Showing 54001 words to 57000 words out of 100637 words

Chapter 19 - Exiled Prince Book Two Complete Hausa Novel

24 Oct 2025

211

Tesnim "

a hankali ta daga kafa ta karaso geffen shi ta zauna ta na sunkuyar da kai
ta na haka kawai ta ji ya sa hannu ya rungumo ta ya na fadin " i'm sorry "

nan take kuka ya kubce mata ta kankame shi da kyau
dan bubuga bayan ta ya yi ya na fadin " shikenan ya isa haka , ki daina kukan nan mana "
cikin kukan nata ta ke fadin " Akhie , yanzu Daddy ya tafi ya bar ni "
" please ki daina kukan nan , ba ga ni ba "

a hankali ta dago da ga jikin shi ta ce " bayan ka kyale ni , tun lokacin da yarinyar nan ta shigo gidan nan ka daina kula ni , kullum ka na tare da ita ka manta da ni "

hannu ya kai ya riko kunnuwan shi ya ce " i'm sorry , ki daina kukan nan kin ji my sister "
rage sautin kukan ta ta yi ta na cewa " ni ka kyale ni "
" me ki ke so na yi , ki hakura ki daina kukan nan "

" ni ka daina kula yarinyar nan ba na son ganin ka tare da ita , na fa girme mata " ta fada cikin shagwaba

a hankali ya kai hannu ya janyo ta ya nuna mata Inaya ya ce " kin gan ta ko ? She is my wife , dan haka ba ki girme ta ba , ita ce ta girme ki tun da ta na auren Big bro din ki "

turo dan bakin ta Tesnim ta yi kafin ta ce " yanzu Akhie wannan yarinyar ita matar ka , ga Rouksar nan why ba za ka aure ta ba , sai wannan yarinyar da ko period ma na san ba ta fara ba , saboda ita ka daina kula ni , tun ranar da ka dawo masarautar nan ba ka sake nema ta ba "

hannu ya kai ya ja mata kumatu ya ce " za mu saka kafar wando guda da ke , idan ki ka ce za ki takura mata kin ji dai na fada miki "

shagwabe fuska ta yi ta na fadin " yanzu Akhie saboda wannan yarinyar za mu bata "
" ni dai ban ce za mu bata ba , amma zan so ki ba ta matsayin ta , nan gaba kadan za ta zama MALIKAT din ku , zan so a ce akwai jituwa tsakanin ku , please ki yi min wannan abun kade "

a hankali ta mike zaune ta na kallon shi ta ce " Akhie , ni gaskia ba na so , Ka fi kowa sanin ba na son raini , idan ta ce za ta raina ni wlh ba ruwa na da matar ka ce , dukan mutuwa zan yi mata "

" oh , kin iya Dukan mutuwa kenan , shikenan nan gaba kadan ke ma zan miki auren na huta "

bushewa da dariya Tesnim ta yi ta na fadin " Aure ni kuma ? Hum "
" kin zata da wassa na ke , ni fa har na samo miki miji , ki jira ki gani "
dan zaro idanu ta yi ta na shirin magana ta juyo Muryar Inaya ta na fadin " zancen me ku ke yi "

a tare Amir da Tesnim su ka juyo su ka kale ta , ta na konce idanun ta a lumshe
juyo wa Tesnim ta yi ta kali Amir ta ce " Akhie ni fa ta ban tsoro , barci ta ke fa "
dawo da kallon shi ya yi kan Tesnim ya ce " ni kai na wani lokacin tsoro ta ke ba ni "

yar karamar dariya Tesnim ta yi , ta na shirin magana kawai ta ga an tilo wani pillow ya bugi face din Amir

a razane su ka juya shi da ita su na kallon Inaya , har yanzu dai ta na konce , amma idanun ta su na bude , ta turo dan bakin nan nata

matse gera Amir ya yi ya na fadin " Ni za ki tillo ma wannan abun "
a hankali Inaya ta mike zaune ta na yi mishi hararrar wassa ta ce " ba kai ne ka ce ina ba ka tsoro ba " ta fada da hausa

dan zaro idanu ya yi ya na fadin " kin ji abun da mu ke magana a kai ? "
dan karamin murmushi ta yi ta na gyada mishi kai
" kennan ba barci ki ke ba ? "
murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce " ai ku ku ka tashe ni "
[26/09 à 10:33] MIMI:



