Showing 27001 words to 30000 words out of 98628 words
a falo zaune da waata na'ura akan cinyarsa ya na Dubawa.
Daga nesa da shi na Tsaya ina fad'in"Manja zan saka maka ko Mangyad'a?
Kansa ya dago ya na kallona kafin yace"Kinsan Ra'ayina ko? Sakamin manja"
Sai na juya na koma a karamar kula na saka masa Danwaken sai na dauko masa Filet da cokali da ruwa.
Manjan ma dabam na sako masa sai Roban yajin duk na jera a gabansa.
Ina durkushen nace"yaji kada ka cika ya na da fad'a"
Batare da ya kalleni ba yace"I see. Ko daga yadda kika jigata nasan ya na da fad'a."
Sai da ya fad'an na kara bin kaina da kallo sai na kara yarda ma kaina a jigace nake.
Sad'af Sad'af kamar barauniya na mike na shige bedroom da sauri.
Ba Kasafai na ke kara yin wanka bayan na yi da Safe ba ammh yau ta kamani dole sai na kara.
Nima kamar shi da ruwan sanyi na yi wanka naji dadi har raina da naga da Soson wanka na ya yi amfani.
Da na fito daga wankan ban ko shafa mai ba na bude wardrope na Dauko Atamfa riga da zani na saka na Daura Dankwali.
Sai na kasa fita falo Saboda kunya na yi zamana aciki.
Zanina da na ke wanka da shi na gani an shayamin saman kofar Tiolet na tashi na taba sai naji da Danshin Ruwa.
Sai nasan da shi ya yi amfani kila ya goge jikinsa tunda nikam ban tsaya Daura wani zani ba na fad'a wanka.
Gajiya na yi da zaman cikin na fito salau salau kamar kazar da kwai ya fashe mata acikin cikinta.
Hankalinsa na kan Na'urar gabansa da ya ke ta dannata sai nima yaja Hankalina.
Kasa na zauna a kujeran da ke fuskartsa ina kallonsa hannunsa baya gajiya Tab! Tab! Kana jin karan abunda ya ke dannawa.
Sai naji ya Burgeni abu kamar aljani bansan ya juyo ya na kallona ba, saboda shagala da kallonsa ina mirmishi sai ji na yi kamar daga sama yace"Kwashe kaya nan na gama tun daz'u."
Sai na yi kamar na Firgita kafin na shiga Raba ido ina Fad'in"Eh."
Bai kara kallona ba yana cigaba da abunda ya ke yi yace"Eh nace ki kwashe su ki kai kitchen.".
Da sauri na mike na fara Tattarawa na mike na zuwa kitchen sai da nashiga sannan na duba naga yaci Danwaken da yawa kadan ya rage.
Sai na ijiye masa sauran ina Tunanin kila anjuma zai bukace shi.
Abunda ya bata na ke wankewa naji bude get da Shigowar mutum.
Sai chan naji muryan Ummi kamar ta na mgana a waya ne.
Ban jira ta bugamin kofa ba ina gama wanke abunda ya bata na kifesu a kwando na fito zuwa kofar dakina.
Sai alokacin ya bi ni da kallo tun ba ma Siraran kafafuna ba.
Ya na mamakin yadda na ke da karfi da Kuzari ashe abun ba daganan take ba.
Ina bude kofar na ci karo da Ummi ta na saka wayarta a jaka.
Cikin washe baki muka tarbi juna na yi mata sannu da hanya muka gaisa sannan ta karisa dakinta ta bude ta shiga ni kuma na maida kofata na kulle na dawo cikin Falon.
Diri diri na yi tunda ni dai ban saba da shi ba, sai na yi tunanin na koma ciki na kwanta zuwa la'asar kafin ya tafi.
Na kama hanya kenan naji ya na fad'in"Kin yi kawa ne?
Sai na juyo ina kallonsa kafin nace'"Amaryan da ta tare ni kwanakin baya Sunanta Ummi."
Jinjina min kai kawai ya yi batare da ya kara mgana ba ni kuma sai na yi wuf na fad'a ciki.
Ban cika barcin rana ba saboda ban saba ba.
