Showing 72001 words to 75000 words out of 100637 words
da sauri ya sa hannu ya na jijiga ta ya na kiran sunan ta , amma ina ko motsi ba ta yi
da gudu ya tashi ya fice dakin tun da ga cikin corridor din ya ke kwallawa MALIKAT INAS kira har ya fito parlour
RIANNA na ganin shi ta mike da sauri ta na fadin " Amir lafiya ka ke wa Ammie irin wannan kiran "
cikin fitar hayaci ya ke ce mata " please ina Ammie ta ke , Cutie ce , ban san abun da ke damun ta sai kuka ta ke na tambaye ta amma ta ki fada min "
da sauri ta raba ta geffen shi ta wuce ta nufi corridor ta shiga bedroom din Inaya
ta na shiga ta nufi bed din ta Haye ta riko shoulder din Inaya dukka biyu ta na jijiga ta ta na fadin " baby lafiya me ya same ki "
ba ta gama rufe bakin ta ba Amir da ke tsaye bayan ta ya ce " She is die ? "
shiru RIANNA ta yi ba ta ce mishi komai ba
cen kuma sai ta sauke ajiyar zuciya ta sauko da ga saman bed din ta kali Amir ta ce " Kar ka damu ina ga Period din ta su ka zo , ko last time haka muka sha fama da ita har suma ta dinga yi mana "
wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauke har sai da ya dan lumshe idanun shi
wani cool murmushi RIANNA ta saki kafin ta ce mishi " To Romeo , sai ka tafi bari zan kula da ita "
girgiza mata kai ya yi kafin ya ce " no zan kula da ita "
"okay " ta fada a takaice kafin ta juya ta nufi dressing room
ta na shiga ya nufi bed ya zauna a hankali ya daura hannun shi saman cikin ta , ya na shafawa a hankali ya san shi ne ke yi mata zafi har ta dinga kuka
ya na a haka RIANNA ta fito da ga cikin dressing room ta na rike da wasu kananan kaya blue color da wasu underwear sai dai pant din ta saka mishi pad ta karaso ta ajiye daya geffen gadon sannan ta ce ma Amir " ga kaya nan na fido mata , idan ta farka sai ta yi wanka ta saka , ina kawo mata drug din da zai rage mata ciwon ciki "
gyada mata kai kawai ya yi , da ga haka kuma ta sa kai ta fice dakin
ta na fita , Amir ya mike ya nufi toilet ya shiga
jim kadan ya fito ya nufi Inaya ya sa hannayan shi biyu ya dauke cak kamar baby ya koma toilet da ita
tom ni dai bari na tsaya da ga waje
After some minutes ya fito ya na dauke da ita , ya nado ta cikin wani towel fari ta kankame shi sai kuka ta ke kassa kassa
kai tsaye saman bed ya nufa ya , ya zauna da ita saman cinyoyin shi
ya kai hannu ya dauko kayan da RIANNA ta fido mata ya saka mata da kan shi sannan ya kontar da ita saman gadon ya janyo Duvet ya rufe ta har zuwa ciki sannan ya koma bakin gadon ya zauna ya na kallon babyn shi
cikin sanyin murya ya ce mata " Cutie please stop crying "
girgiza mishi kai ta yi kafin ta ce " Zafi na ke ji "
" Shikenan Cutie zai daina yanzu konta ki huta zan tafi mosque lokacin sallat ya yi " ya na gama fadar haka ya kai dan bakin shi ya manna mata kiss saman forehead din ta sannan ya mike
da sauri ta riko hannun shi ta ce " za ka dawo ? "
a hankali ya gyada mata kai allamun eh
wani cool murmushi ta saki kafin ta saki hannun shi ta lumshe idanun ta ta na sauke ajiyar zuciya
sai da ya ga ya dan dauki lokaci ya na kallon ta kafin ya juya ya fice dakin ya janyo mata kofar
ya na fitowa parlour RIANNA ta ce mishi " har ka gama kula da babyn taka "
bai ce mata komai ya sa kafa ya fice parlourn ya bar part din
