Showing 66001 words to 69000 words out of 100637 words
ya sunkuyar da kan shi ya ci gaba da shan Tea din shi ,
[28/09 à 09:35] +234 806 127 3970:
❤⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
💔🥀 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) 💔🥀
👑❤ MALLAKIN MEERAH ❤👑
【THE ROYALTY LOVE 👑🕊💖】
Marubuciyar littafin
【TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺】
【 BOOK …………………… 2 ❤ 👑】
____________________🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊___________________
PAGE 20 ✍📚
babu wanda ya ce ma wani ufan har sai da Amir ya Kamala Breakfast din shi , MALIKAT AL'UMU ta kira su Dada su ka gyara wajen tsab
zaune ya ke saman doguwar Sofa , ya daura kafa daya bisa daya ya na latsa wayar shi
MALIKAT AL'UMU kuma ta koma saman sofar ta one seater ta zuba mishi ta na murmushi har ga Allah ta na mugun son gudan jinin ta , specially yanzu da mahaifin shi ba ya nan , sai ya yi mata mugun kama da Malik a lokacin da su ka yi aure
wani murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce " Amir Next week za ka hau kujerar Mahaifin ka , ka sani ko ? "
ba tare da ya dago kai ba ya ce mata " na sani , amma na ce su bari har ku Kamala Idda "
" why ? " MALIKAT AL'UMU ta tambayeshi
" ba na jin zan iya hawa kujerar Mulkin nan babu ke a kusa da ni "
wani cool murmushi MALIKAT AL'UMU ta saki kafin ta ce " Nawfel , duk lokacin da ka bukaci shawara ta ina nan mana , amma bai dace ba a ce Malik ya rasu kuma ya na da magaji amma a bar kujerar shi babu kowa a sama , hakan bai taba faruwa ba "
slowly ya dago kan shi ya marairaice fuska ya ce " yanzu momy ba za ku bari na kamo wanda ya yi wa Daddy haka ba , yanzu shikenan ya ci bilis kenan ? "
girgiza mishi kai MALIKAT AL'UMU ta yi kafin ta ce " kar ka damu General Abdellah ya na kan harkar yanzu haka , nan da lokaci kadan za su kamo shi , Idan ba ka hau Kujerar Mulkin ba , ko an kamo shi babu abun da za ka iya mishi saboda doka a hannun Malik ta ke "
ajiyar zuciya Ya sauke kafin ya ce mata " Shikenan Momy , a fara shirye shiryen na yarda zan karbi Mulkin "
" Alhamdoulilah " MALIKAT AL'UMU ta fada cikin zuciyar ta ta na murmushi
sannan ta ce mishi " Maganar MALIKAT kuma fa ? "
daga mata gera guda ya yi allamun bai gane ba
" ina nufin Yarinyar nan za a nada a matsayin MALIKAT ko kuma ka na son ka kara aure "
" why zan kara aure ? "
" ganin na yi yarinya ce , da wuya mutanan Fada su yarda a nada matsayin MALIKAT "
meda kallon shi ya yi kan wayar shi sannan ya ce mata " ba na bukatar amincewar su "
" Duk da hakan , me zai hana ka kara wani auren "
ba tai karshen maganar ta ba ya katse ta da cewa " momy ni fa babu aure a tsarin rayuwa ta , ko wannan kaddara ce kawai ta hada mu , kuma da ga ita ba zan kara wani ba " ya fada don shi har ga Allah ba ya tunanin zai iya auren wata macen a wannan rayuwar , ko ba dan ra'ayin shi ba , ba zai iya yi wa Inaya kishiya ba
( Ku ba shi hannu don Allah 😭😭 Gaskiya ka rike amanar malam , na san da wani ne sai ya yi hudu ma 🤧🤧 )
wani cool murmushi MALIKAT AL'UMU ta saki kafin ta ce " Na gode , ni ma ba na son maganar ka kara auren , da karancin shekarun ka ba zan so hankalin ka ya rabu tsakanin mata biyu ba , amma zan so yarinyar nan ta daina zuwa part din ka har ranar da za ka gabatar da ita a matsayin MALIKAT "
