Showing 15001 words to 18000 words out of 37209 words

Chapter 6 - Karashan Murucin Kan Dutse Book One Complete Hausa Novel

15 Oct 2025

264

a wanan maganan zan dauki mataki gare shi ko wanene tunda ba son Allah da Annabi suke min ba.
Kai Alhaji ka saurareni da kyau babu abinda zaka boye min yanzu kai bakiji kunya ba akan wata bare can zaka sallami yar uwarka ta jini.
Yace hajiya wacece baren da na sallamay ta akan ta tace maku ?
Waye banda Rahama da ta gama da kai baka ganin kowa da gashi in ba ita ba da diyan ta a gidan ka.
Wayan na a handfree don haka na mike tsam don na bar falon yai min nuni da hannu don na dawo na zauna.
Banki ba duk da ban so ba kada naji abinda raina zai baci gareshi naji yace amma hajiya yanzu in ga halarci ai Rahama ta wuce bare a wurin mu tunda na haihu da ita har diya biyar.
Dama shine gurin ta ta mallake ka da gida ka shiyasa taita haihuwa kamar bera nida naga sugar mai iyali ana nuna min zazagan hanji.
Yai murmushi yace hajiya sai dai ayi hakkuri na riga da na yanke hukuncina a kan su ba abinda ya saura yanzu.
Tace baka isa ba aiba kai ka kawo kanka duniya ba zan dawo da Zulfa idan ka isa ka dawo min da ita nan mu gani.
Yace hajiya gidana ai gidan ta ne tazo ta zauna idan zata iya ga gidan nan gata.
Daga haka sukai sallama ta kashe wayan tana ta fada dashi sai lokacin na nisa nace dama nasan duk laifin a kaina zai dawo ai.
Yace hado min passport din ki dana yara yanzu ki fadawa hindatu kuma ina neman ta shiru nayi sai naji yace dani badake nake bane.
Na mike na tafi hado mai passport din dayace daga can na tura akira mashi hindatun daya yace don mu biyu muka saura a gidan.
Kamar yadda ya fada min haka ya fada mata nakawo yasani daukan permision a wurin aikina ba kakautawa suka bani.
Kwana uku yazo ya ce mu shirya zamu tafi London da yara ita kuma hindatu zasu tafi italy da yaran ta.
Hakan akayi muka tafi hutun dole ga Zulfan ta dawo da yan uwanta da da suka rakota nan muka barsu a gidan muka tafi.
Wanan abin yai matukar bata masu rai sun kwana biyu suna zaton zamu dawo maigadi ke fada masu cewa ai bamu ma kasan gaba dayan mu gidan mun fita waje.
Haushine ya kama hajiyan ta tace su dawo kano har mu dawo maigadi ya rufe gidan bayan tafiya su.
Wasa wasa sai gashi mun kwashe wata uku a can hakan ya bani dama yin couses di da nake son yi.
Allah ya taimake ni a wanan tafitan kuma gurin Nasir ya cika ya samu gurbin zuwa yin ilimin na sojoji a can don dama shine burin mu a kullun da mun dawo zai shirya ya koma tunda sun kammala karatun su.
Airen Amira da ya taso ne ya dawo damu gida duk da ba a kasa daya muke ba kusan a lokaci daya muka shigo su hindatu sun dawo da kwana uku muma muka iso kasan shine bai samu dawowa ba a tare da mu.
Mun dawo da Sati biyu muka kwasa sai kano don a can zamuyi bukin Amirah saboda yan uwa gana mahaifinta dana mahaifiyan ta kowa nason ganin auren ta.
Kwanan biyu muka shiga gidan su daddy gaida hajiyan shi fuska a daure take amsa muna gaisuwan mu.
Hakan bai damay ni ba don ba bakon alamari bane yin haka a gareta sai bayan mun gaisa ne ta mayar da hankalinta ga jikokin ta ta share ni nima ban dade ba namike ina gyara gyalen dake jikina ina fadin zamu tafi tace dani yaran ma bazaki barsu mu gaisa ba dasu zaki kwashe su ki tafi.
Ki sani dai yara jinane ko kinki ko kin so dole dai a kira su da jikokina idan kuma rabasu dani zakiyi don kin iya raba anta da jin shi ke sai mu gani.
Nace hajiya ayi hakkuri idan zasu zauna sai na barsu don ni akwai inda zan tafi dama nai mata sallama natafi tana bina da bakaken magana.
