Showing 18001 words to 21000 words out of 98628 words
wuta kila ta lalace ne ko suna gyara.
Kafafuwana kamar baza su daukeni ba haka nake takawa zuwa gareshi.
Tunda na fito yasan nice saboda yanayin jikina da ya gani.
Idanuwansa na kaina har na kariso gabansa cikin sanyin muryata nace"Sannu da zuwa."
Bai amsani ba illah cigaba da kallon Fuskata da ya yi cikin d'an hasken da ke wajen.
Ni kuma na sadda kaina kasa ina faman tura hannuna cikin Hijabin jikina.
Ajiyar rai ya sauke ganin ina Lafiya domin har ga Allah tunda ya tafi baya cikin natsuwarsa.
In ya ce zai zo ya dubani Tahir ya hanashi ya fara fad'in hakan ba shi cikin Tsarin su ba shi kuma Tsoro ya ke ji kada wani abu ya samu yar mutane ba shi da ta cewa.
In kuma yace Tahir din yazo su je sai yace bazai je ba shima kuma ba inda zai je.
Yau din ma Tahir din bai sani ba ya Sulale ya taho saboda ya gaza samun cikakiyar natsuwa.
Numfashi ya sauke kafin yace"A tsaye zamu gaisa?
Jin haka yasa da sauri na fito da hannu na mai dauke da key din dakin ya matsa baya na bude dakin hannuna na rawa.
Ni ce a gaba sannan ya bi yo bayana dakin da Dubu ban kunna Fitila ba.
Shi ya kunna hasken wayarsa sannan na samu damar ganin fitilan saman kujera na karisa na kunna haske ya cika Dakin dayake tunda na Fahimci basa barin wuta da rana sai na ke sokata a chaji kafin na kwanta zuwa Safe ta cika da Chaji.
Bai jira ni na zauna ba ya samu waje ya na kallona Lokaci daya ya na fad'in"Zauna mana."
Ba musu na zauna kujeran da ke yamma da shi.
Ledan hannunsa ya sauke a gabansa kafin yace"Kina lafiya ko?
Sai na kasa amsa masa da baki kai kawai na gyad'a masa.
Cikin natsuwarsa yace"Kin tabbata?
Sai na dago ina kallonsa kafin na yi mirmishin yake ban yi mgana.
Shi kuma sai ya yi tsam saboda Sai yaga kamar wani kallo na yi masa na irin baka kyautamin ba.
Baya so ma ya na kallona Tausayi na ke ba shi mganar gaskiya.
Shuru na wani lokaci kafin yace"Naga mutane a gidan ne sosai."
Cikin muryata nace"Eh wacce zata tare a dakin chan suka kawo kayan daki"
Jinjina kai ya yi kafin yace"Good akallah zaki samu yar'uwan zama"
Sai na gyad'a masa kai alamun hakane.
Daganan muka yi shuru har na tsawon mintina goma ba wanda ya kara mgana.
Wayarsa ya duba yaga kafin ya Dago ya na fadin"Lokacin sallar isha'i ya yi zan tafi ina so na tsaya a masallaci na yi sallah."
Da idanuwana da suka cika da Ruwa na kallesa kafin na samu zarafin magana ya mike tsaye ya na fadin"Ba abunda ki ke da bukata in zan dawo sai na taho miki da shi?
Sai na samu kaina da fad'in"Bakomai."
Kudi ya ciro cikin Aljihunsa yazo har gabana ya ijiyemin tare da ledan nan ya na fad'in"Ki rike a hannun ki kin ji ko?
Bansa ta ina raunin ya nuna kansa ba sai ji nayi hawaye na bin fuskata.
Shima hawayen ya gani ya sa ya dakata da mgana jikinsa a matukar sanyaye yace"Hasiya Lafiya? Me ya faru?
Da sauri na saka hannu na share hawaaye na kafin na kira sunansa.
"ASSADIQ.."
Yadda na kira sunan shi cikin karyewan Sauti ne yasa sai da ya samu kanshi da dukawa a gabana ya na kallon cikin kwayan idanuwana yace"Menene? Ko baki da lafiya ne?
Kai na girgiza masa kafin nace"Yau ma tafiya zaka yi ka bar ni?
Sadiq yaji kamar an kwarara masa ruwan sanyi saboda yadda jikinsa ya yi wani sanyi kalau.
