Showing 24001 words to 27000 words out of 98628 words
ya fi shekaru ashirin yana aiki a wajen.
D'aya daga cikin ya'yansa ce ta yi sallama a kofar falon na shi ya amsa mata Lokaci daya ya na bata izinin Shigowa.
Wata gajeriyar matashiyar Budurwa ta shigo wankan tarwada ta na sanye da Doguwar riga baka ta yane jikinta da bakin mayafi Dauke da faranti da nug a saman ya na Tiririn zafin Ruwan lipton din da ke ciki.
Gabanta ta karisa ta ja karamin Tebur kusa da shi ta Dora a saman wajen.
Sannan ta duka ta na fadin"Barka da Hutawa Baba."
Cikin mirmishi ya na kallonta ya amsa mata da cewa"Yauwa sannu da kokari Zahra'u yar Baba."
Kanta na kasa ta murmusa shi kuma sai ya ijiye takardan Hannunsa ya sunkuya ya Dauki mug din ya dan kurba sau biyu, kafin ya sake Dagowa ya na kallonta cikin jin dadi yace"Allah ya yi miki albarka Zahra'u."
Ta amsa da Ameen Ameen Baba.
Mikewa ta yi zata fice bayan ta yi masa sallama saboda Tsarinsa in ya na cikin Falonsa ya na Hutawa baya bukatar ganin kowa ko da kuwa Uwar ta su ce.
Zahra'u ce kad'ai ta kan shiga Saboda ita ke hada masa Tea din da ya kan sha in ya na Hutawa kafin ya shiga barci.
Kiran sunanta ya yi da"Zahra'u."
Ta amsa ta na juyowa da sauri yace"Mubarak ya shigo kuwa?
Girgizamai kai ta yi kafin tace"A'a Baba ammh ina jin duk inda ya ke yanzu ya na hanyar gida."
Kai ya jinjina kafin ya yi mata alama da Hannu da ta tafi shikenan.
Har ta kule ma ganinsa ya na binta da kallo.
Kiran wayarsa ya katse masa tunanin da ya so ya fad'a.
Ya na ganin mai kiran jikinsa na rawa ya Dauka ya na faman washe baki.
Sun jima suna mgana kafin su yi sallama ya sauke wayar ya na kurama zanen kwalliyar cafet din dakin kallo.
Wani tunani daki daki na shiga kansa
Ya fara kasuwancin Shigo da gwala gwalai tun shekaru biyar da suka gabata kuma ya tara abunda bai Tara ba Tun fara aikin gwammatin sa.
Bai san Alhaji Sulaiman Shinkafi ba sai ta sanadin wani abokinsa Alhaji Sheshe shi kuma Alhaji Sheshe sun fito daga mahaifa d'aya ne da Alhaji Sulaiman Wato garin Shinkafi.
Ya san ya na da sha'awar kasuwanci da zai rika kawo masa manyan kudad'e saboda ya raina matsayinsa a yanzu sai ko Alhaji Sheshe da ya kasance abokinsa ne shi ya had'a shi da Alhaji Sulaiman har ya Bude masa ido a kan kasuwancin Shigowa da gwala gwalai.
Tsawon shekaru biyar din nan suna Huld'ar arziki, Bai taba haduwa da iyalan Alhaji Sulaiman ba shima bai taba had'uwa da na shi iyalan ba.
Sai dai yasan wasu mutane Biyu masu matukar Muhimmamci a rayuwar Alhaji Sulaiman.
"MAGAJIN GIDA.."
"INNANI.*
INNANI da ita ta kasance mahaifiyace ga Alhaji Sulaiman, Sun jima tare ya na jin sunan magajin gida bai taba kawo ransa wannan magajin gidan D'a ne ga Alhaji Sulaiman ba sai a shekaran da ta gabata yasan ashe d'ansa ne sannan shine kwara d'aya tal d'a Namiji da ya Haifa sannan gatan Duniya yaron nan ya na da shi.
Komai fa in za su yi sai yaji sunan Magajin gida kamar ma Alhaji Sulaiman ba ya iya yanke wani abu kan Dukiyarsa ko kasuwancinsa sai da Izinin Magaji gida.
Bai taba ganin yaron ba ammh yasan matsayinsa ya wuce ya zauna ya na faman wani lissafi.
Innani kuma ya fahimci Umarninta ne Umarnin Alhaji Sulaiman ya na sonta kuma duk abunda tace ta na so shi ya ke so.
