Showing 99001 words to 100637 words out of 100637 words

Chapter 34 - Exiled Prince Book Two Complete Hausa Novel

24 Oct 2025

197

sannan ya kunna laptop din ya fara latsawa

kallon laptop din ya ke ba bu ko kiftawa har ya share wajen good ten minutes a haka
ya na tsaka da kallon laptop din kawai na ga ya rumtse idanun shi da karfi ya na kauda kai gefe murya kassa kassa ya ce " Yanzu wai ni na yi wannan Aikin ? "

a hankali ya bude idanun shi ya na ci gaba da kallon Laptop din
( 😑😑kai gaskiya ni ma sai na ga abun da ya ke kallo )

Ba komai ba ne ya ke kallo face recording cameras na part din , duk abun da ya faru cikin part din da ga safiya har dare sai da gani
har lokacin da Inaya ta shigo part din , lokacin da su ka tafi floor na hudu har ya yi dis virgin din ta duk sai da ya ga komai
ya na a haka ya ga abun da ya faru cikin bedroom din bayan fitar shi

ya na fita bedroom din wadanan Hawayen jini da su ka zubo mata su ka koma cikin idanun ta
a hankali ta fara yin Sama cikin Iska hannayan ta da gashin ta su na reto cikin iska , kamar da ga sama wani farin tissu ya fado ya rufe ta har zuwa kirji
a dubu dari ta bude idanun ta , sun koma farare kal babu ko digon baki a ciki ga shi kuma sai wani haske su ke yi kamar Torch , ta na a haka wani dan karamin Iska ya tashi cikin dakin ya zagaye Inaya na dan second kafin ya baje cikin dakin kamar ba a taba yi ba

ya na bacewa Inaya ta fado saman gadon , wani dogon nunfashi ta ja har sai da kirjin ta ya yi sama
lokaci guda Idanun ta su ka koma dai'dai kamar da farko ta na sauke ajiyar zuciya a hankali dai'dai lokacin da RIANNA ta shigo cikin dakin

bayan zaro idanu ba abun da Malik ke yi har wani Duka uku uku zuciyar shi ke yi , ya ma rasa tunanin da zai yi
ba shiri ya mike tsaye har sai da laptop din shi ta fadi , ya nufi Lift da sauri ya shiga ya koma Floor na hudu

kofar lift na budewa ya daga ya fito , idanun shi ba su sauka ko ina ba sai saman ta
ta na zaune saman chair a dining table ga Maid biyu a bayan ta kai a sunkuye , ta na shan fruits cikin konciyar hankali

ta na ganin shi ta saki wani cool murmushi ta juya ta kali daya da ga cikin Maid din nan ta ce mata " Za ku iya tafiya "
dan sunkuyawa su ka yi a tare kafin su fara takawa su ka bar wajen
sai da su ka zo gaban Malik su ka gaishe shi cikin girmamawa sannan su ka nufi wata door ta glass da ke geffen damar Kofar lift su ka shiga a tare

kallon ta ya ke babu ko kiftawa cikin zuciyar shi ya kassa gaskata abun da ya gani cikin laptop din shi

turo dan bakin nan nata ta yi cikin shagwaba ta ce mishi " baby wai ba za ka karaso ba ka tsaya ka na kallo na haka kar fa ka cinye ni "

ajiyar zuciya ya sauke kafin ya daga kafa a hankali ya karaso cikin parlourn ya nufi dining table ya janyo chair din da ke fuskantar ta ta ya zauna ya na kallon ta babu ko kiftawa

ba ta ce mishi komai ba ta ci gaba da shan fruits din ta
shi dai kallon ta kawai ya ke , cikin zuciyar shi ya na cewa ya so malam ya na nan a yanzu dan ya fada mishi gaskiya a kan Inaya dan shi yanzu ya fara tantama a kan ta , wannan abun da ya gani ya wuce tunanin mai tunani kamar a film haka ya ke ganin abun

ya yi nisa cikin duniyar tunanin shi kawai ya ga ta mike ta zagayo geffen shi ta zauna saman cinyar shi ta zagayo da hannayan ta a wuyan shi

turo dan bakin nan nata ta yi ta ce mishi " wai wannan kallon duk na minene , ko si ka ke na sake fadawa tarkon soyayyar ka " ta kai karshen ta na daga mishi gera guda

a hankali ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce " Cutie ! "
" Na'am baby " ta fada cikin shagwaba

shiru ya yi ya na kallon ta ba tare da ya ce komai ba shi kadai ya san irin tunanin da ya ke yi

wani cool murmushi ta saki kafin ta fara yin kassa da hannayan ta , ta sa hannu ta fara cire button din rigar shi a hankali

