Showing 33001 words to 36000 words out of 37209 words

Chapter 12 - Karashan Murucin Kan Dutse Book One Complete Hausa Novel

15 Oct 2025

262

jiki sosai da kowa a cikin su.
Sai da na share sati biyu cur a gida muka shirya dawowa Abuja don aikin da ake nemana akan shi idan ba haka ba yadda daddy baya kasan da sai na share kusan wata daya a gida tare da yan uwa da iyayyena.
Sai da na kwana uku a kano nagama komai da nake bukatan yi na bar garin da dare muka shiga abuja don haka kowan mu a gajiye yake a lokacin.
Wanka sukayi yaran suka kwanta ni da su Atika muka dan yi abin da ya kamata muka kwanta muma.
Washe gari monday haka da gajiya na shiga wurin aiki don meeting din da muke da shi a ranan wanda ya zama min dole da sai na halarce shi dole.
Bamu fito ba sai karfe uku na rana don haka ban tsaya ba na nufo gida kai tsaye don nai wanka da sallah na samu dan abinda zanci a gidan.
Wanda nayi sa, a an gama abincin wanka na fada nafito na tayar da sallah a gurguje don na makara sosai da sallah da ban samu nayi ba a cikin lokacin sa.
Sai da na idar da sallah na shirya na fito falon wurin su mama da yara na zauna nan kowa ya fara kawo min korafin shi na baida abu kaza na komawa school.
Shigowan maman ihisan yasa yaran dan tsagaita min da damuwada suka sakani gaba dashi wanda bai hanani cin abincina ba a tsanake.
Mun gaisa da ita take tambayana mutanen gida nace da ita duk suna lafiya tace dani kun sha gida wanan karon kan ?
Nace wallahi kamar kada mu dawo da sauri tace dani kauye din kike cewa kamar kada ki dawo maman Haidar ?
Da sauri na dan kallota nace inane asalina maman ihisan ai kowa yabar gida gida ya barshi da kauye da birni in dai da wadata ai duk daya ne ga bawa.
Tace hakane aini nayi dana sanin rashin tafiyana da kuka tafi kuka barni don wanan mara mutuncin matar tashibhaka tazo min da wasu irin tika tikan mata a gidan nan wai suna meeting a wurin ta bakiga iya shegen da sukai muna ba a gidan nan wallahi .
Dariya ne ya subuce min nace da ita ashe kun sha kallo tace kallon takaici ko may abu tun sha biyun rana suke abu daya har muka kwanta ni dai ban san watsewan su ba ranan.
Nace wata sabuwa ke nan kuma yazo muna gidan ke nan gara da bana nan nasan da nawa ya samay ni don dani kowan su zata shigo gidan ranan.
Tunda ni suka saka a gaba tace ko kina nan ai bazaki kula su ba don babu wasu itin kilakan mata ne dasu.
Nace ko ajikina tunda ba a guna suke alamarin su ba sai dai wacce duk ta kulani shine zasu jini kin san ai saniya bata sani ana son ta kauce sai an tokari bayan ta ko ?
Kai kema dai wallahi kawai dai don baki gari ne kawai nace ai gani sai su kara dawowa in don ni dama sukai taron su gani.
Tace dani aini ranan naga ikon Allah zakice gidan nan ko wani wurin sai da motane don irin yadda suka baje motocin su ke da ganin su babu mutanen arziki a cikin su wallahi.
Nace ai in mutum bai mutum ba bai gama ganin duniya ba mu kuma irin namu kaddaran ke nan da muke gani ko wace da nata irin sallon da take zuwa muna.
Tace bari maman haidar wallahi ni har mamakin wanan mutumin nake ji irin wanan rayuwan haka ga yara mu na tasowa suna bude ido da abubuwan barkata a gida suna gani.
Don duk wacce zata shigo da nata irin sallon iskancin da zata zo muna dashi a gidan gida ya koma muna kamar gidan yan iska.
Nace da sauri ga wanda ya damu da abinda suke ciki ba nifa ban damu da kowa ba balle lalurar mutum ya damay ni.
Tace zulfa fa suna lafiya nake cewa da ita suna lafiya ina ga karshen sati mai zuwa zasu dawo nan din itama yadda mukayi da ita.
