Showing 3001 words to 6000 words out of 37209 words

Chapter 2 - Karashan Murucin Kan Dutse Book One Complete Hausa Novel

15 Oct 2025

272

ce dakai ba.
Sai akace don ba ke ce dani ba kada na taba ki kuma ko ?
Kara kai hannun shi yayi yana kokarin lalabana da sauri na kauce tare da mikewa tsaye ina fadin mutum da amarya tsaleliya ya dawo yana taba tsohuwa kuma ?
Sai naji yaja tsuki tare da juyawa zuwa bakin mirrro dina ya tsaya yana fadin ina son mu hadu idan anyi sallah a falo na Allah ya kaimu nace dashi kawai.
Ya fara tafiya ina bin shi da kallon yadda duk mood din shi ya canza daga yin magana kan amaryan ta shi.
Sai na fahinci da akwai matsala duk yadda akayi bisama idan anyi la, akari da yadda suka dawo batare da sunyi sati dayan da sukace zasuyi ba a kano.
Wanda nasan sun zauna can ne dama don ya samu hutu da yar amaryan shi kada ya dawo nan a damay su sai kuma gasu ba sukai satin ba sun shigo.
Yana fita na dan leka yaran na dawo na samu wuri na kwanta sai barci ban falka ba sai da Amira ta shigo ta tayar dani.
A Lokacin har karfe uku saura da sauri namike nai sallah na gyara jikina sai ga wayan daddy ya shigo min ina dauka yake cewa dani wai may kike jira har yanzu muna ta jiran ki.
Nace gani tafe ai tsab na shirya sai kamshi nake na nufi falon nashi inda na samu duk suna zaune a falon nice kawai ban shigo ba.
Nashiga da sallamana abinda ya fara tarona shine yarinyar da na hango zaune gap da daddy a saman kujera daya dashi wanda ba kasa fai muke irin wanan zaman ba indai za ai irin wanan zaman.
Maimakon na zauna saman kujera sai na koma daga bayan kujera naja na tsaya tare da cewa gani naji kace kana nema na ?
Yace zauna mana baki ganin kowa a zaune ne nace dashi eh to na dai gan su a zaune sai dai zaman ne naga kamar babu tsari yau gare shi don kasan ba haka muka saba zama ba ai.
Ya dan yi murmushi tare da daukan remote ya rage vollume din tv dake aiki a looacin ya ce da yarinyar ke Ni,ima koma wurin yan uwanki ki zauna.
Sai taunan chewgun take yi kas kas ta dago kai da sauri ta dan kalli inda nake tsaye kamar zatai magana sai ta mike ta nufo gefen da zulfa take ta zauna.
Na samu dayan kujeran na zauna a kai may karatu kada kiga laifina nayi hakane don saurin yankewa fitsaran da naga yarinyar tana shirin muna shine dalilin danai amfani da wannan hikimar na fahintar dashi yakuma gane bazan zauna ba a yadda suke zaune din nan.
Yace damu ok dama na kiraku ne don na gabatar maku da Ni,ima a matsayin sabuwar abokiyar zaman ku a gidan nan.
Ya juya gunta yana fadin Ni,ima ga mata na da nake aure nake kuma tare dasu kuma uwayen diyana a gidan nan.
Wanan itace zulfa itace ta maye gurbin uwargidana da Allah yaiwa rasuwa sai kuma ta biyun itace hindatu ya nuna ta yace wanan kuma itace kike biwa watau Rahama ke nan.
Sai ta dago kai tana min wani irin kallo tana tauna chewagun tare da wani mayde bakin ta a yatsune fuska.
Ya juya gare mu yana cewa wanan itace Ni,ima da na auro na kara a acikin ku da fatan zan samu zaman lafiya a tsakanin ku.
Babba ya rike girman shi haka ma karami ya rike nashi a matsayin karami Ni,ima da fatan zaki zamo mai biyayya a garesu a zauna lafiya.
Sai may muryan yarinyar naji tana cewa idan sun so a zauna lafiya may zai hana sai dai bazan yarda da saka ido ko shishigi ba a rayuwana.
Na dago ina kallon yadda take magana tana wani har da idanuwan ta baki na magana hanci na magana ido yana magana nace tau, , , ,
Tana fadin haka sai ta mike ta bar falon yana kiranta ko juyowa batayi ba ta shige abinta.
