Showing 12001 words to 15000 words out of 37209 words

Chapter 5 - Karashan Murucin Kan Dutse Book One Complete Hausa Novel

15 Oct 2025

270

a barta a gefe daya wai ala dole sai ta zama borar gida da karfi da yaji.
Sai dai abinda bamu sani ba warw ta a gefe dayan ne zai kara mata kwarjini da fada gun miji.
Nikan a wuri na sai ma hakan yafi mun sauki don babu komai ga wanan irin hadin kan sai makirci da gulma kawai.
Fahintar hakan yasa na gane ni din ke nan wata abune a gidan don haka maganan daddy gaskiya ne bari wasu su fahinci matsalan mu babban jin dadin kowan su ne.
Haka yasa banda lokacin kowan su idan mun hadu dai sai a gaisa a wasance a wurin a wuce .
Mun kai har zamuyi kwanaki mai dan tsawo bamu hadu ba a tsakanin mu sai ma zaman hakan ya fi mun dadi yanzu.
Ranan daddy ya kirani a waya na samay shi a falon shi da safe na saka dogon riga tare da dan gyara fuskana na nufi wurin shi.
Yana zaune ya baza wasu takardu a gaban shi nai mai sannu da aiki ya amsa ba tare da ya dago kan shi ba.
Zama nayi daga gefen shi a kasa bayan na zauna ne ya miko min wasu takardu da akai banding a wuri daya.
Na fara bin takardun da kallo sai na lura takarda ne na shedan wasu aiyuka a ciki.
Sai naji yace ki duba da kyau ki gani takardun yaran kine na gadon su da uwarsu ta bar masu an juya su har sukai haka shine naga ya kamata yanzu na sanar dasu su san komai a kai.
Kwandala ban taba tabawa ba daga ciki tun uwarsu na a raye har zuwa yanzu.
Zan so naji ra, ayin su idan za, a rabane tun yanzu don ita Amira dake shirin aure idan kuma za, a barshi a hakane aita juta masu har nan gaba idan sun kara tasawa gashi nan dai.
Kara bin takardun nayi da kallo na fahinci ba karamin kudi bane a ciki da kaddarori na yaran da suka gada a wurin mahaifiyar su.
Nace Allahu akbar Allah mai hikima da basira buwayi gagara musali Allah mai yin yadda yaso da bayin shi.
Ar, razaku mai azurta bayinsa a yadda yaso ga dukiya haka ga yaran nan amma kuma ya dauke mahaifiyan su a tare dasu.
Ya Allah kabamu ikon tsayawa akan gadkitan ka mu gudanar da rayuwan mu a cikin sauki da kamala kowa da tashi irin kaddaran rayuwa da yake zuwa mashi.
Samun mutum mai gaskiya da adalci irin ka daddy sai an tona a wanan zamanin wanan ba karamin baiwa bane mutum ya rike amana irin haka da wuyan samu a wanan zamanin.
Yace Rahama ba zan taba mantawa da Saade ba a rayuwa don saade mutum ce ta fada a duniya a sanadin ta na samu abubuwan alheri da dama a rayuwana.
Saade ta tafi ne amma tabar min alherin ta a duniya wanda ke kan ki kina daga cikin wanan alherin da ta bar mun.
Dole ne na tausayawa yaranta na kuma godewa Allah da ya rufa min asiri ya hada ni dake kika rike mun su amana tanakar kece mahaifiyar su kika hana su su san maraicin uwa a tare da su.
Rahama yadda kika tausa zuciyar ki ka rike min yara nan shine dalilin da har gobe bana kaunar naji ko naga na sabawa rayuwan ki don kin min abinda ba kowame zai iya wanan ba.
Ban taba ganin banbanci riko ba tsakanin su da diyan ki saima nace kin fi kaunarsu akan diyan ki in ba zuwan su yan biyu ba wanda suma nasan son Saaden ne dani ya jawo kike masu shi.
Don haka banda ma bakin godiya a gareki bani kaidai nai yaki ga hakan ba harda ke da kike bani gudun mawar kan yadda naga kina rikon su haka.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[5/1, 22:20] Ummin Meenat: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , ,


Ban san irin bakin da zanyi magana dashi ba kan wanan abin da daddy yai muna yai muna mana don kamar ni yaiwa hakan.
