Showing 96001 words to 99000 words out of 100637 words

Chapter 33 - Exiled Prince Book Two Complete Hausa Novel

24 Oct 2025

200

Da sauri shi ma General ya mike
cikin sanyin murya Malik ya ce mishi " Idan ku ka yi bincike a kan rayuwarshi za ku gane cewa ba ya da hannu cikin abun da ya faru , kamar yadda Malik ya ke victim haka shi ma Hakim ya ke Victim , kai dai ka yi abun da na saka ka " ya na gama fadar haka ya fara takawa ya nufi corridor ya shige

sai da ya shiga sannan General ya juya ya nufi lift ya shiga ya bar part din
bari dai mu leko su Damba kwana biyu na ji su shiru



β–ͺDAMBA



zaune ya ke kassan bishiyar nan tashi kamar kullum , ya na sanye da kayan nan nashi bakake , da bakin rawanin shi ya rufe fuskar shi idanun shi kadai a ke iya gani

Rouksar na zaune Geffen shi ita ma wannan karan ta rufe Fuskar ta idanun ta kadai a ke iya gani , ga Meli a gaban su ya Zube saman guyiwowin shi ya sunkuyar da kai cikin girmamawa

shiru su ka yi har na dan mintina kafin Damba ya juya ya kali Rouksar ya ce " Wai kin tabbatar kin zuba poison din ki a cikin abincin da a ka kai part din Malik "

gyada mishi kai Rouksar ta yi kafin ta ce " Ni fa da kai na na zuba shi "

" To , ya a ka yi na shiru , ya kamata a ce yanzu masarautar nan duk ta birkice wajen ceton ran yarinyar nan "

" ni fa abun da ya fi damu na , tun jiya ban ga yarinyar nan ba , ko kiftawar ta ban gani ba , kar a je Malik ya taba ta "

Dan karamin tsaki Damba ya ja kafin ya juya ya kali Meli ya ce mishi " kai kuma me ya kawo ka nan ? "

murya na kerma Meli ya ce mishi " ranka shi dade dama na ga fitowar Malik ne da ga part din shi , shi ne na ce bari na zo na fada maka "

wani dogon Tsaki Damba ya yi ya ce " To sai a ka yi me , dan ya fito part din shi , ai dama ya na fitowa "

" amma ranka shi dade , ba fada ya tafi ba , Prison din masarautar nan ya tafi kuma ya share wajen awa guda a cen , bayan dawowar shi part din shi kuma na ga shigar General Abdallah , tare da Azzam mai kula da camerorin masarautar nan "

cikin nitsuwa Damba ya katse shi da cewa " Shi ya sa Diya kadai na gani a fada , Ka san abun da ya je yi a prison din ? "

girgiza mishi kai Meli ya yi kafin ya ce " gaskiya ba sani ba ..... "

da sauri Rouksar ta katse shi da cewa " wajen wanda ya kashe Malik ya je , na ji jiya a zaman fada ya ce a meda shi prison zan yi bincike a kan shi "

wani makirin murmushi Damba ya saki kafin ya ce " Faduwa ta zo dai'dai da zama , Medusa ki san yadda za ki ki kashe yarinyar nan cikin kwanan nan , cikin sauki za mu iya daurawa wanda ya turo Sniper din nan kashe Malik mutuwar ta , kin ga hanyar mu a share ta ke wucewa kawai za mu yi , Idan har yarinyar nan ta mutu kashe Malik zai zo mana da sauki "

ya na gama fadar haka ya juya Kali Meli ya ce mishi " Za ka iya tafiya , amma ina son duk wani motsin Malik ya kasance cikin idanun ka "

