Showing 78001 words to 81000 words out of 100637 words

Chapter 27 - Exiled Prince Book Two Complete Hausa Novel

24 Oct 2025

201

wannan shawarar ta Malik ce kadai , ba wanda ke da izinin fitar mishi da matar da zai aura "

cikin nitsuwa Rafik ya katse shi da cewa " amma ranka shi dade ka sani bisa tsarin masarautar nan a rana daya a ke nada Malik da MALIKAT "

gyada mishi kai Diya ya yi kafin ya ce " mai girma Rafik mun sani baki daya , kun san a ka ce sabon sarki , sabon zamani , wannan tsarin Malik ya kawo shi , to Malik Nawfel ya sauya shi "

da sauri Miram ya mike ya ce " amma haka al'adar masarautar nan ta ke , ta ya za a ce rana guda an sauya ta "

kafin Diya ya yi magana RIANNA ta mike ta ce " cikin dukkan girmamawa Miram , zamani sauyawa ya ke , kamar yadda al'ada ke sauyawa , Idan har Malik ya ce ba shi da ra'ayin nada MALIKAT a yau , babu wanda ya isa cikin mu ya matsa mishi yin abun da ba ya so , a gafarce ni idan na fadi ba dai'dai ba " ta na gama fadar haka ta koma ta zauna

ita dai Inaya da ido kawai ta ke bin su dan da larabci su ke magana ita kuma ba gane larabci ta ke ba

A hankali Malik ya yi gyaran Murya
da sauri Diya ya koma ya dan sunkuyar da kan shi , ya na sauraron Abun da Malik ke fada mishi

mikewa tsaye ya yi , ya tako a hankali gaban Rafik ya mika mishi hannaye allamun ya ba shi box din
ba musu Rafik ya daura Box din saman hannayan Diya

juyawa ya yi ya ajiye box din saman table din Da Rafik ya ajiye kur'ani sannan ya karaso gaban Malik ya tsaya ya juya ya kali Rafik ya ce mishi " za ka iya komawa ka zauna "

ba musu Rafik ya koma ya zauna saman sofar shi
ya na zama Diya ya ce " kamar yadda Gimbiya RIANNA ta fada , zamani ya kan sauya tare da al'adun shi , Haka zalika Mulkin Malik Nawfel zai zo da nashi zamanin , da ga yau za mu kawo canji a cikin wannan masarautar , da ga yau mun janye dokar da ke cewa Rana guda za a nada Malik da MALIKAT , amma Malik ya yarda zai nada MALIKAT da hannayan shi ba na wani ba yanzu ba sai an jima ba "
nan take duk fadar su ka shiga yin hamdalah kowa ya saki murmushi

slowly Diya ya juya ya kali Malik
gyada mishi kai kawai Malik ya yi a hankali ba tare da ya ce komai ba

wani cool murmushi Diya ya saki kafin ya sauke ajiyar zuciya ya fara takawa a hankali ya nufi bangaran mata

kai tsaye wajen Inaya ya nufa , ya mika mata hannu ya na murmushi ya ce mata " baby tasso mu tafi " ya fada da hausa

cikin rudu Inaya ta ce mishi " yaya Moussa ina kuma za mu tafi ? "

girgiza mata kai kawai ya yi ya na murmushi ya ce mata " kar ki damu baby , ke dai tasso mu tafi duk abun da zai faru kar ki yi magana kin ji ko ? "

wani cool murmushi ta saki ta gyada mishi kai sannan ta daura hannun ta saman nashi , ta mike a hankali

a tare su ka fara takawa , har su ka karaso gaban Malik sannan ya saki hannun ta ya ce mata " yi kneel down "

ba musu ta Zube saman guyiwowin ta ta na kallon Malik fuskar ta cike da allamun tambaya

ta na tsugunawa Diya ya dauki yar box din nan ya bude ta

da sauri Mohammed ya ce " ranka shi dade ba dai yarinyar nan za a nada a matsayin MALIKAT ba , she is too small "

