Showing 9001 words to 12000 words out of 37209 words

Chapter 4 - Karashan Murucin Kan Dutse Book One Complete Hausa Novel

15 Oct 2025

269

Ki shirya ta yanzu zamu kaita gidan ta ni da mama Altine da matar maigari nace dashi da sauri daddy yanzu yace an daura aure may zata zauna maki yi a gida nabaku minti goma ku fito min da ita yanzu.
Dole haka muka shirya ta tana kuka nima kukan nakeyi mama Altine ta rike suka fice zuwa part din daddy din inda daga can zasu wuce da ita gidan mijin ta.
Ina zaune aka aiko wai nazo na samu harsu hindatu da zulfa a falon na samu wuri na rakube a kasa bashir na min ba, a ban amsa shi ba sai murmushi raina ba daddi ko kadan sabo da rabuwa akwai daci gare shi duk da a gari daya muke dai.
Ya soma da addua bayan ya gama yace to Aisha yau dai zaki fada a sabon rayuwa duk da yake dai banda wani shakku akan rayuwan ki sai dai ki sani zaman gida ba daya yake da gidan miji ba.
Yi nayi bari na bari da kika ji ana fada to shine aure aure wani bangare ne maigirma cikin bautar ubangijin mu.
Don haka ki zama mai biyayya da sanin ya kamata ki gina rayuwan gidan ki da zurian da zaki samu idan Allah ya kawo su.
Da zaki yi koyi da rayuwan yarki da kika zauna da ita zan iya cewa zaki iya zama da kowa a duniyan nan .
Don kin dai ganni da yar uwar ki duk zaman ki a gidan nan damu bazaki ce ga rana daya da kikaji wani sabanin daya taba shiga tsakanina da ita.
Kinga ashe idan kiyi kwatan kwacin halaiyar ta zance zaki zamo MARICIN KAN DUTSE fitar ka sai an daure.
Dariya suka saka a falon Bashir yace sunan kaunar tawa ke nan ashe daddy yace sunan ta ke na a gare ni.
Anyi baki anyi fari a gidan nan sai idan ka jefota a ciki take saka kan ta abinda bai shafeta ba koda ta gani bata taba saka kanta a cikin sa.
Ga abokan zaman ta nan a gidan nan idan akwai ranan da tazo min da wani korafi a kan su dukkan su.
Don haka yanzu kema zaki dora a inda ta tsaya don muna fatan har ki dara ta ga naki halaiyar da zakiyi a gidan mijin naki.
Kuka take sharba a hankali shi kuma yaci gaba da magana yana fadin Zulfa da hindatu ga Aisha zata tafi gidan mijin ta yau ina fatan idan akwai laifin data taba maku zaku yafe mata.
Sai ya juya gun Aisha din yana fadin Aisha ga yannen ki nan da kika zauna dasu ki toke su gafara bisa kan zama ko akwai wani sabanin da ya shiga tsakanin ki dasu su yafe maki.
Zulfa ne tace Aisha kan ai mu fuka ba Rahama ba zamuyi missing din ta a gidan nan don Aisha ai yarinyar zamace gaskiya.
Idan tana wuri dan ka baida matsala zaka iya fita hankalin ka a kwance ba wani damuwa gareka ko aikine ka saka ta baka taba jin bacin rai a wurin ta.
Mama Altine tace haka ake son dama ka zauna wuri ranan barin ka aji bakin ciki ba ana Allah Allah dakai ka tafi.
Aisha ta mike har gaban Zulfa tace anty don Allah ki yafe min idan akwai abinda nai maki a zamana daku a gidan nan.
Tace Aisha nikan baki min komai ba in ma kin min na yafe maki har ga Allah taje gun Hindatu itama tace ta yafe mata itama din tace ta yafe mata.
Zata koma ta zauna yace ga yarki nan baki roke taba sai ta nufoni tana zuwa tafada a jikina a take ita kuka nima kukan nakeyi.
Cikin kuka take fadin Anty don Allah ki yafe min nace Aisha ni baki mun komai ba na yafe maki.
Sai ta nufi daddy daidai kafan shi ta duka tana rusa kuka tare da rokon shi gafara cikin dauri yace Aisha na yafe maki Allah yabada zaman lafiya.
Sai ku tashi mu tafi mama yace wa su mama Altine da mama Abu kishiyar Inna ta.