Tace dani kuma again nan din ita ma zata sake dawowa da zama nace ba anan din take ba dama may ye amfanin zamata a can da takeyi ita kadai ai gara ta dawo a hade yafi.
Allah ya kyauta tace dani tare da mikewa tsaye tabar falon ran ta babu dadi a raina nace kishi kumalon mata ke nan koni ai ba taki na bar gidan ba ta zauna ita kadai kamar yadda ko wace mace ke bukatan ganin ta ita kadai a gidan mijin ta.
Amma ni may zaisa na wahal da kaina ga haka ni da na shiga cikin mata uku na zo a ta hudu shine zan sakawa raina wani kishin banza can.
Wai ma akan wani mijin zan zauna ina kishi mijin da ko yaushe baya nuna an mashi daidai a cikin kwashe kwashen mata yake da yawan aure a gidan.
Na ja tsuki tare da kiran Hadiza tazo ta kwashe kayan abincin da naci a gabana tare da mike kafafuwana a saman dan stoll din dake a gabana na dafe kaina da hannu daya ina tunanen maganan da hindatu ta fada min nace a raina Allah ya kara hadani dasu wata rana zasu san allura ma karfe ne ba abin banza bane shi.

********* ********* *********
Kamar yadda muka barar da zulfa hakan ne kuwa a karshen satin ta dawo Abuja sai dai tun dawowan ta ban samu zama ba don yara na dake damuna suna fama da lolayin ciki kowan su.
Idan na gama da wanan wanan zata kirani da nata korafin kuma haka suka raba min hankali ga aikin da ya taso min a gabana kuma ban da hutu ta ko ina a kaina.
Ranan jumma,a maigidan zai dawo kasan don haka a bangaren kowan mu sai shirin taron maigidan akeyi kowa na nuna nata bajin ta akan dawowan shi kamar yadda ko wani gida haka mata keyi idan miji ya dan yi nisan balaguro da gida na kwana biyu.
Ashe mu duk shirmay mukeyi a bangaren mu bamu sani ba sai ranan ds zai dawo yai waya zasu iso da karfe sha biyun rana yakuma ce ba sai mun je taron shi ba da yan aikin su yake tare.
Ina dakina ina shiri Atika ta shigo tana ce wa dani ga Anty Amira da Aisha sunzo na ce kai sunzo min da matsalan su ke nan daga mai miyau sai amai a cikin su dariya tayi ta fita daga dakin.
Sai gasu sun shigo tun daga kofa suke kwala min kira da mummy mummy nace ya salam wanan kiran fa na tashin hankali haka fa for god sake ?
Suka fada min a jiki da murnan su muka shiga gaisawa dasu nan Amira take cewa dani mummy wani buki kukeyi ne a gidan yau naga gidan ya cika da motoci mana haka barkatai.
Cikin mamaki nace motoci kuma a ina na mike tare da leka window dakina aiko matane na hango suna shige da fice a bangaren amaryan daddy din.
Nace kun san mun samu yan bidi,a a gidan yanzu kila wani abin sukeyi kuma a nan ashe ni ban sani ba wai duk dawowan daddy akewa wanan shirin haka .
Sai isowan shi gidan ne mukajiyo hayaniya ta ko ina a gidan da shewa wai suna mai sannu da zuwa.
Sai dai kamar hadin baki don babu ko mutum daya daga cikin mu mamaki wanan abin ya bashi don haka yayi zaune a cikin mota yaki fitowa daga ciki.
Suna tsaye sai iskanci suke zubawa irin na manyan mata yan duniya suna wani girgije girgijen jikin su.
Waya ya daga ya kira mu dashi yana fada wai ban mu san ya iso bane kuma wani haukane haka mat?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a suka taru muna a gida haka suna wanan iya shegen haka ?
Nace a gidan nan to banda ma saniya a kan su amma ganinan fitowa yanzu ai.
A tare mu uku muka dinga fitowa daga part din mu nice ta karshe tare da yarana gaba dayan su muka fito shigan mu ma kawai ya isa mutum ya tsaya kallon mu don kowan mu ya kure a dakan sa sosai rike nake da hannun anty da daddy da suka sha irin nasu adon nan kuma kallo ya koma a kan mu duk wanan iya shegen da suke zubawa a wurin.
Motar har lokacin yana rufe haka muka ratsa su har bakin motar daidai lokacin ne ya bude motan tare da sako kafar shi daya waje.