Malik bai ce mishi komai ba ya mike tsaye a hankali
da sauri duk mutanan wajen su ka mike tsaye

hannu Malik ya kai ya cire Alkyabar da ke jikin Inaya ya mikawa Diya
ya kai hannu ya fido Alkyabar da ke cikin box din da Diya ke rikeda

wata dankareriar Alkyaba ce , fara kal ta auduga , da ga gani wannan sakar ta hannu ce , musaman Zaren da a ka yi wa Alkyabar zane na gold ne , sai tashin qamshi ta ke yi

bai tsaya bata lokaci ba ya daurawa Inaya ita , ya saka mata hular , sannan ya mika mata hannu
slowly ta dago kai ta kali hannun shi ta saki wani cool murmushi sannan ta daura nata a sama ta mike tsaye
a hankali ya dago hannun ya kai saitin bakin shi ya manna mata kiss har sai da ya dan lumshe idanun shi a hankali

a hankali ya janye hannun ta cikin harshen hausa ya ce mata " zauna "
ya kai karshen ya na janyo ta wajen Kujerar MALIKAT

har za ta zauna Mohammed ya ce " ranka shi dade haka bai dace ba , ba ta isa zama MALIKAT ba "

ya na gama rufe bakin shi Miram ya ce " Mai girma Rafik ka yi magana mana , wannan ba za ta iya kula da harkokin MALIKAT ba , wannan doll ya kamata mu samo mata ai , ko ba haka ba " ya kai karshen ya na juyawa ya kali sauran mazan

babu wanda ya ce mishi ufan , dan ba wanda zai iya jayaya da umarnin Malik bare kuma wannan da ga gani bai zo da wassa ba

" Ranka shi dade , kar ka manta ita ma MALIKAT ta na da hannu cikin al'amarin masarautar nan " Rafik ya fada
[02/10 à 08:12] MEERAH 🪷🩷:


❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥





( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )




STORY & WRITTEN BY : MEERAH 👑🔥







_________________________※※※※※___________________________




BOOK .....................2 ❤✍📚





♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡



P A G E 2 4 ✍ 📚




ba tare da ya juyo ba Malik ya ce " ba na son na kara jin muryar kowa a cikin wajen nan " ya fada da dan karfi
nan take kowa ya shiga tayi²n shi duk sai da su ka sunkuyar da kan su

ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce ma Inaya da ta tsare shi da idanu " Zauna cutie "
gyada mishi kai ta yi kafin ta zauna saman chair din a hankali ta na kallon shi, ta na zama shi ma Malik ya koma saman chair din shi ya zauna

ya na zama kowane ya koma saman sofar shi ya zauna
banda Hafsat da ta fice fadar da sauri

komawa Diya ya yi geffen Malik ya tsaya ya rike hannayan shi a baya a ya ce " za mu iya farawa "

ya na gama fadar haka General Abdallah ya mike ya karaso gaban Malik ya sara mishi sannan ya ce " ranka shi dade kamar yadda ka bada ubarni , mun kamo wanda ya harbi mai girma marigayi Malik "

a hankali Malik ya gyada kan shi , Allamun a kawo shi
dan sunkuyar da kai General ya yi kafin ya juya ya kali daya da ga cikin sojojin da ke tsatsaye cikin fadar

da sauri biyu da ga cikin su , su ka fice fadar da gudu

ba su wuce Five minutes ba , su ka dawo rike da wani saurayi da a shekaru ba zai wuce 24 years ba , ya na sanye da wasu kaya bakake an daure shi tsam kamar dauri goro

su ka karaso da shi geffen General su ka zubar da shi saman guyiwowin shi

kallon Malik General ya yi ya ce " Ga shi nan ranka shi dade , bisa bincike da mu ka yi , wannan shi ne Sniper din da ya harbi Malik "

kare mishi kallo da kyau Malik ya yi kafin ya juya ya kali Inaya ya kai dan bakin shi saitin kunnen ta ya rada mata " Cutie , kale shi da kyau , shi ne wanda ya kashe Abbi ? "

slowly Inaya ta juya ta kali saurayin nan da ga sama har kassa
sannan ta juya ta kali Malik ta ce " yaya Zayd , ba na ji wannan zai iya kashe mutum , sai dai idan matsa mishi a ka yi "

a hankali ya gyada kan shi kafin ya juya ya kali saurayin , shi ma haka ya ji cikin zuciyar shi , kamar wannan saurayin ba zai kashe mutum na haka kawai shi ya sa ya tambaye ta kuma ra'ayin su ya zo daya