Gwara ma kwanaki kafin na samu waya na kan kwanta na rasa na yi na yi ta tunanin rayuwa har barci ya kwasheni bansani ba.
To yau ma hakane ya faru kwanciyata ba Dadewa barci mai nauyi ya kwasheni.
Barcin da har akayi la'asar bansani ba shi kuma ba ma'abocin yin salla agida ba ne fita ya yi ya nemi masallaci ya yi sallansa ya dawo ya cigaba da aikin da ya ke wani aiki ne aka ba su daga wajen aikin su.
Baisan barci na ke yi ba ya dauka na yi salla ban fito ba ne saboda zamansa a falon shi kuma sai ya samu kansa da Sakewa sanin ina cikin Dakin.
In da yana chan dakin ne bazai iya wannan aikin ba kadaici da kewa duk zata addabeshi ya kasa yin komai.
Sai da yaji ana ta bugamin kofa ne kuma yaga ban fito ba sannan ya tashi ya leka cikin Bedroom din yaga ina ta barci hankalina kwance.
Bai tasheni a lokacin ba jin ana ta buga kofar yasa ya juya ya fita yaje da kansa ya Bude.
Ummi ce ta kawo min abinci ta na ganinsa duk da bata taba ganin mijina ba amnh tasan ba wanda zai shigar min daki a wannan Lokacin in ba Mijina ba.
Da sauri ta gaisheshi ya amsa da Lafiya lau bai kuma saki fuska ba.
Cikin sauri Ummi tace"Hasiya fa?
Kai tsaye yace"Ta na barci."
Ummi sai ta mika masa kulan Hannunta ganin yadda ya wani Daure Fuska ta na fad'in"Ok ga shi na ta ne."
Ba musu ya saka hannu ya karb'a Lokaci daya ya na fadin"An gode."
Daga haka bai jira cewarta ba ya maida kofar ya Rufe a saman Fuskar Ummi da ta rike baki ta na bin kofar da kallo.
A ranta tace Mijin Hasiya ba shi da Fara'a daga haka ta wuce ta koma Dakinta itama ta maido kofarta Ta rufe.
Kitchen din ya shiga da kansa ya ijiye mata kulan, sai kuma ya tsaya ya na Dube Dube sai ya fahimci ta na bukatar cefane tunda ga yan kayan miyan nan ma duk sun bushe da ta shanya a kasa kuma ma ba su da yawa sosai.
Fitowa ya yi daga kitchen din ya na wani nazari hakkin sa ne cafane da komai da komai ammh kuma shi bai san yadda tsarin zai tafi daidai ba.
Wasu abubuwan bai san su ba tunda shi bako ne a harkan.
Har sai da ya zauna sannan ya tuna da cewa Bai tasheni ba.
Sannan ya kara mikewa ya koma Bedroom din daga bakin kofar ya tsaya bai shiga ba ya na kiran sunana a Hankali.
A cikin barci naji kamar ana kiran sunana ban tashi ba domin na Dauka ina cikin mafarki ne.
Sai na juya har ina gyara kwanciya sai naji an ja kafata lokaci daya ana fad'in"Bazaki tashi ba?
Sai alokacin na tabbatar da cewa ba mafarki ba ne.
A sannu sannu na bude idanuwana sai ga shi fes a kansa ya na tsaye ya harde hannayensa saman kirjinsa ya na kallona, kara lumshe idanuwana na yi saboda har Lokacin barci ne acikin idanuwana.
Ganin haka yasa ya kara ja min yatsan kafata ya na fadin"Tashi ki yi sallah mana."
Kasa ta shi nayi sai naji gabadaya gabbaina sun saki sai na kara juyawa ina Umh.!
Ammh na kasa ta shi batare da Tunanin komai ya saka hannunshi Guda d'aya ya Dago kaina sai gani zaune kan Duwawuna a saman gado ina raba ido cikin tsoro da mamaki.
Kai tsaye ya kalleni ya na fadin"Kin yi sallah ne?
Kai na girgiza masa ina sosa idanuwana alamun a'a.
Bai kara mgana ba sai da ya juya zai fice sannan yace"Ki tashi ki yi salla"
Kai tsaye kuma ya fice na bi shi da kallo na dad'e ina zaune kasala ta Rufeni kafin na rarrafa na sauko daga kan gado na fad'a Tiolet na dauro alwala sannan na zo na yi sallah.