❤⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❤


(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥




💔🥀 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) 💔🥀





👑❤ MALLAKIN MEERAH ❤👑



【THE ROYALTY LOVE 👑🕊💖】




Marubuciyar littafin

【TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺】





【 BOOK …………………… 2 ❤ 👑】





____________________🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊___________________





PAGE 17 ✍📚




bai ce mata komai ba ya mika mata hannu a kan ta zo
ba musu ta taso da sauri ta riko hannun shi ta na murmushi ta fada jikin shi ta rungume shi

rungume ta shi ma ya yi ya na cewa " ki na jin yunwa ? "
girgiza mishi kai ta yi allamun a'a
" shikenan tashi ku tafi ke da Tesnim , yau tare da ita za ki zama "

a hankali ta dago da ga jikin shi ta na kallon face din shi ta ce " wacece Tesnim ? "
juyawa ya yi ya kali Tesnim da ta tsare su da ido ta na sakin murmushi
a hankali ita ma Inaya ta juya ta kali Tesnim , sai ta sakin mata wani dan karamin murmushi ba tare da ta ce komai ba

mika ma Tesnim hannu ya yi
ba musu ta aza hannun ta saman nashi ,
a hankali ya ja hannun Inaya ya daura shi a sama , sannan ya ce ma Tesnim " na bar miki amanar ta , ki kula da ita yau "
ya na gama fadar haka ya juya ya kali Inaya ya ce " Cutie tashi ku tafi , ina da aikin yi yanzu "

a hankali ta gyada mishi kai kafin ta ce " amma za ka zo in ka ida ko ? "
a hankali shi ma ya gyada mata kai allamun eh

wani cool murmushi ta saki kafin ta mike tsaye ta na rike da hannun Tesnim ta ce " Aunty tashi mu tafi "
ba musu ita ma ta Tesnim ta mike tsaye ta na rike da hannun Inaya , ta ce wa Amir " Sai an jima "
ta kai karshen ta na juyawa ta fara takawa , Inaya na geffen ta su na rike da hannun juna kamar yaya da kanwar ta

da kallo ya raka su har sai da su ka bar wajen sannan ya tashi ya dauki wayar shi ya nufi corridor ya shiga bedroom din shi

bangaran su Inaya kuma , bayan sun baro part din Amir kai tsaye part din MALIKAT AL'UMU su ka nufa

bakin su da Sallama su ka shigo parlourn MALIKAT AL'UMU , ta na zaune ita da Rouksar babu me ce ma wani ufan

MALIKAT AL'UMU na ganin Inaya ta saki wani kyawatencen murmushi ta ce " Tesnim ina kuma ki ka gamo da ita "

dan karamin murmushi Tesnim ta yi ta na karasowa cikin parlourn ta zauna saman sofa , sannan ta janyo Inaya ta zauna geffen ta , ta ce wa MALIKAT AL'UMU " Amir ya ce na taho da ita "

mika mata hannu MALIKAT AL'UMU ta yi
ba musu ta saki hannun Tesnim ta mike ta nufi MALIKAT AL'UMU ta riko hannun ta sannan ta zauna geffen ta , ta na sakin murmushi

"Allah ya sa dai yaron nawa ba ya takura miki ? " MALIKAT AL'UMU ta fada ta na kai hannu ta shafi kan Inaya

cikin ko in kula Inaya ta ce " Ammie , wane yaron kuma ? "
yar karamar dariya MALIKAT AL'UMU ta yi kafin ta sunkuyo da kai , ta kai bakin ta saitin kunnen Inaya ta yi mata rada

ni dai ban ji abun da ta rada mata ba kawai ganin na yi Inaya ta bushe da dariya
mikewa tsaye MALIKAT AL'UMU ta yi ta riko hannun Inaya ta na fadin " taso mu je "
da sauri Tesnim ta ce " momy ina kuma za ki je ? "
ba tare da Ta juyo ba ta ce " idon matambayi " ta kai karshen ta na shiga corridor

wata yar karamar dariya Tesnim ta yi kafin ta mike tsaye
da sauri Rouksar ta riko hannun ta , ta na fadin " Tes wai wacece yarinyar nan , na ga kowa sai daukar ta da sauke ta ya ke "