Alhaji Jibiril ya gyara zamansa sannan ya dauki ruwan zafin da aka kawosa ya kurb'a sau biyu kafin ya ijiye.
Shuru ya yi kafin kuma Lokaci d'aya ya saki dariya mai kayatarwa shi kad'ai..
Lokaci ya yi da zai kara bunkasa kasuwancina.
Lokaci ya yi da zai kara kusancin da Alhaji Sulaimam.
So ya ke ya fisa ido a kan wannan harkan kasuwanci so ya ke nan gaba kad'an ya shahara da kudi fiye da Alhaji Sulaiman.
Alhaji Jibiri mutum ne mai son kudi fiye da komai a duniya sha zumamu me baya rabar ka sai ya tabbatar da in zai karu dakai in yasan bazai karu dakai ba to bazai yarda ya had'a inuwa da kai ba ko yan'uwan shi ne in yaga bazai karu da kai ba baya doguwar huld'a da mutum.
Ko da wanda suka fito ciki d'aya ne kuwa in yasan sai dai ka karu da shi to mu'amula ta zumunci sai in dai kai ne ka rike zumumcin ammh shi bazai damu da shi ba.
Mutum ne mai son abun duniya da ya gwammace son kudi fiye da komai.
Alhaji Jibirl ne mai Daraja kudi fiye da komai a Rayuwarsa.
Kud'i ne mutumcinsa su ne kimarsa in baka da kudi baka da wani kima ko Daraja a idanuwansa.
Saboda kudi kuwa zai iya aikata komai a rayuwarsa.
Alhaji Jibirl baya son asaran kudi ko ta na naira biyar ce in kuma asaran ta fara ji ya ke yi kamar ya Mutu saboda hakan.
Acikin gidansa macen aure d'ayace Hajiya Murjanatu da ya'yansa guda Biyar mata uku namji biyu.
Mubarak ne Babba sai Fathiha sai Zahra'u sai Kamal sai karamar su Fatima suna kiranta Bintu.
Mubarak ya gama karatunsa ya na aiki ne da Kamfanin Dangote da ke kaduna sai Fathiha ta yi aure a garin kano sai zahra'u da ke shekara ta biyu a kaduna State university sai kamal da ke karatu a Buk kano ya na zaune gidan yar'uwansa Fathiha.
Autansu kuma Bintu ta na SS1 ne yanzu saboda tsakaninsu da Kamal akwai tazara mai yawa.
Ko acikin gidansa daga matarsa har ya'yansa susan babansu na Daraja kudi shiyasa suma suke tayashi Daraja shi komai na gidan nan ya na kan tsari ne komai na abun bukata a Farkon wata zai siya in kuma wani abu ya kare ba'a isa ya fito da wani kud'i ba sai wani sabon watan saboda ya riga ya gama Budget din wannan watan ko rashin lafiya ne kuwa sai dai yace Hajiya Murjanatu ta ranta masa in sabon wata ta shiga zai biyata.
Shi komai na shi akan Tsari ne in kuma ya kuskure ma tsarinsa sai dai a nemi wata mafitar.
Bazazzagi ne gaba da bayansa uwa da Uba aiki ne da Sauyin Rayuwa ya maida shi Dan kaduna.
Saboda makonsa yasa matarsa Hajiya Murjanatu kama sana'an saida kayan yara kuma Alhamdulillah ta na samu domin da shi ta ke Rufamana kanta asiri da ya'yanta.
Tunda ko sha'anin yan'uwanta in bata neman na kanta sai taji kunya shi kanshi Alhaji jibirl din bai yi ma na shi ba ballatana na ta.
Ita yar anguwan kabala ce nan aka haifeta kuma anan ta girma auran Saurayi da Budurwa suka yi tsakaninta da Alhaji Jibril.
Saboda son kud'insa yasa bazai iya zama da mace sama da d'aya ba
baya son kashe kudi ba gaira ba Dalili shi kan shi Dalilin nasa mai karfi ne shima in ya fita cikin Budget sai da ya jira sabuwar wata ta shiga.
Ya na kurban Ruwan zafi ya na mirmishi Saboda ya hango cigaba sasai a hasashensa.
Wayarsa ya Dauka bayan ya sauke kofin hannunsa saman teburin gabansa.
Kiran ya yi sannan ya saka a kunne bayan an dauka suka gaisa kamar ba a yanzu suka gama waya ba.