sai da ya fita sannan ta saki wata yar karamar dariya ta ci gaba da latsa wayar ta
βͺAFTER SOME HOURS
bayan ya Kamala Sallar shi , sai da ya koma part din shi ya yi wanka ya sauya kayan shi sannan ya fito ya nufi part din MALIKAT INAS , amma ta hanyar sirri babu wanda ya ga fitowar shi
bakin shi da sallama ya shigo parlourn , nan ya tardo MALIKAT INAS tare da RIANNA su na zaune a parlour
cikin girmamawa ya nufi Ammie ta shi ya gaishe ta
cikin zolaya ta ce mishi " yau dan Amaryar ka na waje na shi ne ka zo ko , tun bayan dawowar ka da ga Makkah ba ka leko ni ba "
bai ce mata komai ba ya nufi hanyar corridor
da sauri ta ce mishi " wlh kar ka taba min yarinya ta , ka bar ta ta huta " ta kai karshen ta dariya ita da RIANNA
Amir kuwa kai tsaye bedroom din Inaya ya wuce
bakin shi da sallama ya shigo bedroom din , ta na nan konce yadda ya bar ta ko motsi ba ta yi ba
a hankali ya karaso cikin dakin ya cire sneakers din shi , ya Haye saman gadon ya konta ya janyo duvet ya rufe kafafun shi har zuwa kugu sannan ya daura hannu saman cikin ta ya na shafawa a hankali ya na kallon face din ta
[30/09 Γ 04:24] MEERAH πͺ·π©·:
β€β E X I L E D P R I N C E ββ€
(LOVE MEETS POWER ) ππ₯
ππ₯ ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) ππ₯
πβ€ MALLAKIN MEERAH β€π
γTHE ROYALTY LOVE πππγ
γ BOOK β¦β¦β¦β¦β¦β¦β¦β¦ 2 β€ πγ
____________________πππππππππππ___________________
PAGE 22 βπ
ya na tsaka da kallon ta ya ji wayar shi ta fara ringing
a hankali ya janye hannun ta da ga saman cikin ta , ya kai hannu ya fido wayar da ga cikin aljihun shi ya kali screen din
mikewa zaune ya yi ya gama bayan shi da forehead din gadon sannan ya dauki kiran ya saita wayar da face din shi
wata yar karamar dariya Diya ya yi kafin ya ce " Haba Amir ka yi min dan murmushi mana ? "
" lafiya ka kira ni , ba honey moon ka tafi ba , kyale ni " ya fada cikin tsare gida
" oh kar ka ji haushi fa , ba ni na hana ka tafiya ba , dama baby na ce ke son magana da sister din ta ni kuma ban da Number din ta shi ya sa na kira ka "
dan karamin tsaki Amir ya yi ya na shirin magana Ya jiyo Muryar Nesrine ta na fadin " ina wuni yaya Zayd "
gyada mata kai kawai ya yi amma ya ji dadin ganin ta cikin koshin lafya
wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta ce " yaya Zayd ina son ganin Inaya , ba mu yi sallama ba da ita "
bai ce mata komai ba ya juya wayar kan face din Inaya da ke faman kwana sannan ya dawo da wayar kan face din shi ya ce " ta na barci sai dai anjima ki kira ta "
" kai don Allah malam tashe ta " Diya ya fada cikin zolaya
" zo ka tashe ta idan ka isa " Amir ya fada cike da isa
yar karamar dariya Diya ya yi kafin ya ce " A yi min afuwa ran ka shi dade , dan sarki jikan Sarki , Malik din Saudiya baki daya , in sha Allah mu na tahowa Next week , idan baby na ta gama kula da ni " ya kai karshen ya na sumbatar kumatun Nesrine
yar karamar dariya ta yi ta sa hannayan ta biyu ta boye Face din ta wai ita ta ji kunya
shiru dai Amir ya yi ya na kallon su , ba karamin burge shi su ka yi , ya ji dadi ganin yadda su ke shaΖu da junan su lokaci guda haka , har cikin ran shi ya na musu adu'a Allah kar ya bar wani mugun abu ya ruguje musu wannan farin cikin nasu