kallon Diya ya yi , da sauri ya sunkuyo da kan shi Malik ya rada mishi " Ina son na yi bincike da kai na a kan wannan saurayin , ka ce a rufe shi kawai zan yanke mishi hukunci da ga baya "

gyada mishi kai kawai Diya ya yi kafin ya mike ya kali General ya ce " General za ku iya meda shi prison , Malik zai yi bincike da kan shi a kan wannan saurayin , sannan ku rage sasaucin daurin nan da ku ka yi mishi don Allah , sai ka ce mara imani "

yar karamar dariya General ya yi kafin ya juya ya kali sojojin da su ka kawo saurayin
ba musu su ka dauki saurayin su ka koma inda su ka fito
komawa General ya yi ya zauna saman sofar da ya taso

ya na zama Malik ya saki wani siririn Tsaki ya mike tsaye
da sauri su ma mutanan wajen su ka mike har da Inaya
bai ce musu komai ba ya fara takawa cike izza ya nufi kofar fita Fadar ya fice abun shi

ya na fita Rafik ya kali Diya ya ce " Diya , ya na ga kuma Malik ya tafi ba mu Kamala ba ? "

dan karamin murmushi Diya ya yi kafin ya ce " I'm sorry ina ga ba ya jin dadin jikin shi , in sha Allah gobe zai yanke shawara dan gane da sauran case din , yanzu kowa zai iya zuwa babban parlour domin wallimar da a ka shirya "

ya na gama fadar haka ya juya ya kali RIANNA
murmushi kawai ta yi kafin ta karaso ta rike hannun Inaya ta ce " mu tafi wajen momy ? "
gyada mata kai Inaya ta yi ta na murmushi kafin su fara takawa a hankali a tare su ka bar wajen

su na barin wajen Diya ya nufi Nesrine ya mika mata hannu ya ce " za mu iya tafiya madam ? "
dan karamin murmushi ta yi kafin ta daura hannun ta saman nashi , su ka fara takawa a tare su ka bar wajen
daya bayan daya duk mutanan fadar su ka watse



▪MALIK


Kai tsaye part din shi ya koma , duk inda ya wuce sai dogarai sun zube har kassa su na gaishe shi

bai bi ta kan gaisuwar su ba kai tsaye ya nufi building din shi , ya haye floor na uku , ya na isa parlour ya nufi chair din shi ta Gold ya haye ya zauna , ya zame hular Alkyabar shi , tare da rawanin ya tila shi saman sofa , ya jingina bayan shi a jikin chair din ya lumshe idanun shi

kamar da ga sama ya jiyo Muryar Diya ya na fadin " Al-Malik Nawfel bin Jaabar "

dan karamin tsaki Ya yi kafin ya bude idanun shi ya kali Diya da ke zaune geffen rawanin shi ya ce " lafiya ka biyo ni ? "

yar karamar dariya Diya ya yi kafin ya ce " ba komai Amir , oh Sorry ina nufin Malik "

tsaki Malik ya yi ya na kauda kai gefe
" yawwa na ce , wai me ya sa ka ce a kai yaron nan prison ba ka yanke mishi hukuncin kai tsaye ba , bayan bincike ya nuna shi ya kashe Uncle ? "

dan jinkirtawa Malik ya yi kafin ya ce " Gaskiya ba na ji a jiki na yaron nan zai iya kashe mutum haka kawai "

" ka na nufin cilas ta mishi a ka yi ? "

a hankali Malik ya gyada mishi kai kafin ya ce " shi ya sa na ce a rufe min shi , gobe zan je da kai na , na tambaye shi , Idan ma cilas ta mishi a ka yi zan gano da kai na "

" okay , yanzu tashi mu tafi wajen wallimar da a ka shirya maka "

lumshe idanun shi Malik ya yi murya cen kassan makoshi ya ce mishi " tashi ka tafi ni babu inda zan je "

yar karamar dariya Diya ya yi kafin ya ce " Why ? , kai fa a ka shirya wa , bai kamata a ce ba ka wajen "

" please Diya let me , ba na bukatar ganin kowa a yanzu "