Ya zama dole na samu daya daga cikin shakikan su na dangin mahaifiyar su bayan mama Altine na fada mata komai sai naga ya kamata kuma na samu wasu don su sani .
Matsala daya ne yanzu shine yan uwan na marigayi tun rasuwan mahaifin nasu kan gidan ya karasa watse masu kowa tashi ta fishe shi suke.
Ko sisi baka sayen su yanzu duk sun wullakanta dan abinda aka bar masu na gado a wurin su.
Karshe dai naga Sadiya ya dace na gani don ita tana da dama mijin ta kuma na da dan abin hannun shi ai.
Tunda ba wai dukiyan za a danka maasu a hannun su ba kawai dai su sani ne cewa ga halin da ake ciki da dukiytan yaran don fita daga zargi.
Labarin dukiyan da sauran matan daddy sukaji ya tayar masu da hankali don sunce basu yarda ba da zancen shi dai wani hadin kaine mukayi a tsakanin mu da daddy don a fitar da wani kaso daga dukiyan shi a inganta rayuwan yaran su kadai don ni na riga da na inhanta na yarana ba sai sun jira want gadon mahaifin su can ba.
Tun Ana kumbiya kumbiya maganar har zancen ya Kai kunnen daddy yaji don yar rashin kunyar matarshi ce to fito mai da zancen gaban shi.
Abin yai matukar bata mashi rai sosai har yakai ya tara mu a gaban shi ni dai ina falona don ina up a wurin aiki ban fita ko ina sai gashi tunda safe daddy ya kirani a waya na samay shi a falon shi.
Ban kawo komai ba a raina na shirya dama a shirye nake dan gyarawa kawai nayi.
Duk kan su suna falon kowacen su ta hakkince a zaune cikin nata kalar shigan sai shi may gidan da alama ya nuna ko wankan shirin fita baiyi ba a lokacin.
Da mamaki na karasa cikin falon tare da sallama da fargaban may kuma ya faru haka son ruwa baya tsami banza a hakan.
Ina shigowa ya dago kai tare da sauke idanuwan shi a kaina yana mai amsa sallamana.
Na samu wuri na zauna can daga karshe nace gani daddy lafiya dai ko ?
Da hannu ya nuna min na zauna na karasa kaiwa zaune din ina mai kura mai idanuwa na don ban bi ta kan kowa ba dake falon a lokacin.
Shiru falon yayi can ya dan nisa tare da shafo fuskan shi yace na kiraku ne don wani magana da naji daga bakin wanan yarinyar ya nuna inda Niima take zaune da fuskan shi.
Sai kowan mu ya gyara zaman shi don jin may ya faru kuma haka yaci gaba da fadin daren jiyane ta fuskance ni da wani zancen da ya kona min rai a gidan nan akan yaran nan marayu da Saade ta bar min ko nace ta bar mu dasu.
Daga inda nake zaune nace tau fa ?
Yace eh tazo min da zancen wai ita bazata yarda ba sai itama na bata kudi kamar yadda nake bawa kowa a gidan nan don har su Amira da Nasir na ware ma makuddan kudi daka jikina na basu a matsayin kyauta don tallafawa rayiwan su.
Kuma ba kowa yasani yin haka ba sai Rahama don tana bakin ciki na mutu a raba gado kowa ya samu yasa ta bani wanan shawaran
Take naji raina ya yi mugun baci nace a hasale wai wanan matar may kike so danine a gidan nan wai ?
Yace dani dakata hakana magana nake yi sai nai shiru tare da komawa na zauna da kyau.
Yace maganan ya bani matukar mamaki don ban san ina ta samo wanan zancen nata ba haka ?
Ya juya gunta yace Niima jiya da kike min wannan magana kikaga na yi shiru akwai abinda nake tunane ne bawai na kyale ki bane hakana sai kuma kyale kin da nayi ya bani daman karasa sauraren abinda ni ban sani ba a gidan nan.
Kafan ta take kadawa a hankali yayin da tai tagumi da hannun ta daya tana mashi wani irin kallo mai kama da tsanane ko haushi ?
Yanzu ina son ji daga bakinki a ina wanan maganan yafito maki haka na ki fada muna ke muke saurare.
