Showing 75001 words to 78000 words out of 100637 words

Chapter 26 - Exiled Prince Book Two Complete Hausa Novel

24 Oct 2025

205

ya sumbaci forehead din ta ya ce " yeah you're my baby "

wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " amma ni yaya Zayd ina son mu samu baby , me kama da kai , na saka shi a gaba na yi ta kallo "

" ki bar zancen baby , ke da samun baby sai dai wani ikon Allah "
cikin rudu ta ce mishi " yaya Zayd ban gane ba ? "
a hankali ya lumshe idanun shi bai ce mata komai ba , shi sam ba ya tunanin zai iya kula da baby cikin rayuwar shi , babyn ne ma sam ba ya so , ya na tsoron ya rasa ta wajen haihuwa , shi ya sa ya cire rai da ga samun baby cikin rayuwar shi

ya yi nisa cikin tunanin shi kawai ya ji ta kontar da kan ta saman kirjin shi ta na sauke ajiyar zuciya
bari dai mu dan tsagaita labarin



β–ͺAFTER SOME DAYS


yau dai ta kama ashirin ga wata , ranar nadin Amir a matsayin Malik

Tsaye Inaya ta ke cikin parlourn MALIKAT INAS , ta sanye cikin wata dankareriar gown Gold color mai mugun kyau har jan kassa ta ke , ta daura wata Alkyaba Fara kal da ga sama , an yi mata simple make up sai tashin qamshi ta ke , da ga gani kassan yau shirin na musaman ne

ta na tsaye a haka Nesrine ta shigo parlourn ta na sallama
Inaya na ganin ta ta saki kara ta nufe ta da gudu ta rungume ta ta na sakin kara
da gudu RIANNA ta fito da ga cikin corridor ta na fadin " baby lafiya me ya same ki ? "

cak ta tsaya tsakiyar parlourn ta na kallon Inaya da Nesrine rungume da juna
wani irin kyawatencen murmushi ta saki ta nufe su da sauri ta rungume su a tare ta na fadin " oyoyo Nesi ta dawo " ta kai karshen ta na raba jikin ta da nasu

a hankali ita ma Inaya ta raba jikin ta da na Nesrine ta riko hannayan ta ta na fadin " Nesi na yi kewar ki over "

wani cool murmushi ita ma Nesrine ta saki kafin ta kai hannu saman kumatun Inaya ta ce " Ni ma na yi kewar ki sosai baby na , da fatan na same ki lafiya , gaskiya yaya Zayd na kula da ke , dubi yadda ki ka yi haske , kin yi wani Fresh Masha Allah kamar na sace ki "

wani dan karamin murmushi Inaya ta yi ta na sunkuyar da kai wai ita ta ji kunya

wata yar karamar dariya RIANNA ta yi ta ce " a'a Nesi ke dai ki ka yi haske , gaskiya Diya ya iya kula da mace , ki ce mu fara tara kayan baby ? "

wata yar karamar dariya Nesrine ta yi ta na shirin Magana Tesnim ta shigo ta na kwallawa Inaya kira

" Aunty Tesnim me ya faru ? " Inaya ta fada

cike da zumudi Tesnim ta kamo hannun Inaya ta na fadin " baby mu tafi yanzu a ke shirin nada Amir yi sauri "
ta kai karshen ta na jan Inaya su ka bar wajen da gudu kamar kananan yara

da sauri ita ma RIANNA ta riko hannun Nesrine ta ce " mu tafi kar a yi ba da mu ba "
gyada mata kai Nesrine ta yi kafin su fara takawa cikin nitsuwa su ka bar part din

a tare su ka nufi hanyar babbar Fadar Malik , yau masarautar cike da mutane , duk wata masarautar da ke karkashin Mulkin Daular Saudiya sai da ku halartu a fadar , har shi kan shi Sarkin Daular Ottoman

da sallama a bakin su , su ka shigo Fadar ta kofar mata
dan Fadar an raba ta gida biyu , mata nasu wajen daban , Mazan nasu wajen daban Sai kujerar Malik ta zalar Gold an kawata ta da wasu diamond har kyali ya ke , geffen Kujerar akwai wata chair ita ma amma ba ta kai girman ta Malik ba , amma ita ma ta Gold ce har da diamond da Allamun ta MALIKAT ce

cen su ka hango Inaya zaune saman wasu lamusasun sofas ita da Tesnim
kai tsaye wajen su su ka nufa , su ka zauna , duk wani wanda ke cikin masarautar sai da halar ta , MALIKAT AL'UMU da MALIKAT INAS ne kadai ba su cikin wajen saboda Takaba da su ke yi , amma duk abun da ya ke faruwa cikin Fadar su na gani ta camera

