Showing 18001 words to 21000 words out of 37209 words

Chapter 7 - Karashan Murucin Kan Dutse Book One Complete Hausa Novel

15 Oct 2025

266

Shiyasa zaman nasu har yai dadi amma data amu irin ta kinga ta zauna ta zubar da kanta gun karamar yarinya ga banza.
A daiyi hakkuri yanzun ai tasan ta duniya kishiya ko wacce ka san tane sosai ina kake daukan yarda gaba daya ka bata balle wacce ta san ta shigo maka a bakuwa.
Ya mike yana fadin shi zai fita adai ja mata kunne ta yi hankali don idan ta sakw zasu hadu fiye da hakan.
Nan ya fice ya barni tare dasu sai kuma aka koma bani magana ana wai idan naga tayi abinda ba daidai ba na dan rika saka ta a hanya.
Nace mama ai a bar zancen girma a wurin miji a girmay ta girmay ni sosai ma ba kusa ba ita bata lurar dani ba sai nice zan lurar da ita ta dai gyara halin ta kawai shi yafi.
Munyi sallama dasu akan da dare zasu dawo da ita dakin ta ayi buki da ita nai masu rakiya suka tafi zar kunya dasu.
Koda daddy ya dawo lokacin baki sun dan cika gidan na samay shi a dakin shi zaune saman gado na gaidashi da dawowa ya amsa min.
Yana cewa ashe har gida ya fara cika hakan ne da baki don naje shiga naga mutane sun cika wurin.
Nace hakane sai dai ai gidan baya cika idan matan gidan basu kammalu ba baki daya don Allah daddy tunda kayi hakkuri da Zulfa ta dawo itama Niima ai mata hakkuri ta dawo haka ai yanzu sun horu ko sosai.
Wani irin kallon yai min tare da fadin wai ke rahama wata irin yarinya ce mara zuciya haka duk abinda matan nan sukai maki baki gani ba sai wani rawan kai kike wai su dawo dakin su.
Halin su na nan ba wai sun canza bane don haka ita zulfa zan yi dubaiyya akan zumuncin da diyan dake tsakanina da ita ne kawai amma ita wanan da kike magana yanzi fada min riban da na samu a cikin auren ta dana yi.
Dama kaddaran aure ne kawai dake tsakanina da ita yanzu kuma Allah ya kawo min saukin bacin ran da nake zaman yi da zama da ita.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[5/7, 10:34] Ummin Meenat: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON ONLINE NOVEL NE, , , ,


Kafin wani lokaci gidan ya fara cika da jama, a masu zuwa buki don haka banda wani lokacin kaina don yawan jamaan da suka taru.
Daddy bai shigo ba tun fitan da yayi da safe muna tare da su zulfa sai ga hindatu ta shigo tana fadin waiko kin san Zulfa zata dawo gidan nan kuwa?
Don ga ya can naga an bude part din ta ana ta gyara tundazun kinga namiji ko munafuki dubi yadda yake tayar da jijiyoyin wuyan shi a baya amma ashe har sun shirya ba wanda ya sani.
A raina nace gaji kishiya ko nice ma haka zatai bakin ciki da dawowa na gidan sai dai a fili murmushi nayi nace da ita kin sai ai tsakanin miji da mata dama sai Allah.
Balle su da suke yan uwa kin san dama ai da wuya su rabu ko ba iyali a tsakanin su balle ga iyali a tsakiya.
Tace ke dai dama munafuncin maza ba karewa yake ba shiyasa na dawo daga rakiyan namiji yanzu indai bai shiga gona naba yaje can yai tayi balle na miji irin namu mai son tara iyali haka da yawa in bashi ba mu biyun nan ma bamu isheshi ba don Allah dai ?
Mamaki ta sake bani nace da ita kai maman ihisan ke nan da wani zance a tare fa muka samay su duk dake da ita ba wani tsaraiyya a tsakanin ku.
Amma nikan ko ajikina idan ma wasu zai karo basu zasu dawo ba duk daya a gare ni tai min kallon mamaki don jin abinda na fada mata.
Tace haka dama zaki ce ai na sani don ke kin iya boye abu a zuciyar ki ba irin mu bane masu fitarwa duniya ta sani.
Dariya ta bani nace to yanzu da ace na saka a raina wa aka bari a cikin zancen don haka kinga ai gara dai mutum ya tsaya a matsayin sa kamar yadda kika ce yanzu.