Gaba daya muka bishi da kallo don kowa yaga abinda ya dauko wanan karon a gidan kuma a zahiri watau fitsara ya shigo muna kuma again.
Zulface ta kawar da shirun da falon yayi da fadin tau dada yanzu sai yaya kuma ka daiga abinda ka kwaso kuma wannan karon.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[4/21, 19:19] Ummin Meenat: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,


Ba shi ba da ya dauko ko mi dake wurin munji kunyan abinda yarinyar tayi mashi a gaban mu don mijinka daraja ke gare shi a idon ka da kima.
Amma sai ga wata a gaban mu ta zubar da wanan darajan nasa da kima da mutunci da muke gani a gaban mu.
Hindatu ne tai karfin halin karawa da cewa eh gaskiya yau kuwa mun gaskanta yarinya ka dauko wa kan ka don nishadi tunda mun ga irin kalanta ta tun yanzu.
Mikewa nayi tsaye tare da cewa da su Allah ya bamu alheri na barsu a zaune har lokacin bai iya cewa uffan ba.
Ina shiga na zauna falo don duk yaran suna zaune a falo hira suke jana dashi amma na kasa basu amsa sosai sai Amira ce ta dan maida hankalinta a gareni tana cewa mummy halan anyi wani abune kuma da aka kiraku falo naga ranki a bace ?
Murmushi na dan kakaro a fuskana mai kama da yake nake cewa da ita bari ke dai Amira wanan amaryan ta daddy tana da rashin kunya da ranshin mutunci a tare da ita.
Don yanzu ta nuna muna halinta a gaban kowan mu tai mashi rashin mutunci har mu din daya tara don magana.
Mummy ke taiwa rashin mutunci ko daddy din nace da ita shi damu duk daga magana ta sake muna bakar magana ta tashi ta fice yana kiranta ko juyowa batayi ba ta tafi abinta.
Au da shi ta shigo gidan ke nan ashe zata ko hadu damu wallahi don bazatai maku mu kyale ta ba nace da ita babu ruwanku a wanan zancen kada ma ki fara .
Batai min magana ba naga ta turo baki kawai tana zunbura bakin ta gaba Aisha tace ni dama ina ganin ta nasan bata da mutunci baki ga ksyan dana ga ta saka bane a jikin nata.
Tun wanan zaman ban sake bin ta kan koshi daddy din ba balle wata amarya can dake gidan.
Zan fita da dare night duty idan na dawo zan ta barci na sai yamma na tashi in dan zauna da yara muyi hiran mu dasu.
Ga bukinn dake gabana ya gabato min haka ya kara sa banda lokacin komai ma a gidan yanzu sai na abinda ke gabana kawai.
Buki saura sati daya muka tafi aka gyarawa Aisha gidan ta tare mukaje dasu zulfa da hindatu da kawayena uku.
Mun dawo gida da yamna lis don kowan mu ya gaji sosai a lokacin nan waje muka samu amarya da kawayen ta da wasu maza biyu sai kwasan dariya suke yi a wurin.
A motana muke don haka nice ke jan mu gaba dayan su suka yo kan mu da kallo kowan mu takai don babu wacce za, a gani a raina a cikin mu.
Sun rigani fita daga motan don haka nice ta karshen fitowa daga motar ina daga bayan su nake jin abinda suke fadi.
Kai Ni,ima wannan sune kishiyon ki fa kikace amma dai kan akwai magana a wurin nan sai naji tace aff maganar may fa da sannu duk zanyi maganin su ko nai waje da yan iska don ban shigo masu ba sai da na shirya masu sosai.
Juyowa nayi ina kallon su don na nuna masu naji zancen su dasuke fadi dayan tace da ita wanan kan akwai jin aji dafanin su duba fa ko kallon inda muke basuyi ba balle su san da tsayin mu su gaida mu.
Tace da sannu ai duk zasu shigo hannu ne sai kace mu ba ya sokoto ba a kofa na hade da Aisha da Amira zasu fita fadan fitan dare nake masu suke cewa dani ba nisa zasu ba yanzu zasu dawo ai.
Nashige yaran na fita nan Amira ta fara sheda dayan su don ta sansu a school sai ga Nasir ya biyo Aisha da wayan ta data manta dashi ciki don an kirata a bayan su.
