Showing 15001 words to 18000 words out of 98628 words

Chapter 6 - Tmw Book Two Complete Hausa Novel

26 Oct 2025

347

yi kyau sosai duk da bani da wasu kayan arziki sun yi min danki kuma ya yi kyau.
Kitchen din ma karami ne sosai shiyasa ya cinye kayan har da ragowan Fili.
Cikin Lokaci na gama komai bayi ne ban wanke ba, saboda ba ruwa kuma gashi ina so nayi wanka.
Sai na saka takalmi na bude kofa na fita Tsakar gidan ina Dubbawa.
Nice a falt din farko sauran uku suna bayana sannan Famfon gida ya na ta wajen dakina ne.
Kamar wasa na kunna sai ga ruwa ya zo na yi ta mamaki sai da na daga kaina naga tanki ammh kuma ina mamaki kenan suna da wuta?
Da na kara bin wajen da kallo naga ga wayoyin wuta ne da suka shigo ta gidan mahad'in puse na kowani flat.
Ganin na samu ruwa yasa na zage na koma Daki na Dauko botikai na a Makewayi na rika cikawa da ruwa ina kaiwa kitchen a babban bambina na ruwa na rika zuba ruwan har da sai na cikata sannan na koma na fara zuba ma babban bambin da ke makewayi.
Na dauko botikin karshen kenan muka ci karo da shi ya shigo Dauke da gas din da Babban leda a hannunsa.
Dukkammu sai muka tsaya muna ma juna kallon kallon.
Ni kayan jikina me tun na jiya ammh na nade zanin sama na kuma ma kaina Daurin gammo saboda Diban ruwa rabi na duk na jike sai yararin ruwa na ke yi.
Kamar kuma sai naga ya na yar dariya.
Sai na Tsargu da sauri nace"Am, Ba ruwa ne a makewayi shine da na fito naga gidan akwai ruwa shine shinre..."
Bai bari na karisa ba ya wuceni zuwa Dakin ya na fadin"sannu da aiki."
Kunya ta kara kamani cikin sanyin jiki na bi bayanshi baya falon ya shiga kitchen da sauri na shige cikin Dakin kada ya fito ya ganni.
Abunda bansani ba yana leke na ta kitchen mamaki ya ke da siraran hannuwana da kafafuwana ashe ina da karfin Daukan botiki haka?
Ledan da yazo da ita a kitchen ya barta ya fito falo yana jirana ni kuma ganin na jike yasa na kwabe da ruwan sanyin nan nayi wanka.
Da na fito ban ko shafa mai ba na bude babban akwatina ina kokarin Daukan kayan da zan saka duk da kayan ba su da wani yawan kirki.
Kamar wasa naji ana kiran sunana sai na tsagaita da abunda nake yi na kasa kunni sai naji Muryan ASSADIQ ya na fad'in"Ha..Si.. yaaa."
Da Sauri na amsa da Na'am.
Ban tsaya saka kayan ba daman akwai zanin leshin a jikina da na yi wanka sai kawai na nemi hijabi na saka na fita falo.
Yana tsaye daga bakin kofa na zo ina fad'in"Ga ni"
Kallon kafafuna ya yi da ya gansu suna Digan ruwa cikin gargasan gashin jikina.
Kai tsaye yace"Tunda kin jike ki yi wanka mana"
Nima kai tsaye nace"Na yi wanka"
Baki ya bude kafin yace"Da ruwan sanyi?
Da kai na bashi amsa, Kai ya jinjina kafin yace"Baki tsoron sanyi ya kamaki? Maimakon ki saka ruwan zafi."
Sai na kasa mgana kaina na kasa.
Bai damu ba yace"Kin iya kunna gas?
Da kaina na amsa masa kafin nace"eh na iya Adda Fati na da shi"
Kai tsaye yace"Ok sai ki yi amfani da shi ki rika girki, Ni zan tafi kinsan abunga ga takala ina buga bugan neman abunda zan rike kaina tare da ke"
Ya dakata ya na kokarin had'a karyan da zai gayamin.
Dakyar ya cigaba da fad'in"Ina da wani megida da ke shigo da kayan wuta shi na ke bi muna kasuwanci, wani Lokacin sai dare sosai na ke dawowa kuma kinga nan ya yi nisa da inda na ke hidimar kasata shiyasa zan rika kwana in da na ke kwana da Fari."
Ya dagata ya na nazarin yadda na karb'i mganar.
Kamar yadda ya sani ne a tsarace na kalleshi kafin nace"Ba anan zaka rika kwana ba kenan?
Sai ya ji nauyin yace eh ammh ba shi da zab'i cikin karfin hali yace"Eh ammh zan rika zuwa lokaci bayan lokaci ina Dubaki."
Kai tsaye na kallesa kafin nace"Ni kad'i zan rika kwana?
Na fad'a idanuwana na cikowa da kwallah ya kasa kallona saboda kada Tausayina yasa ya bata tsarinsa.
Kansa na gefe yace"nan da sati daya mai flat din kusa dake zata tare kada ki damu zaki samu abokan zama."
Kasa mgana nayi kirjina ya cika da Tambayan kaina daman ana aure haka? Miji bazai kwana agidansa ba sai dai a wani waje?
Ganin ya na shirin tafiya ne yasa nace"Fitila.. b"
Da sauri yace"Na siyo miki ta na cikin kaya a kitchen."
Da sauri na Sauke ajiyar zuciya.
Ya fita daga cikin daki ya na kallona kafin yace"Ki zo ki kulle kofar gida."
Ba musu na saka takalmina dake nan wajen na bi bayansa har waje.
Sai da ya fita sannan ya juyo ya na kallona.
Kad'an ya rage ban saki kuka ba kwayan idanuwana sun nuna masa haka.
Cikin sanyinsa yace"kada ki rika barin gidan a b'ude, sannan har dakin ki ma ki rika Rufewa. Kada kuma ki kuskure ki bude kofa ga wanda baki sani ba kin ji ko?
Da kai na gyad'a masa saboda bakina ya yi nauyin da na kasa mgana.
Har ya juya zai tafi sai kuma ya kara jiyowa ya kalleni kafin yace"Hasiya."
Ina kallonsa nace"Na'am"
Kai tsaye yace"Ki kula da kan ki."
Kaina na maida kasa kafin nace"To"
Ina ganinsa ya wuce da yaga na tsaya kallonsa sai ya yi min alama da ido da na Rufe get din.
Jikina a sanyaye na Rufe ai da gudu na koma daki na shige na maida kofa na Rufe.
Na waiga hagu da dama ba wani motsin mutim bansan Lokacin da na zauna a kasan tayels din dakin na Rushe da kuka ba kewar Amma ya cikamin zuciya.
Sai da nagaji ba mai lallashina na hakura daki na koma na samu doguwar rigar atamfa na saka kayan da na cire kuma na shanya a saman kofar makewayin.
Cikina naji ya tamke nasan kuma na yunwa ne tunda tun jiya rabona da abinci.
Kitchen din na shiga da ledan da ya Shigo na ci karo na budeta naga kayan Tea ne aciki sai Buredi.
Sai Filita sabuwa mai irin na Chajin nan, sai kudi 2k aciki yan dubu Sabbi.
Mirmishi na yi a fili na Furta

