Showing 6001 words to 9000 words out of 41517 words

Chapter 3 - Halin Rayuwa Book 4 Hausa Novel Complete

Sodangi   

28 Jan 2025

245

kice sai an ci dole? To an yi an kuma karawa.
Ta sake gutsura ta kai baki ta sake mayarwa cikin
kwanon, ina daga dakina ina jin su ban san yanda aka
yi ba sai kawai naji an kaure da dambe.
Dambe kuwa ra gaske, tunda dukkansu karfafa ne,
ko motsi ban yi ba balle in yi tunanin raba su, sai
kawai raga an daga Baba Lantana an nanata da kasa,
Safara ta haye kan ruwan cikinta tayi ta kirbar bakinta
da duka, da ta ga hakan ma bai yi mata ba, sai ta
shaketa her sai da wuya ta sa ia bude baki tayi maza ta
kwaso gwajaljelon tuwon da ta tauna ta mayar te
warba mata shi a baki ta matse bakin sai da ta hadiyo
shi.
Sannan ta saketa ta mike tayi tafiyarta tare da fadin
"Haba, ina amfanin babban da bai san ciwon kansi ba?
Ina kyale ki ba ki san kyale ki nake yi ba, to mu zuba
shege ka fasa ni da ke."
Da daddare Babana ya dawo, ta zaunar da shi ta
rattaba mishi bayani, kala bai ce mata ba. Ta sake
tunzura zata tasa shi a gaba da masifa, ya fito yazo
yayi shimfida a tsakar gida yayi kwanciyarshi, duk da
29

sanyin da ake yi bai tashi ba sai da lokacin zuwa
Masallacin shi yayi.
Wannan zaman ai' ba dole ba ne, kai Mallam ai
dama ba mijin mata biyu ba ne, muturmin da baya iya
buda baki yayi magana yaya za ayi ya iya ajiye mata
biyu? Kullum balki a rufe kamar na mai ciwon bubu.
Gara kawai ka sauwake min ka sake ni ka ji ui ko ba
ka ji ni ba?
Bai kulata ba, ta gaji da fadan ita kadai ta shiga
dakinta ta kama fitar da kaya, ai na ce na daina
wannan matsiyacin auren, yau na daina shi ko ka bani
takarda ko kar ka ba ni tafiyata zan yi.
ina ganin ta gama kwashe kayanta ta tafi na shiga
dakin na share yana, na share dattin dakiu tas na ce wa
Anti Safara bari in taya ki ki kwashe kayanki ki koma
can, da sauri ta ce min au haba? Na ce mata eh.
Nan da nan muka bar komai muka koma aikin
jidan kayanta muka maida su dakin Innata, dakin da
nake ganin kamar babu vani daki da zan so kamar shi,
muka gyara komai yayi tsaf gwanin kyau.
Gidanmu yayi matukar yin dadi, Anti Safara tayi ta
tattalinmu ni da Babana, har ma da Sallau. Sai dai sh1
kam bai iya zama ba, yana ganin Baba Lantana ta
kwana biyu bata dawo ba, sai yayi wa Babana sallama.
ya tafi sai dai bai fadi inda za shin ba.
'Yan kwanaki kadan da auran Babana, kwanakin
da ko talatin ba su cika ba, sai ga Babana har ya yi
kyau, yayi fes da shi in muna zaune mu biyu kuwa zai
30

dar rage murya ya ce min, "Oh, ashe lafiyayyar
yarinya ku ka samar min? Ubangiji dai ya jikan
Ramatu da rahamarse. In ce mishi amin.
Randa Baba Lantana ta cika sati biyu da tafiya,
raear Yaya Dijah tazo mana wuni da ita da ya'yanta
duka, dama dan da Anti Safaran ta yaye Nasiru, rabon
Yaya Dijah da yin irin wannan zuwan ni dai na manta.
Babana ya wuni cikin farin ciki yana ta ina yaka
saka da jikokinshi, itama Anti Safaran haka. Sai wajen.
yamma ta shirya zata tafi, ya yi tayi mata addu'a yana
sa maia albarka, ita zuciyarta gaba daya ko daga ji
kuma kasan har da jin dadin abinda tayi mishi.
Da zata tafi sai naji ta ce min ga dan hira nan na
kawo miki, ya taya ki zama nayi maza na ce mata to na
kama hannunshi na riks nayi mata rakiya muka dawo
tarc da shi.
Mu'amalla ce sosai tsakanina da Safara, duk da ta
same ni a shekaruna na budurci sosai wanda a
lokacinmu ma ba a cika samun 'yanmata masu shekaru
irin nawan ba in dai ba a gidajen da 'ya'yansu ke
karatu sosai ba.
Amma hakan bai sa tayi wasa da kulawa da
al'emurana dan kankanin canji in ta gani a tare da ni zata
tsaya taga ta warware min shi. Haka nan sai aiki ya mana
keza gyara abu kaza kar kiyi kaza, kaza da ki ke yi ki
daina babu kyau.
Abinda na tabbatar shi ne da ita ce ta zauna da ni a
shekaruna na kuruciya, to da tarbiya sosai tayi min, n
kuma zan fita to bai zamo meta komai ba in ce mata za ni