slowly ya dago kai ya kale ta ya ce " Why ? "
dan jinkirtawa ta yi kafin ta ce " ka ga ba mu kadai ba ne cikin masarautar , Kuma bayan mu ba wanda ya san ita matar ka ce , hakan zai iya janyo maka kananun magana , zan so ka bar ta a waje na har ranar da za a nada a matsayin MALIKAT sai ta tare a part din ka baki daya "
gyada mata kai kawai ya yi allamun to , ko shi zai so ta tare baki daya a part din shi
wani cool murmushi MALIKAT AL'UMU ta saki kafin ta ce " kafin nan fada min ka na son yarinyar nan ko kuwa ? "
" me ya sa ki ka min wannan tambayar "
" nothing , kawai na lura ne yadda ka damu da ita kamar rayuwar ka , shi ya sa na tambaye ka ko ka na son ta "
" momy dole na damu da ita saboda ita ce rayuwa ta , idan ba ni son ta zan aure ta ne ? "
yar karamar dariya MALIKAT AL'UMU ta yi kafin ta ce " Shikenan , ina jiran jikoki na tom "
dan zaro idanu ya yi ya na kallon ta wane jikoki kuma ? shi fa sam bai shirya haihuwa yanzu ba , at least nan da shekara biyar ya fi son har babyn shi ta kara girma yadda ba za ta samu matsala ba wajen haihuwa
ita dai MALIKAT AL'UMU shiru ta yi ta na kallon shi ta na murmushi
▪INAYA
da sallama a bakin ta , ta shigo parlourn MALIKAT INAS
babu kowa a parlourn Sai Aymane ya na zaune ya na latsa wayar shi
kamar ba ta gan shi ba ta wuce kai tsaye corridor
ta na tsaka da tafiyar ta ta jiyo Muryar shi ya na fadin " Ke ina za ki je ? "
cak Inaya ta tsaya ta juyo a hankali ta kale shi saman da kassa sannan ta tsuke fuska
dan tabe baki ya yi kafin ya ce " ke ina za ki je ? " ya fada da larabci
turo dan bakin nan nata ta yi ta na ce mishi " ni ka min magana da turanci , ba na jin larabci ! "
dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " Okay come here "
dan karamin gunguni ta yi kafin ta dawo a hankali cikin parlourn ta tsaya gaban shi dan nesa kadan ta rike hannayan ta a baya ta ce " ga ni "
Tsaya wa ya yi ya na kallon ta da ga sama har kassa , ya saki wani makirin murmushi kafin yace " what is your name ? "
cikin shagwaba ta ce mishi " Inaya Ibrahim "
dan gyada kan shi ya yi kafin ya ce mata " me ki ke yi a nan ? "
dan karamin murmushi ta saki kafin ta ce " wajen Aunty RIANNA , da Ammie na zo , kai wanene ban taba ganin ka a nan ba "
kwatancen murmushi ya saki kafin ya ce " ni abokin RIANNA ne , zan iya zama abokin ki ? " ya kai karshen ya na mika mata hannu
gyada mishi kai ta yi ta na shirin mika mishi hannu ita ma ta ji an rufe mata idanu ta baya
yar karamar dariya ta saki kafin ta ce " Aunty RIANNA , na yi kewar ki sosai "
murmushi mai dan sauti RIANNA ta yi kafin ta saki idanun Inaya ta tako ta koma geffen Aymane ta zauna ta na cewa " sai yau ki ka tuno da Auntyn ki ko ? "
turo dan bakin nan nata ta yi kafin ta ce " Aunty fa duk shekaran jiya ne fa na tafi kuma ai ke ki ka ce na tafi "
yar karamar dariya RIANNA ta yi kafin ta ce " Shikenan na ji , shiga ciki Ammie ta na nan "
gyada mata kai Inaya ta yi ta na murmushi sannan ta juya ta nufi corridor ta shige abin ta
sai da ta shiga sannan Aymane ya juya ya kali RIANNA ya ce " Who is She ? "
dan karamin murmushi RIANNA ta yi kafin ta ce " she is my sister , Inaya "
" but a sani na Amira Tesnim ita kadai ce kanwar ki "
