Showing 30001 words to 33000 words out of 41517 words
leshi na sanya 'yan kunne da sarka na zinarin
da ake yayi loakcin me ludayi nayi matukar yin kyau ga
kashi na fito na tsaya a bakin kicin din ta juyo ta kalleni
saboda motsin da taji cikin natsuwa ta soma gaisheni
mama ina kwana? Na ce mata lafiya Inna yaya su
Abbati? Ai da wai zasu biyoni Mamanmu ce ta hanasu
zuwa to a kan me? Na yi tambayar daidai na shiga kicin
din na dauko kwalbar zaitun da cokali na dora kan dan
karamin tire saboda hangen Mubarak da nayi a falo a
mike kan doguwar kujera a hankali na ma tsa kusa da shi
na durkusa cikin nutsuwa na tambayeshi, kana bacci ne?
119
Ya yi maza ya bude ido ya kallen, uh'uh ina jiran
farkawarki ne, sai dai kuma idanuwan nashi sun canza
launi watakila bacci gami da gajiyar hidimar da akayi
watakila damuwa ko bacin rai.
Ba ki karya ba, kai kaci wani abu ne? Uh'uh na fara
mikam ishi robar ruwan swan, ya ce a'a na sha ruwa na
ce to ungo zaitun magani ne bai yi musu ba ya karba ya
ci kwaya uku, wai me za ki ci ne? Na danyi murmshi
kafin nace mishi, me yasa ka damu da yawa, a daki na fa
nake maganar tayi mishi dadi ko kina dakinki ai ke din
bakuwa ce Maryam ban amsa ba na mike na shiga kicin
don nasan ina da wasu abubuwan a ciki sai kawai na ci
karo da kayan da Inna ke cewa zata ajiye sinasir ne da
miyar taushe da ya ji kayan ciki a ciki da kashi na bude
oven na sa kwanon farfesun kajin da tun jiya ta aikomin
da shi ban samu naci ba ga kuma gasassun kajin da shi
Mubarak din ya shigo da su bai barni na tabasu ba, nan
da nan na kewayeshi da abubuwa iri-iri kasancewar
kuma dama na riga na saba da cin abinci a gabanshi sai
kawai na zauna muna ci tare, ga dukkan alamu kumna
dadi ne ya kamashi watakila ya ga alamar in ma so ake a
takurashi kan abinda zanci to zai iya samun sauki ta
wurina tunda zan iya kula da kaina kina nufin duk da
bakuntar dake tare da ke zaki iya hidimominki? Cikin
natsuwa na ce mishi me zai hana? To yi min wani
alkawari man Maryam, a hankali cikin natsuwa na
tambayeshi kamar wanne fa? Tsareni yayi da
idanuwanshi kafin ya ce min,n a zaki barni in zauna
lafiya za ki barni in samu natsuwa a tare da ke, na zaki
120
barni in yi hukunci da duk wani abinda kika san nawa ne,
Za ki taimakeni in fita daga mas'aloli in har ina cikin su.
Ban kalleshi ba na ce mishi in har kayi min bayanin
yanda zanyi in yi maka hakan ina ganin kamar zanyi
amma yanda kayi min maganar a haka ai ba zan gane
abinda zanyi ya zama D8 1ya yi maka wadannan
abubuwan ba.
Yana kallona ya ce min, ki taimakeni ki yarda in na
saki iki yi in na hanslki ki cikin sauki na ce mishi zanyi
saboda ba tare da na tsaya yin wani tunani ba saboda
yaya Dija da sauran mutanen da suke ganin sun isa su
gaya min inji sunyi ta gayamin cewar in ya hanaki ki bari
in ya sa ki i yi shi aure da kike gani ba komai bane face
ladabi da biyayya sai ko mututnawa na ce musu to don
haka hankalina a kwance na ce mishi to kamar yanda
Suma na gaya musu.
Wanka yayi ya tsalo wata irin kwalliya da zan iya
cewa ban taba ganin yayi kyau irin na rannan ba ya wuce
can cikin daki, zo mana, na tashi na bishi ina tunanin ya
yi kiran ne don ina tare da Inna.
