Showing 24001 words to 27000 words out of 37209 words

Chapter 9 - Karashan Murucin Kan Dutse Book One Complete Hausa Novel

15 Oct 2025

267

kudi.
Saukina ma shine daga Aisha har Amira duk a Abuja muke zaune dasu ko ba kullun ba dai zan dan dinga ganin su a gidan wani lokaci.
Sannu a hankali na ke koyar da Tani mai aiki dana dauko babu wani tsangwama ko takurawa a gare ta don nima tai muna tsakani da Allah yadda muke mata din.
Ban samu matsala da ita ba don tana da hakkuri sosai matan saboda zama da yara dole sai da hakkuri tare dasu.
Tafiyan Nasir ya taso sai faman shiri muke yi na tafiyan nashi tare zamu tafi dashi mukai shi mu dawo ni da daddy sai ga wani tafiya zuwa India ya taso min daga wurin aiki inda zanyi wata uku a can don wani nazari da aka tura mu mu uku .
Wanan dalilin ne ya hana tafiyan dani a lokacin don haka na shirya ma yaron komai daya dace tare da mashi alkawarin zamuzo muyi mai hutu acan U,S din insha Allahu in na samu lokaci.
Na riga su barin kasan inda nai tafiya da kananan yarana sai Maryam dana dauko don su Aisha na karatu a lokacin.
Inna ta da mama Altine ne zasu zauna da yarana a gidan sai dai kafin ta yarda da hakan sai da akakai rana da ita daddy da kansa yaje ya dauko min ita acan kauyen mu.
Su na bari da yaran a gida su zauna min dasu don kula yadda ya dace na tafi wanan tafiyan idan nayi shi akwai alheri sosai gare ni cikin sa ba don hakan ba ba zan bar Nasir ya tafi badani ba irin yadda yaron ya nuna damuwan shi ga rashin zuwa dani a lokacin.
Gida ne aka kama muna kowan mu mai dakuna biyu da falo sai kitchen don haka na samu wani makaranta a kusa na saka yaran a nan.
Haka yasa banda matsalan komai na ci gaba da abinda ya kawo ni kasan nakan kira yara muyi waya dasu dasu inna mu gaisa dasu sai ranan muna waya ne Aisha take fada min cewa anty daddy fa yayi aure bayan ki.
Duk da maganan ya barna min rai amma sai nake cewa cikin dakewa ashe har yayi auren ko ?
Tace anty dama kin san da zancen auren ke nan ashe, nace da ita na sani mana tunda ba fasawa zaiyi ba ai.
Tace sukan maman Ihisan fada sukayi da daddy sosai sai da mamanta tazo garin baki ga matar ba wata lukekiya da ita wai yar kasuwa ce irin shi Dubai take zuwa nace kuma dai.
Tazo satin ta daya ta wuce bata dawo ba yun lokacin nan dai taita bani labarin yadda zuwan matan aka kwashe da daddy har yake cewa inda Rahama ce ba zata taba nuna tashin hankali haka ba ga duk auren da nakeyi amma ke sai ankai ruwa rana dake ko yaushe baki girma.
Yabon banza nace da ita shi dai ya sani yaje yai tayi ai watarana yana gani zai bar matan wanan wani irin rayuwane ma daddy kamar wanda keda bakin uwa akan sa.
Mun yi sallama da ita ta barni da wanan damuwar a raina ni kadai a kasan mutane daga karshe na tattara na watsar da zancen don ba zan yarda na saka wanan zancen ya ja min matsala ba.
Sai dai ina jiran shi ya fada min da kan shi kancewa yayi auren wanan karon nayi alkawarin zai jini sosai ba dadi don abin ya ishe ni hakana wallahi.
Har ina batun dawowa bai fada min ba nima ban mai magana ba akai sai gashi ranan na kira su Inna muna waya dasu nake fada masu karshen wata zamu dawo insha Allahu.
Sai bayan mun gama hiran mu nace tabawa yaran sai naji tace dani Yarinya dama ina son muyi wani magana dake kafin ki dawo nace to Inna ta.
Tace ba wani abu bane nasan a gurin ki don kin saba da hakan daga mijin ku don ya kara aure a bayan ki don haka kada ki yarda naji wani abinda bai dace ba ya fito daga gare ki kan wanan maganan kamar yadda ya uwan zaman ki sukai mashi.