Sai na karasa bude motar tare da rankwafawa gare shi na dan kamo shi da saurin ta ta karaso bakin motar tana bangaje yaran dake murnan ganin mahaifin su har anty na buga bakin ta a kofar motar wai tana kamo shi.
Wani tsawa ya daka mata tare da karasa fitowa daga cikin motar gaba daya yana kama yarinyar yake fadin kina haukane haka komay da zaki ture min yarinya kina gani.
Jaye min daga nan please ya juya gun matan da suka dandazo a gaban mu yana fadin wa yan nan fa kuma daga ina haka suke su ya busu da wani irin matsiyacin kallo na takaici hindatu ta fada jikin shi ya rugumay ta haka ma zulfa tai mashi ban tafi ba shi da kan shi ya jawoni izuwa jikin shi ya kama hannun su jinior muka shiga cikin gidan yana rungumay dani a jikin shi .
Nan muka barsu tsaye cikin takaici da mamakin wannan irin cin fuskan da daddy nuna masu a fili gava kowa don su suna ganin duk a inda yar wanan kungiyar take dole tana da razara da matan da ta samu a gidan don zaman su hamshakan mata a gari masu kafafen kungiya na kan su.
Wata da take itace hanshakiya a cikin su ce ta fara magana da cewa asha samira banji dadin ganin haka daga gare ki ba ashe kin san baki shirya ba kika taramu a nan don ganin wanan bakin cikin haka ?
Yanzu wanan cin fuskan da mijin nan naku yai muna kinga kin kyauta muna ke nan ko may da har zai dubemu haka a wullakance yaja iyalin shi ya barmu kamar wasu marasa galihu a gurin.
Daga haka bata sake magana ba ta nufi motar ta sauran ma ganin shugaban kungiya ta nufi hanyan fita suka fara sake magana suna fita daga gidan daya bayan daya cikin kunar rai wai an masu wullakanci an nakasa su.
Hankalin Samira yai matukar tashi sosai daga ita sai kawaywn ta biyu aka watse aka barsu a wurin nan suka shiga magana a kaina.
Na yarda da cewan da malam baushe keyi da neman tsari na jiki idan bana sheri bane yana da amfani sosai ga mutum watarana.
Ga yadda irin zamani ya koma a yanzu duk da malamai na fadakarwa amma zuciyan wasu sai kara bushewa yake wurin aikata aikin kaucewa Allah.
Don dai kawai wani buri ko bukata na duniya akan su irin haka ne ga wanan matan don su a nasu ganin kamar duk wata mace a duniya zasu iya shiga da fice su takata yadda ransu ke so a gidan miji idan sun samay ta.
Don koda mijin da baida mata daya su ta aura haka mai shi zai tabbata a duniya ba wata mace sai su haka kuma idan kishiya ko kishiyoyi suka samu ba zasu dauki lokaci a gidan basu watsi da wanan macen ko matar da suka tarar a gidan ba.
Sai dai duk da haka ba wai kullun ne suke nasara akan ko wace mace da suka sama a gida ba akwai wa yanda kan dan fi karfin su a zauna aita fafatawa dasu a gidan Allah ya tsare mu daga sherin irin wa yan nan mata masu mugun hali na rashin tsoron Allah.
Nasan ba komai daddy yakewa wanan rawan kafa haka ba sai yadda zai ga komai ya daidaita a tsakanina dashi wanan karon.
Yayin da su kuma sauran kishiyoyina suke ganin ai asiri ne nai mashi tare kuma da ilimi da kyau din dake gare ni yake min wanan rayuwan haka.
Wanda nina san ba haka bane alamarine na Allah, sai farko idan ka samu daukaka gun Allah sai ya tsare ka ga komai.
Ke dai yar uwa maida al, amarin ki a gun ubangiji a koda yaushe sai Allah ya tsare ki daga duk wani abin ki a gare ki.
Duk wanda ya nufe ki da sheri Allah yana tare da ke sai ya koma a kan mai shi duk wanan aikin dake gabana bai hana ni kullun tsaida dare abokin hirana ba wurin mika koke na ga ubangijina akoda yaushe.
Rana ce kawai nakan dan samu lokacin aiwatar da rayuwana na duniya a cikin sa don shi tashin dare wani alamari ne dake tafiya da sabo da saka abin a zuciyar bawa.