" an gama ya shugaba na , godiya na ke ya shugaba na " ya na gama fadar haka ya mike kai a sunkuye ya juya ya bar wajen da gudu

ya na barin wajen Rouksar ta ce ma Damba " ya kamata ka tafi , saura kwana biyu fa auren ka " ta kai karshen ta na yar karamar dariya

dan karamin tsaki Damba ya yi kafin ya bace bat a wajen ya bar ta
ta na ganin ya bace ta bushe da dariya mai sauti sannan ta bace ita ma ta na ci gaba da dariyar ta
( duk yadda a ka yi wannan Damba a cikin masarautar ya ke , kuma a cikin Fada , To wanene zai kasance Damba ? dan Malik ya na da makiya dayawa a cikin masarautar har ma a wajen ta , wasu na su ya fito fili wasu kuma ya na a ciki zuci , to wannan shi kuma da ga ina ? πŸ€”πŸ€”πŸ€”πŸ€” Hmmm mu je zuwa dai za mu sani da ga baya )



β–ͺ TESNIM


zaune ta ke cikin Zunfar garden , ta na rike da wayar ta ta na faman latsawa , ga dogarai biyar a zagaye da ita , ga kuma uban fruits a gaban ta , ta na zaune cikin konciyar hankali

Ta na a haka ta jiyo Muryar Abdoul ya na yi mata Sallama
A hankali ta dago kan ta , ta na amsa mishi sallamar shi kafin ta ce mishi " me ya kawo ka waje na "

bai ce mata komai ba ya zauna saman sofar da ke geffen wadda ta ke zaune , ya kai hannu saman tray din fruits ya dauki Apple guda sannan ya ce mata " ni ba wajen ki na taho ba , a sani na garden din nan Malik bai mallaka miki shi ba " ya kai karshen ya na kai Apple din a bakin shi

wani siririn tsaki Tesnim ta yi kafin ta ce " wai me na yi maka ne da ka ke yawwan shiga hanya ta na ne "

ba ta gama rufe bakin ta ba ya ce mata " kin yi min ne shi ya sa na ke bibiyar ki "

ba ta san lokacin da dariya ta kubce mata ba har sai da wadanan fararen hakwaren nata su ka fito
tsagaita dariyar ta yi kafin ta ce " na yi maka ? ka kali kan ka , ka kale ni ajin mu daya ? "

wani cool murmushi Abdoul ya saki kafin ya ce mata " amma ke ba yar'uwar Malik ba ce ko ? "

wani kallon wulakanci ta mishi kafin ta ce " ban gane ba , big bro di na ne , uwa guda uba guda "

" hmm kin san Hausawa sun ce Albasa ba ta yi halin ruwa ba , Ba ki dauko halayan dan'uwan ki ba , ni fa da wassa na fada miki wannan maganar , Eh ki na da kyau ki na da kudi , ki na da Mulki ga izza son kowa kin wanda ya rasa za ki iya kasancewa burin kowane namiji a duniya amma banda Abdoul Ibrahim , ba ki kai ajin matan da zan bude baki na furta musu kalmar soyayya ba " ya na gama fadar haka ya mike ya bar wajen

da kallo ta raka shi har sai da ya kurewa ganin ta sannan ta mike da sauri sauri ta nufi Part din MALIKAT AL'UMU

babu ko sallama ta shigo parlourn ta na fadin " Momy , Momy , Momy " ta ke kwallawa MALIKAT AL'UMU kira kamar za ta yi kuka

har ta nufi corridor MALIKAT AL'UMU ta fito a rude ta na fadin " Tesnim lafiya ki ke min irin wannan kiran "

karasowa gaban MALIKAT AL'UMU ta yi ta na turo dan bakin nan nata ta ce " Momy wai ban da kyau ne ? "

cikin rudu MALIKAT AL'UMU ta ce mata " haba baby na , ai duk masarautar nan babu wadda ta kai ki kyau " ta fada ta na daura hannun ta saman kumatun Tesnim

nan take ta saki kukan shagwaba ta na fadin " Wai momy ce min ya yi ban kai ajin matan da zai bude baki ya furta musu kalmar soyayya ba "

" ban gane ba , wanene ya fada miki kuma ? " MALIKAT AL'UMU ta fada cikin rudu dan ita ba ta gane abun da Tesnim ke fada ba

