Showing 51001 words to 54000 words out of 100637 words
ya na shiga Mohammed ya juyo ya kali Miram dai'dai lokacin da shi ma ya juyo su ka yi ido hudu
Murya kassa kassa ya ce mishi " Miram wacece wanan yarinyar , ka na dai ji cewa ya yi su tafi ya mata wanka , ba dai neman mata Amir ya shiga yi ? " Miram ya fada
" ka na ji ko , tashi mu tafi wajen MALIKAT AL'UMU , in ya san wata bai san wata ba , in shi ya na sama da mu , to ita ta na sama da shi a matsayin ta na mahaifiyar shi , ni Batun auren ma ita na so mu tunkara amma ka ce mu nufo wannan sakaran yaron "
yar karamar dariya Miram ya yi kafin ya ce " ni fa ina ga Amir din mu ya fara bin mata , ba ka ga yarinyar da ke tare da shi ba a cikin part din shi kuma , ka ga kuma kayan da ke jikin ta da ga gani ba na mata ba ne "
" matsala ta da kai sa ido Miram , ina ruwan ka da yarinyar , mu gyara mu ma za ta yi , in har ta kama su na aikin banza a tare , za mu iya anfani da hakan dan mu bata mishi suna , yanzu dai mu fara gayawa MALIKAT AL'UMU abun da yaron ta ke yi " Mohammed ya fada ya kai karshen ya na mikewa tsaye
mikewa tsaye shi ma Miram ya yi ya bi bayan shi ya na fadin " gaskiya yarinyar nan ta hadu a ina Amir ya samo ta , da ga gani ba ta yi kama da ta saudiya ba "
yar karamar dariya Mohamed ya yi kafin ya kai hannu ya bugi damtsen Miram dai'dai lokacin da su ke shiga lift ya ce " dadi na da kai mugun son mata , me za ka yi da wannan yarinyar da ka yi jika da ita ? "
hararrar shi Miram ya yi kafin ya ce " To shi Amir me ya ke yi da ita ? ni fa wlh idan ya ida ina so , kwana biyu ban taba ba " ya kai karshen ya na kashewa Mohamed ido guda
yar karamar dariya Mohammed ya yi ba tare da ya ce mishi komai ba , a haka har su ka baro part din Amir su ka tafi aikin gaban su
▪AMIR
[26/09 à 10:33] MIMI:
❤⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
💔🥀 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) 💔🥀
👑❤ MALLAKIN MEERAH ❤👑
【THE ROYALTY LOVE 👑🕊💖】
Marubuciyar littafin
【TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺】
【 BOOK …………………… 2 ❤ 👑】
____________________🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊___________________
PAGE 16 ✍📚
Dan zaro idanu Diya ya yi , a tare su ka juya su ka kali corridor shi da Aymane
Amir kuwa kashe idanun shi ya yi kamar mai jin barci cikin zuciyar shi ya ce " ni na manta da ita wlh " ya na gama fadar haka ya jingina bayan shi a jikin chair din ya dan daga kai ya kali Saitin corridor
dai'dai lokacin da Inaya ta fito , ta na sanye da wata gown Sky blue mai mugun kyau har kassa , ta yafa wani veil fari a kan ta sai tashin kamshi ta ke , ta na tafiya a hankali kamar hawainiya
bakin da sallama ta shigo cikin parlourn
ta na Ganin Diya ta saki wani kyawatencen murmushi ta ce " Yaya Moussa ! "
dan karamin murmushi Diya ya yi kafin ya ce " Babyn malam , ashe ki na nan , shi ya sa da na zo ban gan ki ba "
Shagwabe fuska ta yi ta na fadin " yaya Moussa dama ba ka tafi nema ta ba " ta kai karshen ta na murguna mishi baki
har Diya ya bude baki zai yi magana ya ga Amir ya daga mishi hannu , sannan ya juyo Slowly
har ya bude baki zai yi magana idanun shi su ka sauka kan Aymane da ya tsare Inaya da idanu babu ko kiftawa kamar zai cinye ta
