Showing 63001 words to 66000 words out of 100637 words

Chapter 22 - Exiled Prince Book Two Complete Hausa Novel

24 Oct 2025

207

ya ke yi da ita ? ni fa wlh idan ya ida ina so , kwana biyu ban taba ba " ya kai karshen ya na kashewa Mohamed ido guda

yar karamar dariya Mohammed ya yi ba tare da ya ce mishi komai ba , a haka har su ka baro part din Amir su ka tafi aikin gaban su


▪AMIR
[28/09 à 09:35] +234 806 127 3970:



❤⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❤


(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥




💔🥀 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) 💔🥀





👑❤ MALLAKIN MEERAH ❤👑



【THE ROYALTY LOVE 👑🕊💖】




Marubuciyar littafin

【TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺】





【 BOOK …………………… 2 ❤ 👑】





____________________🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊___________________




PAGE 19 ✍📚




▪AMIR




kai tsaye Bedroom din su ya koma da ita
bai dire ta ko ina ba sai tsakiyar dakin , ya sauke ta saman kafafun ta
ya na sauke ta , ta ce mishi " baby yunwa na ke ji " ta fada cikin shagwaba

ya na kokarin button din rigar ta ya ce " don't worry , yanzu za mu tafi yin breakfast tare da momy "

wani cool murmushi ta saki ta na fadin " da gaske baby ? "
gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya ce mata komai ba ya ci gaba da fida button din rigar ta , har sai da ya Kamala cire su , ya fida mata rigar , ya yi kassa da wandon ta ya fida mata ya meda ta naked
a hankali ya kai hannu ya dauki kayan , sannan ya dauke ta cancak ya nufi toilet da ita

ya na shiga ya sauke ta tsakiyar toilet din , ya nufi basket na laundry ya saka kayan , ya cire jallabiyar jikin shi ya saka cikin basket din , sannan ya nufi bath ya kunna fanfo ya fara tara musu ruwa

ita dai ta na tsaye ta na kallon shi , har sai da bath din ta cika da ruwa , ya ruba soap , da wasu turarrukan shi
sannan ya kai hannu ya riko short din shi , harr zai yin kassa da shi ya tuno ashe ba shi kadai ba ne , kar ta ji tsoron ganin shi naked yanzu ta birkice mishi

a haka ya janye hannayan shi ya juya ya kale ta
ta na tsaye inda ya bar ta , sai kallon shi ta ke ta na murmushi

bai mata komai ya tako gaban ta , ya sa hannu ya dauke ta cak , sannan ya koma wajen bath din ya saka ta a ciki , sannan ya bi bayan ta ya shiga cikin bath din
yar karamar dariya ta yi kafin ta kai hannu ta watsa mishi ruwan a fuska
dan lumshe idanun shi ya yi da sauri dan kar su shiga ciki ga shi kuma da soap a cikin ruwan

bai ce mata komai ba ya kai hannu ya janyo ta jikin shi , ya hannu ya fara yi mata wanka da kan shi kamar baby , har gashin ta sai da ya wanke mata
sai da ya Kamala yi mata wanka , sannan su ka fito da ga cikin Bath din , ya saka mata bathrobe ya ce ta jira shi a waje
ba musu ta fito toilet din , ta nufi dressing mirror ta bude box na farko , kamar ta sani ko ta fido hairdryer ta fara busar da gashin ta , ta nade shi a baya da wata pin ta sako wasu yan sirarren a gaban fuskar ta

shi kuma sai da ta fita sannan ya cire short din shi , ya yi wanka shi ma
jim kadan ya fito ya na sanye da bathrobe shi ma
nan ya isko ta zaune gaban dressing mirror
har zai wuce dressing room ya jiyo Muryar ta ta na fadin " ka tsaya na busar maka da gashin ka mana " ta fada ta na mikewa da ga saman chair din ta na rike da hairdryer

ba musu ya dawo ya zauna saman chair din ta ta fara busar mishi gashin shi , shi kuma ya na kallon ta , ta cikin mirror kamar zai cinye ta
har sai da ta Kamala , ta sa pin ta nade mishi gashin a baya , ta sako mishi wasu yan kananan gaban goshi gwanin burgewa