Hucin zafi ya fitar daga bakin shi kafin yace"Hasiya ba na gayamiki yanayin aikin nawa ba?
Nan ya yi min nisa da wajen aikina ne sannan muna yawan tafiye tafiye ne ni da ubangidana."
So na ke ya kalleni ne ammh ya kasa kallona cikin idanuwana kansa na kallon kasa ne kwata kwata ya ki yarda ya had'a ido da ni.
Ganin haka yasa na kasa bud'e baki na yi mgana saboda ba ni da abun cewa.
Shi kuma nauyin jiki yasa ya kasa tashi ji ya ke yi kamar bai kyauta ba yana ji kamar wannan tsarin na shi ba tsari ba ne mai kyau.
Hakkin Hasiya na kanshi in ya aikata mata ba daidai ba Allah zai tambayeshi.
Bazai iya bude baki ya gayamata cewa auran su ba kamar yadda ta zata ba ne ya kasa yi ma Amma gaddama ne yasa ya karb'i auranta bazai iya gayamata cewa kafin ya gama Hidimar kasarsa nan da wata shidda sakinta zai yi ba.
Da sauri ya mike sai da ya juya mata baya yace"Ki yi hakuri zan rika zuwa ina dubaki Lokaci bayan Lokaci. Kuma ma ba ga shi kin samu abokiyar zama ba?
Bayansa na bi da kallo kafin nace"Hakane."
Jin na amsa shi yasa ya juyo ya na Fadin"Zan tafi. Ki kula da kanki in ban zo gobe ba jibi zan zo in sha Allahu."
Da toh na amsa masa ya fara tafiya ya na fadin"Taho ki kulle kofar.".
Ba musu na mike rike da kudin da ya ijiyemin a saman jikina har zuwa bakin kofa ya na fita ya juyo ya na kallona ni kuma ina rike da kofa kamar zan yi kuka.
Ganin haka yasa ya Rausayar da kai ya na fadin"Babu fa wani abu ki rika addu'a in zaki kwanta sannan ki rika Rufe kofarki kada ki bude ma wanda baki sani ba ok?
Jinjina masa kai na yi shi kuma sai ya zura hannayensa cikin Aljihun sa gabadaya kafin yace"Sai da Safe."
Nima na bi shi a sanyaye da Sai da Safe.
Har ya juya ya fara tafiya ina Tsaye bansan Lokacin da na kira sunan shi ba"ASSADIQ.."
Da Sauri ya juyo ya na kallona cikin mamaki.
Dawowa ya yi kofar dakin ya na fadin"Menene?
Kaina na kasa nace"Na koma wajen su?
Cikin mamaki yace"Wajen su wa?
Da hannu na nuna masa dakin da ke gefena da mu ke jin hayaniya.
Bi na ya yi da kallo cikin nazarina kafin yace"A'a ki zauna a dakin ki kin ji ko?
Saboda ya na tsoron kada naje su gane yanayi na su tambayane ni nw fad'amusu mijina baya kwana a gidan tunda muka tare.
Duk da rai na bai so ba ammh sai na Hakura tunda yace a'a bai tafi ba sai da yasakani na koma ciki na Rufe kofa sannan ya fita daga gidan ya na sauke numfashi.
Karfi da yaji halayensa na so su gurbace Sanadin haduwarsa da Hasiya ya fara karya da kumbibiya ya fara kokarin zama munafukin Namiji.
Ni ko ina kulle kofata ciki na shige na Dauro alwala na yi sallar isha'i sama sama nayi addu'a sannan na fito falo na duba ledar da yazo da shi tsireni mai uban yawa da yaji kuli da albasa da kokumba sai kyalli ya ke yi ga shi da zafi inaga da zai taho ya tsaya a siya.
Sai kuma Lemun fanta da maltina masu sanyi suma.
Miyau na har ya na tsinkewa ko samun daman Dauko Filet ban yi ba na zauna na fara ci sai da naji cikina ba waje daman ban yi girki da rana ba Taliya dawake na dafa da Dadddren jiya ita na Dumama da Safe da ta ragu ne na ci da Rana.
Na rage kusan rabi na kulle shi a ledan na kai kitchen na boye ban sha ruwa ba Maltina nan na shanye duka na yi gyatsa na koma na jingina da kujera ina maida numfsshi.