nan take ya ji zuciyar shi ta fara yi mishi zafi , bai ce musu komai ba ya juya ya kali Inaya ya ce " Cutie koma ciki "
noke mishi kafada ta yi ta na fadin " ni wajen Aunty RIANNA zan je "
ware idanun shi ya yi da kyau cikin tsare gida ya ce mata " Cutie kar ki bari na sake maimaita abun da na ce "
marairaice fuska ta yi nan take idanun su ka kawo ruwa ta juya da gudu ta koma cikin corridor din
sai da ta shiga corridor din sannan Diya ya kali Amir ya ce " har yanzu dai ba ka sauya ba Amir "
" please Diya let me with that , ka bar ni da abun da ke damu na " Amir ya fada cen kassan makoshi
Yar karamar dariya Diya ya yi kafin ya ce " Aymane tashi mu tafi , ina ga Amir na da aikin yi a ciki " ya kai karshen ya na mikewa tsaye
sai a lokacin Aymane ya dawo cikin hayacin shi , bai ma san abun da Diya ya ce kawai shi dai ya mike tsaye , sannan ya yi wa Amir sallama
Diya kuma ya ce " Sai ka tashi ka je ka rarrashi babyn ka " ya kai karshen ya na bushewa da dariya su ka nufi Kofar lift su ka bar part din baki daya
sai da su ka fito su ka nufi part din MALIKAT INAS dan Aymane ya ga RIANNA
su na tsaka da tafiyar su Aymane ya ce " Diya wacece yarinyar nan , kuma a part din Amir ? "
yar karamar dariya Diya ya yi kafin ya ce " ka san Allah Aymane na san halin ka saboda tare mu ka girma cikin gida guda , duk ranar da Amir ya kama ka , ka na kallon yarinyar nan wlh sai ya sa an fida maka idanun nan da ba su zama waje guda "
dan karamin tsaki Aymane ya yi kafin ya ce " ni ba wannan ba , a sani na Tesnim ita kadai ce kanwar Amir , to wannan wacece da gani ba za ta wuce 15 years ba , me kuma ta ke yi a part din shi ? "
dan karamin murmushin geffen fuska Diya ya yi kafin ya ce " Aymane , Amir ne kadai zai ba ke wannan Amsar , amma zan fada maka wani abu guda , duk lokacin da ka ga yarinyar nan ka rufe idanun ka har ta wuce , dan wlh Amir zai iya kashe ko wanene saboda ita kuma a zauna lafiya "
" a kan wannan babyn , ba dai son ta ya ke ba ? "
" ka ga ba mu yi nisa da part din shi ba koma ka tambaye shi " Diya ya fada ya na kara saurin tafiyar shi ya yi gaba dan ya gaji da suruntun Aymane
ci gaba da tafiyar shi Aymane ya yi a hankali ya na sakin wani cool murmushi , gaskiya ba karamin tafiya da imanin Shi Inaya ta yi ba , shi duk duniya bai taba ganin macen da ta burge shi kamar Inaya ba dole ya samo ko wacece
▪INAYA
kai tsaye bedroom din shi ta koma da gudu ta shiga ta nufi gadon ta yi rub da ciki ta na sakin kuka
ita kan ta ba ta san lokacin da ta dauka a hakan ta na kukan ba
a hankali Amir ya turo kofar dakin ya shigo ya na sallama cen kassan makoshi
hannun rike da wani tray , shake da Fruits da wani mug na coffee
karasowa ya yi cikin dakin ya nufi Bedside drawer ya ajiye tray din sannan ya koma ya tsaya bakin gadon cikin sanyin murya ya ce " Cutie tashi na kawo miki breakfast "
Ko sannu ba ta ce mishi ba , ta ci gaba da kukan ta
a hankali ya sauke ajiyar zuciya , ya na lumshe idanun shi a hankali ya sake bude su , sannan ya zauna bakin gadon ya kai hannu saman shoulder din ta ya na fadin " Cutie "
a hankali ta janye Shoulder din ta , ta matsa kadan
janye hannun shi ya yi a hankali , sannan ya mike tsaye