Bayan na idar sai na fara gyangyad'i saman Darduma har da jin jigina da jikin gado.
Sai naji kamar Danwaken da naci ne duk ya bi ya kashemin jiki na kasa jin karfin jikina.
Sai kuma wani barcin ya kara kwasheni bai dadi cike da mafarkin wai gani da Amma muna ta Hira.
Shi kuma ya na falo aikin da ya ke ya Daukesa lokaci mai Tsawo kafin ya gama.
Ya lekani ya ganni saman Darduma ina barci sai kawai ya yi mirmishi abunda yasa bai kara tadani ba ganina saman Darduma yasa yasan na yi sallah kuma shi a tunaninsa tsoro da kadaici baya barina barci shiyasa yau na ke ta yin na rana.
Shiyasa bai tadani ba har aka kira sallar mangariba.
Lokacin ya gama amfani da Laptop dinsa ya maidata jaka agogon Fatan dake hannunsa ya duba ya na auna Lokaci gwara yazo ya tafi kada dare ya yi masa ammh gobe zai Dawo Saboda ya yi min cefane abunda ba ni da shi.
A toilet d'in dakina ya shiga ya Dauro alwala sai da ya fito sannan ya yi amfani da Ruwan hannunsa ya yarfamin a fuska da yasa Dole na mike zaune ina faman mutsakan ido.
Cikin yanayin maganarsa yace"Kinga an kira sallar mangariba"
Da sauri na waro ido cikin Muryan barci nace"Mangariba kuma?
Na fad'a da Sigan tambaya.
Mirmishi ya yi min yana maida agogon hannunsa Lokaci d'aya ya na fadin"Eh ki ta shi hakanan ki yi sallah kada ki koma barci ki bari sai kin yi sallar isha'i sai ki koma ki kwanta."
Ban samu zarafin mgana ba naji yace"In na fita daga chan zan wuce sai gobe zan dawo"
Har ya juya zai fice sai kuma ya juyo ya na fadin"Na manta ki rubuta abubuwan da ki ke so na cefane gobe zan zo kin ji ko?
Kamar wata gaula haka na gyad'a masa kai.
Sai ya fita daga dakin inaga yaji ni shuru ban biyosa ba me yasa ya kara lekowa ya ganni na zaune na kasa ta shi.
Cikin mamaki yace"Ki zo ki rufe kofa zan tafi ne."
Sai a lokacin na yunkura na mike jikina duk ya mutu, na bi bayansa salau salau.
Har zuwa bakin kofa ya na rataye da Jakarsa ya fita sannan ya juyo ya na kallona inaga ya fahimci har lokacin barci bai sakeni ba ne yasa yace"kada fa ki koma ki kwanta baki yi sallah ba."
Nace Toh ina Hamma, kai ya kad'a kafin yace"Sai da Safe."
Nima cikin muryan barci nace"Sai da Safe."
Sai da ya wuce sannan na maida kofata na kulle na dawo falo na zauna kan kujera ina faman lumshe ido.
Sai da na bata lokaci a zaune kamar bazan ta shi ba sannan na tashi naje na Dauro alwala na zo na yi sallah.
Kiran wayata ya fito da ni daga Daki zuwa Falo ina Dauko wayar naga shi ne ke kirana.
Da Sauri na Dauka haka kurum sai naji gabana na fad'i.
Kafin ma nayi mgana naji muryansa ya na fadin"Ina fatan kin yi salla ba barci ki ka koma ba?
Sai da na amsa masa da kai sannan na Tuna baya gabana sai da na yi saurin cewa"Eh na yi."
Shuru ya biyo baya kafin yace"Ki Rubuta duk abunda ki ke so kin ji ko?
Sai na amsa masa da Toh.
Yace sai da safe nima nace sai da Safe.
To wayarce ta sa na watsartsake daga barci na fara game.
Yau ko Amma ba mu yi mgana da ita ba, naa kira da Safe network bai sa na sameta ba.