Wannan hular da wannan wacce ya fi kamata in
saka? Na reba kallo tsakanin hulunan duka biyu kafin
ance mishi, wannan bai sake dubava ba ya sanya wacce nace din.
Me da me kike so a kawo miki? Na gane abinda
yaken ufi na ce ni fa nafi so in yi girki da kaina, kina
amarci kina girki? Ba a yin haka abubuwa sai su yi miki
yawa, ki kwanta ki yi bacci ki huta, nace uh amma ai
Inna tana nan za ta yi min aiki bai sake magana ba kudi
ya cire ya ajiye a gefen madubi, zan turo Isiyaku ki yi
121
mishi lissafin abinda kike so a kawo miki, nace mishi to
a dawi lafiya, ya ce Ubangiji yasa ya fita.
Kudin da ya ajiye din masu yawa ne sosai har
Zuciyata tana tunanin me zan saya da su haka? Ina zaune
ina jiran zuwan Isiyaku cikin tunanin ko dai bai ganshi
bane ko kuma ya manta ya yi tafiyarshi? Sai ga Isiyakun
ya shigo da manya manyan ledoji a hannunshi kicin ya
wuce ya ajiyesu na ce mishi, kai Isiyaku ba nice mai
girkin gidan ba kai musu can, ya ce a'a nan ya ce in
kawo wadannan ga nasu can a waje na ajiye musu, Inna
nasa ta duba kaji ne da koda, sai kayan ciki da kuma
sauran abubuwan da zan nema ba tare da na tambaya a
gidan ba na dawo na zauna ina tunanin a yanda zanyi da
aiki irin wannan na sani da bance mishi zanyi ba saboda
dai karfin hali kawai na ke yi nake daure amma gaba
daya jikina ciwo yakeyi sai ga anti Kubra ta yi saliama
ta shigo bayan na ji ta tana gaisawa da Rumasa'u a tsskar
gida ina ganinta naji dadi ya kamat sannu a zuws anti,
sannu 'yar albarka ke dai ai daga gidan Hadiza nake ina
can sai ga mijinki yaje kunyar ambatonshi a matsayin
mijina ya kamani saboda yanayin da take magana a cilcin
nashi yaje ya kai mata fan hamsin ya ce ta sailami duk
wasu baki da suke nan daga wurinta har zuwa gidan baba
ya kuma sake bada jakar guda ya ce a sai miki abinda
aka san zai yi miki amfani don ya tambayeki kin ce ba
kya son komai.
Kunyar anti Kubra ta sake kamani na sunkuyar da
kaina kasa har na kasa dagowa, ato ina masu cewa ita
tana aiki ne kawai ke kina waje yanzu ai tun a wajen ana
122
tare ne kawai ba komai ake yi ba? Shiru nayi ban iya ce
mata komai ba.
Itace ta sarrafa duka bubuwan da ta samu an kawo
din ta adana na adanawa ta girka na girmawa irin kayan
shan farfesu ki sha romo sosai saboda kula da jikinki
bayanin take yi min bayam ta titsiyeni na ci na sha adadin
da yake nema yafi karfin cikina, ai garama da tayi miki
haka mu kishiya wacce iin yunwa ce bata gana mana ba
ga abin nan a wadace amna bata sarrafa shi ba balle ta
baka sai ita da 'ya'yanta ta san hikimar da tayi ki kula da
kanki na gaya miki ki ci gasasshe nama ki sha farfesu ki
kuma hora kanki ba yanda za ki citu ba kama hanya a tafi
ta bar Inna tana gyaran wajen.
An idar da sallar azahar Mubarak ya shigo baba da
yaya Dija suna gaisheki naje na yi musu bangajiyar baki,
nace ina amsawa ya ka barosu? Lafiya ni zan kwanta ko
za ki zo mu je tare? Na ce uh'uh na nuna mishi Inna da
ke kici bai yi magana ba ya wuce ya shiga daki sai wajen
hudu ya fito.