31
wuri kaza ta ce min kai a'a kina yawan fita ba dab1' ar
budurwa mai mutunci ba ne yin hakan.
Sai dai in makaranta za ni, in kuwa za ni Makarantar
to ko ina da kudina tunda ina sana'ata tana gani zata
kawo kudi ta ce min ungo ki kara, in yi mata godiya.
A haka sai gidan namu ya sake zama wani wuri mai
cike da ni'ima zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali
ga kuma girmama na gaba, tana girmama Babana nima
ina girmamata, tan kyautata min nima ina kula mata da
danta. Gaba daya sai muka zamo muna son junanmu
sosai.
Rannan aka wayi gari Safara tana yin mashasshara da
mura, ban kai gane kan kornei ba saboda ban taba
kawowa raina cewar wani abu zai iya faruwa ba, na dai
ga Babana yana ta kaiwa da kawowa cikin wani iri
yaneyi na tsananin farin ciki, bai isya zama a runfarshi ya
wuni kamar yanda ya saba, sai ya dawo gida dubata.
Wani lokaci sau daya wani ma ahr sau biyu in zai
shigo kuma bai shigowa hannu haka sai yazo oa wasi
abinda zai miko min ya ce "Karbi ki wanke muku." in ce
mishi To. In wanke in kawo mata ita kuma sai ta ce mun
to dibi naki mana, in ce mata to in diba ta ce min kara in
naga zan kara in Kara in kuwa ya ishe ni in ce ya ishe ni.
Anti Safara da kanta ne ta gaji ta ce min ciki ne da ita
saboda Iuran da tayi ta gane ban gane ba, mamaki gami
da farin ciki suka taran mun, har ta gane abinda nake
ciki. Mamakin me ki ke yi haka? Kin yi zaton ba zai kara
haihuwa ba ne? Na ce, "Eh, to ai na gane kamar ya
girma."

32

la sake wani murmushin tare da fadin "Don ya haifi
Hadiza sai ya tsufa ko kuwa dai dun kin ji matarshi tana
yi mishi sharin bai tabuka komai? Shira nayi ban yi
magana ba, don kuwa naga kamar ta wuce sanina.
sNa dai san kawai ba karamin farin ciki nayi ba,
saboda ganin da nayi nima zan samu kani ko kanwa, in
musu nima irin abinda Yaya Dijah take yi min na kulawa da tausayawa.
Muna cikin wannan halin sai ga Baba Lantana tana
shigowa da kayanta kwararam-kwararam tana ajiye su a
tsakar gida, tana komawa tana shigowa da wasu. Ta rame
tayi baki tanfar wacce ta tashi daga jinya mai tsanani.
Yaya haka kuma naga an shigar min claki? Wannan
wane irin neman magana ne? ba sakina aka yi ba, ba
komai ba sai kuma kawai daga na fita da kayana ayi
maza a shige nin daki? Ke Yachuwuna kina ganin irin
wannan neman maganan ko?
Nayi maza na kalleta a firgice na soma gaisheta cikin
wani irin yanayi saboda rashin sabo da yin magana da ita.
Babana ya fito daga dakin Safara ya wuce zai fita bai
kulata ba ta bishi da kallo, Mallam kana gani na dawo
ba za ka kula i ba? shiru yayi yana tafiyarshi, tayi
maza ta sake ce mishi to kayi mata magana ta fita daga
dakina ta bani wuri in sa kayana don kar hakan ya zama
wata fitina a tsakaninmu.
Bai tanka ba yayi ticewarshi ya tafi, bain ciki ya
kama ta ta ce "Wannan shirnu na Mallam, wannan shiru
na Mallam ashe ba zai daina ba?" Ta jinjina kai ta rasa
abinda zata ce. A zuciyata na ee, da dai kin san abinda
33

