Showing 6001 words to 9000 words out of 37209 words

Chapter 3 - Karashan Murucin Kan Dutse Book One Complete Hausa Novel

15 Oct 2025

271

a wullakanta min matana da kika sama ba a gidan ?
Tace ai wanan dama ba alkawari nai maka ba a mayar dani banza a gidan ka don kawai na auri mijin su ai miji yanzu na kowa ne kowa tashi tafishe shi a gidan.
Ina tsaye na harde hannaye na cikin murmushi nace da ita hakane fa yan mata miji fa na kowa kowa ta kada rawan ta ai da na dauka da lalama kika shigo muna amma yanzu muje zuwa na juya na fita daga falon.
Bayan fitana kaca kaca daddy yai mata bai raga mata ba sai data raina kan ta yace ta fice may daga falo kada ki dauke ni mutumin banza kizo ki kawo min fitsara a gidana.
Da taga da gaske yake dole ta natsu yace cikin tsawa fice min daga nan mara mutunci kawai kafin ki zuba da iyalina ni zan zuba dake ai.
Ko maganan da yaran nan ke fadi yanzu a zaton ki ban sani bane ni kyale ki nayi naga iya gudun ki.
Watsatsa mara mutunci kin gaba bayar da kanki ga kananan yara kizo min nan kina son watse min kan iyalina duk wani bakin cushe cushen dakike kina dauka ban san dashi bane ko may.
Na tsani macen dake wanan bakin dabiar na cushe cushen banza a gaban ta don mata ba dabiar su ke nan ba su.
Don Allah honey kayi hakkuri sherin shedan ne kawai amma ba zan sake ba insha Allahu yace inma halin kine wanan matsalarki ce don ke zaki sha wuya a cikin su .
Yarana zakizo ki saka a gaba don kinga ina daga maki kafa nina san dalilina nayin haka amna yanzu kin karasa zube min a idanuwa na gaba daya.
Taji matukar nauyi da kunyan maganan da yake fada mata don ita a zaton ta tana ganin a budurcin ta yake daukan ta gashi hudubar abikan banza ya ja mata rasgin mutunci irin haka a gaban kowa.
Buki yayi buki ban kara ganin taba ban bi kuma ta kanta ba balle na san halin da take ciki a lokacin.
Sai dai zancen ta yana a raina so sai ina tuna kalamin ta a kaina na wai dani rasgigo tazo tayi maganina ne a gidan dama.

********* **********
*********
Da kanta ganin ana shagalin buki tana gefe ba wanda ya bi ta kanta gadhi kuma tana son nunawa kawayen ta ita wata tsiyace yanzu.
Ta samay shi tare da kwantar da kai tana cewa dashi honey ban san may yasa ni ba a fada min yau za, a yi dina ba na tafi naga kowa na shiri.
Yace da ita dole taki fada maki tunda baki da mutunci kin gwada mata koke wacece tace don Allah a barzancen ta gane kuren ta ai yanzu.
Yace zai min magana inajin kiran shi nasan cewa da magana duk jama, an dana tara na mike na samay shi a falin shi yana zaune ya tasa laptop a gaba shi yana aiki dashi.
Nai sallama na shigo da Anty a hannuna data lake min taki yarda da kowa tasha ado itama yarinyar a jikin ta.
Ya dago yana murmushi yake cewa dani har kun shirya ke nan ko may nake cewa dashi ina zama wanan taki barinama aina shirya don fitina taki yarda da kowa yau a gidan.
Yace yau uwarta na aure bata da lokacin ta kuma da ta yarda da Aishan ai don bata da lokaci ne yau.
Daddy gani kace nazo yace eh yana dago kai baki fadawa wanan yarinyar zancen zuwa dinner bane yanzu ta samay ni tace baki fada mata komai ba wai akan bukin.
Nace ya salam wai daddy may yarinyar nan keso danine a gida??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????n nan please akwai fa dalilin da yasa nake daga mata kafa fa..
Na sanu Rahama amma tunda ita da bakin ta tai magana kiyi hakkuri ki fada mata nace wallahi bazan fada mata ba ita wacece da sai naje na fada mata.
Oho tana son zuwa ta nunawa duniya ko ita wacece a wurin ko ta bata min taro da rashin tarbiyan da ta iya komay.