Rannan da daddare mnuna kwance a gadon mu
gwanin dadi yana manne da ni a jikinshi hira yake yi min
yana bani labari baki sani ba Maryam a hankali na
tambayeshi menene, cikin nutsuwa ya ce min, sai in
rinka ganin tamkar a mafarki nake sai na ganki a zahiri
ko na jiki a jikina sai in gane ba mafarki bane, sai in tuna
lokacin da baba yake lallashina yana gaya min cewar in
matarka ce zaka aureta wani ai baya auren matar wan
ashe ashe ashe kuwa haka din ne, a hankali cikin
natsuwa na ce mishi baban? Ya ce eh mana ance miki ni
na iya irin wannan noke noken ne irin naki? Kana son
123
abu kana kaiwa kasuwa? In banda na nuna mishi zahirin
al'amarina zai yi ta wannan zirga zirga ne da ya rinka yi
ke fa kina jin yanda nake ji ko na rinka ji, gaya min
gaskiya sau nawa kika taba yin mafarkina? Ni bana
Rarya maryam bana kaiwa kwana ashirin ban ganni tare
da ke ba a taccina har na rinka sanmun mas ala na wankan
da nakeyi ban san dalilinshi ba na yi kamar ince ishi ai
nima ganin nake tamkar mafarkin nake yi sai na fasa
neyi maza na ja bakina na tsuke, a hankali kuma sai na ce
mishi to mu yi bacci mana yallabai ko zaka samu ka kara
wattsake gajiyarka.
Kwanaki uku a jere ni nake hidimomina ni nake yin
girkina babu fashi kuma kullum yaya Dija zata aiko min
da abin karyawa mai dadi da gamsarwa Inna zata zo tayi
min duk aiyukan da suka dace ta kuma tayani hira sai
lokacin makaranta ta yi shiri ta tafi in ta taso ma nan
wurina zata sake dawowa haka shima Isiyaku kullum zai
kawo min cefane..
Rannan na cika kwana hudu cikin daki ban ito ba
saboda ajiyar Mubarak bai yarda munyi irin kwanciyar
da muka yi a kwanak biyun da suka biyo bayan daren
angwancinmu ba ina jin sanda Inna ta shigo ta gama
abinda zatayi tazo ta tsaya daga bakia kofa ta gaisheni ta
ce min zata je makarantar allo ta dawo na ce mata to kin
karya ne? Ta ce eh nace to sai kin dawo, ina cikin hakan
ne Mubarak ya sake shigowa dakin ko za ki zo muje can
wajen Rumasa'u mu karya, kamar in ce mishi tuntuni
bata kirani karyawa ko cin abinci ba sai yanzu da na riga
na zama 'yar gar? Ban iya yin hakan ba na ja, bakina
kawai na yi shiru.
124
Ya nemi wuri a balkin gadon ya zauna, bana so wata
mas'ala ta taso ace ta wurinki ne Umma ta kirani ta ce
min wai anyi mata fada taji kuma zata gyara kuskurenta,
don kar in yi musu da shi ya sa na tashi na dauki gyalena
na yafa a kan doguwar rigar da ke jikina na bi bayanshi
zuwa dakin nata na kalli zirga-zirgarta na gaisheta kafin
na nemi wuri na zauna a kan shimfidar da na samu ya
riga ni zama.
To ki yi ki kawo mana. ruwan zatin mana, ya yi
magana saboda ganin bata gama kammala abubuwan ba,
ta ce to ta kawo ta ajiey taje zata zauna kadan ta rage ta
hau kan cinyar shi in banda ya yi hanzarin kawar da
jikinshi ina jinda nan din ta zama, nan da nan naji
zuciyata ta yamuise wani bangaren na ta ya rinka
rayamin cewar so take ta una miki cewar nan din wurin
zamanta ne kokari mai yawa na yi kafin na dawo da
kaina ga natsuwata nan taek kuma nayi ta tunawa kaina
da cewar matarshi ce matar sai ce a hankali na zuba
ruwan zafi a kofi na tsoma ifton a cikin a soma sha.
Wane irin karyawa ne wannan Maryam? Kina mufin
duk abubuwan da ke nan ba za ki ci komai ba sai ruwan
lifton, daurewa na yi in banda haka da nayi mishi kuka
na dago idanuwana do in yi mishi magana karab suka
hadu da na Rumasa'u itama ni take kallo ba kuma kallon
dadi ba ne watakila 'yar kulawar da ya nuna ne ba ta yi
mata dadi ba, sai yau muka ga juna ido da ido daga ganin
da nayi mata a asibiti da suka zo duba babana zuwa yau
din ta zabge sosai sai dai in aka barni sai ince tafi kyau a
hakan don da ta bar kanta ta ajiye teba mai yawa.
