayuwa tare da tambayar kaina ko me baba Lantana taje yi a Enugu?
A wannan shekarar ne dai babana ya tafi aikin haji
Alhaji Muhammadu mahaifin Mubarak ne ya biya mishi
amma sai ya ce wai Muhammad dan jariri ne ya biya
mishi.
Shekaru biyar bayan wannan lokacin na sake jin wani
jegon jegona na uku sai dai a wannan lokacin ina yin
jegon ne a wani sabon katafaren gida da Mubarak ya
gina mana in da ni da Rumasa'u muka zama sai wacce
taga dama ne take shiga wurin 'yar uwarta don bama ma
jin motsin juna iyaka dai katanga ta hadamu a wannan
lokacin kuma ina jegon nawa ne bayan na kammala
karatuna na digiri a jami'ar garinmu banda wannan kuma
wani karin jin dadin shi ne ina yin jegon ne a karkashin
155
kulawar uwar miji wacce bata taba zuwa gidan dan nata
ba sai a dalilin haihuwar tawa ga kuma baba Sumaye da
na riketa matsayin uwa saboda sanin da nayi taso
uwartawa sanda take raye taso ta kuma bayan bata nan ta
kuma ike amanar dake tsakaninsu yana kuma daga
daga
kuntatawar da da zai yiwa iyaye a bayansu ya mutunta
wanda suke mutuntawa.
Inna da Izzatu suka shigo su biyun a yanzu manyan
ya mata ne in ka barni ma sai in ce shirin aurensu
Mubarak yake yi ko da dai bai gaya min ba don su din a hannuna suke.
Shirin mikewa nake yi inje wurinshi saboda
dawowarshi da naji sai gashi ya shigo da murmushina na
tareshi ina fadin, yallabai kaji wai ashe musakai da
mabaratan nan da gwamnatin kudu ta tattara ta dawo
arewa da su ashe wai har da baba Lantana a cikinsu ashe
can Enugun da taje bara takeyi sannan wai bata barar
hakan kawai sai ta lallankwaye ta maida kanta tamkar
wacce aljanu suka taba yanzu kuma da aka daw0 ia su
anyi juyin duniyá ta koma yanda take abu ya gagara
komai ya makale tana can sai zuwa kalon ta akeyi tana ta kuka.
Juyawa yayi zai fita ba tare da ya ce min kala ba,
Inna tayi maza ta ce mishi haba kai kuwa wane irin
miskilanci ne wannan? Yarinya tana ina taka saka da kai
sai faman gwaleta kana shassharewa kakeyi me tayi
maka ne?
Ranshi a hade ya ce, haba Inna gajiya nayi da abin
kunyar da yarinyar nan take jawa mutane, yanzu ace ita
ba zata daure tayi hakuri da bainda sauran mata suke
156
hakuri da shi ba? Kullum in zata haihu ta rinka ihu kenan
tana yi mana bankada a wuri ana kallona? Kuma wai har
a gabanki ba zata fasa ba?
Inna ta ce mishi kai tafi can da wannen maganar taka
kai dai fitinannen mutum ne yanzu yanda wurin nan ya
kacame da iface-ifacen mata har kana iya sheda ga
muryar wata a ciki? Duk matan ma yanzu ba kukan
haihuwar suke yi ba? Kai kasanta ne? Da sauri ya ce ba
dukansu bane Inna ai Rumasa'u bata yi shiru take
haihuwarta sai dai a ganta da danta kawai, haushi da
takaici shi suka taru suka lullubeshi in har akwai wani
abidna na tsana bai wuce misalin da yakeyi min da
haihuwar Rumasa'u ba.
Da sauri naji Innan tayi mishi tsawa, kai tafi can ka
bani wuri wadannan 'yan mitsi mitsin 'yayau da take
haifowa in tace za ta yi kukama ba sai a dake ta ba, dadi
ya kamani shi kuma yayi murmushi, Inna ba ki son laifin
Maryam to a dan bani yaron in kaiwa abokaina da suka
zo min barka su ganshi.
Yana barin dakin nayi kwafa na ce bari tunda abin
nashi ya zama hakan nasan abinda Zanyi ba sai na yarda
na kara baihuwar ba ne ma zai sake yi min irin wannan
wulakancin? Ai yafi kowa son 'ya'ya tunda shi ne mai
zirga-zirgar nunawa jama'a su to na daina ba zan kara
ba.
Ta harareni da gefen ido kafin tayi tsaki ta ce min
kinji shirmenki kuma ni ina cewa wani abin za ki yi don
ki kwato 'yancniki a wurinshi ya kame bakinshi ya daina
wannan iya shegen? To in kin bar haihuwa wa kika
yiwa? Danki ai arzikinki ne, yanzu ni baki ganni ba?
157
Haihuwarshi fa akayi aka kwace min shi na hakura na
tafi da ya girma bai nemoni ba? Da sauri na ce mata ya
nemeki Inna, to da wanda ya kai ni morarshi ne a yanzu?