zai faru kenan da ba ki yi mishi abinda ki ka yi mishin
ba.
Baba Lantana taja ta tsaya cikin wani irin yanayi na
rashin sanin abin yi, da dai ba su taba gwada yar kashi
da Safara ba, da tayi wani yunkuri. To babu hali, tana
shakka gashi kuma Safara sai kai kawo take yi ko kallon
inda take kuma bata yi ba, balle ta tanka mata.
Ta gaji da tsayuwa tayi kamar ta kwashe kayan nata
ta koma inda ta fito, ban san kuma me ta tuna ba. Sai
naga ta bude wancan dakin tasa kayan nata a ciki. Ta
gyara tayi zamanta.
Tsoro yayi matukar kama ni, ko me yasa Baba
Lantana tayi irin wannan canzawar? Mace ce mai fadin
rai, nuna isa da ganin kowa ma bai isa ba, wani abu taje
ta gano ya sa ta tayi wannan canzawar ko lkuwa dai wani
abin take shiryawa?
Na gama abincin daren' da nayi don tun zuwan Anti
Safara mafi yawancin girkinta ni take sawa in yi, to balle
kuma yanzu da take fama da laulayin cikinta.
Ina gamawa na zubawa kowa har ds Babs Lantanan
na kai mata nata na yiwa Babana shimfidar tabarma a
tsakar gida inda ya saba zama, na ajiye mishi nashi a nan.
Yana dawowa daga Masallaci ya shiga wurin Anti
Safara yayi mata sannu da jiki, ya dawo ya hau kan
tabarmarshi ya zauna ya soma cin abincinshi.
Baba Lantana ta fito tazo daga bakin kofarta tana yi
mishi magana, bai ce mata komai ba. To ka shiga daga
ciki mana Mallam, wannan hirar da ka ke yi a waje ai ya wuce ka'ida."
34

Bai ce mata kala bá, har bacci ya dauke ni suna nan a
wurin shi yana kan tabirma a zaune, ya jingina da jikin
bango, ita kuma tana daga bakin kofarta.
Ban san yanda aka yi ba, cikin dare ne kawai na farka
a dalilin buga minkofar dakina da take yi da iyakacin
karfintai tana gaya min wai in fito in ga abinda Babana yakeyi, girkinta ne amma gashi nan ya sake ta ya shige
dakin wannan tsinanniyar matar yana yin abinda babu
kyau.
Duk da katse min baccin da tayi ta kuma hana ni sake
runtsawa saboda buga min kofar da taki dainawa ban
motsa ba, balle in yi yunkurin saukówa daga gadon nawa in fito.
Ban saniba ko ta gane ba zan fito ba ne yasa ta bar tawa kofar ta koma buga tasu, a zuciyata na ce dama tuntuni hakan kikayi da yafi miki.
Girki nane fa Mallam, yau a wurina fa kake, nan take ta soma kuka tana fadin "Ban yafe maka ba Mallam. Bazan yafe maka satan kwanan da kayi min kaje wurinta ba.
Ban taba ji ko ganin Baba Lantana tana kuka ba a zaman da nayi da ita ba sai rannan, kuka kuma bana wasa ba, ko da yake babu wata kyakkyawar alaka ko wata kauna sa ke tsakanina da Baba Lantana.
Amma kuma hakan bai sa naji dadin yansa Baban nawa yayi ba duk da dai itama bata taba yiwa wani adalci ba, a lokacin da ta samu damarta.
Gari na wayewa nayi maza na gama abinda zan yi na suri jakata na saba a kafada na fita gidan na bar Baba Lantana a tsakar gida a tsaye rike da shirgegiyar tabarya
35