Shiru nayi sai naji tace kina ko jina yarinya nace ina jinki inna ta ba ruwana da zancen auren shi ni matsala na daya shine idan ya tabbatar da lafiyan matan da yake aure ai shike nan .
Duk da dai nasan ba zai yarda yana aure haka ido a rufe ba don yana da wayen wan shi akai amma ni mace ba a kaina zata zauna ba ai shi da ya dauko shiyasan abin shi can.
Tace haka nake so ji dama a gare ki don Allah ki taushi zuciyar ki irin yadda kika saba don shima ya fadi hakan da bakin shi a gurin sulhun da akai masu da ita wanan hindatun kishiyar ki.
Nace kai maman Ihisan ma dai da wani abu take wallahi mata nawa yake daukowa agidan a yaya ake karewa dasu irin su daddy ai sai ido kawai don abin nashi kamar mai bakin uwa akai.
Inna tace min ai ba kama bane don ance uwar ce tace dashi a lokacin marigayiya na da rai da zai auri su Zulfa take cewa da ita indai kishi ne sai dai taitayi mata hudu sai ya zauna dasu a gidan tana gani ba fashi.
Nai dariya tare da fadin Allah sarki ita Allah bai nufa tagani ba amma su gashi ai suna gani da ran su shiyasa ba a son uwaye nawa diya furci ko yayane cikin bacin rai .
Inna tace hakane sai dai ai bamu ganewa ne kawai odan ran mu ya baci a lokacin komai mutum zai iya furtawa yanzu dai kinga bako a kan shi bane ta furta amma da yake abin ya shafe shi kinga shi da yake nata a gunshi furcin ya sauka ai.
Inna Allah dai ya kuauta amma abin na daddy ai sai addua kawai don ni na rasa may yake ganewa ga wanan yawan auren da yake yi har nakan yi tunanen nace ko dai mune din baya jin dadin zama damu yasa yake hasashen wasu a waje.
Tace ummm, umm yarinya ba haka bane fa abune da ubangiji ya halasta masuyin shi shi kuma kinga yana da halin shi da zai yi wanda ma baida hali yayi wanan kokarin haka rabu da namijin baushe idan yasa rai ga yin abu bawai gazawan ku bane ko wani abu haka dai Allah ya doro mai wanan rayuwan kuma.
In bashi ba ai masu hali ma basu faye yawan aure hakan ba nagani ku dai sai kuyi ta hakkuri dashi kawai tunda haka Allah ya nufe ku da gani.
Nace nagode inna tace may ye na godiya ki dai godewa Allah da bai aza maki zafin kishi irin na hauka ba akai duk da kinayi amma ai ba irin na wasu ba har a wuce wuri akai.
Munyi sallama inna ta barni da tunanen irin matakin da naso daukawar wa daddy kan wanan aure sai naga ai duk maganan inna gaskiyane ba karyaba.
Babu abinda na rasa a rayuwana yanzu duk da ina da hanyan samu ai shi bai rage min komai ba na hakkin na daya rataya a wuyan shi don haka may zai sa na tsaya batawa kaina lokaci kan wanan shirmayn nabaya ma da yayi iba suka kai balle wai wata matafiya kuma can.
Matsala dai daya ne sai na saurara na sa ido naga ita kuma damay ta shigo gidan idan har bata shiga da sunana ba irin na Raliya da Niima may zai damay ni kuma da ita.
Bata zama bana zama banga abin damuwa ba akai kowa tashi ta fishe shi don miji mai aure aure ai ba dan goyo bane na ma godewa Allah da baiyo ni mai rawan kai ba akan miji da zan tsaya nuna ni watace a wurin shi ko wani abu.
Don wanan matsalar ne ke damun hindatu take wanan zafin kishin haka akan shi ya kamata ace tasan waye mijin mu wa muke aure muke zama dashi.
Shi fa mutum ne irin mazajen da basu da gwana a wurin su amma har yanzu basu gane hakan ba sam.
Mutimin da dan matsala kadan zai iya rufe ido a gaban kowa yai maka tas bai dauke shi komai ba ina wata wai mowa a wurin shi ko bora.
Gashi iya gwargwado yana kokarin shi wurin baiwa kowa hakkin ta a tsakanin zamantakewar mu , sai dai da yake mu matane bamu ganin wanan kokarin da yake a kan mu.