Shima daya daga cikin samarin ya san shi a school din su, kallon kallo sukeyiwa junan si don har amarya ta san Nasir din .
May kuka shigo yi gidan mu yake tambayan yaron yace munzo gaida amarya gidan na ne gata na ya nuna mata Ni,ima din dake tsaye tare dasu.
Wani iri yaron yaji a ran shi ya juya batare da yai magana ba ya nufi inda su Aisha suke suma wayan ya mika mata ya juyo abinshi.
Yaro nan ke fadin baba na ne gidan ku dama ashe ?
Yace dashi a kausashe nan ne mana gidan mu yaya akayi ne wai ?
Part din mu yanufo tun daga nesa yake kwala min kira nace kai lafiya wanan kiran haka ina aje cup din ruwa da nake sha a hannu na.
Mummy dama wanan yarinyar ce daddy ya aura ashe budurwar Yasir ne fa abokina a school kuma fa mummy tantiriyar yar bariki ce sosai.
Haba nasir koma yaya take ai yanzu matar baban kace don haka ka fitar da idon ka a kan ta please .
Wani iska ya furzo daga bakin shi yakai zaune tare da dafe kan shi ya dade zaune a wurin bai iya magana ba da kowa.
Hakama su Amira da suka dawo da wanan korafin suka samay ni nace da su sai dai kuyi hakkuri tunda har ta shigo gidan ai.
Daddy baya gari sai bayan ya dawo ne har ya shigo mun gaisa dashi ya fita da yamma sai gashi ya dawo ina zaune da yaran a falo muna shan Apple.
Wuri ya samu ya zauna yake cewa dani Rahama ina son kiwa yaran ki magana don Allah su daina yiwa baki a gidan nan wullakanci.
Nace wullakanci kuma daddy wani yaro ne har yaiwa wani wullakanci a gidan nan kuma ?
Yai dan shiru yace Ni,ima ce take fada min yanzu wai abokan ta sunzo sun wullakan ta su jiya nace dashi ita kuma da shi ta shigo muna.
To ka fada mata bazan dauka ba ko kadan ta tsaya a matsayin ta su ma su tsaya a nasu don tana tunanen cewa sun san komai a kanta shine tai saurin fada maka sheri a kan su.
Yace may suka sani a kanta nace budurwar abokin Nasir ne yasan ta tasan shi yanzu kuma matar ka take.
Humm yace a wanan kuma kuka fito ke da yaran naki kuna ganin maganar taku zaiyi tasiri ne a kunne ko may ?
Ba don ka yarda ko kai wani abuba na fada ma don kawai sherin da ita take son hada ka dasu kawai ta iya kanta ka fada mata don mu bamu da lokacin ta a gidan nan.
Kada ki saka min yara a cikin zancen kishin ku don ba zan dauki hakan ba ko kare na dauko a gidan nan a matsayin zamana dole ne yarana su mutuntashi a idon su.
Balle macen dake zamana a cikin gidan nan koda shi ne ya nemay ta ba abokin shi ba yanzu wanan ya wuce a wurin shi.
Daddy ba sai ka fada ba ai dama yara yaran ka ne banawa don haka ba sai duniya sunji zancen wai bani na haife su ba.
Idan kuma ta turoka ne kazo kai min cin mutunci don ta nuna min ta isa ka fada mata ni da ita da babu duk uwar su daya a wurina a cikin gidan nan.
Don naga take taken ta na rashin mutuncin ta nason ya kawo kaina tun yanzu to ta kama kan ta dani wallahi dama duk wani yaro na don ba zan dauki raini ba ni.
Yace kin dai ji abinda na fada maki kada su bari ta kara kawo min karan su akan irin wanan matsala.
Nace don kawai basu gaida bakin ta ba ko may yace don ne ko banga laifin ki ba ai don kune kuka fara har yaran suka gani ai.
Nace yanzu naji magana kan kafito fili kace dani Rahama may yasa baki duka kin gaida bakin amaryana ba ba kace wai yara sun ki gaida bakin ta ba.
Wanan kuma zancen ki ne ban dago kai na sake ksllon shi ba har yai maganan shi yabar part din.
Yana fita ashe Amira na jin mu tace ashe akwai abukazan uba a gidan nan kuwa ita wacece da zatace mu gaida bakin ta wallahi zamu hadu da ita ai.