"ASSADIQ.."

Kayan Tea din na saka su cikin dirowan kitchen din, Gas din kuma na sama ma wajen zama zan kunna.
Sai kuma naga ba ashana sai idona ya raina fata, sai da na kara duba kayan da ya shigo da shi naga ashana sannan na kunna gas din na dora ruwan zafi cikin karaman tukunya na jira har ya tafasa na kashe gas din na samu karamin kofi na shiga na had'a tea na yanki buredi na fito falo na zauna kan kujera ina sha.
Gabadaya kadaici ya dameni ga shi ni ba waya ba sai yau na karajin takaicin da a baya Amma ta matsamin sai na siya waya na ki bin shawaranta.
Da ace na siya da yanzu na kira su mun yi mgana.
A zatona su Adda Fati za su zo min ammh sai ga shi har yamma ko kare ban gani ba sai dai haushin na makota masu manyan gidaje.
Sai dai na zauna nayi zuru tunanin duniya sun rufeni ina tunanin shi kuma wannan auran nawa ya sunan shi?
Kila shi kuma ahaka zai kare shima.
Sai dare na samu na Dafa taliya da mai da yaji tunda ba ni da kayam miya sannan ban ga ko almajiri ba ballatana na samu yaron aike.
Sai da dare ya yi na kara raina kaina a firgice na kwana kuka na sha har barci ya kwasheni shiyasa na tashi da Fuska duk ta yi ja.
Sannan ga sauro duk sun cicijeni ba maganin sauro.
Babu kuma wayar da zan samu na kira ko Adda Fati Allah Sarki ashe mutane Rahma ne.
Ni kadai acikin wannan gidan har na tsawon kwana Hudu ko kafar dakina ba na fita komai aciki na ke yi.
Barci duk sama sama ne kuma a firgice ko motsin iska naji ya taba get haka zan fara rawan jiki da na zuciya.
Ba Labarin Assadiq ba labarin su Adda sai ranar da kwana biyar da Safe sai ga Ramatu
Ashe ta jima ta na buga get ban ji ba ina wanka sai da ta zagaya ta bayan gida wajen falt dina ta rika kwalamin kiran sannan na jita.
Na fita naje na bude mata kofa haka na Rumgumeta ina murnan ganinta.
Ranar Ramatu tamin yini ina ta korafin ba su kara nema na ba.
Ramatu tace"Saboda menene zamu nemeki? Haka kurun ango na armaci mu takura masa"
Kallonta kawai nayi na kasa bude baki na fad'a mata tun washegarin da suka kawoni wannan gidan ban kara ganin Assadiq ba ammh sai naji na kasa gayamata gaskiya.
Har kuma tambaya ta yi ina ya ke? Nace mata ya fita ba da dadewa ba.
Ta shiga ko'ina ta na min murna tunda muna da ruwa.
Yini muka yi hira bayan na yi mana girki mun ci ina goye da Noor kamar ta barmin ita.
Ashe Adda ta koma Shekaranjiya shine ba wanda ya neme ni ya sanar dani.
Ramatu ke fad'amin matan gidanmu na son zuwa suna ta ma Inna talatu mgana.
Da sauri nace"Don Allah su zo ina son ganin su."
Ramatu ta yi dariya ba ta yi mgana nasan zata ce saboda kad'aici ne ba dadi.
Da wayarta na samu na kira Adda Fati ina rokonta da Allah tazo tace ba yanzu ba sai nace to ta turomin Habiba ta zo min da kayan miya bani da shi jin haka yasa tace sai gobe zata zo in ta dawo daga makaranta.
Sai mangariba Ramatu ta tafi kuma ni na rakata har bakin titi na ga anguwan sosai ba wasu yalwar jama'a sosai sai da ta samu adaidaitan sannan na dawo gida.