ya yi nisa cikin duniyar tunanin shi ya jiyo Muryar Diya ya na fadin " Amir , ina son mu yi wata magana please "
gyada mishi kai Amir ya yi allamun ya na sauraron shi
kallon Nesrine Diya ya yi kafin ya ce " baby , za ki iya tafiya an jima zan sake kira miki ita "
gyada mishi kai ta yi kafin ta kali Amir ta ce mishi " sai an jima yaya Zayd , ka ce ma Inaya ina kewar ta sosai da sosai " ta na gama fadar haka ta juya ta bar wajen
ta na barin wajen Diya ya ce ma Amir " maganar auren Aymane ne da RIANNA "
" me ya faru ne ? " Amir ya tambaye shi
dan jinkirtawa Diya ya yi kafin ya ce " Amir auren nan bai konta min a rai ba , ina ji a jiki na wata muguwar manufa gare shi bayan auren nan , na san Aymane big bro di na ne , ban taba fada maka ba amma shi ne babban dalili na na baro Daular Ottoman , mu ka tafi Nigeria tare "
cikin rudu Amir ya ce mishi " me ka ke nufi ? "
ajiyar zuciya Diya ya sauke kafin ya ce " Aymane fa so ya ke ya zama Malik , dalilin ma da ya sa zai auri RIANNA , na san halin shi wlh ba son ta ya ke ba , kuma ni abun da ya fi tada min hankali shi ne ya na aiki da tsafi "
cikin nitsuwa Amir ya katse shi da cewa " wait ka na nufin dan tsubu ne shi ? "
" ban sani ba gaskiya , amma da na ke tasowa na sha ganin shi ya na wasu abubuwan da har yanzu ba zan iya fassare maka su ba , Yau din nan na yi wani mafarkin da ya girgiza tunani na , Amir duk abun da za ka yi ka sakawa Aymane Ido , duk da dan uwa na ne amma kar ka yarda da shi , wlh ya na da hatsari ba kadan ba "
ajiyar zuciya Amir ya sauke shi dama bai wani yarda da Aymane ba , dan tun lokacin da ya kama shi ya na yi wa Inaya irin kallon Sha'awa ya ji babu wanda ya tsana a duniyar nan sama da shi , in har abun da Diya ya fada mishi gaskiya ne , to kamata ya yi ya janyo Aymane a jiki yadda duk wani motsin shi zai kasance gaban idon shi , ko da kuwa ya yi kokarin kashe shi zai gano shi kafin ya aiwatar
" Diya , kar ka damu kai dai ka kula da matar ka , honey moon ku ka tafi , kar ka bari wannan tunanin ya bata muku....... "
bai kai karshen maganar shi Diya ya katse shi da cewa " Amir , maganar rayuwar ka da ta Inaya na ke maka magana a kai , zancen honey moon din mu kuma kar ka damu da ita , ba zan so silar ahali na ba wani abu ya same ka , ka sa a matso da ranar nadin ka please "
gyada mishi kai Amir ya yi kafin ya ce " shikenan , zan yi magana da Momy "
wani cool murmushi Diya ya saki kafin ya ce " yaushe ne ma da ranar nadin ni na manta "
" Ina ga ashirin ga wata ne "
dan zaro idanu Diya ya yi ya na cewa " Yau fa goma sha biyu mu ke "
Amir na shirin magana ya jiyo wata razananiyar kara da ga bayan Diya
ba shiri Diya ya mike da gudu dan ya san ba kowa ba ce sai Nesrine
Amir kuwa ya na ganin Diya ya bar gaban camera din ya katse kiran ya ajiye wayar shi saman bedside drawer ya na rokon Allah ya sa dai lafiya
bari mu leko su Nesrine mu ga
βͺDUBAΓ π¦
wani tanpasheshen Bedroom ne mai mugun kyau , komai na ciki white color ne , cen cikin dakin na hango wani wall na glass ka na iya hangen wani Teku Sky blue mai mugun kyau
cen na hango Nesrine zaune saman katafaren Bed din dakin ya na shinfide da wata bedsheet white color ta jingina bayan ta a jikin forehead din shi , ta na sanye da wata yar karamar riga dai'dai cinya blue colour mai mugun kyau