Cikin sauke Murya yace"Alhaji yanzu na yi wani tunani. Me zai hana mu kara fad'ada Zumumcim mu ta hanyar sanin iyalan juna?
Mgana ake masa ta d'ayan bangaran ya na ta mirmishi da annushuwa.
Daidai Lokacin da wani matashi ya yi sallama ya shigo falon.
Hannu ya daga masa alamun ya na waya a yadda Mubarak ya ga Baba na mgana cikin Dariya da Farinciki yasan cewa wata harkace ta karuwa in ba haka ba haka Kurum bazaka gansa ya na Farinciki da Dariya haka ba.
******
In yace Hasiya bata ransa ya yi karya, sai dai ya na boye tunanin hakane Saboda Tahir.
Tunda ya siya mata waya ba shi da ikon zuwa ya ganta sai Tahir yace ba ga waya ba in da matsala zata kirasa.
In ya dawo daga wajen aiki haka zai kwanta ya na ta Tunane tunane hakikanin gaskiya har rama sai da ya yi saboda zullumi
Gida ya ke so yaje ammh kuma kunya baza su iya barinsa yaje a wannan Lokacin ba.
In ya gan su zai kara shiga damuwa cin amanan da ya yi musu.
Sun kusa gama Bautar kasar su ba za su wuce wattani uku nan gaba ba. akwai bukatar kowa ya yi ma kansa tsarin da zai taimakesa anan gaba.
Yana da Burin ya koma gida in ma karatun zai cigaba da yi bazai kara yi a Zariya ba sai dai ya sauya muhalli kuma nan gaba.
Sun taba mgana da Tahir akan me zai fara yi bayan sun gama Hidimar kasar su?
Kai tsaye Tahir yace masa gida zai koma ko saboda Hajja sannan yan'uwansa daman sun matsu ya dawo gida, zai koma yaga abunda zai fara sannan kuma Zai taba siyasar yankinsu.
Ba haka kurum Tahir ya ke karantar Siyasa ba, yana son siyasa shiyasa kaf Shafukansa na sada zumumta shi ne bin yan siyasa ya na musu comment da like karatu ya Dauke masa Hnkali daga Fad'awa siyarsa.
Kuma ya na da tabbacin in Tahir ya samu dama zai shiga siyasa tunda ya na da Ra'ayi.
Da ya tambayeshi mganar cigaba da karatu fa? Sai Tahir yace ko zai cigaba sai ya kama wani abun a hannunsa sannan.
Shi ko ya na da Burin cigaba da karatu in sha Allahu kuma ya na da Burin ya samu aikin da zai Dogara da kansa baya so ya zauna saboda mahaifinsa na da kudi.
Shiyasa duk inda aiki na ma su irin karatunsa suke ya kan duba wajen sosai kamfanin da yake bautar kasa ma sun ce zasu daukesa aiki ammh bai amsa su ba saboda ba shi da Burin kara zaman zariya.
Ya na Tunanin in ma Mastars dinsa zai yi sai dai ya je BUK kano ya yi chan bazai kara zaman zariya ba.
Kuma Bazai ji dad'in zama ba Tahir ba.
Wata zuciyar tace ga Hasiya?
Sai ya ba kanshi amsa da cewa Hasiya sakinta zai yi ta koma wajen mahaifiyarta shima ya tattara ina shi ina shi ya koma Gusai gaban iyayensa Sultana na chan na jiransa.
Ko a waya da ya kira Hasiya Sau d'aya da bai kara kiranta ba ya na da Dalili baya so ya cigaba da kiranta har ta Fahimci ya yi mata karya gwara su tsaya nesa nesa da juna kamar yadda Tahir din yace.
Kuma sannan kunya yake ji in ya ganta ga Tausayinta sannan da kuma jin nauyin kansa da ya zama makaryacin karfi da yaji gabadaya wata Rayuwa ya ke yi ba rayuwa irin ta Abubukar Sulaiman Shinkafi ba.
Yanzu Rayuwa ya ke yi a matsayin Assadiq maraya wanda ba shi da komai kuma wanda yaci Amanar iyayensa da karya sannan wanda ya kasa kula da Hakkin matar da ke kansa.
Cikin wannan satin Tahir ya tafi Daura an kirasa Hajja ba lafiya har ta kai ga asibiti ya so ya bisa su tafi tare sai daga wajen da ya ke bautar kasa suna da wani aiki yasa ya barsa ya tafi shi kadai akan in ya samu Sarari zai biyosa sai su dawo tare.
