Showing 21001 words to 24000 words out of 37209 words

Chapter 8 - Karashan Murucin Kan Dutse Book One Complete Hausa Novel

15 Oct 2025

268

gaskiya yarinya tana iya kokarin ta da yara amma babu kunya kuzo muna da zancen wai dukiyan yara idan an baku dukiyan may zakuyi dashi baku za a yi ku rike ko may ?
Mama Altine ne da ranta ya baci take fadin wanan maganan cikin bacin rai da damuwa daddy ya juya gun su yace dukiya wani dukiya kuma ?
Maryam tace na yaran mana da mukaji ance wai an fitar masu kwanaki shine muke son ji idan wanan mai wawason bata wawaahe masu ba ?
Ke kuma tsohuwar munafuka Altine da kike wanan magana don an shan ye ki an gama daku ana baki na goro idon ki ya rufe har kike wai ana zaune kalau.
Kai ku dakata don Allah ba wacce zata shigo min har cikin gidana tazo taba son ciwa iyalina mutunci a zauna kalau.
Dama ai na fada maki keda kike daukan su wasu tsiya ko yar uwar nasu dake da rai yaya ta kare dasu sai yanzu ne kuka san ta bar baya a duniya ?
Wa ya taba zuwa da sunan yazo gidan nan don ya ga yaran da ta bari sai yanzu to bari kuji na fada maku.
Idan ba girma da arziki ne zai kawo ku wurin wanan sha a nin ba na rokeku da ku zauna a gidajen ku daga yau idan yaran suna so zasu tafi inda kuke amma ba a gidana ba .
Ku fice min gida idan fitina ya kawo ku ai akwai hukuma sai kukai karana a can ina jiran sanmacin ku.
Ya nuna masu hanya da su fice mai a gida nan suka fara sake mai bakaken maganganu suka fice daga gidan a fusace.
Suna fita hajiyan harka tana shigowa nan take samun labarin abinda ke faruwa a gidan tace kayya ai dama ace tana gidan haka ya faru da sun ji magana.
Wa ya hanavzaman lafiya a tsakanin marigayiya da Rahama ba su ba ta kasa gane va son ta suke tsakani da Allah ba a kullun cikin zuga ta suke da tai rashin mutunci a dakin ta don suna hassada da bakin ciki da samun ta cikin su.
Ina kafin ta mutu ta gane gaskiya nan ta mutu ba kunya suka wawashe abin da ta bari a dakin ta yanzu kuma sun dawo dan abinda ya saura ga yaran su kuma wawashe shi a tsakanin su.
Nace wallahi hajiya ni ban taba kai zuciyana a irin wanan abin ba a rayuwana duk abinda zanwa yaran tsakanina da Allah nake masu don ina kwadayin samun lada a kan su balle Allah na tuba har anty zata bar baya na ce ni Rahama wai na gaji dasu ko na watsar dasu don ina butulu ko may.
Kuma duk abinda zanyi fa tare da sanin anty Asamau nakeyin shi gidan nan don kafa sheda irin haka dama.
Ko ba sheda fa Rahama sai makiyin Allah zai ce ga sherin ki akan yaran nan a gidan nan wallahi.
Sai da lokacin fita yayi aka sasauta maganan daidai lokacin kuma hajiyan daddy ta shigo gidan kan maganan ita ma tace zata tafi har gida ta samay su tai masu tas yara dai nasu ne su da yar uwar su ta mutu suka kasa rikewa har suna da bakin zuwa yin wani magana yanzu don basu da kunya ko may ?
An dai bata hakkuri na hada mata duk wani abinda za a raba gun kamun a ka kai mata a mota suka tafi.
Ko ba komai dai naji dadi don dani kadai suka sama ba wani abin da zan iya yi a lokaci sai kuka don takaici amma Allah ya rufa min asiri a gaban mutane suka zo min kuma sunji magana sosai ranan.
Anyi kamu anci ansha komai yayi kyau yadda ya dace ayi an tafi da dadin rai a gidan an barmu yan gida muna ta kawar da kayan da aka fitar.
Da dare misalin karfe tara sai ga su anty Asmau sun shigo gidan sunzo bada hakkurin abinda ya faru don ashe daddy ta tafi wurin wani kanin mahaifin su ya fada mai.
Shine ya kira su daya bayan daya yana masu kashedi akan gida daddy tare da fada masu abinda su anty Amina suka zo sukayi.
Sun bani hakkuri nace babu komai ai zama tare ne ya kawo hakan take cewa don Allah abawa daddy hakkuri don tana ma jin nauyin shi da kunya su hada ido don basu da bakin magana akan zancen din an riga da an bata zance ko.