Don a kullun gani muke ai ya karkata a wani bangaren yabar sauran mata ke nan ba a iyamu duk kokarin namiji a kan mu sai mukai zuciyar mu akan abokiyar zaman mu maga may take dashi may suke da miji wanda shine wahalan mu a yau.

Mun gama abinda ya kaimu india na dawo da sakamako mai kyau akan course din da muka je inda da mun dawo zan zama consalta da zan iya shiga ko wani asibiti na kasan mu nai aiki mai amfani a cikin sa.
Ranan jumma, a da dare muka sauka lagos Nigeria ni da yarana da sauran abokan aikina wanda zamu dan tsaya lagos din muyi dan kwanaki don yin wasu cleares din wasu takardun mu a can.

Duk wanan abin maigidan bai masan mun dawo Naija ba yana can tare da amaryan shi sun tafi kaduna wai wani aiki ya kai shi can daga can zasu shiga kano da ita
Zaune yake a bakin gadon dakin hotel din da suka sauka shi da ita ya dauki waya yana hira da bashir nan dai yake wa daddy da sherin kadai san kaunata ta kusa dawowa daga course din ta gashi ina ga baka fada mata zancen auren ka ba ko ?
Ya dan shafo fuskan shi kadan yana sauke ajiyan zuciya yace hakane Bashir sai dai kuma ina ga ai ba zata rasa jin wanan nan labarin ba ko hindatu da zulfa zasu iya fada mata duk da nayi warning din su ga hakan.
Bayan gama wayan su da Bashir din a lokacin itama amaryan na gefe ta na kishingide tana waya da wata kawar ta na shakiyanci sai kwasan dariya suke yi ta wayan.
Gyara kwanciyar shi yake shirin yi yayin da yaji muryan amaryan nasa hajiya Samira tana fadin waini wanan matar taka da kowa ke magana a kanta tana ina ne wai ?
Da sauri ya dan juyo gare ta yake cewa mata wacce matar daga cikin matan nawa kike magana ne ?
Ta dan tabe baki tare da jawo room fresh tana dan fesawa a ko ina na dakin daga kwance tana fadin ita dai wacce ake cewa wai likita ko may ?
Murmushi yayi kawai yace a zuciyar shi anzo wurin indai Rahama ne ai zaki san ta ko sai dai a fili nuna mata yayi da cewa matatace mana ko wani abin ne sai tai shiru don ta fahinci irin yadda yai mata magana din.
Sunyi haka washe gari da safe ya shiga wanka na bugo nombar wayan shi baya kusa yana ban daki sai tai caraf ta daga wayan.
Muryana ne ya daki kunnuwan ta ina fadin hello daddy an tashi lafiya ya aiki ya iyali da sauran jama, an gidan ?
Ke ko wacece ta daina kiran wayan mijina da safe haka don bazan dauki wanan halin ba ga kowace mace.
Murmushi nayi nace ke kuma wacece karuwansa ne ko dadiron sa ko kuma wata yar aikin hotel ce.
Ki kama kan ki ga daukan wayan mijin wasu kina yadda kika ga dama dashi, idan kina son kafa doka gina raminki da kan ki sai ki zauna a ciki amma ba ramin da wata ko wasu suka gina ba kizo kice zaki shige ki mamaye.
Idan kina son ki san ko ni wacece tambayan shi kice dashi uwar diyan shi takwas ne ta kira layin shi don haka kibawa kan ki amsa dani dake wake da mijin yanzu ?
Ina fadin haka nai sauri na katse layin nawa ban staya sauraren abinda zata fadi ba a lokacin don kada ta jefo min mai zafin da yafin da yafi wanda na fada mata din.
Sai dai tana cikin kunduma zagi daddy din yafito daga ban dakin yana goge ruwa a kansa tambaya ta yake tare da kai idanuwan shi aka wayan shi dake hannun ta yana fadin keda waye haka ?
Take cewa wata banza ce ta bugo layin ka shine nake fada mata kada ta kara kiran layinka a wannan lokaci sai kawai ta kai min zagi ,
Ko wacece zamu hadu da ita don bata san wace ta zaga ba ke nan dan ni bana ba da bashi ko kadan,.
Bata ma san ya kawo bakin gadon ba sai ji tayi ya wafci wayan shi a hannun ta da karfi yana duba wanda ya kira layin nasa sai yaga ai nombana ne na nan gida Nigeria na kira shi dashi.