Ban san yaya akayi ba don nafita zancen yaran kuma shima bai kara maganan ba tun lokacin don ba ma wani haduwa mukeyi ba sosai.

********* ********* *********
Bakina sun fara zuwa don halartan bukin don haka na zama busy sosai da jama, a a gidan ban da lokacin komai yanzu.
Yaran ne sun dawo da kawayen su daga wurin gyaran kai da suka tafi nake jin suna ta surfa zagi daga inda suke zaune.
May ke faruwa ne daku dawa ke fada nake tambayan su sai suke cewa dani wanan yar iskance mana muna shigowa ta tare muna wuri da motar ta munyi magana take son fadawa mutane maganan banza kuma.
Wacece ke nan na tambaya cikin son jin ko dawa suke fada haka amaryan daddy mana nan dai suke fada min yadda suka kwasa da ita a wajen.
Da yamma kuwa daddy ya kirani na samay shi falo, da su Amira bamu dauki lokaci ba muka shiga falon nan muka samay shi zaune yana cin abinci ita kuma tana zaune akusa dashi.
Saye take cikin wasu english wear duk sun matse ta ga gashin dokin data kara ya zubo mata a goshin ta da bayan ta.
Ta koma kamar wata yar arniya da ita sai wani yauki takeyi a gaban shi nai sallama muka karasa shiga tare da yaran.
Daddy gamu nace dashi ya nuna muna wuri mu zauna mina zama ya jawo kwano wanke hannu ya fara wankewa.
Sai da ya gama ya juyo gare mu fuskan shi a daure yace Amira may ya hada ku da wannan dazun kuka zage ta ne ?
Wake nan daddy Amira ta tambaya yace da ita Niima Niima Amirah ta sake maimaita sunan yace eh gata nan zaune.
Tace ba komai daddy motar ta ta aje a gurin da nake aje motana shine nace ta jaye sai kawai ta kai min zagi sai kawai mukaji tace .
Na zage ki ke wacece da zakice sai na jaye wallahi ko kina so ko bakya so dai da uban ki nake kwana na tashi dashi.
Da sauri nace subbahanallahi wanan kuma wani irin zance ne haka ba dadin ji kuma ?
Sai naji Amira tace idan kin kwana da ubana nima ai mace ce sai naje na auri ubanki na kwana dashi kinga anyi daidai ke nan.
Ba sai kin fada muna kina kwana da daddy ba tunda ba shine na farkon kwana da ke ba su Yasir ma suna kwana dake ai a baya.
Innalillahi nace tare da mikewa tsaye nace to yanzu an kai ga yadda ake so a gidan sai cewa daddy keyi ke Amira Amirah a gabana kike fadin wanan magana haka ?
Daddy wallahi ba zan tsaya wanan ballagazar ta fada min magana ba ko kina nufin cewa bamu san yadda kika mannewa daddy har kika aure shi ba ne.
Nace ke Amira tashi mu tafi sai sauran yaran suka mike Ihisan tace wallahi daddy wanan idan bata fita idon mu zamuyi maganin ta a gidan nan ka fada mata.
Nace ku fice nace daku sai suka fice daga falon na juyo tare da nuna su da yatsa nace ke na fahinci da rashin mutunci kika shigo ko wata bakiyi ba kina son haddasa matsala tsakanin shi da yaran shi haka.
To ki natsu ki kama kan ki don ba zan dauki wanan ba idan kin shigo ne dasu a zuciyar ki ki sauke.
Tace ni yara basu ne a gabana ba don ba sune sa,oin yina ba ni dake zanyi keda kike kishiya na dama ina da labarin ki kuma ban shigo ba sai da na shirya zama daku mussan man ma kedin da kike jin kan ki wata tsiya ga kowa.
Dariya nayi nace to kaji da kunnuwan ka don kada ka zarge ni daga baya don ta shigo dani a rai ni kuma ba zama zanyi kalkon ta ba.
Tace dama haka nake so dan da ke wata tsiyace a wurin shi da ba zai dauko ni ha ko ya kalli wata mace bayan ke da sunan aure.
Sai naji yace ke, ke Niima dama haka mukayi dake ko alkawarin da kika daukar min ke nan na wanzuwar zaman lafiya a cikin iyalina ?
Ban fada maki zaman lafiya nake da iyalina ba ban fada maki ba zan lamunci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login