Nifa ban sa akai balle nauyin zancen ya damay ni a zuciya tace ai kin huta wa ran ki wallahi yanzu haka zata dawo babu ko kunya a idon ta.
Mamaki tabani nace a raina lallai manya sunyi gaskiya laifi tudune ka take naka ka hangi na wani ke nan ita ta manta da lokacin nata harda sakin ?
Ta mike har ta fara tafiya ta juyo tana fadin yanzu kuma nasan ita ma wanan fitsararar itama dawowa zatayi ke nan ko ?
Ai dai yanzu mai daki shiyasan inda ruwa ke mai yoyo don shi ke da kayan shi ba wani ba in dai mutum ya shiga gonar ka shine ba zaka kyale ba.
Tace ke ai zaki iya sai ankai inta,ha zaki tankawa mutum amma nikan gaskiya yanzu da sake sosai a wurina wallahi.
Allah dai ya sauwaka nace da ita ina murmushi bata fahinci komai daga wuri na ba ta fice tana bakar magana da akan mijinta da matan shi.
Daddy bai iya shigowa wurin na ba don jama, a da sukai yawa a gidan don haka na shirya mai dan abin tabawa na samay shi dashi a wurin shi.
Kamar kullun yana zaune yana fama da laptop a gaban shi na shigo da sallama dauke da kayan abinci na dire a kasa gaban shi sai dana aje na samu wuri nai mashi sannu da zuwa.
Ya dago kai ya dan kalle ni yana fadin ashe kin san na shigo nace dashi yara ke fada min don dazun na tambaye su suka ce dani baka dawo ba.
Gidan naku ne naga ya cika da jama, a ko ba zan iya shiga wurin ku ba nace aikuwa mata ne dam a gidan namu.
Dama ku ai buki ne harkan ku a taru ana gulman kayan jikin ko wace da ta saka ba wani abin yi sai wanan din.
Dariya nayi na gyara zamana ina fadin ga abin tabawa nan ka dan taba ko kadan ne baiki ba naga ya ture kayan da yake aiki dasu a gefe daya.
Ya sauko don ya fara cin abincin dana kawo mashi din ganin haka yasa nai saurin saukowa daga kujeran na fara zuba mai a plate.
Ina gap da gama zuba mai ne naji yana cewa naga wurin Zulfa a bude mana ko yau ne zata dawo din ?
Murmushi nayi nace yallabai ai kai zan tanbaya wanan don kai ne mai yuka a hannu a gidan.
Don nima a wurin hindatu nake ji wai taga ana gyaran wurin Zulfa din yai murmushi yana cewa daidai yana daukan spoon a hannun shi.
Ashe shiyasa naga tana shan toka a fuskan ta da na shigo gidan wanan ne dalilin nata ashe ?
Murmushi nayi kawai ya fara cin abinci nace dashi ita Niima fa daddy yaushe zata dawo gidan don yakamata ai mata hakkuri itama.
Dakatawa yayi daga kai abincin da ya diba zai kai bakin shi tare da watso min Wani irin kallo yana fadin waike Rahama wani irin zuciya ne gare ki haka ?
To kiji bana son jin zancen yarinyar nan daga yau a gidan nan don nike zama da ita ba wani ba, har yakai spoon din kamar zai dibi abincin ya sake cewa dani wai ke yanzu don rashin zuciya irin naki har zaki ce wai yarinyar nan ta dawo gidan nan da zama ?
Wai kin san ko wacece Niiman da kike magana a kanta ni nasan irin hakkurin da nayi da zama da yarinyar nan a gidan nan don bana son mutum mai zalama da yawan korafi.
Ya debi abincin ya kai bakin shi tare da kada kan shi yace hakkuri nayi dama don bana son wani abinda zai hada ta da wani har yakai mu ga samun sabani da ita.
Kinga hakkurina yaci akan diyana zata iya kallon idona tace wai na fifita su da ita ita har yaushe ta shigo gidan da zata iya fada min hakan.
Ko ku dake gidan yau akwai wacce ta isa tace don may zanwa yarana gata da nai niyar yi ita kuma wanan munafukar har da biye mata su zauna suna wanan irin maganan haka ?
Ko ita taci albarkacin iyayye da diyan ta ne a gare ni da duk wani makircin ku na bani hakkuri haka ba zai taba tasiri a kaina ba.