Sai tai shiru tunda naji Zulfa tace da ita ke Niima may yakaiki yin wanan maganan don Allah nasan akwai wata a kasa in baki manta ba mai karatu Anty marigayiya tasha fada min cewa nai hankali sosai da Zulfa don munafukace ta gaske amma a zatona ta daina halin nata ne yanzu girma yazo mata .
Muryan daddy yadawo dani daga tunanen da nakeyi naji yace ke muke saurare fa kada ki shanya mu anan ?
Shiru tayi sai ya dan gyara zaman shi da kyau yace saurara kiji wallahi ki???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?nji na rantse maki ko ki fada min ko yanzu ki raina kanki ga hukuncin da zan yanke a kan ki.
Don duk wanda har yake jiran ka mutu yaci gadon ka to kuwa zai iya kashe ka ya kaiga manufan shi a tare da kai.
Tace nima ai fada min akayi gadon ka kuma ai ba ni kadai ke jiran ci ba don duk wacce ke tare dakai shi suke jira suma.
Ko don an fini wayon iya gilibibi yasa nawa kawai za a gani don nai magana kawai.
Hindatu tace ke ki iya bakin ki don mu ba mayunwata bane irin ki sai ta watsa ma hindatun harara tace shi kan shi ya sani ai .
Badon cin gadon akace Rahama na haihuwa akai akai don tafi kowa kaso ba a gidan dariya maganan ta ya bani ban iya magana ba don ya kwabe ni da farko nasan ko yanzu ba zai bari na sake wani maganan ba ma.
Yace ai saiki fada muna wanda ya fada maki tace akan may zan fada don an raina min za ace don nai magana da kai za a zo a tsureni gaban kowa nai magana.
Da suke siri dakai tsuresu kakeyi ko may dani za ai min hakan don raini.
Wani uban tsawa ya daka mata sai data dan razana yace zaki fada ko yanzu na zartan da hukuncin da nai niyya a kan ki don ba zan iya zama da macen da ta iya fitar min da zuciyar ta damanufanta ba haka a fili.
Jin abinda ya fada yasa tace a dai muna hukunci da wacce ta fada min don nima daga bakin uwar gidan ka na samu labari.
Da sauri zulfa tace ke kada ki fara ki min sheri wallahi ko don yanzu za a jimu dake a gidan nan.
Tace sherin may zan maki bake kika fada min ba kikace duk yadda zanyi na kawar da Rahama a gidan nan nayi ko bata fita ba ta koma ita da babu duk daya.
Daddy yace kinji Zulfa kinji yanzu abinda ta sake fada ko Niiman tace ai ba kazafi nai mata ba.
Kince kudin shi Rahama ke komai dashi tana labewa ga aiki take samu sai abinda tace ake kuna kallo a gidan daku da yaran ku kamar babu ku a wurin shi.
Daga inda nake zaune nace Allah na gode ma da baiwar da kai min ka rabani da hassada a rayuwa na.
Nace Zulfa ai kun riga da kunyi sake diyar zakanyya ta girma sai hakkuri yanzu don haka munafuncin ki da hassada zai sa ki tabbata a boran ki har abada don babu mai iya sauya ma wani hali shi sai Allah.
Don da zaki daina munafunci a bayan ido zama dani dayasa kin daina ko tuntuni may yafi nan kunya ki zauna da yarinya karama kina gulma irin haka don hassada kawai da bakin ciki.
May na rage ki dashi na mutuntawa a rayuwan zaman mu dake ba yau ba na sani akwai wanan ranan yana tafe gun munafuki ai.
Kada ki kara kirana da munafuka Rahama karya ne may Saade din ta bari da za, ace wai gadon yaran tane wanan kudin da ake fada.
Tace dakata gaskiya dai ya baiyyana yanzu kundai yi maganan da Niima ke nan a gidan nan ko ?
Tace munyi sai dai ba yadda ta fada ba aiko hindatu ta sani da sauri hindatu tace da kukazo min da maganan may na fada maku ni ?
Ba cewa nayi yanzu na gaji da wanan halin ba abinda ke gabana ya isheni kuma ke Zulfa na fada maki Rahama bada tsiya take nufar mu ba kibi a hankali koba haka mukayi dake ba.
Tace yanzu ko da maganan ya zama haka amma aiko ke da cewa kike don tafi kowa kaso take haihuwa akai akai haka a gidan nan bake kika fara fada ba.
Tun fara cacan baki a wurin ya dafe kan shi baiyi magana sai da yaga abin bana karewa bane yake cewa damu.