su na a haka wasu jibga jibgan sojoji sanye da kakinsu kowane rike da manyan bindigu su ka fara shigowa Fadar da gudu su ka zagaye ko ina
da sauri Diya ya shigo cikin Fadar ya nufi bangaran Maza ya zauna saman wata sofar

ya na zama Wasu dogarai su ka fara shigowa , su ka tare hanyar wuce , su ka bude manyan rigunan su ta yadda ba ka iya ganin komai da ga zaune

su na a haka su ka fara jiyo a busa Algaita duk Fadar ta dauki sautin
daya bayan daya su ka fara mikewa su na sunkuyar da kan su
da sauri ita ma Inaya ta saka hular Alkyabar ta , ta sunkuyar da kai ta na kallon kassa ta wutsiyar ido

su na a haka su ka jiyo wani dadaden qamshi mai sanyaya zuciya ya gwauraye Fadar baki daya , duk irin qamshin da ke cikin fadar sai ya kashe shi

a hankali ya Shigo Fadar , ya na taku cike da Izza , ya na sanye da wasu manya kaya irin na gidan Sarauta , da ga ganin kayan ka san miliyoyi a ka kashe musu Alkyabar jikin shi ma kadai ta kai wajen one hundred million , dan zaren da a ka yi mata zane ma na gold ne , duwatsun da ke cikin ta zallar diamond ne

tun da ya shigo , duk sojojin wajen su ka fara daga kafa su na sara mishi ji kawai ka ke dip dip dip kassar har girgiza ta ke

kai tsaye Kujerar Gold din nan ya nufa a hankali ya juya ya zauna saman kujerar
ya na zama ko sautin Algaita ya fara tashi cikin fadar , da sauri dogaran da su ka tare bangaran Maza su ka saki manyan rigunan su , su ka koma da ga baya gaba kadan da sojojin nan su ka tsaya

su na tsaya wa Wani dattijo Fari kal ya tara kyasumba har zuwa saman kirjin shi , da ga gani zai kai shekara 60 ko fi , ya na sanye da manyan kaya , ya na rike da wani Abu kamar box haka nade cikin wani farin Tissu
( Ina ga kamar Kur'ani ne πŸ€”πŸ€”πŸ€” a nawa tunanin )

a hankali ya fara takawa ya nufi gaban Amir ya tsaya
( Ni dai ban san ko wanene ba gaskiya πŸ˜‘πŸ˜‘, amma bari mu duba labarin shi kadan )

RAFIK BILAL wannan shi ne babban Wazirin Malik , da ga Malik sai shi indai a ciki Fada ne , shi da hannun shi ya nada Malik HICHAM bin JAABAR , kuma shi zai nada Malik Nawfel Bin Jaabar yanzu , duk cikin Fadar , da ga Sarkin bayi , Sarkin dogarai da sauran su duk a karshin shi su ke , duk wata shawara da Malik zai yanke tare da Rafik ya ke yanke ta , yanzu kuma Amir zai zabar nashi Wazirin , wanda ko Amir ba ya nan za a iya tunkarar shi , kuma idan ya yanke shawara ta zaune tamkar Malik ya yanke ta




[01/10 Γ  09:39] MEERAH πŸͺ·πŸ©·:



❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀
(LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯





( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )





STORY & WRITTEN BY : MEERAH πŸ‘‘πŸ”₯



Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA πŸ’–πŸ’πŸŒΊ




TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i




_________________________β€»β€»β€»β€»β€»___________________________






BOOK .....................2 β€βœπŸ“š






β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘




PAGE 23 βœπŸ“š




Murya sama sama yadda kowa ke jin shi ya ce " Al-Amir Nawfel Hicham bin Jaabar , Ka yi rantsuwa da Kur'anin da ga ke cikin hannu na , za ka kula da masarautar Saudiya ? "

a hankali Amir ya daga Hannun shi ya daura saman Kur'anin murya cen kassan makoshi yadda Rafik ne kadai ya jiyo shi ya ce " Na yi rantsuwa da Alkur'ani mai girma zan kula da Masarautar Saudiya "

" Za ka rike Mulkin Saudiya cikin gaskiya "

a hankali Amir ya gyada kan shi kafin ya ce " Na yi Alkawari "

" za ka yanke hukunci kamar yadda Shari'ar mu ta musulimci ta tanada "