Da haka dai da zasu tafi suke cewa sunji ance za a taimaka akai masu amarya ta kwana don Allah kada abi ta zancen nasu.
Na aika aka kira Amira tazo sai dai tana zuwa ta nuna bazata tafi ba da lalashi da komai ta shirya suka tafi da ita.
Su suwaiba na fadin wai don may zan bari a tafi da ita yin haka kamar na nuna jin tsoron su ne ai, nace haba hakan ai ba komai bane diyar suce fa a barta ta san iyayen ta ta san darajan su tun yanzu don yan uwan uwa ba wasa bane.
Dama sune suka watsar da yaran har haka yakai ga faruwa amma ai tasan anty Asamau don idan muna waya tana kusa nakan bata su gaisa da ita ta dan tambaye ta wasu abu gamay da rayuwan su .
Sai gashi kuma bayan tafiyab su da yarinyar washegari daddy ya samay ni da nashi fadan don may zan tura Amiira wurin su tunda basu da mutunci.
Hakkuri na fara bashi nace daddy yar su ce fa dole ne ko yaya ne su san su don jinin su ne yaran, yace dani cikin bacin rai ke dakata Rahama.
Sai nai shiru ido rufe ya hauni da fada akan naje na dawo mai da yar shi kafin raina ya baci inda yake shiga ba nan yake fita ba sai da mama Altine ta bashi hakkuri tare da fadin bari ta tafi ta dauko Amira din tin da safe.
Abubuwa duk sun taru sun min yawa a kaina ta ko ina babu dadi a gareni kan wanan magana don daddy ya rufe idanuwan shi yai min tas akan yan uwan anty Saade.
Yadda mama ta fada hakan akayi don tunda safe ta shirya nasa driver ya kaisu ita da mama Abu matar maigari da gwagon daddy da take zuwa gun mu akai akai idan muna kano.
Sai da aka kwasa dasu don gidan anty Amina suka fara zuwa tace vaza su ba da ita ba sai gobe zasu dawo da ita din.
Amma mama ta fada masu cewa idan har basu ba yarda yarinyar ba komai ma zai iya faruwa akan maganan.
Haka dai dole suka ce yarinyar tana gidan maryam daga gidan maryam aka kira masu Asmau itace ta bada Amira din suka dawo da ita gida tare da su.
Har lokacin raina ba dadi ga jama, a da suka taru don ni a gidan zakace ko yar cikina ne akewa aure a lokacin irin yadda yan uwa na sukai min kara a bukin.
Sai dai yan uwan marigayiya sun kawo min cikas a rayuwana kan zargin da suke min na wai nayi rub da ciki da dukiyan yaran yar uwan nasu.
Kamar yadda daddy ya dauki zafi nima haka na dauka dashi don ban kara bin ta kan shi ba, tun wanan lokacin.
Ban san may ya gani ba da dare ya aiko kirana ina zaune tare da su mama Suwaiba na ta ta faman hada kayan da za a kai hidan iyayyen mijin Amira na gara a cikin manyan robobi don da safe zasu tafi da kayan bauchi.
Mutum biyar aka zaba da zasu tafi Aisha Sister din daddy da fatiman shi sai Asamau sister din anty don ita kadai tace zata tafi sai Zarah yanzu ga Suwaiba tace zata tafi itama don mota biyu zasuyi amfani dashi.
Sai da na dan bata lokaci na mike na tafi inda na samay shi tare da Zulfa a zaune tare da shi.
Sallama nai masu tare da gaida daddy din sai Zulfan take tambayana yaya naji da jama, a dazun ta shiga ance mun dan fita bana ciki.
Na dan bata rai na nakai zaune ina fadin wallahi fa mun tafi wurin mai aikin cicin ne tana son kawo muna cikas ga aikin bayan munyi da ita a yau muke son mu kammala komai gobe za a tafi dasu.
Take cewa dani ai haka mutane suke wani lokaci basu da alkawari nace ai tayi muna don har ta aiko dashi ko tun dazun yanzu ma hada kayan mukeyi aka kirani.
Tace wai gashi har kin wani fada kin ramay ki na ko samun cin abinci kuwa doctor ?
Murmushi nayi nace da ita ina naga ta zama naci abinci idan banga an kamala komai ba tace ai shine ance rana baya karya sai dai uwar diya tai kunya inji manya.
Wanan uwar diyan kan a tsaye take don tun da safe ban ga kin zauna ba ga jama, a sun taru haka abin tubarkallah wallahi.
Nace gaskiya mutane sunyi kokari sosai wallahi don hakane kawai za ai wa mutum a nuna mai so da kauna yasan cewa shi din da dangi ne ta ko ina.