Nan suka fita suka bar mu shi da bashir a gaba suna baya zaune su sai gidan mijin ta.
Aisha yau ta tafi ta barni nida yara da kewan ta don zan iya cewa duk haihuwan da nakeyi Aisha ce tafini sanin zafin wahalan dawainiya da yaran iyakana dasu shan nono ko wani abin can na daban.
Nasan ba niba har yaran sai suji kewar rashin ta a tare damu a gidan haka na mike na barsu nan zaune a na hira na nufi part dina.
Kowan mu yayi kewar rabuwa da junan shi da dan uwa a ranan don duk abinda nakeyi ina dai yine kawai a ranan har dare.
Washe gari baki suka fara tafiya garuruwan su da sannu duk gida ya watse aka bar mu mu kaida yadda muke.
Amira raguwa ce don haka yanzu kusan Atika ce takoma jan ragaman part din nawa don ni kaina bana son ma na matsawa yar marainiyar Allah da damuwa kada Allah ya kamani da laifi.

********* ********* *********
Saida na huta na koma girki na sai dai abinda na kula dashi shine Niima bata taran ranan girkin ta koda yaushe idan daddy yana gida tana manne a falon wurin shi koda kuwa aiki yake shi.
Na dawo aiki sai da nai wanka na shirya tare da daukan abincin daddy na kai falon na jera na koma ciki don na tsawata wa yaran da kada suyi fada kin san yara ba a raba su da fada a tsakanin su.
Ban jima ba na dawo falon tun kan na karasa na hango kafanta kwance a saman dogon kujera shi kuma yana zaune a kasa yana dubar wayan shi.
Mamakine ya kama ni haka dai na daure na shiga gun shi don dama bayan gani da ido naji sauran na korafin hakan da ita.
Ban zauna ba sai na shige bedroom har na gama abinda nake a ciki na kwanta daddy bai shigo dakin ba kuma ina jin muryan ta.
Can har na fara barci naji shigowan shi dakin yana fadin kwanciya kikayi ashe ban tankashi ba naji ya shiga bathroom don yai wanka.
Tsam na mike zaune na hado komai nawa na bar mashi part din na koma wurina na saka sakata na rufe har dakina saida na saka sakata a cikin shi na kwanta a gefen diyana dake kwance.
Da safe ina shafa mai sai gashi ya shigo dakin yana saye daga shi sai jallabiya a jikin shi.
Fuskan shi babu walwala a cikin sa yake cewa dani a wani dalili jiya kika bar wueina kika dawo nan bada sani na ba ?
Nace au tambayana ma kakeyi daddy ai na ga banice dakai ba shiyasa nabarwa mai girki wuri taci gaba da aikin ta.
Yake cewa dani wanan wani irin magana ce haka kuma wacece mai girkin ban sani ba ?
Nace wacce tazo debe ma kewa kasan ni ban iya ba wallahi daddy in dai don ka muzantani akan wanan yarinyar ne ba zan kara lamunta ba a gidan nan anyi na farko anyi na karshe.
Bana shiga hakkin kowa daga cikin matan ka don haka bana son wata ta shiga min itama.
Yo itama ta san yin hakan waye ba zai ita ba idan yaso don haka ta kama kan ta dani tun kan mu karasa saka kafan wando daya da ita a gidan nan.
Yace yanzu dan zaman da tayi shine matsala kuma bata fada kowa da zai debe mata kewa tare da ita shiyasa take shigowa guna.
Auto hakane ashe to shike nan ba hira ba har kwanan ma ku dinga yi a tare indai don ta Rahama ne na yafe aje akarata can.
Dama na dade da sanin cewa baki damu dani ba Rahama ba sai kin fada ba ai nace ban damu ba kuma ba zan taba damuwa da abinda bai damu da nawa damuwan ba.
Yanzu dai muje ki hada min ruwan wanka nace ai sai dai ita data fini muhinmanci ta karasa wanan duty din amma ba dai ni Rahama ba kuma wallahi.
Yace kina son ki zarga min sheri ne ko may Rahama kike shirin yi ga maganar ki ?
Wallahi ba sheri ga wanan maganan ni ba zan dauki a wullakan tani a kan wata ba tunda ban wa kowa haka ba ina iya kokarina wurin tsare doka ga kowa a gidan nan.