Duk sai kadaici ya kamashi ya saba komai tare suke da Tahir.
Shekarun nan kusan tare suke sai ko in ya koma gida Hutu.
Kwanan Tahir d'aya da Tafiya ranar dakyar ya yi barci ya na ta faman juye juye.
Sai yaji Tausayin Hasiya ashe haka ta ke fama da kadaici bai sani ba?
Batare da Tunanin komai ba ranar ta biyu daga wajen aiki Gidan Hasiya ya wuce Direct da Niyar zuwa ya Duba lafiyarta har acikin zuciyarsa.
Baisan Allah da na shi nufin ya ke sarrafa namu zuciyoyin ba.
Sannan abunda ke rubuce a zanen kaddaranmu bamu isa mu kauce masa ba.
🌿 Ina manyan mata masu MATSALOLIN rashin Ni'ima Ina sabbabin aure Wanda basu juku yanda Mai gida zai sume ba😂Ina wayanda zasuyi sabbin aure
Nazo muku da magani SAHIHI ingantaccen TSIMIN TABAJE🤌🏽🥰😍 hmm uwar gida, amarya, tsoffin aure kuna Ina ko kuntsaya tsilla tsilla tohm maza kuzo nazo kusiya TSIMIN TABAJE 💃💃😂hajiya ta tunda kukaji na yaba wannan magani toh tabbas yakai inda yakai yanada matukar kyau, Yana saurin saukar da niima baya illa domin andafashine da saiwoyin da kuka San suna maganin dakyau... Hajiya ta 🙈wlh Mai gida zaiyi Santi zakiji dadi Kuma zakuzo ku godemun domin yanasa Gurin yayi dumi ya Kuma ciko miki da gaba Gurin Kuma zaiyi dadi zoyzoyy😂🙈💃Kuma duk afarashi kalilan akwai gorina 1k akwai galan, akwai jarka ga duk meso, hmmm duk Wanda yasha Sai ya Gode mun domin nice na baku tabbaci 💃😂kunsan banida burin daya wuce Inga anasaka Mai gida farinciki 💃😂🥰Toh kuzo kusiya zakuji dadi insha Allah Kuma Sai kun dawo.... muka hada miki maganin TSIMIN TABAJE sha'awa zaki koma kamar marka..game bukatar TSIMIN TABAJE ya kiramu tawa innan numbobin kamar haka
*Location* *Zaria and kaduna* *but nation wide delivery* *for more details 07062349732 or 08143450259* 💃💃💃
*Janafty*
*TMWB2K007*
*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*
https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk
Ku zo ku yi sayayya tare da Yar Gidan Imam cikin aminci da kwanciyar hankali komai akwai harda kayan gyaran jiki hamshakan mata na supliments kala kala wanda ba su da illa, akwai kuma gagarumin haɗin mu na Arabian sabaya powder wanda babu kamarsa wannan ba irin sabayar da ki ka saba gani bace, kayan kicin dogayen riguna kuwa ba'a magana ke dai ki yi sauri ki shigo domin kwasar roman wadannan kayan.
Yau Danwake na yi da yaji mai manja, Ummi ba ta nan ta na makaranta karfe biyu ake tashi na rana kafin ta kariso gida uku ta yi wani lokacin kuma gida ta kan biya sai bayan la'asar ta ke dawowa.
Yaji na cika ma danwaken nawa da yasa bayan na ci na kasa ta shi sai faman shi! Shi! Na ke yi saboda harshena da bakina ya nad'e da yaji har cikin kaina.
Ta ko'ina zufa ke ketomin gabadaya rigar material d'in da ke jikina ya jike da zufa idanuwana sun yi jajir harta Fuskata ta nuna alamun na sha wuya.
Zaune na ke kasan tayels din falona filet din da naci danwaken na gabana na kasa Daukewa harta ledan da na sha ruwa nan na watsar da shi ga Roban yaji da yar roban da na zubo manjan bayan na soya.
Saboda kwazzaba danwake bai wuce guda ashirin na jefa ba, sha'awansa naji ina yi shiyasa na yi kad'an saboda ba na so ya kai min dare.
Kamar daga sama naji ana kwankwasamin kofa agogon wayata na Duba dake gefe na, naga biyu da wani abu na rana sai a raina nace kila Umma ce ta dawo tunda in dai ta dawo sai ta fara bugamin kofa na leko mun gaisa kafin ta bude dakinta ta shiga.