Fitina ce sosai a tsakanin Samira da maigidan yayin da mu kuma sauran iyalin nashi muke a cikin farin ciki da dawowan shi don mun godewa Allah yadda taso taga mun nakasa a kan shi hakan bai samu ba a gare ta don bai shiga guntaba ma balle ta aiwatar da duk wani shiri nata akan shi balle abin yai tasiri gareshi yadda take so.
Don ba karamin gagarumin shiri tayi ba kamar yadda mata da yawa suke wanan irin shirin ga maigida idan ya kwana biyu baya cikin iyalin shi.
Wanan baiwan ne daga Allah don badon Allah yaba tsare bayin sa ba da wata irin shirin da kishiya take a kanta ko daga kai miji baya iya yi ya kalle ka da suna wai abokiyar zaman ta.
Amma da yake abin daga Allah sai kaga ubangiji yana kare bayin sa masu dogaro a kan shi suna yawan kai kukan su a gareshi ko da yaushe.
A nan Allah ya taimakeni a kan Samira don haushin ba nawa bane ni kadai don ya shafi kowan mu saboda ta shiga wurin shi ta samay shi tare da zulfa suna soyewan su washegari da ta koma kuma ta sake samun shi tare da hindatu .
Sai haushin nawa ya rage ya koma a kan su take cewa da kawarta dama hakane ana zaton wuta a makera sai a samayta a masaka.
Don haka tai muna bugun dan kade gaba dayan mu tace mune mukai mata wani sihiri miji ke ganin bakin ta haka daga dawowan shi.
Ranan da girki ya dawo a kaina ne muka kwasa da daddy din don har lokacin ina a kan bakana na rashin yarda dashi da banayi.
Ya kirani a waya yake fadin nazo na samay shi ya dawo nan na shirya na samay shi a falon wuri na samu na zauna daga nesa kada dashi tare da gaida shi da dawowan shi.
Ya amsa min ba tare da ya dago kan shi ba yace maman Jinior ke nan wai ni ban fahinta ba ya fadi yana kokarin rufe takardan dake a hannun shi.
Ya dago yana mai kallona cikin mamaki nake cewa dashi na may fa ke nan daddy don da zaran ya kirani da wanan sunan na maman jinior nasan da akwai magana ke nan daya taso a kaina.
Yace wai har yanzu kina nan akan bakarki ne na kina guduna ina da cuta ko may ?
Nace ni bance kana da cuta ba daddy kawai dai don na fahinta da irin auren nan da kake a yanzu ko a kai tsaye ne ko da binciki gama yadda duniyar nan ta mu ta koma a yanzu.
Murmushi yayi yace dani yayi shine har yakai bana samun kulawan da aka saba bani ko kadan kamar baya.
Nace ba haka bane wanan kawai dai dorowa ne don ni ban ma san ka dawo ba gidan ai.
Yace dani karbi wanan na mika hannuna na karba a cikin ladabi tare da budewa sai naga ai form ne na wani makaran ta a kasan saudiya dake garin madina.
Ga kuma sunayen yarana a jere a ciki su hudu a form din na gani da dan wurin zulfa guda, da sauri na dago kai cikin mamaki ina kallon shi tare da son jin na may ye wanan form din kuma daddy ?
Yace dani kin karan ta aiko ?
Nace na karanta sai dai ban fahinta ba yace ok yaran nan nake son akai su can suyi karatu dukkan su.
Nace dukkan su daddy yace ko baki ra, ayin hakan ne ke nace a, a ni may zance abinda ka zartan ai shine nawa.
Yace good ina da raayin yarana su fahinci addini sosai a rayuwan su tunda Ubangiji ya hore min abinda zan iya daukan nauyin su a hakan dashi.
Masha Allahu nace dashi yace na gama komai akai saura tafiyan su idan lokaci yayi Allah ya kaimu nace tare da fatan Alheri ga wanan tsarin.
Yace haka nake son ji wanan halin naki yasa nake kara son ki a raina ko yaushe Rahama don biyayyan ki a gare ni sai dai kuma gashi ana yabon ki ga sallah kina son kasa yin salati kuma.
Nai murmushi nace ni din kuma daddy may kuma nayi baiyi magana ba ya miko min wani takarda dake gefen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login