" Na yi Alkawari , zan kula da Saudiya tamkar rayuwa ta , Zan kare ta tare da Al'umar da ke cikin ta , Zan bawa me gaskiya gaskiyar shi , wanda ya yi laifi kuma zai fuskanci hukunci dai'dai laifin da ya aikata ko da kuwa Ni ne , na yarda zan fuskanci hukuncin da ya dace " ya fada dan ya fara gajiya da tambayoyin Rafik , shi so ya ke a yi da sauri ya bar wajen ya na da aikin yi

wani cool Murmushi Rafik ya saki kafin ya janye Kur'anin Ya juya ya kali dogaran da ke tsaye a baya ya gyada musu kai a hankali

juyawa ya yi ya ajiye kur'anin hannun shi saman table din da ke geffen Chair din Malik
dai'dai lokacin da dogaran nan su ka karaso wajen rike da wasu Tissu farare kal
hannu Rafik ya kai ya karbe su , ya bude ashe Rawani ne
cikin nitsuwa ya nadawa Amir Rawanin nan sannan ya ja hular Alkyabar ya rufe mishi kai , ba ka iya ganin komai sai wadanan Hazel eyes din nashi

ya na gama nadawa Amir rawanin shi ya koma wajen sofar da ya taso ya tsaya

ya na tsayuwa ko , dogaran da su ka tare bangaran Mata su ka sauko da rigunan su , su ka koma baya da sauri sauri

Slowly Inaya ta dago kan ta , ta kali Amir Dum ta ji gaban ta ya fadi , dan ba karamin kwarjini ya yi mata ba
ba ita kadai ba , duk matan wajen sai da su ka ji zuciyoyin su sun buga , gaskiya Mulki na kama Amir , specially irin zaman nan da ya yi na izza na Mulki , nan take Hafsat , Muntaz da Rouksar su ka ji wani mugun son shi cikin zuciyoyin su a tare ji su ke kamar su hadiye shi , ga kyau , ga kudi , ga Mulki ai kowace macen da ke wajen sai ta kamu da son shi , ita dama Inaya ta jima da son shi cikin zuciyar ta , ba abun da ya sauya kawai ta tsaya ta na kallon shi ta na sakin Wani cool murmushi

RIANNA ma murmushi kawai ta saki , gaskiya ta na alfahari da dan uwan ta , har kawo ruwa idanun ta su ka yi

su na a haka su ka Jiyo Muryar Rafik ya na fadin " Al-Malik Nawfel bin Jaabar "

a tare duk dogaran wajen su ka daga murya su na fadin " Allah ya ja zamanin mai martaba " har sau biyar
sojojin nan kuma su na ta sara mishi

sai da su ka Kamala sannan Rafik ya koma saman sofa din shi ya zauna
a tare duk mutanan wajen su ma su ka zauna saman sofar su , kowane ya zubawa Amir
( Kut Yanzu Malik ya ke 🀭🀭🀭🀭 )

kowane ya zubawa Malik ido , shi kuma ya kurewa Kofar fita Fadar ido ya na jiran kawai a Kammala ya tashi ya bar wajen da gudu , akwai wani abu na musaman da ya shirya yi

ya na a haka ya jiyo Muryar Rafik ya na fadin " Ranka shi dade mai grima Malik , lokaci ya yi da za ka zabar wanda zai maye maka gurbi na , bisa tsarin masarautar nan "

gyada kan shi Amir ya yi a hankali kafin ya nuna Diya da yatsa ko tunani bai tsaya yi ba
dan Zaro idanu Diya ya yi ya na kallon Malik ya saki wani cool murmushi kafin ya mike tsaye , ya karaso gaban Malik ya zube saman guyiwowin shi

a hankali Malik ya daga hannun shi ya daura saman kan Diya
ya na aza shi Diya ya ce " na yi Alkawari zan taya mai girma Malik rike Saudiya da hannun gaskiya "

ya na gama fadar haka Malik ya janye hannun shi
slowly Diya ya mike ya juya ya nufi gaban Rafik ya Zube saman guyiwowin shi
cikin nitsuwa Rafik ya zame rawanin kan shi , ya nadawa Diya
sai da ya Kamala nada mishi rawanin sannan Diya ya mike ya koma geffen daman Malik ya tsaya ya rike hannayan shi a baya ya ce " Bismillah "

a hankali kowane ya koma ya zauna , su ka fara kuskus kowane da abun da ya ke fada