125
A hankali na ce.mishi, na manta ne na fito ban yi
brush din bakina ba ko inje in yi in dawo? Har ya ce eh
ban san abin da ya tuna ba sai naga ya miko min kwano
guda daya na karba na dawo na ajiye na shige bandakina
na kwanta cikin zuciyata ina tunanin ba zan sake yarda
ya dorani a kan cinyar shi ba wato dama shi dabi'arshi
kenan dora mace a kan cinya to na daina yarda in
hau.nan take naji zuciyata tana raya min Wasu al'amuran
da nan take na ji babu abinda nake so iri in yi kuka shi ne
Tmutumin da nalke so a rayuwata na yi ta bunn auren shi
sakacinshi da sharrin baba Lantana su ne suka taru suka
yi sanadin da burin nawa bai cika ba a wancan lokacin
har yaje ya auri wata matar ya Soma yi mata abubuwan
da ya kameta a ce ni kadai zei yi wa, motsin shigowar da
ya yi ya sani nayi amza na share hawayena amma duk da
haka sai da ya gane kukan nakeyi, me ya saIneki? Na yi
shiru zuwa dakin nata ne bakya so? Nayi maza na ce
mishi a'a, to menene? Na ce mishi bana jind sdi ne, to in
bakya jin dadi sai ki yi kuka ba za ki gaya min ba? Ko
dai wani abu yana yi miki ciwo ne, nayi amza na ce
mishi a'a, a kaiki asibiti nas ake cewa a'a Isiyaku ya siyo
min maganin zazzabi.
Ya ce in to ki yi wanka ki yi kwalliya in ganki in ji
dadi na ce mishi to a haka na wattsake, ana gobe zai fita
dakina ma sai da ya sake takurani ya yi yanda ya so da
rannan kam kuka nayi ta yi msihi saboda na kasa hakuri
in jure tun yana rarrashina har va soma mita wato kenan
baki gamsu da adalcin da nake vi miki ba kenan ko So
kike in tattara hannu in zuba miki ido ina kallonki, banyi
magana ba iyaka dai ranar ya koma dakin Rumasa'u ni
126
kuma na kwana tare da Inna shi ne ya cew yaya Ibrahim kar a ga bata dawo ba zata tayani kwana yace mishi to.
Tunda karyawar safe ta zama ka'ida za mu yi ta tare har da shi sai ya zama ka'ida kullum sai ta san abinda tayi ta bata min rai da na yi tunani naga abin bana karewa bane sai na yi maza na cire abubuwan da nake ganin tana yi mishin a raina tunda dai ni ba zan iya yi mishi hakan a gabanta ba bale ince zan rama.
Satina uku da zuwa gidan aka soma azumin watan ramadan babu yanda banyi da shiba ya barni in je in yiwa babana barka da shiga watan mai albarka ya ki wai shi ya je ya yi mishi hakan itama yaya Dija ban jeba bata zo ba nayi aike har na gaji na hakura taki zuwa sai ana gobe zamu tafi umarar da aka yi ta rikici akan tafiyar da yace zai yi da ni har sai da babanshi ya sa baki cikin maganar shine wai tazo yi min sallama, na sunkuyar da kaina kasa na ki kallonta naki yarda kuma nayi shiru in daina kukan da nake yi mata, wata uku? Wata uku bamu ga juna ba amma baki yi marmarin ganina ba? Baki kuma ji tausayina ba? Tayi murmushi, to yi hakuri Maryamu yi hakuri Merona ai Meron Alhaji Ahmad kwanaki talatin din nan da kikayi a gidanshi kinga yanda kika zama? Ko da yake dai shima naji babansu yana cewa wai kwanciyar hankali dai shine wani abu banga yanda Alhaji Ahmadu ya zama ba amma zai yiwu ne inyi tayi muku zirga-zirga a gida? Yanzu ma ba ki ji ana cewa kullum sai na aiko Inna ta kawo miki magani ba da sassafe? Na daga ido na kalleta saboda jin maganar tata tayi maza ta kawar da zancen ta hanyar fadin in kin yi dawafin Umra kiyi addu'a Ubangiji ya baki 'yan
127
tagwaye, ban kulata ba na shiga daki naje na kawo mata
abinda nake nufin kawo mata watakila sai gab da salla
mu dawo watakila sai bayan sallar ki yi wa su Inna
sayaiya ta ce min to.