Washegari gari wajajen la'asar sai ga Habiba da Hanif sun kawomin kayan miya mai yawa.
Da sun so tafiya da wuri na rike su sai shidda na barsu suka tafi.
Yanzu neman mutane na ke yi ido a Rufe ban samu ba.
Sai da ranar da na cika Sati da wuri Adda Rukkaya ta zo min yini ba ta jima da zuwa ba sai ga Inna talatu da matan gidammu.
Duk da gulma ya kawosu haka na rika washe bakinsu ganinsu naga jama'a.
Ba inda ba su leka ba sannan ba su ga wani alaman wahala ko damuwa tare dani ba sai mamaki suke yi.
Sai dai sun ta tambayana ina angon? Ana so aji labari ni kuma naki ba su wani dama da zasu fahimci wannan karon abubuwan sun sha Bambam.
Sai yammah suka tafi Adda Rukayya ta riga su tafiya saboda mijinta.
Ta kawomin kalolin maggi da su korin kamshin girki.
Ta tambayeni ba matsala nace mata ba wata matsala.
Nasan suma a firgice suke ba sa son su kara jin wani abu kuma ya faru.
Ni kuma ba na so na tada musu  hankali ai da na fad'u musu wannan karon ba irin na sauran ba ne.
Har na kwana goma ban kara saka Assadiq a idona ba duk sai na damu.
In har ya sakeni ne gwara ya fad'amin da wannan zaman da na ke yi ba wani a tare da ni.
Sai kuma daga baya na fara Tunanin ko wani abu ya faru da shi ne bansani ba?
Ina cikin wannan firgicin ne da yammah naji ana buga gida.
Da sauri na saka Hijabi na fita jikina na rawa na Dauka ASSADIQ ne ashe ba shi ba ne.
Saboda rudewa ko tambayan waye ban yi ba na bude get.
Sai kawai na ci karo da wata mata yar babba haka.
Tamin mirmishi na yi mata ni na fara gaisheta ta amsa cikin sakewa kafin tace"Mun kawo kaya ne"
Cikin mamaki na kalleta ban samu zarafin mgana ba tace"Yarmu ce zata zauna a d'aya daga cikin flat din gidan"
Ina jin haka kamar an min bushara da gidan Aljannah
Da sauri na bata hanya ina fad'in"Sannun da zuwa."
Shigowa ta yi ni kuma na leka ina ganin motar kaya cike da kayan su kujeru da gado sannan na Rufe get din.
Matar na da fara'a ita ta gayamin ita ta fara yin gaba da motar kayan sauran matan suna hanya a daidaita za su zo yanzu ma surukin na su take jira ya kariso ya bata makulin dakin tare da yaran da zasu taimaka a kwashe kaya..
Jin haka yasa na ce ta shigo dakina ta yi tamin godiya kuwa.
Na kaita har dakina ta zauna na bata ruwa.
Na zo na zauna ta na min hira irin matan ne masu shigen surutu.
Daga zuwanta har sunan Amaryan ta fad'amin Fatima ana ce mata Ummi.
Har ta kayan dakin da aka siya mata sai da ta lissafa min.
Sannan ta gayamin ita kanwar babanta ce a saudiya ta ke zaune tazo ne.
Ni ban tambayeta ba ammh har ta fesamin Ummi ta gama Digree d'inta anan Abu zaria.
Koyarwa ta ke yi a wata makarantan Secondary a sabon gari.
Surukin na su kuma ma'aikacin gwammati ne a nan zariya.
Cikin jiran awa dayan da tayi ne fa duk ta sauke min wannan labarin.
Ni ko ina zaune ina jinta Eh a'a sai ko mirmishi.
gidan haya mai tara jama'a da Mutane kala kala.