Da sauri nace babu. Ta gyada kai, to nemo wata mafitar
amma ba wannan ba na ce to.
Kwanakin jego sun kare har inna da baba Sumaye
sun koma gidajensu daga ni sai iyalina ne a gida 'yayana
uku Muhammad, Khadija sai mai sunan babana
Abubakar Siddik sai kuma 'yan mata na Inna da Izzatu
da masu aikin gidan a yanzu ban cika lura ko neman
sanin me Rumasa'u ke ciki ba balle ta dameni
musamman da na gane irin roaganganun da yake yi min
suke yi min ciwo na ita dabn ce ba halinku daya ba ita
ai tana jin maganata, ashe itama yanayi mata dace nayi
naji shari'ar da akayi musu inda take ta kuka tana fadin
kusan kullum sai ya kirata da sunan Maryam banda haka
kauma sai ya gaya mata ni din daban ce ni ina girmamashi
ina jin maganrshi ina gudun bacin ranshi tun daga nan na
tattara maganganun nashi na ajiye a gefe saboda na gane
dabi'ar shi ne in za a yi fada da shi ya fadi mai zafi in
kuma ana zaman lafiya kaga tamkar bai iya komai ba sai
alheri.
A yanzu kokarina yafi tafiya re wajen ganin ban
bashi damar da ya sake shigo min da wata ba amma,
Rumasa'u wata a tsakaninmu ya fada ya kara nanatawa
wacce bata shigo ba za a iya hana shi kawota ya hakura
amma wacce take ciki to babu mai rabashi da ita don shi
din wani irin kishi ne da shi da ba zai iya lamuntar ganin
wani kato ya aurar mishi matarshi ba don haka sai ya
158
gwammace in tayi mishi yayi mata in anji jiki a gyara
amma ba saki ba.
Ita kuwa Rumasa'u a yanzu babi abinda take so irin
ganin ya kara aure ya dai kawo wata wai nima in ji irin
abinda taji sanda aka kawoni.
Mubarak ya shigo dakina bina yakeyi da kallo ban fa
gane irin yangar da kike yi min ba na lura wani yanga
kike yi min kin a wani shan kanshi kina jammin rai ko
sanda zan karbi ajiyata a wurinki ai ba irin wannan jan
ajin kika yi min ba, wuce shi naje zanyi yayi maza ya
cafko kuguna ya rike zo ki gaya min me ya faru? Wata
uku da haihuwarki amma har yanz ba ki yi min ban
gajiya ba.
Na daure fuska sosai don kar yaga alamar wasa na ce
ai ni na daina irin wadannan abubuwan, wadanne? Nayi
shiru ban amsa ba ia magana dai kenan ya jani zuwa
inda yake nufin kainin ya shimfideni shima ya kwanta a
gefena nayi maza na tashi na zauna, me kike yi ne haka?
Na ce mishi a'a ai ba zanyi bane ba kuma zan yarda in
sake ba da inje ina yin abinda zai zama sanadin da zan
rinka ja maka abin kunya a cikin mutane suna kallonka ai
gara ba a fara ba.
To a ina kika ga ana yin hakan Maryam kicekin daina
samun ladan mijinki kin daina faranta mishi rai, kin
daina menene menene? Wai zna me yakawo wannan ma
ganar ne kinji wani ya ce miki wani abu ne? Na bata rai
na ce, ina ruwana da wani? Me wani zai yi nin ya
dameni? Wulakancin ka ne kawai ya isheni na gorin da
kake yi min a kan kukan hai...
159
Ban karasa ba ya yi maza ya ce, ni Maryam ai babu
sharri a tsakanina da ke to ni yaushe nake iya sheda wata
murya a wurin nan abinda Inna ma ta ce gaba daya duk
matan zamanin yanzu kukan haihuwar sukeyi, ai in dai
don ta wannan ne sha kuruminki gasa wannan bakin
nawa' zanyi ba za ki sake jin wata kalma ta fito daga
cikinshi in dai a kan ihun nan ne sai san barka da godiya,
don haka sa bannayenki biyu kawaiki rage min kayan
nan dake jikiniki don ki sa ni in ji dadi in samu farin ciki
da natsuwa a zuciyata saboda sanin duk abinda nake yin
yinshi nake bisa yarda da amincewarki, kina so ne nima
ina so ba tilastawa ko fin karfi na nuna miki ba.
Sannu a hankali cikin yanayi na natsuwa da jan rai
irin na mace don dai in kara sashi ya kara matsuwa da
abinda ya riga ya matsu, nasa hanu na soma zare kayan
dake jikin nawa ina jifa da su daidai da daidai ba tare da
na danu ko na lura da inda kayan suke faduwa ba.
Wassalam
Taku
HAFSAT C. SODANGI
Fatan alheri gareku dukanku, na gode Ubangiji ya
saka muku da alheri bisa kulawar da kuke yi ma
rubutuna na gode.
18/2/2015
160