Tesnim na shirin magana ta jiyo Muryar MALIKAT AL'UMU ta na cewa" Tesnim ! "
kwace hannun ta , Tesnim ta yi ta nufi corridor din ta bar Rouksar nan

kai tsaye bedroom din MALIKAT AL'UMU ta nufa , bakin ta da sallama ta shigo dakin
Inaya na zaune bakin gadon MALIKAT AL'UMU

" ina momy ? " Tesnim ta tambayi Inaya
da yatsa ta nuna mata kofar Toilet ba tare da ta ce komai ba
a hankali Tesnim ta daga kafa ta nufi toilet , har ta kai bakin kofar sai ga MALIKAT AL'UMU ta fito

" yawwa Dauko min box din Turaren nan da ke dakin ki " ta kai karshen ta na rabawa ta geffen ta ta wuce ta nufi Inaya

Tesnim kuwa ta juya ta fice dakin , ta koma dakin ta
" baby taso mu tafi " MALIKAT AL'UMU ta fada , ta na mika mata hannu
ba musu ta riko hannun MALIKAT AL'UMU ta mike tsaye su ka nufi Toilet a tare
sai da su ka shiga sannan ta dauki wani towel fari ta mikawa Inaya ta ce " cire kayan ki "

ba musu Inaya ta cire rigar jikin ta , da underwear ko kunyar MALIKAT AL'UMU ba ta ji ba ta daura towel din a kirjin ta
dai'dai lokacin da Tesnim ta shigo Toilet din ta na rike da wani box navy blue mai mugun kyau , ta mikawa MALIKAT AL'UMU sannan ta juya da sauri ta fice dan lokacin sallat ya yi

bude box din nan MALIKAT AL'UMU ta yi , nan take wani dadaden kamshi ya tashi ya gwauraye duk toilet din
Ajiye box din ta yi bakin bath ta dauki wata kwalbar Fara fes ta bude ta zuba turaren a cikin ruwan bath din
sannan ta rufe , sai da ta zuba kalar turare har biyar sannan ta mike ta ce ma Inaya ta shiga cikin ruwan ta yi wanka , sannan ta yo Alwalla ta fito
da to Inaya ta amsa mata sannan ta nufi bath din , MALIKAT AL'UMU kuma ta fito toilet din

Bayan wani dan lokacin Inaya ta fito da ga cikin Toilet din , sai tashin kamshi ta ke mai dadi
ta na fitowa MALIKAT AL'UMU ta mike ta na murmushi ta mikawa Inaya wata Abaya pink color , da wasu underwear da Tesnim ta je part din MALIKAT INAS ta dauko mata dan nata ba za su shige ta ba

ba musu Inaya ta karbi kayan , gaban idon MALIKAT AL'UMU ta tsaya ta saka kayan ko kunyar ta ba ta ji ba a matsayin ta na sirikar ta , haka Zalika MALIKAT AL'UMU ko a jikin ta , dan Inaya ta sake kaya gaban , Amir da kan shi ya sauya kaya gaban ta bare Inaya

ta na kallon ta har ta Kamala saka kayan ta sannan ta ce " Sai ki yi sallat , yanzu ina zuwa kin ji ? "
da to Inaya ta amsa mata , Sannan ta nufi daddumar da ta gani shinfide gaban gadon ta Haye , MALIKAT AL'UMU kuma ta nufi kofar dakin ta fice

Jim kadan ta dawo cikin dakin ta na rike da wani tray , ta nufi Table din da ke gaban sofar dakin ta ajiye sannan ta zauna saman sofar ta na kallon Inaya da ke zaune saman daddumar , ta daga hannayan ta sama ta na jero adu'a
a haka Tesnim ta shigo dakin ta na sallama , ta zauna bakin gadon ta na kallon Inaya ita ma

sai da su ka share wajen good ten minutes a haka kafin Inaya ta shafa adu'ar ta
MALIKAT AL'UMU na shirin magana Tesnim ta riga ta cewa " wannan Adu'ar duk ta mallakar zuciyar Dan uwan nawa ce ? " ta fada cikin zolaya