Gidan Zarah na nufa mun dade muna hira da ita wayan gajiye ne ya isheni na dauka take ce min ga yara an dawo dasu daga gidan hajiya tun dazu suna kuka.
Nai murmushi don dama nasan bazasu zauna ba ai son fitina ne irin na hajiya kawai dani yasa tace nabar mata su.
Nadawo ne jinior ke fada min irin zagin dataita masu wai sn biyo mugun hali irin na uwarsu shiyasa basu san kowa ba a dangin su ko sunki ko sun so ita dai ce kakar su don ita ta haifi uban su.
Nai dariya nace ai tana da gaskiyan ta watarana ma acan zai kaiku ku kwana wurin ta jinior yace wallahi basu zuwa nace yaro dole ku tafi ai.
Niji dadin zama kano da mukayi kwana biyu don muna ta ziyaran yan uwa da abokan arziki wurin raba kayin buki.
Daddy bai shigo kano ba sai ana gobe kamun Amira ya shigo garin da dare don haka da safe ya shiga gaida mahaifan shi.
Har gidan su Zulfa ya tafi wurin mahaifiyar ta kamar yadda ya saba nan ta tutsiye shi tana fada wai yana wa yar uwarshi wulakanci saboda bare.
Murmushi kawai yai mata ya mike tare da aje mata abindaya saba aje masu ida yazo gaidasu.
Yaran shi yaja suka fita sun dauka zasu dawo sai gida ya nufa dasu don sai daya biya wurin hajiyan shi suka gaisa itama din dai fadan tai mashi bata gane komai ba a gareshi.
Muna nan sai gashi ya shigo da yaran gidan part dina ya nufo dasu yana fadin ga karin baki kin samu kuma.
Na dago don naga bakin sai naga yaran Zulfa ne ya shigo dasu gabana yai mugun faduwa amma a fili na nuna farin cikina ga ganin su.
Nan muka zauna da yaran suna ta jin dadin ganin yan uwan su har dare naga bai ce yaran su fito ya mayar dasu ba gida.
Ban yi magana ba sai gashi ya shigo da dare yake cewa wanan ta bugo maki waya ne na tambaye shi wa ke nan fa ?
Yace Zulfa mana nace wayan ma baya hannu na ai yana ciki yana charge wata kila ta kira ban sani ba dai.
Yace yanzu hajiya ta kirani take tambayana yaran nasan sun tafi gunta ne da tsegumin su da suka iya.
Yara ne kuma ba zan maida mata su ba sun dawo gida ke nan don ba zan barsu a can ba su lalace da mugun hali.
Yana gama magana kiran wayan ta na shigowa gare shi again ya dauka ba ko sallama yake cewa da ita lafiya wai ?
Idan kirana kikayi akan yara ina son ki cire su a ran ki don ni na karbi yarana daga hannun ki daga yau.
Bai jira a binda zata fadi ba ya kashe wayan shi yace dani ki basu wiei su kwanta nan da yan uwan su ba dama nai magana amma duk da haka sai da nace to amma daddy, , ,
Katse ni yayi dacewa ko ba zaki iya rike min su bane na sani shiru nayi ban tanka shi ba yace idan baki iya rike min su zan kwashe su na kaiwa Fatima ko Aisha su zauna a wurin su.
Nace akan may daddy ba zan iya rike ma jinin ka ba koda kuwa sun fi nan yawa ne kawai dai gani nayi kamata yayi kayi hakkuri uwarsu ta dawo hakana ta zauna dakin ta.
Kada yin hakan ya jawo maku matsala irin na zumunci a tsakani ai yanzu ta gane kuren ta ko.
Rahama ina warning din ki a kan zancen nan tun farko don haka ki iya kan ki daga shiga zancen.
Allah ya baka hakkuri bai ce uffan ba ya juya ya fice daga dakin ran shi a bace nabi bayan shi da kallo har ya bace min na juya ina kallon yaran dake barci tare da sauke ajiyan zuciya.
Don nasan cewa wani sabon aiki da rikici ya samay ni kuma ke nan in ba son dora min laifi may zai hana shi shiryawa da uwarsu ta dawo ta rike yaran ta da kan ta .
Mikewa nayi na gyarawa yaran kwanciyan su tare da sauran yaran na samu wuri na kwanta nima don da safe nasan ban da wani sauran time din kai bakine zasu fara shigo muna ta ko ina.