sai da ta Kamala sannan ta meda Hairdryer din a wajen shi
shi kuma ya mike ya shiga dressing room

jim kadan ya fito ya na sanye da trouser Navy blue , da T-shirt white color , ya saka wasu sneakers Farare kal ma su mugun kyau
hannu shi na rike da wasu box guda uku ya nufi bakin gadon ya zauna ya ajiye box din a geffen shi

slowly ya juya ya kali Inaya ya ce mata " na saka miki , ko kin saka da kan ki ? "
cike da shagwaba ta ce mishi " um um ni kai za ka saka min " ta kai karshen ta na mikewa tsaye ta karaso gaban shi ta tsaya
( 🤣🤣🤣 wayooo yarinyar nan za ki kashe min Amir lokacin bai yi ba , abun naki iskanci ne ma 🤣🤣 )

a hankali ya kai hannu ya warware Madauri bathrobe din ta , sannan ya fida mata ita ya ajiye gefe
ya kai hannu ya dauki box din da ke a tsakiya , ya bude ya fido wasu underwear pink color ma su mugun kyau , ya saka mata da kan shi

sai da ya saka mata su sannan ya tsaya ya na bin ta da kallo kamar bakuwar shi
cen kuma sai ya kai hannun shi saman cikin ta ya shafa a hankali cikin ran shi ya ce " wannan dan karamin cikin nata , zai iya daukar babys di na kuwa ? "

kamar ta san abun da ya ke fada , sai ta yi yar karamar dariya ta ce " babu komai a ciki "

slowly ya dago kan shi ya kali face din ta ya ce " amma na kusa saka wani abun a ciki "
daga mishi gera guda ta yi allamun minene

bai ce mata komai ba ya janye hannun shi a hankali ya fido wata gown da ga cikin box din
gown din Sky blue ce mai mugun kyau ta sha stone har da wasu sarkoki a wajen kugu kwanin burge
kamar ko an awna ta zauna mata cib cib a jiki

bayan ya saka mata gown din ya bude box din da ke a sama , ya fido wasu sneakers farare kal irin na mata masu ratsin blue
ya sunkuya ya dago kafar ta ya saka mata da kan shi , da allamun ya san lambar da babyn shi ke sakawa dan Sneakers din sun shige ta dai'dai

bayan ya saka mata sneakers din , ya bude box ta karshe , ya fido wata Alkyaba fara kal , an yi mata zanen flowers da zare mai launin gold , ya saka mata ita
sannan ya mike ya riko hannun ta , su ka fara takawa su ka nufi dressing mirror a tare
ya kai hannu ya dauki wani perfume ya feshe jikin ta da shi sannan ya meda shi ya ajiye saman dressing mirror din

dago kai ya yi ya na kallon ta , Masha Allah ta hadu gaskiya kamar na sace ta na gudu
sai da ya dauki lokaci ya na kallon ta , sannan ya kai hannu ya rufe mata kai da hular Alkyabar ta , sannan ya kai lips din shi ya manna mata kiss saman forehead din ta ya riko hannun ta ya ce " mu tafi ? "

gyada mishi kai ta yi kafin ta juya su ka fara takawa a tare su ka baro bedroom din
bari mu leko su Miram na san kafin nan sun iso part din MALIKAT AL'UMU



▪MIRAM



Zaune ya ke shi da Mohammed a parlourn MALIKAT AL'UMU
MALIKAT AL'UMU kuma ta na zaune saman Sofa one seater ta zuba musu ido

cike da kissa Miram ya ce " Ranki shi dade , mun tunkari Amir da wata magana , kuma gaskiya amsar da ya bamu ban ji dadin ta ba "

cikin rudu MALIKAT AL'UMU ta ce " To micece wannan maganar kuma "