a hannunta, tana rantsuwar sai dai in ba za su fito ba,
amma sai ta rafke su da tabaryar hannun nata.
Na wuce na tati makarantar da nake zuwa TP, wato
(Teaching Practice) saboda gab nake da kammala
karatuna a Makarantar addini mai zurfi.
A hanyata ta dawowa gida zuciyata tunani take yi
kan yanda ta kare tsakanin Baba Lantana da su Babana.
Ina isa gida ban san yanda aka yi ba sai kuma naga
Baba Lantana da na bari da tabarya a hannu da kulu a
goshi, ban tambayi Safara yanda aka yi ba, to balle kuma
Baba Lantana da ban ma iya yin wata magana da ita ba.
"Kin dawo ne?" Na ce mata "Eh." "To ga fura nan da
nama Babanki ya aike da shi, na diban mii, nace to
sannu. A zuciyata nace ko ba komai dai yanzu ina da
kaso a abinda Babana yake kawowa.
Na gama cin naman ina shan furar sai ga Baba
Lantana ta fado cikin dakin nawa, nayi maza na mike
tsaye saboda tsoratar da nayi, tunda ban taba ganin ta
shigo dakin nawa ba.
Ban sani ba ko itama ta gane tsoratar da nayi da itan
ne yasa ta fara yi min bayanin avinda ya kawo tan cikin
sauri kinga kulun goshin nan nawa ko?"
Na daga ido na kalli kulun goshin nata da take
tabawa da hannunta, kan in ce mata na gani sai kawai
naji ta ce min, To Mallam ne yayi min shi.
Nayi maza na sake kallon kulun saboda razanar da
nayi da jin bayanin nata, kulun ya amsa sunan kulun ban
san yanda aka yi ba naji bakina ya ce mata sannu, tayi
maza ta ce yauwa.
36


A tsakanin wannan lokacin ba sai an gaya min ba, ni
da kaina nasan Baba Lantana tara cikin wani halinba
tsananin bacin rai kowane lokaci a cikin kuka take.
Ashe haka Mallam yake? Tafdijam! Ashe shiru-
shirun nan na shi ba na kalau ba ne? dama fa nasha jin
ana cewa ka ji tsoron mai shiru-shiru, ban taba yarda ba
sai a wannan lokacin, yanzu ne na gane lale Mallam
munafuki ne.
Ko kadan bana jin tausayin Baba Lantana, saboda
azabtarwar da tayi mana ni da Bbana, ta wulakantamu
ta tozarta mu, gara ma ni komai tayi min da sauki tunda a
kuruciyata tayi min, amma shi Babana ta same shi ae da
girmanshi da mutuncin shi a tsakanin mutanen unguwa.
Kowa ya 1a girmnamasbi saboda ya kame kanshi bai
shiga harkar kowa, bai sa ido kan abinda wani yake yi,
balle ya yi gaba ya bada labari.
Bai sa ido kan abin wani ya gamsu da abinda yake da
shi amma zuwan Baba Lantana gidanmu sai da ta maida
shi abin kwatancen mutane.
Komai aka yi sai ka ji sun co kai haba, kar ka maida
mu Mallam Habu mai anatir Mana, to amma duk da
haka ba na jir dadin ganin yanda yake yi na hanata
kwananta da yake yi yana barinta tana kwana ihu tunda a
karatun da ake yi mana Malamai suna yin bayani kan
rabon kwana a tsakanin mata wajibi ne abinda kayi a can
ne bai zamo lalle sai kayi shi a nan ba.
Amma akaiwa mace kwanan wannen dole ne, to shi
Babana baya kaiwa. Da dai ace ina cikin masu baiwa
Babana shawara, to da nace mishi cikin biyu ya zabi
daya.
37

Ya yi ko dai ya rinka shiga dalkin Baba Lantana yana
kwana tunda dai zaman aurenshi take yi ko kuma ya ce
mata ta tafi. Ya sake ta don ya sauwakewa kanshi
al amura.
Sanin da nayi hakan da ake yi bai yi ba, ya sa ni
tafiya gidan Yaya Dijah nayi mata bayani, a yatsine ta
kalle ni to ke ina ruwanki? Inta ji babu dadi ta tafi mana.
Na ce, A'a Yaya Dijah, ai ba don ita nake maganar
ba, nayi mata gwargwadon bayanin da zan yi mata, ta ce
to naji in na zo gidan zan yi magana da ma ina so in zo
wurin Baban na ce mata ko na kama hanya na dawo
gida.
Yaya Dijah ba ta zo gida ba sai a ranar Laraba da
safe, muna zaune a falon Anti Safara inda nan ne wurin
zaman Babana a kowane lokaci.
Hira muke yi cikin yanayi na jin dadi ni da shi da
Yaya Dijah, yayin da Anti Safara ke kicin tana shirya
abincin rana, ita kuwa Baba Lantana da yanzu ko tsakar
gida bata cika fitowa ba take dakinta.
"Oh Baba, yanzu har a irin alherin nan da yake shirin
samunmu na Mero ma zata samu kani a bayanta zamu
sake samun dan uwa ke 'yar uwa, maimakon mu biyu ko
mu koma mu uku ba za ka yi hakuri ka gaya.mana inda
danginka suke ba?
Ba don mu kadai ba Baba ba ma don mu ba tunda mu
kam ni da Mairo ai mun riga mun mallaki hankulanmu,
mun fuskanci rayuwa mun kuma fara gane yanda take
ba, komai dan Adam yake so yake samu ba.
Don wadannan da za su zo daga baya Baba gaya
mana inda danginka da garinmu yake in wani laifi suka