Mun dai dan taba hira akan bukin da ita t yana ta faman aikin shi bai tanka mu ba sai can naji yace damu.
Naga, har su suwaiban ki ai sun shigo da wuri haka abin ya ban mamaki nace ai dole ne suzo daddy wanake dashi bayan su.
Ranan wuya akace sai naka inji zulfa sai Daddy yace ga wanda yasan da hakan ko naga wasu na jikina ne amma suna ja baya ga bukin .
Sai duk mukai shiru saboda mun fahinci inda maganan shi ya dosa a lokacin da zulfa yake wanan magana din.
Yace dama na kiraki ne naji su waye zasu tafi gobe sai kuma jibi din idab za a kaita da suwa za ai tafiyan kuma ?
Na dan ya mutsa fuskana da babu saki a cikin sa nace tau dama dai ga goben sai na lissafo mai masu tafiyan kai kayan .
Nace jibi din dai ne ban san masu zuwa ba don kowa na son zuwa yaga dakin nata a can yace ba gaskiya bane kin san dai ba za, a kwasa akai masu dawainiya ba can kuma da yawa.
Nace ai yanzu sai ka fada kowa yaji yace ba manya ne zasu tafi ba idan za a je din nace ai yadda kace haka ne za ayi.
Amma maganan yana hannun Aisha da Fatima don sune masu gudanar da komai na gani yanzu don ni ba zan iya ba saboda kowa abinda ya kawo shi ke nan.
Yace to ji nan kada a wuce mutim goma dai kuma a tabbatar da an tafi da mama Laraba da mama Altine idan za a kaita din don hankalina yafi kwanciya dasu a ciki.
Nacd zan fadawa Aisha din don yanzu ta fita ta tafi aurin matar da zasu dauka don gyaran Amira din.
Yace gyara wani irin gyara kuma ni dai murmushi nayi sai Zulfa ne tace dashi kai dama ka dauka haka ake dunkula mace akaita gidan mijin ta kai tsaye ba wani dan kwaskwarima tare da ita.
Balle wanan Amaryan yar gata duk kawayen uwar ta madu ido a bude sun san komai ko su da kan su zasu iya mata komai ai.
Nace kai haba dai abin ya zama sheri kuma ai anty gyara kan Amira ta sha shi sai dai muce Allah ya bada zaman lafiya kawai.
Nace a kasalance shike nan ni zan tafi don aiki muke a can aka kirani yanzu din.
Yace tunda kika ji na kiraki aikin san magana zanyi da ke ko nace na dauka wanan maganan ne kawai ai.
Yace to bashi bane zauna kijirani ina zuwa sai yaci gaba da aikin shi kawai.
Dan lokaci kadan Zulfa ta mike tana fadin bari naje na duba yaran nan don yanzu nasan suna can sun min kaca kaca da shiya na.
Ta mike ta fice ta barni dashi zaune a wurin tana fita yake cewa dani komai dai ya kammala ke nan ko don banji kince dani komai ba again ?
Nace dashi ina ganin ba komai ai da nayi magana cikin daure fuska ya dan dago yana ksllona don jin yanayin da nai maganan.
Wai ke may kuma ke faruwane haka kike wani shan kamshi dake haka tun dazu nake lura dake a hakan.
Nace may fa kawai dai daurowa ne yace ba gaskiya bane wanan maganan ko dan maganan da akayi dazun ne kikewa wanan cikan kina batsewa haka ?
Nace dan magana fa kace daddy fisabillilahi yanzu ni may ye laifina a cikin wanan zancen haka da har ka rufe idon ka kai min haka don kawai na tura Amira wurin dangin uwar ta.
Kuma na ga dai wanan maganan ai munyi shi dakai ranan ko yace amma kuma ai daga baya da sukai min rashin mutunci na fada kada a kaita.
Nace yanzu sunzo sun bada hakkuri ai na dauka komai ya wuce ne ko idan kuma na hanata zuwa yadda suka bukata sai kuma nai wani sabin laifi ga hakan.
Yace ba dai kin tura ta ta tafi din ba ina shike nan nace kasan da hakan kuma ka rufe ido ka nunawa mutane ni ba kowa bane ga yaran da maganan.
Yai murmushi tare da ture takardun dake gaban shi yace dani yanzu dai in waban ne laifina ayi hakkuri ina shike nan ko ?
Nace ai hakkuri ya zama dole gare ni tunda haka Allah ya doro min wanan nauyin a kaina dole duk yadda yazo min na rungumay shi da hannu biyu.
Yace haka ake son musulmi dama da hakkuri amma kin daure haka aiko jama an dake tare dake bazasuji dadin ki ba don haka a washe don Allah.