*Janafty*
*TMWB2K005*


*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk

Ku zo ku yi sayayya tare da Yar Gidan Imam cikin aminci da kwanciyar hankali komai akwai harda kayan gyaran jiki hamshakan mata na supliments kala kala wanda ba su da illa, akwai kuma gagarumin haɗin mu na Arabian sabaya powder wanda babu kamarsa wannan ba irin sabayar da ki ka saba gani bace, kayan kicin dogayen riguna kuwa ba'a magana ke dai ki yi sauri ki shigo domin kwasar roman wadannan kayan.

Sai da Surukin na su yazo da yaran da zasu kwashe kayan zuwa cikin gida sannan ta min sallama ta fito daga dakina ni dai ban fito ba.
Ammh naji ba jimawa sauran tawagan da tace suna hanya suma suka iso, na leka ta window na gansu Rurututu kamar a nan ake yinin biki kusan zazzagawa akwai kara.
Duk ina cikin daki naji an fara shigowa da kayan dakin cikin gida ba gulma ba na mike na saka gwiyoyina saman kujera ina leken su.
Kaya ne na alfarma ma su kyau burin kowacce macen da ta isa har aka kira mangariba ba su gama shigo da kayan nan ba shiyasa na koma daki na Dauro alwala na yi sallah.
Ina kan darduma naji ana kwankwasamin kofa na tashi da hijabin jikina na fita na bude sai naga wannan matar da ta ce min sunanta Zainab.