Don may zaka zauna karamar yarinya tana son juya ka ka fada ga halaka da saboda tana takama ta iya yin kissa da kisisina watake zaton bai iya hakan ba ne.
Don haka kaje dana zauna ka dinga wullakantani a gabanta gara na yafe na san ban jiba ban gani ba ku karata can kaida ita yafi mun sauki.
Kara dan step yayi daga inda yake tare da fadin hummm sam ni ban dauki wanan abin a wani abuba a rayuwa na amma kowan ku yai min wanan korafin kan hakan .
Duk macen da tasan darajan kan ta ai zata gujewa shiga hakkin wanj kada itama ai mata hakan watarana.
Ba komai bane ka nuna mata cewa ita din tafimu daraja da kima a gunka shiyasa take ganin tafi kowa ne a gidan nan.
Da sauri ya dan kallo inda nake ranshi ya baci yace Niimar ce tafiku daraja da kima a gurina komay ?
Tafimu mana tunda a gabana kuma gaban ta ka shanya ni a daki kana zaune tare da ita kada ka taso ranta ya baci.
Murmushi yayi yace kaiyya ita din har ita waye da zata ce tafiku a guna nace ita matar ka mana kuma amaryan da kake diban karfin kurciya a gare ta.
Tsuki yaja ya juya rai a bace yana fadin wanan maganan ke kika san shi ni nasan abinda nakeyi kada ki maidani wani wanda bai san abinda yakeyi ba mana.
Bishin nayi da kallon haushi naci gaba da shirina har na gama na fice tare da yara da nake kaisu wani nursery mai kyau da tsada.
Ban dawo ba sai uku na rana naje gidan Fati na dauko yaran muka tsaya hanya nai masu sayayya su da yan uwansu na doso gida.
Tun a haraban gidan nasa daddy yana gida ban tsaya bin ta nasu ba na kwaso kayan tare da kamo hannun yara na zamu shiga gida.
Sai gashi fitowa daga ciki bin mu yayi da kallo don bai masan yaran sun fara zuwa makaranta ba sai ranan.
Don duk yan uwansu ba a saka su ba tukun niko don fita aiki gashi Aisha bata nan yanzu yasa nakaisu karatu da wuri.
Yaran suka nufe shi nai mai sannu na shige da ledojin dana shigo dasu a hannuna zuwa part dina.
Ina daki naji shigowan shi da yaran wurina wanka nake son shiga don har na fara tubewa suka shigo.
Yaushe ne yaran nan suka fara zuwa makaranta ban sani ba Rahama ?
Yanzu kece mai bugun gaban kan ki a gidan nan kike nufi ko may don ban san may kike son dauka na ba.
Ba wai makaranta na saka su ba saboda Aisha tayi aure isan na fita kuma kada su shiga damuwa yasa nake kaisu day care na wata yar shuwa data bude wurin ana bada kulawa ga yara sosai.
Alright don banda hakki yasa ba a fada min ba aka kai min yara can ko nace dashi kayi hakkuri kawai batare da na sake wani magana ba kuma.
Amma dai kin san yin haka zai kawowa sauran iyayyen yaran zargi ko wani abu ko ?
Nace daddy yanzu shike nan kuma banda right din yiwa yara na komai sai na hada da na wasu komay ?
Nifa wanan irin matsalolin sun fara isata daddy kowa yasan ina aiki yaran kuma suna son kula shiyasa na daure nakaisu can don su samu kulawa a wurin.
Sai yaron yake ja mai hannu yana fadin daddy mun yi karatu alifun ba un da kuma cake muka ci.
Yana fadi yana jan hannun uban nashi ya dan kai kallon shi ga yaron sai yaja su suka fita daga dakin .
Wankana na shiga na fito na tayar da sallah ina gamawa na shirya na fito falo abinci na nema don ina jin yunwa a lokacin.
Na zauna na fara ci ke nan yaran suka dawo sai dai su biyu suka shigo wanan karon.
Zasu zauna nace su bari nai masu wanka don manyan basu dawo ba a lokacin mama ce kawai muke bari a gida helen ta koma kauyen zatai aure itama.
Wanka nai masu na shirya su muka zauna cin abincin tare da su na dan fahinci tun bayan bukin Aisha akwai dan matsala agida namu don kowa yaja baya da dan uwan shi.