" momy ba dan Uwan Baby ba ne , shi ne ya fada min hakan " ta fada ta na kumbure fuska

bushewa da dariya MALIKAT AL'UMU ta yi har da tapi kafin ta ce " to se mi dan ya fada miki hakan , mutuwa za ki yi ne ? ni wlh kin bata min lokaci da shirmen ki " ta na gama fadar haka ta juya za ta koma inda ta fito

da sauri Tesnim ta saki kukan shagwaba ta na fadin " Amma Momy ya raina ni fa kenan , ni wlh sai ya ce ya na so na "

ajiyar zuciya MALIKAT AL'UMU ta sauke kafin ta ce " Oh Allah , Tesnim to in ya ce ya na son ki me za ki yi , ko ke ma ki na son shi ne ban sani ba ? "

tsit Ta yi shiru ta na kallon MALIKAT AL'UMU , ta rasa amsar da za ta ba ta
ganin yadda ta yi shiru ne ya sa MALIKAT AL'UMU Sakin tsaki ta juya ta na fadin " Idan ke ma ki na son shi ki fada min , tun kafin ya fada soyayyar wata daban , ki rungumi Sorry " ta na gama fadar haka ta shiga Corridor ta koma part din ta

sai da ta shiga sannan Tesnim ta saki wani makirin murmushi ta ce " Za ki gani sai ya bude baki ya ce ya na so na , ni kuma na ce ba na son shi " ta kai karshen ta na murguna baki ta shige corridor ta koma part din ta
[06/10 Γ  08:15] MEERAH πŸͺ·πŸ©·:






❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀
(LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯





( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )




STORY & WRITTEN BY : MEERAH πŸ‘‘πŸ”₯




Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA πŸ’–πŸ’πŸŒΊ





BOOK ________2 βœπŸ“šπŸ”₯





____________________β€»β€»β€»β€»β€»_______________________






P A G E 2 9 πŸ₯€ ❀




β–ͺMALIK



a hankali ya kai hannu ya janye Duvet din da ta rufe jikin ta da shi ya fido face din ta
ta lumshe idanun ta ta na barcin ta cikin konciyar hankali ta na sauke ajiyar zuciya
ajiyar zuciya shi ma sauke kafin ya gyara zaman shi saman bed din ya na kallon face din ta
murya cen kassan makoshi ya ce " Oh ni Nawfel , wannan yarinyar ba ta da aiki sai barci da shan Fruits , Hmmmm Kin yi sa ba na son abun da zai taba min ke da na ba ki wani sabon aikin "

a hankali ya lumshe idanun shi ya na sauke ajiyar zuciya kafin ya sake bude su saman face din ta ya ce " amma Sai dai ki yi Hakuri My Cutie , gaskiya ba zan iya jurewa ba ina son na sake jin wannan dadin naki "

ya na gama fadar haka ya fido wayar shi ya fara latsawa na dan lokaci kafin ya ajiye ta saman bedside drawer
ya mike tsaye ya cire Alkyabar shi , da rigar shi ya bar Trouser sai singlet a jikin shi ya ajiye saman Chair
sannan ya Haye gadon ya konta geffen ya janyo duvet ya rufe su har kai
😴😴😴AH TO NI BARI NA KOMA DA GA GEFE HAR KU GAMA BUGA MATCH DIN KU ZA MU CI GABA DA LABARIN



β–ͺAFTER SOME HOURS



a hankali ya bude kofar toilet ya fito ya na sanye da bathrobe
kai tsaye bed din shi ya nufa , ya zauna a bakin gadon ba tare da ya kale ta ba ya ce " Cutie wai ba za ki daina kukan nan ba ? "

ya na gama fadar haka ta fito da kan ta da ga cikin duvet din cikin kuka ta ce mishi " Yaya Zayd ni ka kyale ni , ba zan sake yi maka magana ba "
ta na gama fadar haka ta ja duvet din ta sake rufe fuskar ta ta na kuka kassa kassa

ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juyo ya marairaice murya ya ce mata " ai na ce ki yi hakuri , ba zan sake ba "

shiru ta yi ba ta ce mishi komai ba , amma ta na jin abun da ya ke fada mata

a hankali ya kai hannu ya riko duvet din ya ja , amma ta rike shi gam ta ki bari ya ja shi

ba dan ya so ba ya sakin mata duvet din ya ce mata " Shikenan tashi mu je ki yi wanka , zan ba ki chocolate "

a hankali ta fido idanun ta ta kale shi ta ce " da gaske ? "
gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya ce mata komai ba

da sauri ta janye Duvet din , ta diro da kafafun ta kassa ta zauna geffen shi
ta na shirin mikewa ya meda ta konta ya mata runfa da fafadar kirjin shi
kokarin kwatar kan ta ta yi ta na fadin " ni yaya Zayd ka kyale ni , mun bata "

cikin nitsuwa ya ce mata " yi min shiru , ai ni ban ce mun bata ba "
turo dan bakin nan nata ta yi ta na ce mishi " to ni na bata da kai , kuma da ga yau kar ka sake yi min magana "

" Shikenan zan kyale ki , kuma da ga yau ba za ki sake gani ba , wajen Rouksar zan koma na San ita ba za ta ki yi min abun da na ke so ba " ya na gama fadar haka ya sake ta sannan ya mike tsaye ya nufi dressing room ya shige

da kallo ta raka shi har sai da ya shiga sannan ta murguna mishi baki ta ce " ni ina ruwa na in ka tafi wajen ta "
cen kuma wata zuciyar ta ce mata " in ki ka bari ya tafi wajen ta , to kin rasa shi har abada kenan "

nan take yanayin face din ta ya sauya kamar za ta yi kuka

ta na a haka ya fito da ga dressing room ya na sanye da Trouser Navy blue da Shirt white color , ya daure wanan lalawsan gashin kan shi a baya sai tashin qamshi ya ke , ya na tafe ya na gyara watch din hannun shi

da kallo ta ke bin shi har sai da ta ga ya karaso wajen kofar fita dakin bai ce mata komai ba ko kallon ta bai yi ba
da sauri ta ce mishi " yaya Zayd ! "
cak ya tsaya bai juyo ba ya ce mata " Yi sauri ki fadi maganar ki ta karshe , dan wannan shi ne gani na karshe da za ki yi min "

kamar za ta yi kuka ta ce mishi " baby don Allah kar ka tafi "
slowly ya juyo ya kale ta , ashe ba kamar kukan ta ke ba kukan ne da kan shi ta ke ga hawaye nan bibiyu na zubo mata
duk sai ta karaya mishi zuciya , shi fa wassa ne ya ke mata kawai zai je duba sakon da ya bar ma Azim

ba dan ya so ba ya tako a hankali ya komo bakin gadon ya zauna ya kai hannu ya janyo ta jikin shi ya rungume ta tsam ya na dan bubuga bayan ta ya ce " Shikenan kukan ya isa haka ni fa wassa na ke miki "

a hankali ta dago kai ta na kallon face din shi ta ce " Da gaske ba za ka tafi wajen ta ba ? "
girgiza mata kai ya yi allamun a'a sannan ya daura da cewa " ashe haka a haka a ke so na ban sani ba ? "

yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " baby ai ki fa kowa sanin irin son da na ke yi maka "
" ni ban sani ba , gwada min ina wannan son ya ke " ya kai karshen ya na daga mata gera guda

" ba gashi nan ba " ta fada ta na nuna mishi saitin zuciyar ta da yatsa

a hankali ya matso bakin shi ya manna mata kiss saman forehead sannan ya ce mata " tashi ki je ki yi wanka ki yi sallat , zan je mosque yanzu zan dawo "
ya na gama fadar haka ya mike tsaye ya nufi door ya fice bedroom din

da kallo ta raka shi har sai da ya fita sannan ta saki wani cool murmushi ta sauko da ga saman gadon ta nufi toilet ta shiga dan ta yi wanka

Malik kuwa kai tsaye floor na uku ya sauko
bakin shi da sallama ya shigo parlourn , amma babu kowa
kai tsaye chair din shi ya nufa , ya zauna ya kai hannu saman table din geffen ta ya dauki laptop din shi da wata USB key da ke a sama

ya daura laptop din na shi saman Cinyar shi ya saka USB din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login