a hankali ya konto saman bayan ta , ya kai dan bakin shi saitin kunnen ta , ya ce " in ba ki son wannan breakfast din , bari na baki wani "
cikin kukan nata ta ce mishi " yaya Zayd , ka kyale ni don Allah ka kyale ni "
" me kuma na yi da za ki ce na kyale ki "
" ni fa kawai na je na ce maka yunwa na ke ji , zan je wajen Aunty RIANNA mu yi breakfast tare "
" Kennan ba za ki yi breakfast tare da ni ba ? " ya fada ya na tashi da ga saman ta ya koma gefe ya zauna
a hankali ta fara rage sautin kukan ta , sannan ta juya ta na fuskantar ceiling ta kai hannu ta fara goge hawayen ta
hannu ya kai saman kumatun ta ya fara goge mata hawayen ta ya na fadin " in ki na kuka sam ba ki yin kyau "
buge hannun shi ta yi ta na kauda kai gefe ta turo dan bakin nan nata
ta na a haka kawai ta ji ya mata runfa da fafadar kirjin shi , ya na kallon face din ta ya ce " yau dai bari na cinye wannan dan bakin Tsiwaar "
a hankali ta juyo ta wurga mishi wata muguwar hararra ba tare da ta ce komai ba
daga mata gera guda ya yi ya na fadin " ya ne yan mata , na yi miki ne ? "
yar karamar dariya ta yi har sai da dimple din ta ya fito
dama abun da ya ke so kennan ya ga ta yi dariya ko zai rage radadin da ya ke ji cikin zuciyar shi
sai da ya ga ta Kamala Dariyar ta sannan sauka da ga saman ta ya koma gefe ya zauna , ya kai hannu ya dauko tray din Fruits ya ajiye saman cinyar shi ya ce " shikenan tashi ki yi breakfast "
mikewa zaune ta yi ta kali tray din sannan ta dago ta kale shi ta na turo baki ta ce " Fruits kadai ? "
" eh , ko ki na son wani abu ne " ya fada ya na dauko wani barin Apple ya kai mata a baki
girgiza mishi kai ta yi ta na bude baki ta karbi Apple din
ajiye mata tray din ya yi saman cinyar ta sannan ya mike ya na fadin " ki same ni a parlour idan kin ida " ya kai karshen ya na nufar kofar fita dakin
da kallo ta raka shi har sai da fita sannan ta ci gaba da shan fruits din ta cikin konciyar hankali
▪TESNIM
zaune ta ke cikin garden , ita da Rouksar , ta yi zugum waje guda ko kiftawa ba ta yi , ga idanun ta sun yi jazir , ta yi kukan har ta koshi
Rouksar kuwa ta na faman latsa wayar ta
Su na a haka su ka jiyo sallama
a tare duk su ka juya su ka kali Abdoul da ke tsaye gaban su , ya saki wani cool murmushi
a tare su ka amsa mishi sallamar shi sannan Rouksar ta ce " kai kuma da ga ina ? "
" I'm sorry , ina son magana da ..... " bai kai karshen maganar shi ba ya juyo ya kali Tesnim allamun da ita ya ke son magana
a hankali ta bude bakin ta , ta ce " me ya faru ? "
" nothing , ina son Magana da Amir , shi ne a ka ce min na zo wajen ki "
cikin rudu ta ce " ni kuma ? wa fada maka hakan ? "
" please ni ba wannan ba , ki kira min shi kawai , ina son magana da shi "
shiru ta yi na dan lokaci ta na kallon shi kafin ta kai ta dauki wayar ta , ta shiga contact ta fara neman number din Amir ta danna mishi kira
ko ringing biyu ba ta yi ba ya dauki kiran
dan karamin murmushi ta saki kafin ta yi mishi sallama , sannan ta ce " Akhie , akwai wanda ke son magana da kai "
cikin nitsuwa Amir ya ce mata " ina jiran ku , ke da shi " ya na gama fadar haka ya katse kiran
ta na jin ya katse kiran ta sauko wayar a hankali , sannan ta fara kokarin Tashi