Hakan bai wani damuna ba don dama na saba zama a hakan don shirin dama na iya baki ne kawai akeyin sa baikai zuciya ba .
Muna gap da gama cin abincin ne daddy ya shigo falon ya sauya tufafin jikin shi wanan karon duk wanan sintiin da yake na fahince shi na lalashine kawai kan matsalan dake tsakanin mu dashi.
Ban sake fuska ba sai naji yace dani may ye na ganki kuma rai a bace haka dake ?
Nace batare da na dago ba may kuwa zai bata min rai yace har yanzu a kan wanan maganan kikewa fushi haka ko may ?
Wani takaici naji a raina watau shi bai dauki maganan a bakin komai ba ke nan a gunshi.
Takaici duk ya kamani nace fushin may zanyi aini nagama magana ta don na sallama mata kai kuje kuyi tayi can.
Murmushi yayi yace dani Rahama dago kai ki kalleni mu gani idan kin salama wa watani da gaske ?
Ban dago ba ya sake cewa dani dago kanki mana mu hada ido idan da gaske kike zan gani ai.
Kin dagowa nayi don ma ba zan iya ba din don nauyi da kunya ba zai barni ba naji ya sake cewa dani maganan taki iya baki ne ke nan.
Nace don Allah daddy mu bar wanan zancen tunda munyi shi tun safe mun gama banga dalilin dawo da zancen ba kuma.
Shiru yayi nasan kallona yake a lokacin ya dan sauke ajiyan zuciya tare da kara takowa zuwa inda nake naji yace dani Rahama ina son ki sani daga yau bana son irin wanan maganan daga bakin ki a gidan nan.
Laifi akai maki kuma kin fada ya wuce don haka ki tabbatar da zancen ya wuce ke nan ke ma wurin ki.
Bana son ki na bari wani na fahintar halinda muke ciki don a kulun so ake aga wani dan baraka a tsakanin mu.
Nace nasan da hakan amma dole ne na kwaci yancina a gare ka don ina gudun ai mun dariya zai sa na ki fadar ra, ayina ko may ?
Tsaye yayi yana min kallon mamaki na dago kai muka hada ido ya sakar min murmushi na shuumanci.
Nunani yayi da yatsa yana fadin ban taba sanin son da ake min ya kai haka ba sai yau din nan.
Na dan kara kallon shi nace so fa so fa kace yace cikin daga giran shi yes so mana gashi kinga akan yarinya karama kina wanan haukan haka .
Nace ba wai hauka bane ai yarinyar ne da son wuce wuri na fahinci bata da wayo tare da ita ban so shiga shirginta ba amma naga tana son ja danine a gidan nan.
Yace amma shine ke zaki biye mata ku zama daya ko yaushe nace aida ace na biye mata da tuni ta raina kan ta ko a gidan nan.
To naji bani son dai kiyi abinda zai kai ga zubar da mutuncin ki akan ta ki barni da ita ni da na dauko ta ni nasan halin kowan ku kuma.
Don haka wanan maganan abarshi nace an barshi ya wuce sai dai idan an sake baza ai mai kyau ba kan .
Yai min sai ya dawo ya fice sai da yara suka dawo na samu kaina na nufi part din daddy din ina tsaka ga aiki kamar ance na leka window sai na hango zulfa da Niima a tsaye suna ta faman magana a tsigar munafunci murmushi nayi tare da fadin kaico a fili.
Tun wanan ranan na kara kama kaina da wani hafin kai na kishiya bana shiga harkan kowa a gidan nima na kuma lura da cewa ita Niima ta daina wanan tsagerancin da takeyi yanzu ko tanayi ba dai ranan girkina ba kan.
Duk wani kumbiya kumbiyar su na gaiyar tsiya bai damuna don hassada ga mai rabo taki ne gareshi.
Hindatuce nake ga kamar ba a gama sakata cikin shirin ba sosai don itama ta mayar da kan ta gun sana,ar ta.
Wanan halin ba wani bakon alamari bane a gidajen mu tun fil, azal haka ake a gidajen hausawa masu tara mata.
Da zaran anga kamar namiji ya doshi wani wuri ko yana dan tausayawa wata sai kiga saura suna hafin kan karya wanda ko su a tsakanin su ba wani son juna.
Sai a ware dayan ace tunda miji na kulata ko tafi samu a rayuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login