gyada mishi kai ta yi kafin ta ce " Eh " a takaice kafin ta sunkuyar da kai ta fara latsa wayar ta
dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " Mrs Aymane , batun auren mu kuma fa ? "
ba tare da ta dago kai ba ta ce " Duk lokacin da ku ka shirya "
" okay , me zai hana a yi auren ranar da a ke nada Malik ? ko ya ki ka gani "
" uhm no wonder " ta fada a takaice
cikin sanyin murya ya ce mata " please RIANNA , ki ban hankalin ki mu yi magana , Idan ba ki son auren nan ki fada min tun kafin mu yi nisa "
slowly ta dago kai ta kale shi ta saki wani dan karamin murmushi ta ce " kar ka damu , kawai dai ba na jin dadi zan rabu da family na , zan rabu da Amir bayan tsawan shekarun da na yi ba ya tare da ni "
dan karamin murmushi ya yi kafin ya kai hannu ya riko nata ya ce " za ki samu Sabuwar Family , kuma zan kasance tare da ke , zan so na barki cikin ahalin ki , amma kin san ba dai'dai ba ne "
" please mu zauna a nan mana , akwai part dayawa cikin masarautar nan da har yanzu ba a bude su ba , me zai hana mu zauna a nan , ba na jin zan iya rabuwa da Amir , specially yanzu da zai hau mulkin Malik na san zai bukace ni a kusa shi "
marairaice fuska ya yi ya na fadin " masarautar tawa kuma fa ? Family na za su ga kamar ba za ki iya zama tare da su ba ne , ni na rassa ya zan yi wlh , auren nan sam ba ya cikin tsarin rayuwa ta , amma kuma da na gan ki na ji na kamu da son ki , kuma ba na jin zan iya janye maganar auren nan "
dan karamin murmushi ta saki kafin ta ce " shikenan ba komai " ta kai karshen ta na janye hannun ta da ga cikin nashi
wani cool murmushi ya saki kafin ya ce " ni zan tafi "
gyada mishi kai ta yi kafin ta ce " amma za ka dawo gobe ko ? "
daga mata gera guda ya yi ya na cewa " ba za ki iya yin kwana guda ba ki gan ni ba ko ? "
yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " shikenan tashi ka tafi ka fara damu na "
mikewa tsaye ya yi kafin ya riko hannun ta ya dan sunkuyo ya manna mata kiss saman hannun ta ya ce " Sai na dawo Gimbiya ta " ya na gama fadar haka ya saki hannun ta ya mike ya juya ya fara takawa ya fice parlourn ya bar part din
ya na fita ko Inaya ta fito da ga cikin corridor ta na fadin " Aunty RIANNA ba ki ga waya ta ba "
dan karamin murmushi RIANNA ta yi kafin ta ce " zo zauna ki ji "
ba musu Inaya ta karaso geffen ta ta zauna ta na turo dan bakin nan nata
dafa Shoulder din ta RIANNA ta yi kafin ta ce " my baby kin ga wani haske da ki ka kara , kin yi wani Fresh kamar wadda a ke yi wa barin madara "
turo dan bakin nan nata ta yi kafin ta ce " Aunty minene kuma barin madara "
yar karamar dariya RIANNA ta yi kafin ta ce " idan kin je ki tambayi Amir , yanzu fada min ya ki ka baro min dan uwana , Allah ya sa dai kin kula da shi yadda ya dace "
" Shi dai ya kula da ni " ta fada cikin shagwaba
zaro dan idanun ta RIANNA ta yi kafin ta ce " da gaske ki ke ? to me ya sa ki ka baro shi yanzu ? "
" wajen Momy mu ka zo yin breakfast , shi ne na taho dan na gan ki , ni yanzu Aunty RIANNA ina waya ta pleaseeeee " ta kai karshen ta na marairaice fuska
yar karamar dariya RIANNA ta yi kafin ta ce " Tashi ki je ta na cikin Bedside drawer "
ba ta gama rufe bakin ta ba Inaya ta mike da gudu ta nufi corridor ta shiga