Mohammed ne ya amsa mata da cewa " maganar Hawan shi Mulkin Saudiya , ya ce ba za a nada shi ba a matsayin Malik sati me zuwa har sai kun Kamala Idda tare da MALIKAT INAS ranki shi dade "

cike da izza MALIKAT AL'UMU ta ce " bai isa ba , Malik ba shi da wani magaji bayan shi , Miram , Mohammed , ku je ku fara shirye shiryen Nada shi Malik , ba za a bar kujerar Malik babu kowa a sama har tsawon Wata hudu , babbar matsala za mu fuskanta da ga wajen al'uma "

wani makirin murmushi Miram ya saki kafin ya ce " hakan zai fi ranki shi dade , sannan magana ta gaba "

cikin rudu MALIKAT AL'UMU ta ce " to ku ce maganar mai tsayi ce ? "

yar karamar dariya Mohammed da Miram su ka yi a tare sannan Mohammed ya ce " to ranki shi dade , kin san Amir kamar yaro ya ke a waje na , duk da bai bani matsayin uncle din shi ba ni zan rike nawa , ranki shi dade kin san a rana guda a ke Nada Malik tare da MALIKAT , ni kuma a sani Amir ya isa aure , mai zai hana ya auri yarinyar waje na Hafsat "

wani cool murmushi MALIKAT AL'UMU ta saki kafin ta ce " ni ba zan matsa wa Amir a kan ya yi aure ba gaskiya , Ku nada shi kawai a matsayin Malik duk ranar da ya fitar da matar aure sai a nada mishi MALIKAT din shi , in kuma ya yarda da Batun auren fine sai a daura a rana guda "

cikin nitsuwa Miram ya katse ta da cewa " ranki shi dade zai fi a aura mishi ita da wuri , kar a zo a yi abun kunya , kun ga Amir ba yaro ba ne , ya na da nashi bukatun , kar a je ya janyo mana abun kunya "

cikin rudu MALIKAT AL'UMU ta ce mishi " kamar ya abun kunya ? "

dan jinkirtawa Mohammed ya yi kafin ya ce " to ranki shi dade ban so na fada miki ba amma dole zan fada miki , mun tarda Amir tare da wata yarinya a part din shi , yanzu ranki shi dade da wani a waje ne ya ga wannan abun , zai iya ɓata mishi suna "

dan zaro idanu MALIKAT AL'UMU ta yi kamar ba ita ta kai yarinyar part din nashi ba ta ce " Nawfel din nawa ? "

gyada mata kai Miram ya yi kafin ya ce " ki yi hakuri ranki shi dade , dalilin da ya sa mu ka ce a yi auren nan da wuri kar a...... "

bai kai karshen maganar shi ba MALIKAT AL'UMU ta katse shi da cewa " Ya isa haka , ku je ku fara shirye shiryen nada shi Malik , batun auren kuma ku bar ni da shi "

cikin girmamawa su ka yi mata Sallama , sannan su ka tashi su ka bar part din ransu fari kal burin su ya kusa cika

su na barin wajen wasu , mata guda Uku da ba su wuce shekara 33 ba su ka shigo parlourn kowace sanye da Gown off-White , sun yi Rowling wani veil green a kan su , kowace ta na rike da tray su ka nufi Dining room

da sauri MALIKAT AL'UMU ta tseda su da cewa " Dada , ku kawo su nan "
wadda ta kira da Dada ta ce " An gama ran ki shi dade "
ta fada ta na dawowa cikin parlourn su ka ajiye tray din , sannan Dada ta tashi da gudu ta koma kitchen
jim kadan ta dawo rike da wani tissu irin tablecloth haka ta shinfida saman Carpet din tsakiyar parlourn
sannan su ka shirya kayan breakfast din a sama ni bayan Fruits da Tea , da bread sauran abubuwan sam ban gane ko minene ba dan a irin abincin mu ba ne na hausawa

sai da su ka shirya wajen tsab gwanin burgewa sannan ku yi wa MALIKAT AL'UMU sallama su ka bar wajen



▪AFTER SOME MINUTES



sai da ta dauki wajen good 30 minutes ta na zaune a haka kafin ta jiyo Muryar Amir ya na yi mata sallama

slowly ta dago da kan ta , ta na ganin su ta saki wani kyawatencen murmushi , ba karamin kyau su ka yi ba , ya na rike da hannun babyn shi