Nace cikin marairai cewa daddy mu mata sai hakkuri yanzu ai ta gane kuren ta ba dadi ne ace anyi aure ko shekara ba a kaiba an rabu.
Yace ke za a zaga ko ni Rahama zama da wanan yarinyar mai jiran cin gado na nagama shi don dama ni nasan abinda nake zama dashi ba wani ba.
A daiyi hakkuri daddyn mu ai mata afuwan hakana har ta sake bai tankani ba yaci gaba da cin abincin shi ba tare da yai wani magana ba kuma.
Can ina dai zaune shiru naji yace dani mutanen gidan su Saade sun shigo kuwa gidan nan don naji suna korafi wai ba akai masu Amira din ba wurin su.
Nace suna da gaskiya ai daddy shiyasa nace dakai tun zuwan mu a bari taje ta dan kwana masu biyu can su gan ta.
Sai daya kurba ruwan dake aje a gefen shi cikin cup yace dani, wurin wa kike ganin zan iya turata cikin su ?
Mutanen da suka nuna basu ma san da zaman yaran ba a duniya wa kika taba gani ya wanko kafan shi yazo gidan nan da sunan yazo duba su cikin su.
Nace wanan kuma ruwan su ai tunda sune sukai watsi da zumunci don basu san falalan shi ba su da basu bar diyan yar uwar su data bari a duniya ba sun yi watsi dasu don wata manufa dake gare su.
Yace wani manufa ina dai kan su rike ita Amira din ne nikuma sun san ba yarda zanyi da hakan ba itace ma dai ba yar goyo ba.
Don ba don ke ba waye zai iya rike ta irin yadda taso mayar da kan ta a baya abin ya damay ni sosai a lokacin ban da yadda zanyi ne kawai idan nagan ta a lokacin.
Ba laifin ta bane nace dashi akwai kurciya da kuma zugi ana fada mata maganganun da ba zasu fisheta ba ita a ganin ta ta dauka so ne.
Yanzu ai ta gane gaskiya ita da bakinta ranan naji suna hira da mama Altine irin maganganun da sukai ta fada mata ba don Allah ya gyara ba ai lalata suka so yi kawai.
Amma shi yaro ina yasan wanan irin raayin da sukai ta koya mata kan taki ubanta da yan uwan ta.
Nifa shiyasa Nasir da jinior har gobe nake son rayuwan su don tun uwar su na raye basu taba nuna min ko diyana wani banbanci ba dama shi da namiji haka rayuwan shi yake sai kalilan ne ake samu da wani halin na daban.
Bar ni dasu ai zasu sha mamakina don koda ita marigayiyar take a raye may suka mayar da ita a cikin su in ba suna son abin hannun ta ba zasu zagayo ta.
Daddy ba zamu bi ta nasu ba azama daya zan kaita anjima idan an gama kamu sai ta kwana a wurin su zuwa gobe ko jibi ta dawo kaga ai an dai wuce wurin ba shike nan ba.
Yace idan kinga hakan ba matsala shike nan amma ni naso ne kawai a share su, nace kada ku zama daya dasu daddy bari dai kawai nakaita da dare gidan anty Amina sai gobe kuma na tura taje can babban gidan ta wuni masu.
Yace yayi idan ba zai kawo matsala ba nace insha Allahu ba komai shigowan hindatu falon ya dan katse hiran da mukeyi taje cewa ashe kina nan ne nace da ita eh kawai.
Na fara tattara kayan da yaci abincin don na basu wuri sai naji tace ashe yau zulfa zata dawo gidan shine ba a fada muna ba.
Hindatu kina da hankali kuwa ko kuwa raini ne ya kawo hakan tsakanin mu matana don zata dawo zaki ce wai sai na fada maki ke lokacin da kika tafi wana fadawa cewa zaki dawo gidan.
Ko akwai wace ta biya min sadakin wata a cikin ku ne fice min daga falin yar rainin wayon banza kawai.
Ni dai ficewa nayi ina jin yadda yake zagin ta a raina nace wanan kuma ta daukowa kan ta wani sabon fitina a zaune kalau.
Na koma na samu wasu bakin sun shigo gidan nan muka baje ana hira su Zarah na ta faman shirin buki da za ayi da karfe biyar na yamma ranan.