bai Ankara ba kawai sai ji ya yi ya riko nipple din shi ta cikin singlet din shi
a dubu dari ya damko hannun ta a razane ya kali jikin shi ya ga duk ta cire mishi button din shirt din shi

a hankali ya dago kai ya kale ta cikin sanyin murya ya ce mata " Me za ki ne kin cire min button haka ? "

turo dan bakin nan nata ta yi ta ce mishi " nono zan sha , tun ranar nan na ce ka ba na ni amma ka ki "

a hankali ya lumshe idanun shi ya na furta " ya salam " cikin zuciyar shi kafin ya bude idanun shi saman face din ta ya ce " wlh Cutie kashe ni za ki yi watarana "

shagwabe fuska ta yi ta ce mishi " ta ya zan iya kashe ka , ni ka ban nono na sha ko na yi maka kuka "

matse gera ya yi ya ce mata " Cutie ni wai tsaren wassan ki ne , na ga kwana biyu kin fara raina ni "

murguna mishi baki ta yi kafin ta tashi da ga saman cinyar shi ba ta ce mishi komai ba ta nufi lift za ta barin wajen maganar shi ba karamin bata mata rai ba ya yi , da ga ta na yi mishi wassa

a dubu dari ya mike da ga saman chair din shi taku biyar kadai ya yi ya damko kugun ta ta baya
ya na riko ta , ta saki kuka ta na neman kwatar kan ta ta na cewa " yaya Zayd ka kyale ni na tafi , wajen mama zan je "

a hankali ya juyo ta su na fuskantar juna ya ce mata " Cutie yaji za ki yi min ? "

cikin kukan nata ta ke ce mishi " yaya Zayd ka kyale ni na tafi don Allah "

shiru ya yi ya na kallon ta sai kuka ta ke hawaye na zubo mata bibiyu
cikin sanyin murya ya ce mata " i'm sorry my Cutie " ya kai karshen ya na sakin ta
ya na sakin ta ta juya da gudu ta shiga cikin lift
ya na kallon ta har ta shiga dai'dai kofar za ta rufe ta fudo tongue ta yi mishi kwalo

shi dai bai ce mata komai ba , sai da kofar ta rufe sannan ya juya ya koma cikin corridor ya shiga bedroom din shi

bangaran Inaya kuma ta na baro part din kai tsaye ta nufi part din MALIKAT HOUDA kamar ta san hanya

bakin ta da Sallama ta shigo parlourn MALIKAT HOUDA
nan ta tardo Muntaz zaune tare da MALIKAT HOUDA
cikin girmamawa Inaya ta karasa wajen MALIKAT HOUDA ta tsuguna ta gaishe ta
da fara'a a fuskar ta ta amsawa Inaya gaisuwar ta har da zolayar ta irin wassan nan na sirikai sannan ta ce mata ta shiga mamar ta na ciki
ba musu Inaya ta tashi ta nufi corridor ta shiga bedroom din Mama

tun da ta shigo parlourn Muntaz ke yi mata wani kallon kaskanci kamar ba ta san ita ce MALIKAT din Saudiya ba a yanzu

sarai MALIKAT HOUDA ta lura da Muntaz shi ya sa ta ce ma Inaya ta tashi ta je
sai da ta bari ta shiga bedroom din mama sannan MALIKAT HOUDA ta ce Muntaz " kin san ko wacece yarinyar nan a yanzu ki daina yi mata irin wannan kallon banzan "

cikin bacin rai Muntaz ta ce " yanzu Mamie ki na ji ki na gani za ku bar Malik ya auri yarinyar da ya yi biyun shekarun ta , kuma har ta hau kujerar MALIKAT "

" Muntaz Malik ya na son yarinyar nan dan idanun shi kadai za ka kala ka san ya na matsanincin son yarinyar nan , da kin tsaya kin ga abun da ya faru a ciki fadar lokacin da za a nadda ta MALIKAT , bai bawa kowa damar yin jayaya da shi ba , kin sani wanda ya nadda Malik shi ke nadda MALIKAT , amma wannan da hannayan shi Malik ya nadda ta , kin ga ko ba damar yin jayaya "

kamar za ta yi kuka ta ce " yanzu shikenan mamie ta raba ni da shi "

dan karamin tsaki MALIKAT HOUDA ta yi kafin ta ce " Dama a tare ku ke ne ? dama a ce shi ma ya na son ki ne da farko da sai ki ce ta raba ku amma a sani na ko hira ba ta taba shiga tsakanin ku da Malik dan haka ki bawa kan ki lafiya sakara kawai "
ta na gama fadar haka ta mike ta shiga corridor ta koma bedroom din ta

ta bar Muntaz nan sai faman cika da batsewa ta ke sai ita ta ji haushi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login