Bazan fada mata ba kuma ban gaiyace taba ga sha, anina idan kuma tai gigin zuwa duk abinda ya faru da ita a gurin ita tajawa kan ta.
Yace tunda kince baki gaiyyace taba ai shike nan amma ki sani wanan halin ba zan dauke shi ba don naga kuna so kawo min matsala a gida na.
Nace dashi take dai son kawo maka matsala amma ba ni ba da ina da matsala ai da kai kafi kowa sanin haka a baya.
Tace ita bata da kunya ta ta zauna taci rashin kunyar nata mu gani mana idan shine maganan ni zan tafi do mutane na jirana aiki mukeyi.
Yace is ok kutafi za ce ta zauna ba sai taje ba shike nan ko nace dayafi mata ai bataso hakan ba da tabi da mutunci da wanan ba komai bane.
Amma ban sanin halin mutum na bari ya shanmace ni kuma na dauki diyata muka bar mashi falon ban dade da fita ba sai gata ta dawo wurin shi kamar manya tana cewa wai ya fada min yace ke ki bar zancen nan kawai ki zauna.
Za tai magana yace ai kinji abinda na fada maki koma may ye aikece kika soma da kinzo da mutunci daba hakan ba ai a tsakanin ku.
Bataji dadi ba na samu su Zarah ina fada masu hajiyan harka tace may kikace ke sai nake fada masu Zarah da Fati sukace kinyi daidai wallahi.
Bata zuwa yar iska mara mutunci kawai gasa mata kwakwanta ga hannu sai ta raina kan ta a gidan nan.
Wai harda fadin da ke tashigo tana ganin tagama dashi take zaton harda ke sai ta juya ki.
Aisha da fatiman sister din shi dake gefe don isowan su ke nan garin suna cin abinci sukace karya take ko a can ma kwasa sukayi dashi bakuga sun dawo maku a bazata ba daga shan amarcin da ya gudu nan yayi a kano.
Aisha tace wallahi ina ga watsatsar yarinya yai karo da ita don mun je gidan mun samu suna fitina dashi da alama dai amarya fanko ce sai dai maneji kawai.
Ai kaji abinda akewa gudu inji Fati yanzu tazo zataiwa mutane rawan kai a gida ita a dole ga yar iska ko?
Wuri ta samu ai daya gwada mata ita ba komai bane bata da kima da daraja da ta shiga hankalin ta da kowa.
Ai kinsan mazan yanzu ba kowa ya damu da wanan ba sai kiga sun share har ma su so fifita ta banza akan na kwarai akan ta sai su rufe idanuwan su duk da sun san watsatsace.
Basu san maganan Allah baya tashi ba akan zina ko tai haifa masu ko a samu jika hakana sai anyi daya biyun a garesu.
Nace ai yasani don data shiga gonar Amira ta fada mai a gaban shi sukai yi .
Da Amiran Aishan shi ke tambaya nace da ita fa cewa yarinyar tayi tafi karfin ta don da ubanta take kwana ta tashi ita.
Sai dakin ya dauki salati hajiyan harka tace dama ido ya bude sai fatiman daddy tace wani amsa aka bata to nace Amira kuma cewa tayi ko ita ai mace ce sai taje ta auri ubanta ta zauna kishi da uwarta ba komai bane.
Dariya suka sa kai yaran yanzu sai kace koya masu magana akeyi nace wallahi ni kaina sai da naji kunya a wurin ai.
Amira bataji nauyin uban ba tace da ita kuma don kin kwana da daddy nina sa ba bakon abu bane a wuein ki tunda da abokan Nasir yara kanana kike kwana kafin daddy din.
Dakin ya kara kwashewa da szbon dariya bandani sai Aisha tace don Allah ji wanan irin magana zata sa yara su fitsare muna a gaban mu.
Hajiyan harka tace ai yaron yau ka barshi kawai inda ka gan shi kinga ta karbewa uwarta fada ke nan ya zama nata don kin san dai ita Rahama bazata iya fadin hakan ba a gaban shi.
Shiyasa ake cewa kasada ne shiga gidan dake da yara yan mata in har zaka shiga to shigo da salama a zauna lafiya amma in har kace zaka taba masu uwa kaiko naka ya samay ka a gidan.
Kai shi da yara kayi da uwar su nace ai ni Amira ta ban mamaki data rufe ido ta gasa mata zance haka ko Nasir don ina mai tsawa ne shima nasan da yanzu sun kwasa dashi ko tuni tunda rawan kan ta har ga yaran kullun cikin kai karan su take a gaban shi.