A bun ka ga wanda ya ci ya koshi sai naji na fara jin barci sama sama sai na tashi na haye saman kujera na kwanta ba jimawa sai barci.
Bansan na jima ina barci ba sai da naji bugun kofata kamar a sama na tashi a firgice kuma a tsorace.
Tashi na yi naje na bud'e sai naga Hajiya zainab matar nan masu danki.
Ashe sallama za su min sun gama zasu tafi sannan ta dawo min da jug dina da Kofina.
Na karb'a cikin murya barci muka yi sallama da juna har ta na cewa a gaida megidan rashin sani bata san ni kad'ai ce acikin dakin ba.
Maida kofata na yi na kulle saboda barcin da ke idona nan falo na ijiye jug din na shige ciki na kwanta ko kayan Jikina ban cire ba.
Washegari ma ban tashi da wuri ba, barci na sha sosai sai wajen goma na tashi, ban dafa komai ba Sauran tsiren nan na du'mama a tukunya na ci na sha Lemu fanta duk da ina da Ulcer ma naji ina Sha'awan lemum shiyasa na sha.
Da rana kuma Macaroni na Dafa jalop guda daya, naci ni kadai a gida sai da yammah wasu matan suka kara zuwa sun kawo wani kaya ba su jima ba dai suka tafi.
Kuma har dakina suka shigo muka gaisa na ba su ruwa suna ta min godiyan Dawainiya.
Wata mata acikin su ta kalleni ta na Fad'in"Ai ba ma zata wuce sa'an Ummi ba."
Ta gefenta tace"Nima haka nace acikin raina."
Su naji suna hiran su na ko a baya an daga bikin ne suna ta fad'in ba ga shi har Lokaci ya yi ba satin nan ne bikin da Daurin aure.
Acikin raina murna na ke yi kamar wacce za'a kawo wata yar'uwata.
Ko bakomai zaman kadaici bazai kasheni ni kad'ai ba.
Assadiq yace gobe ko jibi zai dawo ammh Shuru bai dawo ba ni ko har ina ta tsammanin shi.
Na fara tunanin meyasa bazai kwana anan ba? Hujjar da ya ba ni ba hujja bace mai karfi tunda muna gari daya ne ba wani gari ba ne zuwa wani gari ba.
Indai ko hakane ya na da dalilinsa na yin haka, kila ko ya na gujema hakanan ne saboda Canfin da ke kaina.
In dai ko zai cigaba da tsira da lafiyarsa gwara nesa nesa da kusa kusan nan da baya haifar da d'a mai ido.
Tunanin haka yasa na cire abun a raina na rika zirga zirgata.
ina kewar yan'uwa mussaman ma Amma ina so na kirata mu yi mgana na roketa ta yafemin domin na tabbata gatan da ta yi min ban da ita ba wanda zai iya yi min wannan gatan.
*****
Sadiq kunyar kallon Hasiya ya ke yi shiyasa ya kasa komawa.
Gefe d'aya Tahir na gayamsaa in ya cika zuwa za'a zo a samu matsala.
Wanda samuwarta bazai haifar masa da d'a mai ido ba.
Ya nuna ma Tahir ba wanda ya san shi anan ballatana yace ya na tsoron kada labari ya kai gusai.
Shi kuma Tahir ba ma wannan ne Tunaninsa ba yasan tunda nan din babu wanda yasan daga ina suke abokan karatunsu d'ai d'ai ku ne yan zariya duk yan wasu jahohin ne.
Gwara ma shi za'a iya sanin wanene shi ammh Sadiq tun farkonsa ba mai iya nuna kansa ko shi waye bane.
In ba na kusa da shi ba balle ka Fahimci wanene shi ba.
Shi Tsoron sa d'aya Kada Sadiq ya cigaba da shigema zabiyar yarinyar nan ta ribacesa ya fara sonta ko wani abu ya shiga tsakaninsu ta Bata masa Rayuwa.
Domin shi har ga Allah ya aminta da Mganar mutane akan Hasiya ballatana da yaji daga bakin iyayenta da yan'uwanta.
Ba rami fa ba abunda zai kawo mganar rami gwara dai tunda ya Riga ya kai kansa to a samu hanyar da zasu rabu lafiya shine kawai taimakon da zai iya yima Sadiq ya saka masa da Tarin alherinsa garesa.