" ko da kuwa MALIKAT Inaya ce ? " Diya ya fada ya na dan lekon face din Malik

Shiru ya yi bai ce mishi komai ba , dan duk duniya ita kadai ce yanzu ya ke son gani , tun bayan da ta Kamala period din ta yanzu wajen kwana biyar bai sake saka ta a idanun shi ba sai yau , yau din ma ba wani gani kirki ya yi mata ba , ga shi ta yi wani fresh ta kara haske , ta samu kula da ga wajen MALIKAT INAS da MALIKAT AL'UMU , fatar jikin ta ta yi wani laushi kamar ta baby , hannun ta kadai da ya taba ya ji wata muguwar sha'awar ta ta taso mishi dalilin da ya sa ma ya baro fadar ba shiri , dan kar mutanan wajen su lura ya na cikin sha'awa

ya yi nisa cikin tunanin shi kawai ya jiyo Muryar Diya ya bushe da dariya
dan karamin tsaki ya yi kafin ya ce mishi " wai minene abun da dariya , kai ba ka da aiki sai dai dariya "

tsagaita dariyar shi Diya ya yi kafin ya ce " ba dole na yi dariya ba , Bari zan je na fadawa Ammie a kawo maka matar ka tun yanzu ba sai dare ya yi ba , ko kuma na sa a kawo maka lemun tsami ? "

bai ce mishi komai ba ya mike cikin nitsuwa ya nufi corridor ya shige
da kallo Diya ya raka shi har sai da ya shiga sannan ya sake bushewa da dariya har da dafe ciki kafin ya tashi ya sauko Floor na farko , dan a nan ne a ka shirya wallimar



▪ROUKSAR


tsaye ta ke gaban Damba , da ke faman Dariya har wasu hawaye na zubo mishi
cike da bacin rai ta ce mishi " Damba don Allah ka daina wannan dariyar mu san abun yi "

tsagaita dariyar shi ya yi ya ce mata " Sai da na fada miki ki kashe yarinyar nan , amma ki ka tsaya wai sai an yi nadin Malik , dan ki na da tambacin ke zai nada a matsayin MALIKAT , to yanzu wa gari ya waya ? dan haka ki bar ni na yi dariya "

dan karamin tsaki Rouksar ta yi kafin ta ce " Damba , a sani na kai ma cewa ka yi kai ne Malik zai nada a matsayin na hannun daman shi , amma mi ya faru yanzu "

" Diya ya nadda a matsayin na hannun daman shi , amma kar ki manta wassan Mulkin Saudiya yanzu ya fara , ko shekara dubu zai dauka mulkin Saudiya sai ya dawo a tafin hannu na "

" yanzu Damba ya ka ke so mu yi , dan gaskiya ba zan iya kallon yarinyar nan ta zauna saman kujerar MALIKAT ba , yanzu kennan aura mishi ita za a yi ? "

wani murmushi mai dan sauti Damba ya yi kafin ya ce " wa ya sani may be matar shi ce tun farko , dalilin da ya sa ta ke makale mishi kennan "

a hankali Rouksar ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce " ko ba komai da sauki tunda ba wacen Hafsat a ka aura mishi ba , yar iskar yarinya tun kafin a yi auren ta dame ni da MALIKAT Hafsat , MALIKAT Hafsat , za ki ci uban ki ba MALIKAT Hafsat ba "

" kar ki manta , kin kashe maciji ne ba ki dare kan shi ba , ita wadda a ka nadda a matsayin MALIKAT ta fi karfin mu , idan har ki ka bari a ka kai ta part din Malik cikin daren nan , to tabass da ga ita har Malik sai dai kallo ba abun da za mu yi musu , cikin daren nan ki tabbatar kin kashe ta da poison din ki , Idan kuma mu ka yi sa'a Malik bai taba ta ba cikin daren nan , har yanzu da sauran damar mu "

wani makirin murmushi Rouksar ta saki kafin ta lumshe idanun ta , ta fara motsa lips kamar ta na magana

nan take duk jelar gashin ta ta koma green , duk ya koma kamar fatar maciji
a hankali fatar jikin ta ita ma ta fara komawa green wasu scale irin na maciji su ka fara fito mata saman Fuska
daya bayan daya jelar gashin ta , ta fara komawa manya manyan macizai , sai murkuso su ke yi su na fido harshen su waje su na wata kara abun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login