Aisha tace takama ka ta in dai kan yaran shi ne don yanzu na sabanta yake mata nan gaba sai ta rena kan ta gareshi indai yaya ne.
Mikewa nayi tsaye ina cewa nifa sam bata gabana yanzu ko kadan don na fahinci kurciya na diban ta.
In bashi ba zata kalli idona tace wai dani ta shigo da badon tsoron Allah ba ai tun ranan zata zama bazawara.
Hajiyan harka tace na rabaki in ke baki mayar da ita ba indai yaran yanzu ne ita zata mayar dake don yaron yau baijin kunya tubbuke icce har sayen shi a gida.
Daga uwar har diyan ta jefa tsanar su a gurin maigida komai sai its ta zama mai juya gida yadda suke so.
Nace wanan dai tana da niya yadda na gan ta da halayen ta don fitsaran ta yayi yawa sosai wallahi.
Fita nayi daga dakin na barsu suna ci gaba da zancen ina shigowa dauke da wani tire na zubo sayyayen nama a ciki naji Fati na fadin .
Kin sai ai yaran sokoto nan suna kadagi da iya iskanci haka suke dama su da kishin hauka kan kishi sai su kashe mutum kishin da uwa da diya ake yin sa da yan uwan ta baki daya.
Ai da a garin sune da kunga abu wallahi don zakuga inda kishin hauka yake ba sanayya ko kadan koda kuwa yan uwa ne.
Nace dako sun raina kan su wallahi da na gwada masu waye Rahama sun sanni ke kyalewa fa mutum yake ba wai tsoro ba.
Zarah tace kaiyya Rahama na rabaki kishin da ake hadawa da asiri shine kishin balai bakiji tace saida ta shirya maku ta shigo ba tasan abinda ta takane inkiji hakan ai.
Nace indai hakane muje zuwa ni ga Allah na dogara ba da mutum ba sai mu zuba ta gani ai ni da kaina zan zauna na kai karan ta ga Allah.
Ba sai naje gun wani ba don abinda zanyi shi wanda taje wurin shi zaiyi Allah zan fadawa yai muna maganin ta..
Nace da mutane kuci nama don Allah bari a kawo maku abin sha ku dan sha kafin ku shirya don lokacin tafiya holl ya kusa.
Aisha tace yanzu kin hana min amarya zuwa ta taka nata rawan kafin nabada amsa Zarah tace ba inda zata wallahi bafa komai bane take son zuwa don kawai ansan itama matar gidan ne yanzu.
Shine fa kawai in bashiba may ye na nacewa da sai ta tafi ance ba ayi dakai kace kai sai anyi dole ta tsaya gareshi shi da ya dauko ta tayi.
Ashe maganan bai kare ba don ta fadawa iyayyen ta suka kirashi akan maganan don may ana buki a gidan ita zamu ware ta a gefe.
Wanan ai an nuna mata kiyayya ne da tsana tunda itama matar gida ce dole a dama da ita ina shiri a dakin mama Altine sai gashi har dakin ya biyoni kin san namiji wani lokaci kamar baida wayo yake.
Sun gaisa da mama yake cewa dani zarah na zaune don Allah Rahama kubar yarinyar nan ta tafi bana son yawan korafi wallahi.
Caraf Zarah tace wallahi idan taje muko sai mun muzanta ta don bamu gaiyyace taba a harkan mu kawai taje muna da rawan kai ko ta saka muna fitina ta watsa muna taro tunda bata da hankali.
Yace haba tunda tana so ku barta mana ta tafi ba shike nan na juyo nace ba dai harkana ba kan ta bari idan nata ya tashi idan ta ganni duk abinda taga dama tai min.
Mama tace kai itama dai yar nan ance ba ayi dakai dole ne yaran nan nada gaskiyan su fa fitina ne ba a so tayi da yara balle su da take ganin sa,oin tane tunda ta shigo da rawan kai haka ba kama kai kagama ganin gudun mutanen da ka sama.
Ai ba a mulki da karfin dole sai an lalaba akanci gari bada karfin tsiya ba yadda tazo masu.
Yace to shike nan ya fice ta sake samun shi wai ra shirya ya bata motar da zata da ita nata yai karama a wurin.