Bansan Ummi ta aikomin da abinci ba sai da na shiga kitchen na gani sai na samu tabbacin sanda ina barci ta kawomin shi kuma ya karb'a
Dambun shinkafa ne da Zogale shi naci na sha ruwa na kwanta.
Da safe da muka hadu a bakin Famfo bayan mun gaisa na mata godiyan abinci.
Sai ta yi mirmishi kafin tace"Ashe megidanki ya dawo jiya?
Da Eh kawai na amsa mata daganan sai na Datse maganar.
Bani da takarda da Biro wajen Ummi na ara kafin ta fita na Rubuta masa abubuwan da na ke so na Cefane.
Kayam miya me sai kayan lambu sai mangyad'a da ya kusa karewa sai kayan maggi su kenan na Rubuta masa. Sai flower saboda ina so na rika Dan sululu da wainar Fulawa.
Ina da tabbacin zai zo tunda yace shiyasa ko kafin yazo na yi wanka na har da kwalliya na yi na saka Jan baki da Hoda da Kwalli.
Sannan na Fesa Turare yau ma kamar jiya daga wajen aiki ya biyo ta nan ya iske na Dafa Shinkafa da wake da mai da yaji ammh shi sai na soya masa manja saboda yace min da shi ya ke so yaci.
Ammh bai fara ci ba sai da ya yi wanka sannan ya zauna ya ci saboda Rana ta Daga yasa yace sai la'asar zai fita ina gani ya kwashe wayarsa ita kuma Na'urar yau na cikin Jaka bai Fito da ita ba
A gajiye ya ke yasa a kan kujeran da ya ke zaune barci ya kwashe shi. Abun mamaki ana fara kiran sallar La'asar ya tashi.
Takardan ya karb'a ya duba baice komai ba ya saka a aljihu ya fita zuwa masallaci.
Bai gayamin dagachan zai wuce cefanen ba shiyasa da naji shuru sai nayi tunanin ko ya tafi ne?
Ammh ya tafi kuma ya bar jakarsa a nan?
Ashe cefane yaje ya yo sai ga shi da ledoji niki niki kuma kamar na sani ban rufe kofata ba.
Dakyar ya bani Leda Biyu yace wai bani da karfi bazan iya ba.
Ni ya na bani mamaki wai bazan iya ba?
Kayam miya ne da kayan lambu sai abubuwan da nace.
Sai kifi da Nama da ya siyo sai dankalin Turawa da na Hausa sai mangd'aya king na karamar Roba.
Shi ya tayani muka jera komai a muhallimsa kifin da Naman yace na soyasu kada su lalace tunda bani da Fridge.
Bansan bayason karnin kifi ba sai da naga bayan na wanke na fara Soyashi ya bar Falon ya koma bedroom dina har ya na Turo kofa.
Sai da na shigo ya fara Toshe hanci ya na cemin na rufe kofar baya son karnin Kifi amai ya ke saka shi.
Cikin mamaki nace"To kasan baka so meyasa ka siyo?
Kai tsaye yace saboda ni baisan ko ina so ba.
Sai naji raina ya yi wani haske jin haka yasa ina gama soya kifin daman naman na fara Soyawa na dake na goge kitchen din da omo har Falon ma na share na goge na kunna Turaren wuta na tsinke da na Rushi da Adda Rukkaya ta kawomin.
Sannan Ummi ma ta dibar min nata yau bata dawo da wuri ba kila gida ta Biya.
Ina so na yi wanka ammh ya na Dakin kuma in na shiga zai ji karni Saboda kayana da ni kaina ina karnin kifin ne.
Sai kawai na fara greetin din kayan miya na Dora girki Shinkafa da Miya na Dora sai kuma na fara yanka kabeji da zan yi salat da tun tuni na iya shi a gidan Adda Fati.
Ina kitchen din ya fito yace zai je masallaci.
Ina jin haka na fito da Sauri sai dai ban zo kusa da shi ba daga kofar Kitchen din na Tsaya ina fadin"Ammh ba dagachan zaka wuce ba ko?
Kai tsaye yace"Dagachan zan wuce me ya faru ne?
Sai na samu kaina da marairacewa ina fadin"Don Allah ka dawo kaci abinci."