Tun da safe Zulfa ce da mahaifiyar ta tare da su mama hanne autan su hajiyan daddy sukai muns sallama a gidan.
A lokacin yaran sunyi wanka suna zaune suna karyawa koma su nuna sun ga iyayyen su a gidan basu nuna hakan ba sam.
Mun gaisa da su sama sama don fuskan su babu annuri a cikin sa ko kadan a lokacin sai wani daurewa da suke min kawai.
Bayan mun gaisa ne mama hanne take cewa dani ko may gidan ya fito ai muna iso gun shi nace da Jinior ya fadawa baban su ga su mama sunzo .
Bayan fitan yaron ne mama zulai mahaifiyar zulfa ta dan nisa tare da fadin ikon Allah ke kuma naki sallon yaidaran ke nan ki kore iyayyen yara ki sa miji ya dauko maki su a wurin ki don wani manufa na sheri.
Murmushi nayi nace ni kaina ai ba daban nake ba a gidan balle na saka shi yin abinda zai cuta mai ko wata a gidan nan mama.
Nima mace ce mai haihuwa idan na saka shi yin haka watarana nima haka za ai min a kan diyana ai .
Ga Zulfa nan idan tayi fada dani ko wani abu da har yasa na jawo barin gidan mijin ta da yaran ta ta fadi yanzu a ji.
Idan ma laifine ni akaiwa laifi amma hakan da sukai min bai damay ni ba a rayuwa na don ba shine farko ba a tsakanin mu da ita.
Wanan dadin bakin ne kike cin mijin naku dashi ai ko yaushe bai iya fahintar komai akanki idan bake ba baya ganin kowa da gashi a idon shi.
Yara dai ne yau sai na tafi dasu in ma tarbiya ne ban dashi a gida na da har yaje ya dauko su yakawo maki ke uwar iya tarbiya ba zan dauki wanan rainin ba ni.
Mama kada kiga laifin Rahama a cikin zancen nan don ba ita ta dauko yara ba ni mai abu na dauko su na kawo mata su da kaina ba don ta so ba ita ma.
Mara kunya kai yanzu bakajin kunyan kare wanan mayaudariyar da ta gama da kai da matan ka yara dai ne yau da su zan tafi ba zan bar gidan nan ba sai da jikokina tunda kai ka zama sallamamay namiji sai abinda ta saka kakeyi a rayiwan ka.
Kana ganin don ka wullakanta yar uwar ka kamar kayi abin kwarai ke nan ko may kake ganin kayi zama da kai a gare ta ai bai zama dole ba ko ?
Haba mama don Allah ki bari abi zancen nan yadda ya dace shiyasa nace kada ma ki zo kika nace da sai kin zo din.
Yara dai ba ita ta haifa ba ta tsaya a iya wa yanda ta haifa ma tayi iko dasu ba wanda bata haifa ba ta bari idan ta kashe uwar su sai ka kwaso ka kawo mata din amma ba yanzu ba.
Mama nifa ban yi fada da Rahama ba don da abin ta na ta tun ranan da abin baikai hakan ba ma da kuma ina bin shawaran ta na kama kaina duk wanan abin da bai faru ba dani.
Ke dallah rufa wa mutane baki wawiya mara wayo kawai kishiya ce har zaki tsaya kina wani yabo haka don rashin sanin ciwon kai.
Mama don Allah ki bari abin zancen nan yadda ya dace a fahinci juna ba wai hakan da kike yi ba mana don Allah dai.
Mama gaskiya Zulfa ke fadi gyara ya kamata ayi ba wai hakan yadda kikeyi din ba don shi babba gyara aka san shi dashi ko ina.
Ban iya gyaran ba sarki iyayi da munafunci ki mun shiru ko yanzu naki ya samay ki a wurin nan don ke yar kauye dake kin yi kadan ki fada min abinda ya dace nayi kiyi da wa yanda basu san ciwon kan su ba ga sunanan a gaban ki.
Daddy yai murmushi tare da kaiwa zaune yana cewa to yanzu kin gani ai zaki kama kan ki na fada maki tun farko ki barni da yan uwa na kuma matatace ni na san mafita da sauki ga kaina.
Amma akan zancen nan na zulfa da zan biye maki da yanzu mun samu matsala dake akan damuwana da kike yi ta dawo dakin ta a hakan ne mutum yai laifi ba a tsawata mai ba ake son wai na mayar da ita gidana.