ta na a haka kawai Diya ya turo kofar dakin da karfi ya na fadin " Nesi "
" Na'am " ta fada mishi cikin sanyin murya
a rude ya karaso bakin gadon ya zauna ya na fadin " lafiya me ya same ki , ba ki dai ji ciwo ba "
girgiza mishi kai ta yi allamun a'a
ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce " to lafiya ki ka yi kara haka , kin san irin tsoron da na ji kuwa "
yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " Film na ke kallo " ta kai karshen ta na nuna mishi Tv din da ke fuskantar bed din da remote din hannun ta
slowly ya juya ya kali Tv din kafin ya juyo ya kale ta baki sake ya ce " Nesi , kin san irin tsoron da ki ka ba ni kuwa ? "
girgiza mishi kai ta yi ba tare da ta ce komai ba ta na ci gaba da kallon Tv din ta
kare mata kallo da kyau ya yi cikin zuciyar shi ya na fadin " Zan yi maganin ki " ya na gama fadar haka ya saki wani makirin murmushi ya sa hannu ya kwace remote din hannun ta ya tila saman bedside drawer ya Haye saman gadon ya janyo kafafun ta ta konta ya Haye saman ta ya mata runfa da kirjin shi
wata yar karamar kara ta saki ta na cewa " yaya Moussa ka kyale ni Film na ke kallo "
da sauri ya ce mata " yi min shiru , shi ne za ki tsorata ni ? Nesi ni tsaran wassan ki ne wai , na ga kwana biyu duk kin raina ni "
wani cool murmushi ta saki kafin ta zagayo da hannayan ta a bayan shi ta ce " uhmm , ni ban raina ka ba "
" to minene ? " ya fada ya na daga mata gera guda ya daura hannun shi saman kumatun ta
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " Duk cikin L.O.V.E ne "
wani cool murmushi ya saki kafin ya ce " sai kin kashe ni ki huta "
a hankali ta dago kan ta ya hade forehead din su ta ce " zan kashe ka da soyayya ta "
ba ta kai karshen maganar ta ba ta ji saukar Lips din shi saman nata ya fara kissing ta ido rufe
( πππa'a bari na koma inda fito wadanan har yanzu ba su Kamala honey moon din su ba )
βͺDAULAR SAUDIYA π₯
βͺAMIR
ya na ajiye wayar shi saman bedside drawer ya juya ya kali Inaya dai'dai lokacin da ta bude idanun ta
ta na ganin shi ta saki wani cool murmushi kafin ta yi magana ya riga ta cewa " cikin ki , ya daina yi miki ciwo ? "
a hankali ta gyada mishi kai kafin ta ce " Eh , amma har yanzu ina jin zafi kadan "
" kar ki damu zai daina " ya fada mata cikin sanyi murya
wani cool murmushi ta saki kafin ta juya ta rungumo kugunshi ta na fadin " baby yaushe za mu tafi Honey moon wai ? "
a hankali ya zame hannayan ta da ga kugunshi , ya konta ya janyo ta jikin shi ya rungume ya na kallon face din ta ya ce " ba yanzu ba "
turo dan bakin nan nata ta yi ta na ce mishi " to sai yaushe ? "
" Idan ki na sarar turomin wannan dan bakin naki sai na cinye shi , rigimamiya kawai " ya kai karshen ya na ja mata kumatu
yar karamar dariya ta yi har sai da dimple din ta ya lotsa ta ce mishi " ina son mu samu baby "
" ni kuma ba ni so "
matse gera ta yi ta na cewa " Why ba ka so ? "
dan jinkirtawa ya yi kafin ya ce " Ban shirya kula da wani babyn ba "
dan zaro idanu ta yi ta na cewa " yaya Zayd dama ka na da baby ban sani ? "
gyada mata kai ya a hankali sannan ya ce " ba ga shi nan ba tare da ni "
daga mishi gera guda ta yi ta na fadin " Uhmmm ni ce babyn ka ? "
bakin shi ya kai