Kai ya isheni haka na yanzu na gane inda maganan nan ya fito don haka dake da kika fada min da ita data fada maki duk hukuncin da zan yanke ya hau ka ku.
Zulfa ba zanyi duban irin zumuncin dake tsakanina dake ga don na fahinci duk wani tsegumi na gidan nan daga gareki yake fitowa don haka dake da Niima ku saurara da kyau kuji.
Kudi dai banawa bane bana Rahama bane dukiyan yara ne da nake juyawa na uwar su tun tana a raye kamar yadda ta dauki amana tabani haka na rike wanan amanan har shekara goma sha tara ina rike dasu a hannuna.
Sune yanzu ganin yaran sun kawo hankali na fara gabatar masu da dukiyar su don su san dashi a gare ni.
Rahama ga tanan a matsayin ta na mata na dake rike mun yaran ita na fara gabatawa dukiyan yaran.
Sai Allah ya taimake ni ta bani shawaran da ya dace akan na kafa hujja da yan uwana da kuma yan uwan mahaifiyan su.
Nasan kuma zaman da mukayi da su a kano har yasa kuka samu wanan labarin yazo gare ku.
Amma da yake baku da tsoron Allah a tare daku ita da ta taimaka min ta bani mafita kuka dauki sheri da zargi kuka saka mata dashi.
Mai son abinka har rayuwan ka yana so idan ya samu don haka bazan taba iya zama da irin mutanem nan ba a rayuwa na .
Ya fadin haka ya mike daga inda yake zaune yace ku bani wuri don Allah zan shirya ni.
Nice ta farkon mikewa a nan zabbar kunya na barsu su uku suna cacan baki a tsakanin su ina shiga wurina wani kuka mai sosa zuciya yazo min a lokaci daya.
Ban fito ba sai da lokacin zuwa dauko yarana makaranta yayi naiwa mama Sallama na fita daga gidan gidan yai shiru ba motsin kowa ko irin kidan da kakeji yana tashi a part din Niima yau babu shi a gidan ko kadan.
Haka na fita daga gidan naje na dauko yaran muka juyo zuwa gida muna shiga ne na hadu da wata kawar Niima zata fita tabini da kallo ban kula taba na shige abina.
Naiwa yaran wanka muna zaune ina basu abinci sai ga daddy ya shigo wirin mu nai mashi sannu da dawowa yake cewa da shi.
Yaran har sun dawo ashe nace eh yanzu na dauko su yake cewa zan tafi lagos yanzun nan tafiyan ya kamani sai dai kafin na dawo na fadawa Zulfa da Niima su bar min gida don haka ina fada maki ne babu ruwanki da zancen su kuma.
May hakan ke nufi da subar maka gidan ka dakace dasu yace maganin kiyayya nace rabuwa.
Yace dani to na rabu dasu duk su biyun ba zan iya zama da masu son rayuwana ba, don ni dukiyana na nemawa iyalina rufin asiri ne banga abinda na rage wata daga cikin ku dashi ba da har suke jiran mutuwa don na bar masu dukiyata suci.
Ita Zulfa yanzu zataci na diyan ta idan na mutu din ita ko Niima ta tafi da abinda ta samu a wurina a yanzu.
Daddy don Allah kayi hakkuri da wanan zancen haka na kowa da halin sa ake zama dashi ai.
Yace naki ra, ayin ke nan nikan ba zan iya zama da masu son rayuwana ba.
Yana fadan haka ya fice daga part din nawa da kyat na bude bakina daga kalkon mamakin da nake mai nai mashi Allah ya tsare hanya.

********* ********* *********
Zulfa kan bai dawo ya samay ta a gidan ba don ta tafi kano tun washegari sai Niima ce taki tafiya kamar yadda yaba da umurni.
Ya dawo ya samayta a gidan yai mata cin mutunci badon taso ba dole ta bar gidan kamar yadda yace din.
Da dare ina gurin shi yana cin abinci sai ga wayan hajitan shi ya ahigo mai suka gaisa suna gama gaisuwa da ita take tambayan shi dalilin turo Zulfa gida dayayi don gata sun samay ta da uwarta.
Yace eh hajiya nina sallamay ta don ba zan iya zama da ita ba haka laifi sukai min kuma na riga da na yanke hukuncin duk wanda ke da hannu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login