Shiyasa batare da tunanin komai ba na mike ina faman shan yaji Saboda Rud'ewa ko dankwali ban saka ba Kitson Shukun da ke kaina tun wanda Adda Fati ta min ne ranar da suka zo da na saka Habiba ta tsifemin na biki.
Shi ma wannan din ya tsufa ballatana Sumana na da Santsi kitso ba ya Dadewa sai ya fara warware kanshi.
Kai tsaye batare da tunanin komai ba na bude kofar lokaci daya ina fad'in"Ummi yau kin..."
Sauran kalamai na sun makale ne samakon ganin abunda ban taba zata ba.
Yana tsaye a kofar dakin sanye da riga da wando baki da fari da jaket a saman kayansa sai kafarsa sanye da Rufaffen takalmi na bakin fata mai kyau
Sannan bayansa goye da jaka kamar ta yan makaranta.
Hannayensa sanye acikin Aljihunsa kyam ya na kallona, sai naji na tsargu na kasa magana sai na fara sosa kai da Hannu guda d'aya mai kyau.
Wanda ya yi dama dama da manjan sai na maida shi baya.
Kunyar duniya duk tabi ta lullubeni cikin sanyin jiki da na murya nace"Sannu da zuwa."
Daga sama har kasa ya karemin kallo kafin ya dan saki fuska kad'an
Cikin maganarsa yace"Yauwa in shigo?
Sai na gyad'a masa kai ammh bansan cewa na tsaya kyam na bake kofar shigowa ba.
Sai da ya kara kallona sannan yace"To ba ni hanya ko Hasiya?
Sai da ya fad'i haka sannan na yi gefe da Sauri ina kif kifta ido kamar mara gaskiya
Sai da ya shigo sannan na kulle kofar na bi bayansa Lokaci d'aya ya na fad'in"ke haka ki ke bude kofa batare da kinsan wa ke miki knooking ba?
Ya fad'a daidai muna karisowa Tsakiyar falon.
Na kasa mgana ganin ya na bin inda na tashi da kallo cikin mamaki ya juyo ya na kallona bai yi mgana ba sai ma ya samu d'aya daga cikin kujerun falon ya zauna lokaci d'aya ya na sauke Jakar hannunsa.
Ajiyar zuciya ya sauke na alamun gajiya ni kuma ganinsa da jaka sai na yi tunanin kila daga tafiyar da suka yi yake.
A gaggauce na duka ina kwashe kayan gabansa cikin jin kunya da nauyi.
Da akwai sauran danwake a Filet din yaji ya yi min yawa yasa ban karisa cinyewa ba.
Filet din yabi da kallo sanda na ke mikewa cikin yanayin mganarsa yace"Danwake ki ka yi?
Kai na gyad'a masa ban yi mgana ba kai tsaye yace"Zan ci. Ammh bari na dan watsa ruwa tukunna."
Ina so nace masa babu ya kare ammh na kasa mgana.
Ya mike ya na fad'in"Akwai ruwa a cikin Tiolet din?
Da rawan baki nace"Eh ammh ba ruwan zafi bari na saka maka."
Bai jiyo ba ya na nufar hanyar Bedroom din yace"Zafi na ke ji ruwan sanyi is ok a wajena."
Daga haka ya wuce ciki sai a lokacin na samu damar Sauke numfashi.
Kitchen na Rumtuma kwanukan wanke wanke tun jiya ban wanke su ba su na fara wankewa sannan na Sake dora masa ruwan danwaken.
Sai alokacin na taba kaina naji ashe ban da dankwali a kaina da gudu na sake dawowa falon na Dauki Dankwali na Daura, sai alokacin naga ashe manja duk ya zuba a saman tayels din ga shi da haske ya bayyana.
Da gudu na koma kitchen na jika Tsumma da ruwa na dan barbard'a omo na goge wajen.
Sannan na dawo na kwaba garin Danwaken na jefa masa cikin mintina sai ga shi na gama komai har na kara gyara kitchen d'in.
Nasan ya na san manja ammh ban yi gaban kaina ba nace bari naji Ra'ayinsa.
Ammh har alokacin yaji bai bar auna min Rad'adi a saman harshena ba.
Sai ga shi mura ta kamani ina ta faman jan majina saboda azaban yaji.
Ina fitowa na gansa