Mun kai wani lokaci sai ga su anty Amina da anty maryam sun shigo nan muka tare su a cikin mutunci na sa Gajiye ta kawo masu abin tabawa.
Barshi inji maryam ta fada cikin rashin damuwa nace a dai kawo masu su taba anty Amina yau fa a gidan ki Amira zata kwana nace da ita.
Tace cikin ya tsune fuska ai mu darajan mu bai kai ace za a kawo muna yar mu gare mu ba don yanzu kin fi iko da ita ai.
Nace haba anty nina isa don dai kawai bamu kusa ne kin san aikina ba lokaci ke gare shi ba ita kuma Amiran tana karatune kun sani.
Yanzu dai bashi ba mun zo ne muji abinda ake ciki tunda mu matsayin mu baikai na anemay mu ba mu san komai akai.
Mun ga idan mun kyale ki zakiyi muna rufarufa ba zurfine ki rubda ciki ga komai don kina ganin kin fi kowa wayau.
Nace haba dai anty may yai zafi haka kuma ai abin baikai can ba duk abinda ake ciki ina kiran anty Asamau na fada mata komai balle ni ai komai shiya saya da kan shi ya kuma tura a gyara mata dakin ta can bauchi.
Bakaji ba ina ruwan an haifa maki jari ashe har jere kin saka ai mata bamu sani ba mu inji anty maryam ?
Tace anty ai saiki tashi mu tafi don wanan ta riga da ta mamaye komai ba komai zamu gane ba sai dai shi may gidan ya kamata mu gani.
Sai dai ki sani duk cin amanan da kikewa yaran nan a kunnuwar mu yake in zalunci abinyi ne sai ki hau ki zauna ga yaran nan kinwa uwar su ma data kafaki balle mu din.
Wasu hawaye ne suka zubo min nace cikin kuka hab??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a anty maryam ban taba zaton irin wanan sakamakon a gareku ba wallahi.
Muryan Zarah ne naji tana fadin may ye na kuka a nan doctor da har zaki tsaya kina zubar da hawayen ki ga banza diyan da aka bari ai ba a ke kadai aka bari ba.
Wa ya nuna nashine har yasan da zaman su a gun ki sai yanzu ne da ake ganin sun zama mutane aka san dasu ko may da za a zo ana fadawa mutane wani magana can mara tushe.
Ke kuma a suwa wai wakike a cikin maganan ko karan kada miya baki kai ba ga zancen nan don haka ki ja bakin ki kiyi shiru ga maganan nan.
Aikuwa nan fada ya tashi a tsakani sai ga suwaiba ta fito daga daki itama ta saka baki aja su aja su anty Amina din fada suke sosai da gori a tsakanin su.
Sai ga Amira ta fito da abokan ta don jin hayaniyar da yai yawa tana ganin ina kuka ta nufe ni bata nufe su ba tana fadin.
Mummy may ya samay ki may my ya faru hakane kuma ina dazun nan kike cewa zan tafi gidan su na kwana.
Sai nace ba komai Amira ina share hawayen dake fuskana ba komai kamar ya uwayen ki ne sukazo suna zargin ta wai ta kakace komai ta hana su shiga har kan bukin ki inji suwaibana take fadin hakana a hasale.
Kamar ya ta daga kai tana kallon inda suke tsaye suna fada take cewa dama wa ake son yai min wani abu bayan mummy ina da wata uwace data fi min mummy ne yanzu.
Nifa yanzu ba zan yarda ba don yanzu ba irin da bane da ake fadawa mutum magana yana yarda amma may mummy ta rage mu dashi a duniya ni da yan uwa na ?
Ke rufa muna baki shanyayun banza kawai daku da uban naku duk an shanye ku baku dana fadi a kan ku.
Duk dukiyar uwar ku da ta bar mai an handamay wama ya sani ko yanzu babu komai da ya saura gare ku.
Haba mama Amina wanan bai dace ba gaskiya kudin dama kuke magana ai ba a hannun ta yake ba kuje ku samu daddy mana shi da komai ke gurin shi amma za a zo a saka mum a gaba da wanan magana haka ?
Kai kai wai may ke faruwa haka ne a nan anyi taron arziki za a kawo muna fitina kuma ana zaune kalau wai may ke faruwa ne wai ?
Gasu nan gara dai da ka shigo don wannan abin baiyi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login