38


yi maka i Hadiza yarica na roke ka ka yafe musu ta kai
menene? Ai ya wuce Baba kayi hakuri ka...
Tayi maza tayi dib taja balkinta tayi shiru ta bar
Karasa maganar watakila sai lokacinne ta daga ido ta
kalli yanayin da ke fuskarshi wanda ni tunda ta fara
maganar nasa na gani shi yasa nayi ta taba ta bata gane abinda nake nufi ba.
Ta tashi ta bar dakin saboda daurewar fiaskar tashi, ta
kai matuka nima na tashi na biyo ta muka dawo dakina
muka zauna tayi kuka har a gaji tnyi shir ta iar
hawayenta.
Kwana biyu bayan nan Anti Safara take bani abarin
cewar Babana ba lafsya te da shi ba, kartin hali ne kawa
yake yi yasa ake ganinshi yana yawo.
Na ce, To. A zuciyata dai fatana da addu'ata bai
wuce ya zamo ba maganar da Yaya Dijah tayi mishi ba
ne yake nema ya tayar mishi da jikin.
Na rasa yanda zaa yi in fuskance shi da maganar
rashin lafiyar tashi, saboda tun daga. ranar da na raka
Yaya Dijah tayi mishi wannan maganar fuskarshi daure take.
A zuciyata na kudurawa Kaina ba zan sake yarda
Yaya Dijah ta ce min za ta yi mishi irin wanan maganar
in bar ta ba, tunda baya so, shi kenan a kyale shi, yan
uwanshi shi yasan abinda ke tsakaninsu.
Abunda ya fi komai muhimmanci wurin da uba ne,
tunda shi ne asali to mun gode tunda muna da shi kowa
yasan muna da shi mun kuma san shi, mun rayu tare da
shi, babu wanda zai yi mana gorin rashin uba, sai na
rashin 'yan uwan uba.
39

Wasu suna nan su ba su ma san ubannin nasu ba balle
suyi maganar danginshi suna nan kila a dadin su ma
kuma suna rayuwarsu don haka na hakura itama zan
gaya mata ta hakura suma yan bayan in sun hakura
kamar yanda suka same mu mu ma akan hakurin.
Rannan da daddare Anti Safara ta buga min kofa
gabana yayi mummunan yankewa don kuwa na tabbatar
jikin Babana ne yayi tsanani yasa aka tashe ni tunda tun
da rana ina kallon iin wahalar da yake yi akan lai
kawon numfashinshi da bai karasawa ya sauka cikn ciki
sai dai a Kirji.
Babu yanda Yaya Dijah da naje na kirawo a dalilin
jikin nashi bata yi da shi ba akan muje asibiti ya ki yarda.
Da sauri na 6alle kofar na fito na ufi dakin Anti
Safara da ke bude a kasa, na samu Babana na zaune a
cikin yanayin rauni mai yawa.
Ko zama da kyau bai iyawa saboda ya riga ya rasa
karfi a tare da shi, numfashi sai kaiwa da kawowa yake
yi a tsakanin kirjinshi da makogoronshi.
"Sannu Mallam, Ubangiji ya baka lafiya." Tana
sannun tana share mishi hawayen da ke diga daga
goshinshi, tana kuma kuka.
Jikina ya dauki bari saboda yanda al'amarin ya tuna
min da yanda naga Innata a daren da zata bar duniya. Da
gudu na juya na bude kofa na bar gida.
Nufina wai in je gidan Yaya Dijah in kirata tazo ta
taya ni ganin abinda Babana yake yi, sai kawai muka yi
kicibis da Isiyaku.
Ban san daga ina yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login