" to , malama ina ruwan ki da adu'ar ta " MALIKAT AL'UMU ta fada ta na yi wa Tesnim hararrar wassa

murmushi mai dan sauti Inaya ta yi kafin ta ce " Ni Abbana na yi wa adu'a , kullum in na yi sallat sai na yi mishi adu'a , ina rokar mishi rahamar ubangiji "

a hankali Tesnim ta dago kai ta kali MALIKAT AL'UMU da ke kallon ta ita ma
cikin sanyin murya MALIKAT AL'UMU ta ce ma Inaya " Ki na nufin Mahaifin ki ya...... "

cikin nitsuwa Inaya ta katse ta da cewa " ya rasu , sati biyu kafin mu dawo nan tare da yaya Zayd "

a hankali Tesnim ta mike ta dawo gaban Inaya ta zauna ta kai hannu ta riko hannayan ta dukka biyu cikin sanyin murya ta ce " ki yi hakuri kin ji , Allah ya jikan shi ya yi mishi rahama "

yar karamar Dariya Inaya ta yi kafin ta ce " Aunty ki daina ba ni hakuri , ni fa Abba na bai mutu ba , kullum ya na tare da ni cikin zuciya , mutanan da mu ka daina tunanin su ne kawai su ke mutuwa a wajen mu , amma ni kullum ina tunanin shi , shi ya sa ba na kewar shi sosai saboda kullum ya na tare da ni a nan " ta kai karshen ta na nuna saitin zuciyar ta

dan karamin murmushi geffen fuska Tesnim ta yi ta na sunkuyar da kai ta ce " ni kuma ina kewar nawa sosai duk da bai yi kwana biyu ba da ya tafi ya bar ni , ji na ke kamar na yi shekaru ba na tare da shi "

cikin rudu Inaya ta ce mata " uncle ba tare da Amir ya dawo ba ? "
dago kai Tesnim ta yi ta kali Inaya ta girgiza mata kai a hankali ta ce " a'a bai dawo ba , ya tafi inda Daddyn ki ya tafi , ya tafi har abada , ba zan sake ganin shi ba " ta kai karshen kamar za ta yi kuka

cak Inaya ta tsaya ta na zaro idanu ta na kallon Tesnim " Hakan na nufin Uncle ya rasu ? , kuma yaya Zayd bai fada min ba , Shi ya sa Ammie da Aunty RIANNA su ka ce na je wajen shi ya fi bukata ta ? " ta fada cikin Zuciyar ta hawaye na zubo mata

da sauri MALIKAT AL'UMU ta ce musu " ya isa haka , adu'a ya kamata ku yi musu , ba kuka za ku yi ba , please ku daina kukan nan kun ji , ku taso ku ci abincin nan tun bai yi sanyi ba "

a hankali Inaya ta dawo cikin hayacin ta , ta kai hannu ta goge hawayen ta , sannan ta goge wa Tesnim nata , ta saki wani dan karamin murmushi ta ce " Tashi mu tafi kin ji , ki daina kukan nan , na san uncle ba zai ji dadin ganin ki , ki na wannan kukan ba , ki daina don Allah , in ki na kuka fa ba ki yin kyau " ta fada cikin zolaya wai ta rama abun da Amir ya yi mata da safe

yar karamar dariya Tesnim ta yi ta na fadin " Shikenan na daina " ta kai karshen ta na mikewa tsaye , ta mikawa Inaya hannu
a hankali Inaya ta riko hannun Tesnim ta mike tsaye su ka nufi MALIKAT AL'UMU , su ka zauna saman sofar , su ka saka Inaya a tsakiya

su na zama MALIKAT AL'UMU ta kai hannu ta kai hannu ta bude mata plate din Abincin , ta dauki spoon ta fara bawa Inaya da kan ta
sai da Inaya ta koshi sannan ta daina ta dauki ruwa ta ba ta ta sha
sannan na ga ta dauki wani mug ta bawa Inaya , ni dai ban san mi ke cikin mug din nan ba gaskia , kawai ganin Inaya ta yi ta daga kai sama ta shanye abun da ke cikin mug din sannan ta sauko da kan ta

yar karamar dariya MALIKAT AL'UMU ta yi kafin ta kai hannu ta dauki wani bowl da ke rufe , ta bude shi ta dauki wata yar karamar spoon ta sa a ciki sannan ta mikawa Inaya bowl din
ba musu ta kai hannu ta karba , ta na kallon Abun da ke ciki , Inibi ne da coconut , da dabino cikin zuma ,

daukar tray din Gaban su MALIKAT AL'UMU ta yi ta mike tsaye ta na fadin " ki ci , sai ki tashi ki konta ki huta kin ji "

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login