Shuru ya yi kamar mai nazari ganin haka yasa na kara sauke murya ina fadin"Kaji ASSADIQ. Don Allah na ce in ka ci sai ka tafi."
Kallona ya yi cikin ido kafin yace"Bazaki dauki Lokaci ba ko?
Da Sauri nace masa In sha Allahu.
Kad'a kai ya yi kafin yace"Ok."
Sai da na tabbatar da ya fita sannan na Daka Tsalle.
Sauri sauri na tsane shinkafar sannan na had'a miyar naje na yi wanka.
Ina cikin salla ya dawo sai da na Idar sannan na saka kaya ko mai ban Tsaya shafawa ba.
Ina fitowa daga ciki yace"ke nake jira kada dare ya yi na rasa abun hawa. Sannan garin kamar da Hadari."
Ni kuma kai tsaye nace masa"Da wuya fa ayi ruwa kasan farkon damina."
Bai ce min komai ba na shiga kitchen daman bayan na fito wanka na zo na Duba miyan naga ta yi sai na kashe gas din
Daman tuni na wanke salat dina had'a masa na yi miyan daman nama na saka masa saboda yace baya son kifi ni kuma bazan saka masa abunda baya so ba.
Ban dauka ba zai ci abincin da yawa ba sai naga kuma yaci ba laifi da ya tambayani ni bai ga na zubo nawa ba? Sai na ce masa ba yanzu zan ciba sai anjima.
Ruwan gora na Dauko masa Tunda ya siyomin da lemun Fanta kanta d'aya kowanne.
Kamar wasa sai iskan Hadari ya taso yana jin haka ya mike yace zai tafi sai me? Ba sai ga Ruwa ma su karfi ba dole ya dakata da Tafiya tun ya na zaton ruwa zai Dauke har ya Sare.
Sallar isha'i ma shi ya jamu jam'i Saboda Ruwa bai samu fita ba.
Kamar ranar da farko ni yace na kwana aciki shi kuma zai kwanta afalo.
Sai nace masa akwai sanyi shi kuma yace kada na damu.
Ammh ban barshi haka ba sai da na Dauko masa zanin gadona nace ya yi Rufa da shi.
Ummi ma ruwa ya taresu ita da Mijinta ni dai har na kwanta banji dawowarsu ba.
Kwana aka yi ana ruwa har asuba ana ta yafyaf na alamun ruwa.
Shiyasa Sallar asuba ma shi ya kara jamana Jam'i.
Samakon wekeend ne yasa bai yi Tunanin zuwa wani waje ba
Bayan mun karya da Safe tunda shinkafar jiya yace na Dumama masa ita zai ci nima ita naci.
Gani na yi ya na ta juya wuyansa kamar yana masa ciwo yasa nace ya shiga ciki ya kwanta ya mike Zuwa anjuma.
Bai yi gaddama ba ammh yace sai ya yi wanka saboda sanyin gari yasa na saka masa ruwan zafi ya yi wanka sannan ya koma ya kwanta.
Ni daman tun safe na yi wankana, abun da ya ke bani mamaki in dai yazo gidan nan to kashe wayarsa ya ke yi baya kunnawa ballatana ma akirasa.
Kuma ya sha barci sai azahar ya tashi ya yi alwala ya tafi masallaci Ummi kuma da na fita har dakinta na kwankwansa naji shuru sai nayi Tunanin a gida ta kwana Saboda Ruwa sannan ga dare.
Na dauka zai ce zai tafi da yammah ammh sai naji malamin ka shuru.
Ina dafama abinci kuma yaci sosai sai da mangariba ne ya fita sallah yace min sai an yi sallar isha'i zai dawo.
To har wajen tara bai Dawo ba sai chan ga shi ya Dawo da wata karamar jaka ashe kayansa ne aciki ya Dauko.
Tunda ba shi da wanda zai sauya na jikinsa sun yi datti ba shi da wasu.
Aiko ya na cire kayan washegari da Safe na wanke masa su tas na shanya.
Bai ma gani ba sai da suka bushe na kwaso ina ninke masa.
Fad'a ya yi min da wai hannuna da ba kwari ne zan iya wanki.
Dariya na yi har sai da na rike ciki ina mamakin in ya na Tunanin Saboda