ta kali Abdoul ta ce " mu je ya ce na raka ka "
da sauri Rouksar ta ce mike ta na fadin " tsaya min , mu tafi sai ku bar ni ni kadai "
gyada mata kai kawai Tesnim ta yi kafin ta fara takawa , Rouksar na geffen ta , Abdoul na biye da bayan su , su ka nufi part din Amir
▪AMIR
konce ya ke cikin parlourn shi , a kassa saman carpet , ya tada kan shi da wani pillow
Inaya na konce saman shi , ya daura hannun shi guda saman bayan shi , gudan kuma saman forehead din shi , ya na kallon ceiling , ta na rike da wayar shi , ta na game , ko da Tesnim ta kira ma ita ce ta dauki kiran , sannan ya kai hannu ya karbi wayar
ita kuma ta kontar da kan ta saman chest din shi ta lumshe idanun shi kamar mai jin barci
Amir kuwa bayan ya katse kiran ya ajiye wayar shi gefe , ya lumshe idanun shi shi ma
sun dauki wajen good five minutes a haka , kafin Amir ya jiyo Muryar Tesnim da Abdoul su na yi mishi Sallama , sai kuma wata Muryar ta uku
ya na jin su amma bai bude idanun shi ba ko sallamar su cikin zuciya ya amsa musu ita
a tare su ka karaso cikin parlourn , Abdoul na ganin Inaya konce a jikin Amir ya saki wani kyawatencen murmushi " dube su don Allah Ko kunya ba su ji " ya fada cikin zuciyar shi
Tesnim kuwa ta na ganin Inaya ta ji duk zuciyar ta ba dadi , yau ga wata konce a jikin yayan ta kuma bai ce mata komai ba , ta yi matukar kishi
Rouksar kuma kamar ta yi tsuntsuwa ta je te shako Inaya ta jefa ta , ta cikin glass din gaban su ta fada ta mutu ta huta ma
gyaran murya Abdoul ya yi mishi sannan ya ce " Zayd , sai a saki yarinyar mutane ko , ga ta Na kawo maka " ya fada da hausa
ba tare da ya bude idanun shi ba ya ce " ka daina kira na da Zayd , in ba za ka ce Amir ba ka yi shiru , sannan ni Tesnim kadai na ce ka kawo min , wacece a tare da ku "
slowly Abdoul ya juya ya kali Rouksar sannan ya juyo ya kali Amir ya ce " ni ma ban sani ba , a tare na gan su "
" shikenan sai ku koma kai da ita " Amir ya fada har yanzu dai idanun shi a lumshe
gyada kan shi kawai Abdoul ya yi kafin ya juya
har ya yi taku biyu ya tsaya cak , ya juyo ya kali Amir ya ce " Please Amir , idan Auta ta tashi ka ce mata mama na son ganin ta , tun kafin a fara Azumi rabon ta da Auta , dama² Nesrine ita ta na zuwa wajen ta "
a hankali Amir ya gyada mishi kai allamun to
dan karamin murmushi Abdoul ya yi kafin ya juya ya nufi Rouksar ya tsaya gaban ta ya ce " mu je , ya ce ya na son magana da sister din shi " ya fada da turanci
kare mishi kallo da ga sama har kassa Rouksar ta yi kafin ta ja dan siririn tsaki ta juya ta bar wajen
dan tabe baki Abdoul ya yi kafin ya juya ya kali Amir ya yi mishi sallama sannan ya juya ya bar wajen shi ma
su na barin wajen Amir ya juya da Inaya ya kontar da ita saman bayan ta , sannan ya mike zaune ya bude idanun shi ya kali Tesnim ya ce " ba za ki zauna ba kin yi tsaye saman mutane "
sunkuyar da kai ta yi ta na marairaice fuska ba tare da ta ce komai ba
" shikenan , zo zauna " ya fada ya na nuna mata geffen shi
girgiza mishi kai ta yi kamar ta yi kuka ta ce " ai ga Sister din ka nan kusan ka , ni na tsaya a nan "
slowly ya juya ya kali Inaya da ke barcin ta cikin konciyar hankali
sannan ya juyo ya kali Tesnim ya ce " kar ki bari na maimaita abun da na ce