Showing 27001 words to 30000 words out of 37209 words

Chapter 10 - Karashan Murucin Kan Dutse Book One Complete Hausa Novel

15 Oct 2025

265

uwa da harara da hassada a fili na kishi.
Nan ta fice tabar hindatun na kallon yanayin shi ta fahinci akwai bacin rai a ciki sannu da zuwa tai mashi don har lokacin ba dadi a tsakanin su.
Washegari da safe sai shirin zuwa taron mu akeyi don na bugo waya muna iya port a lokacin da zamu taso daga lagos din.
Tsayawa fadin irin shirin da nayi bata lokaci ne dagani har yaran munyi kyau sosai don zama indiya ba wasa ba gaskiya.
Ban kawo komai ba a raina na cewa zamu hadu da wai wata amaryan shi ni dai daukina kawai shinenaga yarana dana share tsawon watan ni bama tare da su.
Mun kai wani dan lokaci kafin mu tashi don haka sai sha biyu muka sauka a Abuja inda shi da yaran ne suka zo taron mu da hindatu.
Da murna na rungumay yarana ban ko bi ta kan sgi muka kuma rugumay juna da hindatu din sai yaran da suka rugumay mahaifin su don murnan ganin shi.
Jinior yana lake a jikina na dago kai muka hada ido dashi alaman radhin gaskiya irin na maza karara a gareshi nace yallabai mun samay ku lafiya ?
Ya dan murmusa yace lafiya kalau ya karatu da zaman india nace sai hamdala na dauki yar wurin hindatu dake murnan ganin mu.
Mun dan dauki lokaci muka kwasa sai gida ina tare da yarana har muka kawo gida ina maijin dadin ganin yadda yaran ke a cikin walwalan su babu wani mairaicin rashina da suka yi.
Wani abin sai uwa dama abinda nake so ke nan na dage akan sai Inna tazo ta zauna min da yaran duk da kunyan da take nunawa na rashin son nuwa duniya itace mahaifiya na a matsayina na yar fari a gurin ta.
Muna shiga gida na hango wata mace a tafe tana bun kasa a kasa da waya a hannun ta bayan na bude motan kafana kawai na sako a kasa ba tare da na fito ba muka tsaya magana da yaran dake fadan daukar jakana na hannu.
Sai da na raba gardaman na karasa fitowa daga motar gaba daya hankalinta na a gurin mu yayin dana karasa fitowa daga cikin motar gaba daya sandarewa tayi a tsaye inda take tana rayawa a ranta ta ina zata fara dani.
Ga dai Ilimi ga kuma uwa uba kyau da tsari da ta hango muraran a wurina ga wani kwarjini da nai mata a idanuwanta a lokaci daya.
Ban ko koma ta kanta ba na ja yarana muka fara hawa steps din shiga gidan hankalina a kwance.
Sai naji shi yana fadin Samira ga do???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?cter ta dawo fa daga india ita da yaran ta yadda tai min wani irin kallo nima haka na juyo nai mata tare da fadin wacece kuma Samira ?
Kafin yai magana sai naji tace wace kike gani a gaban ki nice amaryan maigidan da fatan zaki gane ni daga yau.
Wani kallo nai mata tare da sake shuumin murmushi nake cewa amarya amarya fa ko dai uwar gidan wanan ai ba a kiran ta da amarya don ta haife mu ko ?
Ai sai dai mu bata kambun uwargidan cin gidan gaba daya shi zai fi sauki na fadi haka ne don irin yadda ta mayar min da magana itama.
Murmushi daddy tayi daga inda yake tsaye yake cewa shiga dai ki huta kafin muyi magana ko nace magana kuma may ya saura tunda ka gabatar da mu ga junar mu na juya muka shige da yaran ina jin tana fadin.
Duniya na haifa ba ku ba sai ki tsaya ga wanda ya aje ki in kina takama da kurciyane ai ya ganki a gaban shi ya dauko ni.
Ban tsaya ba don nasan su Inna na gidan muka shige ciki nan muka tari junar mu da murna ban sake bi ta kan shi ba ga yarana sun baibaye ni.
Ban samu kaina dasu ba sai da akai kiran sallah na kora su suje sallah na samu na shiga dakina sai dai zuciyana fam yake da tunanen wanan matar.