Don Allah wanda na bata wa rai yayi hakkuri dani yanayi ne idan anyi la akari da yadda ake samun novel din a baya da kuma yadda yanzu yake delaiy gurin samun shi.
Ayi hakkuri dani please ba haka naso ba nima da fatan an sha ruwa lafiya yan uwa Allah ya sada mu da rahamarsa da gafaran sa albarkacin wanan watan mai albarka da muke ciki

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[5/8, 15:18] Ummin Meenat: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE ONLINE NOVEL NE NA KUDI, , , , ,


Washegari tunda safe masu zuwa bauchi suka shirya tafiyan don su samu su dawo a lokaci.
Bayan tafiyan su anyi wasu event da ya shafi yan matan bukin na Amira wanda akasarin su sunzo ne daga Abuja don taya ta murnan bukin nata.
Sai yamma lis su Zarah suka dawo garin a gajiye suna ta faman yabawa irin taron da akai masu a can da kuma irin namijin kokarin da mukaiwa Amira din a dakin ta.
Don duk wani kayan kitchen da uwa zataiwa yar ta nice na sayawa Amira su da komai da ya dace na nauyin uwa a gare ni.
Haka uban nata ba a cewa komai don ya gwadawa yarsa gata sosai yadda ya dace duk wani uban da ya dace yaiwa yarsa don nuna hali.
Sun yaba sosai ga abinda idanuwan su ya gano masu a gidan na Amira da aka gyara mata shi.
Mutane nan suka shiga magana kan irin wannan gatan da aka gwadawa Amira din wanda itace ya ta farko da ya aurar ta jikin shi.
Haka yasa kowa ke son zuwa ya ganewa idanuwan shi abubuwan da ake fadi da akwai a gidan na Amira a can bauchi.
Mun tashi da aiki washegari don tun karfe hudu muka falka aka shiga yin abubuwan abinda ya dace na sha,anin bukin.
Koda gari zai waye an gudanar da komai a yadda ya dace, ayi shi don haka muka samu sararin da muka samu hutu da kimtsa kan mu sai taron jamma, a da muke muna kuma ciyar dasu da abinda ya sauwaka na bukin da muka tanada.
Daga hakan ne aka daura aure aka shiga shirin wucewa da amarya sai daga bayane nake jin ai shi daddy da kansa ne zasu kaita shi da Bashir aminin shi.
Kamar yadda yayi da za akai Aisha wannan ma haka akayi akan amira din don sai da muka gurji kukan mu a wurin kafin mama laraba da anty Asmau suka ja hannun ta suka fice da ita a falon tana kuka ina kuka har suka bacewa gani na.
Haka na wuni cikin rashin walwala a tare dani haka nai ta gudanar da harkan buki har mutane suka watse aka barni da bakin da suka zo min daga wasu garuruwan wurin bukin.
Bayan bukin kwana biyu kawai na yi a kano na kwasa sai Abuja don akwai aiki a gabana banda wani lokaci na hutu a gare ni.
Nan na bar Hindatu a kano wai bata gama abinda takeyi ba a garin ni dai na kwasa da yarana muka bar garin.
A na samo wata yar aiki sai dai ba yarinya bace ita ta dan manyanta hajiyan harka ce ta sama min ita don haka da ita muka dawo garin.
Nazo da yar wurin Suwaibana daga can da zata zauna dani sai kanina Audi daya biyo ni don zai fara karatu shima yanzu saboda sun kiyi a can sun tsaya shiririta wai neman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login