da kallo RIANNA ta raka ta har ta shiga sannan ta ce " oh ni RIANNA yanzu haka Amir ke fama da wannan rawan kan nata "
ta na a haka Inaya ta fito da ga cikin corridor ta na cewa " Aunty RIANNA , ina Nesrine ta shiga ne ? "
" sun tafi Honey moon Ita da mijin ta "
" Aunty ni ma ina son na tafi Honey Moon " ta fada ta na tsayawa gaban RIANNA ta na latsa wayar ta
Dan karamin murmushi RIANNA ta yi kafin ta ce " kar ki damu in sha Allah nan da Next week ni da kai na zan shirya muku Honey moon "
yar karamar dariya Inaya ta mikawa RIANNA wayar ta na cewa " Aunty saka min number din Nesi ina son na kira ta "
hannu RIANNA ta kai ta karbi wayar ta saka mata numbar Nesrine ta yi mata saving sannan ta mika mata wayar
hannu ta kai ta karbi wayar ta murmushi ta ce " Na gode Aunty , ni zan tafi garden " ta fada ta na fara takawa ta nufi hanyar fita parlourn
da sauri RIANNA ta ce mata " amma za ki dawo ko baby ? "
ba tare da ta tsaya ba ta ce " eh zan dawo an jima " ta kai karshen ta na ficewar ta
da kallo RIANNA ta rakata har ta fita sannan ta saki wani dan karamin murmushi ta shiga latsa wayar ta
Inaya kuma kai a sunkuye ta na latsa wayar ta , ta fito Part din MALIKAT INAS
kai tsaye hanyar garden ta nufa ta na tafe ta na sakin murmushi
ta na tsaka da tafiyar ta , ta ji ta bugi mutun har wayar ta , ta fadi
dan karamin kukan shagwaba ta saki ta na dago kai ta ce " dubi don Allah ki yarda min waya ta " ta kai karshen ta na sunkuyawa za ta dauki wayar ta
babu ko tausayi Hafsat ta daga kafa ta take hannun Inaya
wata yar karamar kara ta saki ta na dagowa da karfi ta ture Hafsat da hanayan ta biyu ta fadi kassa kan ta ya bugu cikin wani dutse
wata razananiyar kara Hafsat ta saki kafin dan ba karamar buguwa ta yi ba
Inaya kuma ko a jikin ta sai ma daukar wayar ta da ta yi ta fara takawa ta bar wajen ta nufi garden ta na duba wayar ta
abun kamar an shirya yanzu ma sai ji ta yi ta bugi mutun amma wayar ta ba ta fadi ba
slowly ta dago kai ta kali Rouksar ta ce mata " wai duk kun koma makafi ne ? in kun koma ku fada min na dinga sauya hanya idan na gan ku "
ba karamar fusata Rouksar ta yi ba ta daga hannu za ta wanka ma Inaya mari
cak ta taro hannu ta na kallon ta cikin ido ta ce " Kar ki kuskura ki ce za ki taba ni , wlh wlh sai na lahira ya fi ki jin dadi "
wata yar iskar dariya Rouksar ta yi kafin ta janye hannun ta , ta matso dab da fuskar Inaya har su na iya jiyo nunfashin juna murya kassa kassa ta ce mata " Ki bar ganin ki na karkashin kulawar Amir , ina iya zama mumunar mafarkin ki "
ta na gama fadar haka idanun ta su ka juye kamar yadda a ke juya PAGE din littafi , su ka koma kamar na maciji
sai da na ji gaba ya fadi dan ba karamar razana nayi ba , tunda na ke ban taba ganin irin wannan abun ba kenan ba banza Amir ya ce mata mai idanun maciji ko kuwa ?
abun mamaki kawai sai Inaya ta yi wata yar karamar dariya ta ce " idanun maciji ? Hmmm tsaya na gwada miki nawa "
ta na gama fadar haka ta lumshe idanun ta , ta sake bude su a hankali
Dum Rouksar ta ji zuciyar ta ta buga , ba shiri idanun ta su ka koma kamar da farko ta ja baya kadan ta na kallon Inaya da idanun ta su ka koma baki kirin ko digon fari babu
wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " Idan wannan bai miki ba ina da wani "
ta kai karshen ta na lumshe idanun ta