Bayan nai wanka na sauya kayan jikina sai ga Atika tashigo dakin da murnan ta don bata gida da muka iso tana school muna cikin hira da ita ne daddy ya shigo dakin ya samay mu.
Wani kallo na tsana na watsa mashi yayin da Atika ta gaidashi tafice daga dakin yake cewa dani basu dai barki kin huta ba ke nan.
Nace ba kadai barni na huta ba kai da ka kara jajibo muna wani wahala a gidan kuma.
Wahala kuma Rahama aureb nawa shine wahala nace a lalace aure ina aure a nan ka kwaso muna uwar mata wai kishiya wanan ai a gidan dabe ya dace a ganta ba a gidan ka ba.
Mace haka babu fasali a tare da ita daganin ta ma irin matan nan ne yan safara ba abin kwarai bane don tanayin ta yai kama da yan kano jidda.
Dariya yayi min cikin shuumanci yace duk ita kadai nace ni na rasa gane wanan irin rayuwan for god sake may ye ka rasa daddy a gurin mu da baka da aiki sai auren barnan suna ko yaushe.
Wanan ce zan zauna da ita a cikin gidan nan haka ga yara a haka yara zasu tashi da irin tarbiyan da muke so a garesu.
Ko yaushe suna ganin nauin mata lalatattu iri iri gaskiya ya zama dole a gare ni wanan karon na nisance ka kaje duk abinda kake nema a gun mata kaita nema amma wanan tanbadar badani Rahama ba gaskiya.
Ysi yar dariya yace dake kuwa zaku zauna a gidan nan ba wani gida ba auren da nake may nake rage ku dashi dakuke wanan kishin haka wai ?
Nace kishi kishin wa zanyi wanan ai uwatace ba kishiya ba ni bata a gabana gani nayi kawai a tsaye take tana daukan kanta hamshakiya .
Ya kai zaune tare da kai hannun shi a saman cinyana nai saurin kabe hannun nashi ina fadin kada ka soma don nagaji da wanan halin naka daddy a yau nayi nadamar auren ka da samun zuria da kai a duniyan nan.
Da sauri ya katse ni yana fadin Rahama ni keke fadawa kinyi nadaman aure na da kikayi nace na fada don abin ya isheni haka.
Bai yi magana ba sai naga ya mike ya fice daga dakin ran shi a bace nima na raka shi da haraea tare da tsuki na haye gadona don daukan shi ma nake bai san ciwon kan shi ba kuma.
Mutum ya koma na mamajo haka baida aiki sai aure may ya rasa a gun matan shi da yake muna wanan hakin auren kuma ko yaushe kamar ba aure na kai sake ba idan yayi.
Kai da zakaga matan sai kaji nauyi da kunya don basu dace da ajin shi ba abu dai gashi bai faduwa ga mutum.
Abinda mu ba musani ba shine ashe idan namiji ba mazinaci bane haka wani lokaci yakan kasance dashi ga matan yanzu basu tunkaran namiji sai sun shirya mashi da saddabaru da dan sihiri shi ke saka idan namiji ya yi wani abin kaji wani iri a ran ka.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

Kuyi hakkuri masu fadin wai novel din ya dau lokaci anayin sa ba laifina bane yadda labarin yazo ne idan kuma na katse shi yadda na katse tarko nasan bazaku ji dadina ba zan ta samun korafi ne kuyi hakkuri saura kadan mu karasa da yardan ubangiji
Na gode da fatan zaku fahince ni yan uwa kuma kuyi hakkuri dani please rashin waya ya kaimu har wanan lokacin haka.
[5/18, 22:51] +234 703 214 5167: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , , ,

108
Daga wanan fitan bai kara kulani ba nima haka inda na shiga harkokina da yara da abokan arziki masu zuwa yi min sannu da zuwa .
Ba wai share junan da mukayi baya damuna bane a a na dai yi niyar daukarwa kaina matakin da ya dace ne don abin nashi ya fara bada tsoro a zuciya na.
Tafiyan wata uku kacal sai aure a bayana daga mutuwan anty yai auren Raliya, Raliya tana fita ba a dade ba ya dauko Niima itama ta debi rabonta tai gaba.
Nisawa nayi a fili nace mijin bahausa ke nan ke mace baki da tabbas zama da mata daya ko biyu zuwa uku sai ranan da rayuwa ya kare wa bawa.