Cikin Fara'a MALIKAT AL'UMU ta ce " Sai yanzu ku ka yi niyar tahowa ? "

cikin girmamawa Amir ya karaso Wajen MALIKAT AL'UMU ya sunkuyar da kan shi ya manna mata kiss saman forehead din ta ya na cewa " Good morning momy "

da sauri Ita ma Inaya ta ce mata " Good morning Momy "
yar karamar dariya MALIKAT AL'UMU ta yi kafin ta ce " Good morning my pleasures , kun tashi lafiya ? "
Amir ya amsa mata da cewa " Fine momy , na same ki lafya ? "

mike tsaye MALIKAT AL'UMU ta yi ta riko hannun Inaya ta na cewa " Kamar dai yadda ka ke gani ina lafya , ku zo ku zauna tun dazu a ka shirya muku breakfast amma sai yanzu ku ka iso " ta kai karshen ta zaunar da Inaya a gaban tablecloth din , ta zauna geffen ta ita ma
a hankali Shi ma Amir ya juyo ya nufi wajen ya zauna a daya geffen MALIKAT AL'UMU , su ka saka ta a tsakiya shi da Inaya

cikin So da kauna MALIKAT AL'UMU ta ce saka Inaya a gaba ta fara ɗura mata fruits

sai da ta kusa shanye wajen Rabin fruits din saman tray din sannan Amir ya ce mata " momy kar ki fasa min ita " ya fada da larabci

yar karamar dariya MALIKAT AL'UMU ta yi kafin ta kali Inaya ta ce " baby , za ki sha Tea ? "

girgiza mata kai Inaya ta yi cikin shagwaba ta ce " Oun oun momy ni na fi son fruits sun fi gina jiki "

juyo wa Ta yi ta kali Amir irin kallon nan na ka gani ko
tsuke fuska ya yi ya na kauda kai gefe cikin zuciyar shi ya na cewa " wannan matar za ta fasa min ita da fruits "

kamar ko MALIKAT AL'UMU ta san abun da ya ke cewa sai ta amsa mishi da cewa " ka na dai ji ita ta ce ta fi son fruits "

ya san da shi ta ke amma sai ya shanye bai juyo ba , ya Ci gaba da shan Tea din shi cikin nitsuwa

sai da su ka dan jima a haka kafin Inaya ta kali MALIKAT AL'UMU ta ce " momy ina Aunty Tesnim ta ke ? "

" Su na garden ita da Friends din ta " MALIKAT AL'UMU ta ba ta amsa

cikin harshen larabci Amir ya ce ma MALIKAT AL'UMU " har yanzu yarinyar nan ba ta koma masarautar su ba ? "

" wace yarinya kuma ? "

cikin ko in kula Amir ya ce " wannan mai idanun maciji "

dan zaro idanu MALIKAT AL'UMU ta yi kafin ta ce " Allah ya tsare mu to , Amir na san Halin ka fa , wlh ka bawa Rouksar lafya , me ta yi maka ? "

shiru ya yi bai ce mata komai ba amma cikin ranshii har yanzu ya na jin haushin ture Inaya da ta yi har ta fadi gown din ta ta yage bai manta da ranar nan ba

ya yi nisa cikin tunanin tunanin shi ya jiyo Muryar MALIKAT AL'UMU ta na tambayar Inaya in ta koshi
cike da Shagwaba Inaya ta ce mata " momy ciki na na ya cika kamar zai fashe "

MALIKAT AL'UMU na shirin magana Amir ya riga ta cewa " Sai da na ce miki kar ki cika ta da Fruits " ya fada da larabci

salati MALIKAT AL'UMU ta yi kafin ta juya ta kali Amir ta ce " Nawfel ba na son shirme fa , shi ne za ka gwada min kai ma ka damu da matar ka "

" ni fa gaskiya ce na fada miki "

dan karamin tsaki MALIKAT AL'UMU ta yi kafin ta juya ta kali Inaya ta ce " Shikenan baby , tashi ki je wajen Ammie , na san ta yi kwana biyu ba ta gan ki ba "

gyada mata kai kawai Inaya ta yi ta na murmushi kafin ta mike tsaye ta fara takawa ta nufi kofar fita parlourn

har ta kai bakin kofar ta jiyo Muryar MALIKAT AL'UMU ta na cewa " ni gaishe min da ita idan kin je "

da to Inaya ta amsa mata ba tare da ta juyo ba ta ficewar ta
da kallo ya rakata har sai da ta fita sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login