Watau ke nan da Rahama wanan take cin mutunci haka ko, sai dai gaskiya bata kyauta mai ba don ba haka yaso ba da zancen don shi so yayi sai na dawo muyi maganan.
Batare da ya damu da tana gurin ba, ya kira layin nawa kamar kada na dauka dai na dauka yake cewa kina ina ne naga nomban nigeria kika kirani dashi ?
Nace ina lagos yau six days kenan da dawowan mu gobe zan iso Abuja insha Allahu sai dai nakira ka wata yar iska naji ta dauki waya har tana min barazana wai wayan mijin tane wanan na daina kiran ka a wanan lokacin haka .
Ita din wacece daddy kardai nace kana hurda da matan banza ne kuma abinda ban san ka dashi ba a baya ?
Yace bar wanan zancen idan kin iso zamuyi magana akan sa ina yaran suke ne mu gaisa nace dashi yanzu suka fita da doctor Hauwa zuwa cikin gari.
Mukai sallama dashi ya kashe wayan tare da sauke ajiyan zuciya tana furzo iska daga bakin shi ya lumshe idanuwan shi a hankali don bai san ta ina zai fito min da zancen ba.
Muryan tane yaji tana fadin wai wata yar iskace a cikin matan naka har zatace dani wai na gina ramin kaina wanan ramin ba nawa bane naje gaba ?
A hasale yace da ita matar nawa zaki zaga da yar iska a gabana ita bata zage ki ba sai kece mai zagin ta a gabana matar da nake da zuria da ita fiye da kowa a duniya matar da, , , , ,
Haba malam ya isa haka ko ba a fada ba nasan wanan yar iskan likitar matar takace da ake fadin kana ji da ita don naga alama tunda gashi ka rufe ido a kanta kana son ci min mutunci.
Yace idan kika sake maimaita zagin da kikai mata a gabana yanzu ranki zai baci dani a wurin nan.
Ki shirya yau Abuja zamu koma don Rahama ta iso Nigeria gobe zata shigo Abuja din ita da yaran da ta tafi.
Yana fadin haka bai tsaya bin ta nata ba ya fara shirya kayan shi nan ya barta da mamakin wanan irin rawan kafan da kaduwa da yayi akan matar shi .
Wai wacece wanan da yake wa rawan kafa haka ita dai taga matan nashi ba wani abin kai gida a kan su balle ace wai wata tafita a cikin su.
Shiryawa yayi ya fita daga dakin yana fadin zai je ya dawo kafin ya dawo ta shirya yana fita taja uban tsuki wayan ta ta jawo tana fadin ni za a kawowa iskanci akan wata banza can wai Rahama ?
Kawarta ta kira take fada mata komai har take cewa ba inda zata don kano yace zasu tafi amma yanzu ya canza saboda wata wai su koma Abuja.
Kawar tace wallahi Samira kibi a hankali kin dai san ko shekara nawa muka kwasa wurin samun hankalin shi kafin ya yarde muna don haka ki rufawa kan ki asiri kibishi ku tafi.
Baki ko san yaya matar take ba balle har kikai ga daukan mataki a kan ta sai idan kin ganta ne ai zaki dauki mataki a kan ta.
Take cewa hakane kuma fa bari na shirya naje ko ganin yar iska nayi naga nata kalar wanka wata kila ma wata cus ce can ilimin ne kawai a kai.
Sai suka kwashe da dariya a lokaci daya kawar tace koke fa mutumiyar aiba haka kai tsaye ake kama makashi ba sai da kwana kwana.
Nan ta mike ta shiga shiryawa sai dai ranta abace don gani take duk ajin ta da kima ace akan wata zata rushe plain din ta da tayi na zuwa kano ziyarar dangin shi a karo na farko ?
Da yamma suka shiga Abuja kai tsaye part din maigidan ta sauka don nuna isa da gadara ga matan gidan ta nuna ita ta isa ga kowa don hamshakiyace.
Amma sai ya karya mata takon da cewa akan may zata zo nan bayan ga gurin ta can takoma can don a cikin iyalin shi ya shigo.
Duk da ranta ya baci amma dole ne tabi shawarar kawar ta ta lalaba shi taga gudun su tukun.
Haka ta mike a likacin hindatu tashigo suka hade a falon kowa yabi dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login