Mun koma bakin aikin mu bayan sati daya ga Inna sai shirin komawa take kano don zaman nan ya kai mata ko ina don bata saba ba zaman dole takeyi.
Ranan da na fara fita na dawo a gajiye don yan aiyukan da nayi a office wanka nayi na shirya nafito zuwa dakin da su inna da mama suke na gaidasu.
Suna zaune hiran su suke na shigo da sallama na dakin tare da masu barka da gida suka amsa min cikin kulawa da kauna.
Na samu wuri na zauna tare da kallon kwanon abincin da aka aje a gefen su basu ci ba har lokacin nake cewa dasu sai naga kamar baku taba abincin ba mana ?
Mamace tace dani Rahama in ba so kike mu fashe ba da wanan irin dadin da kuke bamu haka Allah dai ya baku hakkuri zama da mijin ku.
Inna tace ai mai kuli wanan mutumin ba abin da za, ace dashi sai fatan alheri ku dai ta hakkuri kowa da halinsa ake zama dashi duniya balle ni banga wani abin gazawa a gare shi ba akan ku.
Baida maraina akan iyalin shi ko kadan tunda duk wani nauyi da hakkin daga matan har yaran shi yana saukewa kai bama iyalin shi ba har masu aikin dake karkashin shi bai barsu a baya ba dubi gajiye yadda ta koma matar mai gadi fa kawai ba wani ba can.
Kin kai nisa ai inji mama ninan fa yar uwar matarshi ce amma ji yadda yake min tankar mahaifiyan shi ce ke a gidan sau goma zai shigo sai ya shigo nan ya duba ni tare da tambayar banda matsala dai ko ?
May yafi wanan dadi Asiya a duniya ai irin mazan nan ko wace mace na fatan samun iri su a duniya.
Murmushi kawai nayi na gyara zama na araina nace wanan kuka sani ku may yafi bacin rai kullun namiji sunan kuna zaune kalau amma baida aiki sai na kadin aure.
Kamar wanda bai samun jin dadi gun iyalin shi irin wanan ma ai sai duniya ta zagi mutum don baza mu fita sai ace mune bamu gamsar dashi ga wanda bai san halin shi da raayin shi ba.
Sai naji Inna tace kinga ta nan tun dawowan ta na fahinci ba dadi tsakanin ta da shi don ko yawan shigowan da take dubamu ya rage.
A, a haba dai Rahama may kuma kike so a duniya yanzu ilimi da daukaka Allah ya baki ga miji na gwadawa tsara kin samu ga zuria dayyaba Allah yabaku a tsakani may kuma kike nema Rahama ?
In dai don wanan auren da yake yawan yi ne sai ku barshi da halin shi tunda auren nasa bawai yana takura maku bane ko wani abu.
Gaskiya in har hakane abinda uwarki ta fada baki ko kyauta ba don banga abin damuwa ba ga wanan dai.
Bafa a kan ku matan ke zama ba ke ku godewa Allah ma da ba irin mazan nan bane da idan sun dauko wata a gida ke ra gida dake da babu duk daya kuke a wurin shi.
Iya hakkuri bawan Allah nan yana dashi a gare ku iyalin shi ki duba irin tsiyar da yaran nan hindatu da zulfa ke shuka mai amma yana hakkuri yana takewa yana kuma zaune dasu lafiya.
Duk masu shigowan nan ni a ganina kaddaran aure ne a tsakanin shi dasu inba ita wanan daya aura mara tarbiyan ba bayan mutuwan diyana waya haihu dashi ?
Balle ita wanan uwar guzumar daya kwaso yanzu ai ba batun haihuwa a gare ta ma mufa a zamanin mu bamu kishin komai inba na haihuwa ba ki zuba in zuba kowa ya cika gida kuma babu wani abindake ga namiji in dai ba wanan din ba.
Nace mama ni ba wai auren shi bane ko wani abu ke damuna yanzu fa ba irin da can baya ne aure haka a zamanin nan abun tsoro ne ga namiji don zamani ya canza lafiyan mutum akewa tsoro.
Haba yar nan har ke kin fishi sanin hakan ko kin kaishi sanin abinda duniya ke cikine wai inna tace fada mata dai mai kuli yarinyar nan bata ji ne tun bata dawo kasan nan ba mukai wanan maganan da ita.
Ashe ita da manufa a zuciyar ta yanzu kinji inda ta bullo wai ita malamar lafiya dariya inna tabani nace inna ba haka bane ku baku ganewa ne shiyasa.