Sati uku cif mukayi sai ana gobe salla muka dawo,
kudin sadakina da wanda baba Abba Gana ya bani
kyauta ya ce a kawowa 'yar uwata ta sai min abinda ya
dace su yaya Dija ta kawo min da zamu tati da su na
sayo ra rai masu kyau don ma naki karbarj aka gudan da
Mubarak ya bani na ce ya rike su.
Hirar da Mubarak ya yi min a car wanda a ciki ya
tabbatar min da labarin da baba Sumaye ta taba bani na
cewar ba ummanshi ce mahaifiyarshi ba ya sani yiwa
ban gaya mishi ba, nayi rabon tsaraba na dai dai
mahaifiyar tashi sayaiya mai yawa don tsarabarta sai dai
gwargwado na kuma yi rabon har da mutanen Gaidan na
aika musu da shi.
A wannan lokacin ni da Mubarak anarci sosai
mukeyi saboda duk abubuwan da a farkons l'amarin
suke masu tsanani da sanya faduwar gaba a tsakani sun
zamo masu sauki a yau da sanya nishadi in tsaya fadin ji
da ni yake yana tarairayata ya zama tamkar sakarci ne
zanfi gwammacewa in ce muku duk abinda yake so shi
nake yi mishi.
Ashe duk wannan kwaramniyar da wannan kai
kawon Maryam ashe dai ke din matatace, ince mishi eh
yallabai ni taka ce da rabon dai kawai za a ji jiki ne, sai
ya yi maza ya ce a1 babu komai ba gashi yanzu ya wuce
ba darussan da muka koya tare da mu kuma suna nan
128
Zamu rkesu iya tsawon rayuwarmu? in ce mishi eh, sa
ya ce to ai shi kenan.
Kwananmu shida da dawowa randa mka dawo ya
sauka a dakin Rumasa'u ne ni ma ranar ban wani damu
sO nake in dan samu sararawa ya yi kwana biyu ya dawo
wurina ranar ma ina hutun sallah ya yi biyu yau koma
can ya sake yin wasu biyun ranar zan karbeshi ya shigo
wurina da safe akwai wata mas'ala ne? Na ce mishi, a'a
ni kin fara ealla ikuwa? Na sake ce masa a'a har ya juya
zai tafi sai na ce mishi da ina so in rokeka wata alfarma,
ya juyo yana kallona, kamar wace iri kenan, nace so nake
ka sa a kaini jaji ina so inje wajen su Inna.
Ya danyi shiru kadan kafin ya ce min, to ki saurareni
na ce mishi to ya juya ya tafi.
Banda vvannan girkin da nayi da ya koma wajen
Rumasa'u zai sake dawowa wurina sai muka tafi.
Wajen karfe hudu da rabi muka isa duk da ya ce
sammako zamu yi mu isa wajen sha daya ko sha biyu in
mukayi la'asarm u wuce Kaduna gidan Abdulhamid mu
kwana a can ban san yanda akayi sarnmakon bai yiwu ba.
Hirar baki ba za za ta iya fahimtar da mutum ya gane
irin son da Mubarak yake yiwa mahaifiysarshi ba sai yaje
inda take da zama yaga irin gatan da yayi mata shi ba
mutum ne ma yawan magana a kan mahaiñyarshi baa
ssannan bakina da nashi sai ya tabbatar min da cewar
yana dadewa baije wurinta ba a dalilin babu wata
shakuwa a tsakaninsu ya santa ne bayan ya girma har ya
soma karatu a jami'a ya nemeta don kanshi ita bata taba
waiwayowa ta kalleshi ba watakila an bata mata rai ne ya
sa tayi mishi hakan watakila kuma don ta ga ta haifi
129
wasu mnasu yawa ne ya sa