Yace ke sunce basu bukatan zuwan ki zuwan dole ne ko lahira ake rabo a wuein mai abu yace baya bukatar ka wurin ba sai kayi hakkuri ba.
Aiko nan ta tubure mashi har da son zagin shi wai dama ashe shi mijin tace ne bai iya gidan shi ba ya dauko ta ashe mace tafi karfin shi bata sani ba.
Suna cikin wanan rikicin ne sai ga Zulfa take tambayan may ya faru itace ke fada mata sai Zulfa tace da ita kama kanki da Rahama wallahi.
Ba irin su akewa a zauna lafiya da ace kin iya bita da kinfi kowa jin dadin ta amma yanzu tunda kikaga haka kama kan ki kawai da ita don duk abinda kike ji Rahama da kike gani tafiki iya shi wallahi.
Nan fa ta shiga fada wallahi ita danine mu zuba in karatu nake takama itama tana dashi dariya Zulfa tayi tace a hakan kama kanki wallahi Rahama tafiki iskan ci shiru shirun mutum mugu ne.
Ke ma in ba hauka ba may ya kaiki shiga harkan Rahama ki zauna lafiya ai kun kulan da kikace ke nan a gida nan da ita.
Hindatu tashigo ta gan su tana sake magana tai mata wani kallon banza tace wanan kuma fa haka ?
Shi dai yana zaune bai bar abinda yakeyi ba bai kuma bita kan su ba nice na shigo karshe da yarana har Nasir munyi kyau sosai damu.
Jin muryan Anty yasa ahi dago kai yana dariya yace kai kai kai my princess kece haka yau ta haye jikin uban nata sauran duk suka rufe shi ko kallon inda take zaune banyi ba tana zaune sai harara take waysa muna nace ke ba yar iska bace a raina.
Daddy banga ka shirya ba ko kai zamu bari gadin gidan ne da dukiyoyin mu don har su mama da kowa watsewa zamuyi mu.
Yace nikan ina nan sai Zulfa tace da yar amarya shi ba tare zasu zauna ke nan a gidan tunda bata zuwa ai.
Hindatu tace da zulfa din kai maman hanif taje ina kuma don Allah ki bar wanan zancen mana haka wanan ai rashin fahinta ne.
Sai yarinyar tace tunda ni ba mutum bace ba ko in dai bukine ai ba yau nake zuwa ba balle ace za ai min maganan banza a kan wanan din wani irin bukine ban gani ba a rayuwana.
Eh kin gani kan wuein bin yara kanana asha gara ba dai don matsayi ba wanan kan ba irin ku ke zuwan shi ba.
Kafin tai magana nace oya ku karbi kudin ku mu tafi kada mu makara sai ranan ashe ta fara ganin yarana a gidan don su ba su ma san da ita ba a gidan.
Hankalinta na kan abinda uban keyi da yaran sai ga yan matan suma sun shigo amsan kudin kari ihisan tace daddy mukan sai dubu dubu ko ?
Nan suka baibaye shi suna abinda yasaba dasu yama fita batun mu a wirin tsoki ta buga ta fice daga falon sai kowa ya kwashe da dariya ta juyo tana fadin dariyan ku zai koma kuka soon mu zuba daku a gidan nan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[4/22, 08:43] Ummin Meenat: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,


Buki yayi buki don an cika an min kara sosai a wurin zakace ko Aisha yar cikina ne nake bukinta.
Anci ansha an raba gift don angon yayi kokari shima sosai zan iya cewa a gaskiya Aisha tayi dace da mijin aure mai mutunci ga addini a tare dashi.
Mun dawo gida a gajiye kowa ya nufi wurin kwanciyar sa masu yin wanka da sallah suka je yi.
A falona muka baza kolin mu nan muka dasa wani sabon hira a wurin sai biyu da wani abu kowan mu ya samu wurin kwanciya don an gaji.
Washe gari kuma da aiki muka tashi gidan don akwai walima ga daurin aure ranan kan yan uwan mu sunzo maza da mata sai da suka tuna min da rayuwar kauye.
Ayi dauri aure a massalacin uguwar mu bayan an fito sallah azahar anci an sha karfe hudu aka fara shirin walima daga shi za, a kai amarya dakin ta.
Biyar da rabi aka tashi walima sai ga daddy ya shigo har part dina yace ina Aisha amarya nace dashi tana ciki.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login