Shi kuma Sadiq a lokacin ya zama wani ga shi nan ne abunda ya aikata ba da sanin iyayenshi ba ya fara Damunshi shiyasa duk abunda Tahir sai ya kasa masa musu, duk da yana jin Tausayin Hasiya fargabansa kada ciwo ko wani abu ya sameta cikin Dare ba bu wani a kusa da ita gida ita kad'ai, fargabansa ta ragu ne ma da yaga dakin kusa da ita mutane za su shiga da Sauki sauki zata rika jin motsin mutane.
Yanzu haka Dari dari ya ke da kiran Abba ko Umma sai yaji kamar suna kallonsa da abunda ya aikata batare da sanin su ba ko yarda ko kar ya yarda yaci Amanar iyayenshi da ya iya aikata babban al'amari batare da saninsu ba.
Baisan me ya shiga kansa ba har ya amince da auran Hasiya ba sai dai komai ya faru sannan ya dawo hayyacinsa.
Shiyasa ya rage kiransu a waya sai dai su su kirashi suma baya tsawaita mgana da su hakama Sauran Sisters dinsa kowa ya Fahimci yanzu Magajin gida ya sauya ya rage sakin jiki da su su sha hira ko a waya ammh sun masa uzuri Tunaninsa aiki ne ya yi masa yawa tunda ya kusa gama Hidimar kasar na shi..
Ya gama tsara yadda abubuwa za su cigaba da kasancewa gwara ya siyama Hasiya karamar wayar da zata kiran yan'uwanta ta na rage kewa kafin ya yi natsuwar da zai san irin taimakon da ya yi niyar yi mata na inganta Rayuwarta kafin su rabu.
Sannan shima zai rage fargaban ko wani abu zai sameta zai rika kiranta yana jin lafiyanta.
Sannan kuma in wani abu ya same ta ko ta na bukatar wani abu zata iya kiransa.
Shi kad'ai ya yi wannan tunanin shiyasa bai aiwatar ba sai da ya tambayi Tahir shawara.
Shi kuma sai yace shawaran tasa ta yi ya siya mata waya ammh sai ya gargadeta.
Sadiq ya kallesa cikin mamaki kafin yace"Gargad'in me?
Tahir ya gyara zama ya na fad'in"Kada ta fallasa sirin zaman ku ga yan'uwanta ko kawayenta. Saboda in sukaji zasu dora ayar tambaya akan motsinka da kuma Dalilin ka."
Sadiq ya yi shuru kafin yace"Hakane to ta ya zan ce mata kada ta gayama kowa?
Tahir yace"gayamata zaka yi kai tsaye."
Sadiq ya yi shuru bai yi mgana ba ya na Tunani Tahir yace"Kada dai ka gayamata mganar rabuwar ku yanzu sai mun kusa komawa gida tukunnah Lokacin ka bata taimakon da kace kaga bazata damu ba sosai."
Shi dai Sadiq bai amsa ma Tahir ba ammh kallonsa ya yi da mamaki yana jinsa ne kawai in yace wai bazata damu ba in suka rabu.
Aure sunan shi aure ko ya ya yake kuwa kuma saki ba shi dad'i ko da a fatar baki ne kuwa.
Da kansa yaje pizzet ya siya karamar waya Tecno dubu takwas tare da layi ya kuma yi mata Rigister bai kai mata ba sai da ya chaja mata ya saka mata lambarsa a wayar ya kuma yi saving da sunan da ta ke kiran shi ASSADIQ.
Ranar asabar da daddare ya je ya kaimata da tare da Tahir za su zo sai kuma yace ya fasa sai in zai koma da Rana ido na ganin ido sai su tafi dare.
Har Sadiq na zolayansa da cewa ya gane wayonsa girkin Amarya ya ke so yaje ya ci.
Tahir ya sheke da Dariya kafin yace"girkin wata Amaryan? Su Amarya sun ji jiki. Wannan yarinyar bazata dafa abinci na ci ba."
Sadiq ya kallesa kai tsaye kafin yace"Tahir ba sunanta yarinya ba. Hasiya sunanta."
Ya fad'a ya na hade rai Tahir ya kara sakin Dariya kafin yace"Angon karya na Hasiya. Angon gaskiya na Sultana."