Nan gaba idan ta tashi min wani kullin kuma sai yafi wanda sukai min ke nan a baya ni da diyana dana haifa kafin su kashe ni su kwashi ganima ni zan fara ganin nasu bayan tukun.
Sai mahaifiyar nata tace Allah bai yarda kaga bayan diyata sai dai taga nata nan dai taita sake bakaken magana inda take shiga ba nan take fita ba shi kuma ya kafe akan ba zai ba da yaran ba ya dauko su ke nan gidan shi.
Text ne ya shigo min a waya ina dubawa naga Zulfa ce take cewa dani na bawa maigidan hakuri na tura mata cewa mu bada tare yanzu a gaban kowa a wuce wurin.
Itace ta fara mikewa zuwa gaban shi ta tsugun na sai nima na mike na yi kamar yadda tayi tare da fadin don Allah don annabi duk abinda zulfa tayi a yafe mata kaddara ne insha Allahu ba zata sake ba da yardan Allah.
Kuka sosai zulfa din keyi itama tana rokon shi da ya yafe mata don Allah mama hanne ne tai magana yadda mukayi hakan itama tayi takai kasa tana fadin don Allah Alhaji karami ka yi hakkuri ka mayar da zulfa dakin ta ta zauna da iyalin ta.
Shiru ya dan yi tare da sadda kan shi a kasa ya rasa abinda zai fadi a wurin ita ko mama Zulai sai jikin ta ya mutu ta kasa ci gaba da fadan da takeyi.
Mama Hanne ta ce Rahama ko ba komai ni dai yau kin fitar da duk wani zargi a zuciya dama zulfa ta fada muna komai yadda kikai masu shawara da su kama kan su da wanan shedaniyar yarinyar da ta shigo cikin ku amna tai biris taki daukan shawaran naki
Yanzu may gari ya waya wa aka bari a cikin maganan ba ita ba da take fama da dacin rai akwai abinda yafi zafi da kunya ace ka dawo gidan ku da zama ka kashe auren ka bada son ran ka ba.
Mama zulai ta bani mamaki da naji tace Alhaji karami kayi hakkuri bacin raine dama ya kaini ga hakan yadda ka rufe ido kaiwa yar uwar ka sai nake ganin ba don kowa kai hakan ba sai don Rahama don muna ganin burin ta ne na ta zauna ita kadai ya kai kai masu hakan da kayi.
Har lokacin baiyi magana ba da kowa yana duke da kan shi yayi shiru kamar mai nazari sai mama hanne ta sake cewa ni wanan abin ma da yaya tayi kunya ya bani don a tsakanin mu bai kamata haka ya kasance ba kan diyan mu.
Ga zahiri mun gani zulfa bata da gaskiya a cikin maganan nan amma kuma zafin rai ta hana mu ganewa kai babba ne kuka kai keda ragamar aure a hannun ka don haka don Allah kayi hakkuri da yar uwar ka ku zauna lafiya.
Ai yanzu in kunne yaji gagan jiki ma ya dauka don ta zauna gidan nasu taji abinda ke cikin sa in har wani abu ke rudin ta dama da take hakan.
Iska ya furzo tare da dago kan shi idanuwan shi sun kade sunyi ja jawur dasu yace da mama hanne din.
Mama a matsayin ku na uwayena da banda wasu bayan ku idan nace ban hakkura ba a yanzu ban kyauta maku ba.
Amma a gaskiya irin yadda mama zulai tazo min koda borin da zatai min yafi hakane na riga da na yankeyank yanke shawara zulfa ba zata dawo gida na ba da sunan aure.
Da sauri mama zulai din tace kada kai muna haka don Allah nima ai na fahinci itace bata da kan gado yanzu.
Yace yanzu ai tunda ta fada da bakin ta komai ya wuce zata iya dawowa dakin ta ta zauna sai dai ba zan tafi da ita Abuja ba kuma.
Dama ga ta nan ya nuna ni da hannun shi inda nake tsugun ne a gefan shi kamar mai neman gafara, yace itace ta matse ni akan sai na tafi da ita can ni kuma na riga da na san halinta kamar yunwar cikina kan sari ka noke.
Duk wanan dadewan da kukaga tayi can don ita Rahamar ba mai tafiya da magana bane inda ta fada nan zata bar shi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login