Washe baki ta yi kamar yadda nima na washe mata sannu da gida ta min kafin tace in ba damuwa na san musu butoci suna so su yi sallah.
Ganin suna da yawa yasa na dauko musu botiki karami na zubo musu a ruwa aciki na bata buta guda biyu ta na min godiya.
Chan kuma sai gata ta dawo min da botikina da butocina ta kara cewa na san mu su ruwan sha.
Kitchen na shiga na samu katon jug dina na zuba ruwaan tunda nima shi na ke sha ba ni da pure water duk da akwai dubu biyun da ya bar mun ammh yaron ma da zan aika babban aiki ne.
Na cika musu shi na had'a musu da kofunansa guda hud'u na kawo mata ta karb'a ta na fad'in sun gode.
Cikin yanayina nace"Ku yi hakuri ba ni da pure water"
Sai ta yi dariya kafin tace"Bakomai kin ji"
Har ta juya ina shirin Rufe kofata ta juyo ta na fadin"Nace ki fito mana ki zo ki ga yanayin jeren namu kinsan ku ne yaran zamani sai mu gama kokarin mu ku ce bamu yi daidai ba."
Kamar tasan nagaji da zama ni kada'i da Sauri na fito ina amsa mata da toh.
Akwai key din kofar ta baya shi na cire na Rufe kofar na bi bayanta sai min hira ta ke yi.
Muna shiga sauran matan suka bi mu da kallo ni kuma na gaishe su suka amsa cikin sakewa itace naji ta na musu bayanin anan gidan na ke.
Gani mai hankali Ummi zataji dadin zama dani.
Ina jinsu suna ta min godiyan ruwa, falon ga kaya nan zube ina ga ciki ne kanfintocin ke had'a gadon wata mata na gani ta na salla a kasa acikin raina sai naji ban kyauta ba meyasa ban basu Darduma ba?
Gefe na koma na tsaya ina kallon abubuwan da su ke yi, ban san me ya tsaidani ba ammh naji gwara na zauna cikin mutane da na koma daki ni kad'ai kamar wata mayya.
Gani na tsaye yasa matar nan tajani kitchen wai nazo na rika nuna musu yadda zasu jera kayan kitchen d'in, aiko zuwa na ya yi amfani da sun mata barna duk sun fara yaaga mata wasu kwalayen kayan sai da nace musu su bar su a kwalayensu in ba haka ba in ta jima ba ta yi amfani da shi ba za su lalace.
Muna kitchen din suna ta aiki nima ina taya su babu bambamcin da Falt dina komai iri daya ne har girman ni da ya ke ba ni da wasu kaya yasa dakin nawa bai cika ba ammh ita ko da ta ke da kaya da yawa waje ya cika Damkam.
Har sun gama gyara ciki sun fito falo bamu sani ba, sai da wani cikin samarin nan ma su kwashe kaya ya shigo ya na fad'in"Wacece Hasiya a nan?
Mu muna kitchen shiyasa ba mu ji ba su kuma ba su dauka ni ce Hasiyan ba sai suka ce ba Hasiya anan wajen.
Sai da ya fita ya kara dawowa yace matar dakin nan dake kusa da nan ake tambaya mijinta na jiranta.
Muna cikin aiki wata yar matashiya ta leko ta na kiran sunana.
Cikin mamaki na juya ina amswa da Sauri tace"Au daman ke ce Hasiyan?
Sai na gyad'a mata kai.
Da sauri tace"To ki je ga mijin ki chan ya dawo ya na jiran ki."
Sai naji abun wani barambarakwai namiji da suna Hajara.
Idanuwana na zuba mata har ta fice daga kitchen sai naji kamar ban ji daidai ba.
Hajiya Zainab ce tace"To maza mana kije kada ya gaji da jira ransa ya baci."
Jiki na a sanyaye na yi mata dariya na wuce suka bi ni da kallo.
Ban dauka da gaske ba ne sai da na fita na ganshi tsaye a kofar dakina ya jingina da kofar, sanye ya ke cikin kananun kaya riga da wando.
Hannunsa daya akwai Ledan d'ayan kuma ya tusa cikin Aljuhun wandonsa.
Hasken gen din kusa damu ya haske Fuskarsa domin ni dai inaga tunda nazo gidan nan sai cikin dare suke bamu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login