Ya na yi masa wannan shakiyancin ya fita ya barsa.
Sai da ya tsaya a hanya ya samu jam'in sallar isha'i sannan ya karisa koda yaje ya iske gidan cike da yammata ga shi akwai wuta.
Ya na ganin haka yace an kawo amaryan kusa da Dakin Hasiya kenan.
Lokacin da yazo dakina ya na bude tunda wasu daga cikin yanmatan Amarya sun shisshigo dakina wasu nan ma suka yi sallah iyayen ana kawo Amaryan ba jimawa suka tafi.
Hajiya zainab ce tace ma yan matan in suna Bukatar wani abu su yi min mgana.
In ka ganni sai kace nima ina cikin yan bikin ne sabon materil dina na saka Doguwar riga bakina a washe saboda ganin mutane, Allah ya gani na saba zama cikin jama'a shiyasa na ke murna da wannan sha'anin.
Bansan zai zo ba har wata na tambayana miji na ya na gari? Sai nace a'a ya yi tafiya ban jima da bata amsa ba suna kuma zaune afalo in da suka yi sallah ni kuma ina kitchen na Dora Taliya jalop ganin baki kada su ce ba na girki ina da Rowa.
Ban ji sallamansa ba ballatana shigowarsa dakin ni dai fitowa falo na yi naga ba yanmatan nan sai shi ya na zaune ya na latsa wayarsa.
Cikin mamakin ganinsa na yi masa sannu da zuwa ya amsa.
Ruwa a jug naje na debo masa sai da na kawo sannan ya kalleni ya na fadin"wannan wani ruwa ne? Kai tsaye nace na nan gidan nan ne.
Bude baki ya yi kamar zai yi mgana sai ya fasa ya tashi ya fita.
Ba jimawa sai ga shi ya dawo da ledojin pure water wajen guda Biyar nazo zan karbesa ya matsa gefe ya na Fadin"Kaji min yarinya ke yaushe zaki iya?
Jin haka yasa na matsa baya ya shiga kitchen ya sauke ruwan.
Sai yaga ina girki ya fito ya na kallona Lokaci daya ya na fad'in"Girki ki ke yi?
Da kai na amsa ban yi magana ba Mirmishi ya yi kafin yace"Ki ce yau zan ci girkin Amarya."
Dariya na yi ina Rufe fuskata da Tafukan hannuna.
Wuceni ya yi ya na fadin"Rufe kofa ki zo ki gani."
Ban kawo Tunanin komai ba naje na Rufe kofa na dawo.
Na gansa da kwalin waya kirana ya yi nazo gabansa na zauna ya mikamin kwalin ya na fad"in"Ga wayarki nan"
Ido na zaro kafin nace"Eh..'"
Dariya na bashi sai da Fararen Hakoransa suka bayyana
Cikin kwarin gwiwa yace"Taki ce ni na siya miki."
Sai gani kan kafafuna bakina kamar zai yage.
Na warce kwalin wayan ina dubawa cikin murna nace"Ka siya min waya? Ni?
Da kai ya amsamin kafin yace"Bud'e ki gani."
Rawan jiki yasa na kasa budewa sai da ya karb'a ya bude min ya fiddomin wayar ya kunna min ita ya mikamin
Bakina a washe na karb'a ina dubawa dai na kalleshi na koma kuma ina kallon wayar bakina ya kasa Rufuwa.
Ya yi min abunda na ke so alokacin da nake tsananin bukatar waya.
Na kallesa ya na min dariya ganin yadda na kasa Rufe bakina.
Gira ya dagamin kafin yace"Kin samu ta kiran Amma da su Adda Fati. Zaman kadaicin ya kare ko?
Idanuwana suka ciko da kwallah kawai sai na duka ina fadin"Nagode sosai Allah ya saka da alheri ya kuma kara budi."
Ya amsa da Ameen lokaci daya ya na saka Hannu ya dagoni Tsaye ya na fadin"To baki latsa wayar ba."
Ai ya na cewa haka na koma na zauna na fara latsa wayar ina shige shige.
Gefena ya zauna ya na fadin"Kin iya sarrafa wayar ko?
Cikin murna nace"Eh mana Abubakar ya taba siyamin irin ta kafin auran mu."
Sai da