Bafa ganin mutum yanzu haka lafiyyaye shine lafiya ba ciwon ba a goshi ake ganin shi ba nan dai nai masu bayan komai kan irin cutar da nake gudu gare shi ga yawan auren da yakeyi.
Na kara da fadin yanzu fa ki duba waban matar da ganin ta irin yan duniyan matan nan ne dake zaman kasu a wani kasan bama a na kasan ba kawai.
Nan nake fada masu yadda mukayi da ita ranan da muka dawo garin mama tace yo ga yar iska ita kuma dashi ta shigo watse gida ko may ?
Nan dai suke min nasiha da kuma fadakar dani irin halakan da nake daukawa kaina na wanan zaman doya da manjan da mukeyi dashi a gidan.
Maganan su ba wai ya shigeni bane sosai don ina a kan bakana na sai naga takardan gwajin da sukayi da ita kafin auren su dashi.
Baya gari da ya dawo ya shigo gaida su nan yake magana akan tafiyan inna da zatayi ga jibi sai inna take cewa dashi Alhaji mun gode kwarai da kokarin ka a gare mu ko yaushe don Allah adai ta hakkuri da iyali.
Murmushi yayi yace Inna ai hakkuri ya zama dole tun da an zama daya yanzu suna dauka na ban san may nakeyi bane shi ya kawo haka kawai.
Hakkuri za ayi don mu mata dama sai hakkuri balle ga wanda ya aje mace fiye da daya ko biyu a gidan sa.
Ya mike yana fadin barsu ai mun saba in dai halin su ne komai zai wuce ne insha Allahu.
Da dare na shiga falin nashi don na fada mai ina sin ni da kaina zan mayar da inna gida idan zata tafi do ina son zuwa na duba jikin mahaifina.
Ya dago kai yana cewa dani ashe ina da darajan da za a nemi wani alfarma a guna nace ni ba wana ya kawo ni ba yanzu.
Yace ban amince ba in dai nike da wanan dokar a hannuna nace ba matsala Allah ya bashi lafiya don ban tsaya jan maganan ba .
Namike zan wuce yake cewa dani kina ganin wannan matakin da kika dauka a gare ki shine daidai ko kina min daukan mara hankali ne wai ?
Nace namay kuma nifa auren ka ba wai ya damay ni bane kawai dai magana ta daya ne a nan shine naga takardan ku na gwaji da kukayi da wanan yar duniyar matar tunda abin bana kai sake bane nake gani.
Ko makaho ai sai ya lalaba yake taka wuri ba wai tafiya yake babu lalabe ba mutum tun yana dauko abinda duniya ke iya dan kallo har ya koma dauko abinda za ai mai dariya don bakin jaraba kawai.
Na sa kai zan bar falon naji yace dani Rahama nine yau kuma jarabbabe ko may ?
Nace ai haka din ne don in ba jaraba ba banga abin gani gun wanan curarar matar daka dauko ba a gidan nan ban da magana babu abin ganewa a nan.
Yace a ganin ki ba ni abin dake min na dauko kune baku ganewa kawai nace sai kuje kuyi ta ganewa kai da ita ku da jaraba ya dama a rai.
Ina fadin haka na juya na fice daga falin dakina na nufa kai tsaye na fada saman gado siffan wanan matar dana gani mai kiba wai amarya nake tunane da yace shi yana gane abin sa.
Nace a raina to may daddy ya gani har yace mune wai bamu ganewa a nan dayake fadi ni dai banga wani tsiya ba a gunta in banda muni sai ko launin jikin ta da ya nuna mai take shafawa na zamani.
Shima na barshi can yana tunanen magana na abin ashe ya bata mai rai yace watau ke nan ina nufin baida hankali ko may da zai afkawa mace irin haka kai tsaye shiko Niima da ya aura a budurwa bata shigo gidan shi ba sai da sukai gwaji da ita.
Balle wanan dashi kan sa yasan zaman barikin da tayi a waje dama nan kasan don ba diyar kowa bace ita irin matan nan ne kawai masu sai sunyi kudi da karfin tsiya ko ta wani hanya.
Shi kan shi wani lokaci yakan yi mamakin yadda ya aure ta ba dai tsari takai ko wace mace dake gare shi a gida ba balle auren dai ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login