a hankali Inaya ta rage sautin Muryar ta , ta ce " Aunty Tesnim , Me ya sa shi yaya Moussa bai zauna ba ? "

rage sautin Muryar ta ita ma Tesnim ta yi kafin ta ce " Da ga yanzu shi ne na hannun daman Malik , duk wata magana da Malik zai yi a bakin Diya za a ji ta "

yar karamar dariya Inaya ta yi kafin ta ce " kenan shi Malik ya koma kurma ? "

girgiza mata kai Tesnim ta yi cikin sanyin murya ta ce mata " a'a , kawai haka tsarin masarautar mu ya ke , ba a so a ji Muryar Malik , shi ya sa ki ka ga Diya ya tsaya a geffen shi ta yadda duk abun da zai fada Diya kadai zai ji shi "

" Shikenan yanzu an nada shi a matsayin Malik ? "

gyada mata kai Tesnim ta yi allamun eh

" shikenan ku tashi mu tafi ko ? "

RIANNA ta amsa mata da cewa " a'a babu inda za ku tafi , ba a nada MALIKAT ba "
slowly Inaya ta juyo ta kali RIANNA ta ce " Aunty RIANNA wace MALIKAT kuma ? "
wani cool murmushi RIANNA ta saki kafin ta ce " Za ki gani ke dai duk abun da a ka ce miki , ki yi shi kar ki yi magana "

da To Inaya ta amsa mata kafin ta juya ta kali Malik dai'dai lokacin da wani dogari ya shigo Fadar ya na rike da wata Box ta Gold ya nufi Rafik ya Zube saman guyiwowin shi ya mika mishi Box din

hannu Rafik ya kai ya karbi box din sannan ya mike tsaye cikin girmamawa ya ce " Ranka shi dade Malik , Lokaci ya yi da za a nada MALIKAT din ka , ga Alkyabar MALIKAT AL'UMU "

da sauri Sarkin bayi Mohammed ya mike ya ce " cikin Dukkan girmamawa ran ka shi dade Malik , kowa a nan ya sani ba ka da aure , ina ga ba sai an nada MALIKAT ba a yau "

slowly Rafik ya juya , ya kali Sarkin bayi ya ce " ba zai yi yu ba , rana guda a ke nada Malik tare da MALIKAT din shi , ga yan mata a nan zaune , ya zabi koma nawa ya ke so a aura mishi ita , a nada MALIKAT "

wani Makirin murmushi Mohammed ya saki dama da gangan ya yi hakan
dan sunkuyar da kai ya yi kafin ya ce " ran ka shi dade mai girma Malik , ga yar uwarka Hafsat , na baka auren ta a aura muku aure da ita , Idan har Mai girma Malik ya amince "

Gyada kan shi Rafik ya yi kafin ya ce " Masha Allah , hakan ya yi kyau "

slowly ya juya ya kali Malik ya ce " Mai girma Malik , zan kasance Waliyin ka , a aura maka ita a yanzu , a nada ta a matsayin Malikat "

shiru shi dai Malik ya yi bai ce komai ba bai ce musu komai ba
shi ko Rafik a tunanin shi Malik ya Amince kawai sai ya juya ya kali Mata ya ce " wacece Hafsat Mohammed a cikin ku "

da sauri Muntaz ta mike ta fice Fadar da gudu ta na kuka
da kallo duk su ka raka ta har sai da ta fice sannan Rafik ya sake maimaita tambayar shi

cikin kissa da kisisina Hafsat ta mike ta yi taku biyu gaba ta sunkuyar da kai ta na sakin Murmushi

Slowly Rafik ya juya ya kali Malik sai dai kafin ya yi magana Malik ya daga mishi hannu allamun ya yi shiru
ba musu Rafik ya yi shiru ya na kallon Malik

Da dan yatsar shi ya yi wa Diya allamun ya guso
da sauri Diya ya sunkuyo ya kai kunnen shi wajen face din Malik

cikin sanyin murya Malik ya ce mishi " ka yi abun da na ce maka "
wani kyawatencen murmushi Diya ya saki kafin ya gyada kan shi ya mike tsaye

kallon Hafsat ya yi ya ce mata " Za ki iya komawa ki zauna "
a tare duk mutanan wajen su ka zaro idanu Hafsat kuwa sai da ta dago kai ta kali cikin idanun Diya ba shiri nan take murmushin da ke saman face din ta bace

da sauri Mohammed ya ce " amma ranka shi d...... "

bai kai karshen maganar shi ba Diya ya katse shi da cewa " a'a Sarkin bayi ,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login