Showing 3001 words to 6000 words out of 98628 words
yi kuka ina kallonta fuskata har ta koma jajur Saboda kuka nace"Eh mana da kun bar na zauna da rayuwata da ya fiyemin auran nan shine ke jawomin komai, in ban auri kowa ba wazai ce nayi sanadiyar rasa lafiyan wani? Balle ace an rasa dukiya!? ni rayuwata ba tare da kowa ba ta fiyemin kowacce Rayuwa da ki ke yi min Fata Amma."
Zuwa Lokacin har Ramatu kuka ta ke yi Hamma Isuhu ne ya yi jarumtar rikeni yana kiran sunana da karfi ammh ina kuka kawai na ke yi ina fad'in"Assadiq ya sakeni yanzu ba na bukatar auransa a kaina."
Amma ce tace Ramatu da Adda Fati su fitar da ni daga Dakin haka suka Rikeni ina kuka ina kururuwa suka fita dani daga Dakin daman matan gidanmu suna fara jin kuka suka yi Dafifi ana son jin gulma.
Suna ganin an fito da ni suka yayyame mu suna tambayan ba'asi ba wanda suka tanka suka shige da ni Dakin Maman Boy.
Ramatu rikeni ta ke yi ta na Fad'in"Hasiya don Allah ki yi shuru"
Na kasa domin komai da ya faru da ni tundaga farko ne ya ke dawowamin da kuncin acikin raina na kasa Sarrafa kaina.
Kawai sai na Rungume Ramatu ina Fadin"Ramatu kamar na mutu haka nake ji. Gwara mutuwata da wannan rayuwar"
Baki ta Rufemin ta na Fad'in"Kada ki yi sabo Hasiya ki bari don Allah kin ga jama'a hankulansu ya dawo kan ki."
A tsakar gida kuwa Adda Fati sai shan Tambayoyi ta ke yi har da masu cewa ko wani abu ne ya samu angon?
Ita dai ta ma kasa mgana ta sulalane ta koma Dakin Amma ta isketa ta na ta kuka Inna Talatu na faman lallashinta har Adda Rukayya ta kasa tsaida kukanta.
Adda Fati Sadiq ta kalla da kansa ke kasa kanzil bai ce ba Tahir ne ke kallonsa a ransa ya na Tunanin shi ko Sadiq ya na da zuciya a kirjinsa kuwa? Duk yaji irin wannan bakaken kaddarorin ammh bai iya furtama yarinyar nan saki Lokacin da ta bukata ba? Shifa ko alama bai Tausaya musu ba su san su na da matsala meyasa suke kokarin gayyato wani cikin rayuwarsu?
Wannan abunda suka aikata ba Adalci acikinsa sam itama yarinyar ai tasan gaskiya abunda aka aikata akwai cutarwa acikinsa.
Hamma Isuhu ya ji hon din mai Mota yasa ya fita da sauri ganin haka yasa Adda Fati ta kalli Sadiq ta na fadin"Amma yau zata koma garinsu gabadaya. Mganar Hasiya kuma kayan Dakinta suna hannuna kana da inda za'ayi mata jere ne yanzu.?
Tahir ya kalleta kamar zai yi mgana sai ya fasa ya jira Sadiq da ya kawo kansa yasan mafitarsa.
Kai Tsaye cikin natsuwarsa yace"Yanzu kam babu ammh za'a samar in sha Allahu. "
Adda Fati tace"Shikenan daman in tambaya ya za'ayi ne zaka tafi da itan ne?
Tahir ya yi tsam yaji amsar Sadiq yaji bai ce komai ba, kawai sai shi ya kalli Adda Fati ya na fad'in"Mu tafi da ita mu ijiyeta a ina? Bamu da inda zamu sauketa dakin da mu ke ciki Falle d'aya ne da ni da shi muke kwana aciki."
Tahir ya fad'a cikin jin Haushi Sadiq yasan Halin Tahir aka cigaba da mgana sai kuma ya sauya zencen yasa da Sauri yace"Zata iya zama a wajen ki na wani lokaci kafin na sama mata muhallin da zata zauna?
Ya fad'a lokaci daya ya na kallon Adda Fati wacce ta kalli su Amma sai suka gyada mata da yasa ta jinjina kai kafin tace"Shikenan bakomai. ga lambata in ka samu wajen sai ka sanar da ni akan Lokaci."
Ba muau ya fiddo karamar wayarsa ya mika mata ta saka masa lambarta shi kuma ya kirata saboda ta ga Lambar sai ko ga kira ya shigo wayarta dake cikin jaka ta Dauko ta na Fadin"Bari na yi Saving din lambar."
Bai ce komai ba ta na cikin Adana lambar Isuhu ya leko ya na fadin"Amma ya kamata mu tafi yanzu Direban ya matsa dare ya ke gudu."
Jin haka yasa Amma tace"Hakane to bari na fito"
Jin haka yasa Sadiq ya mike shi da Tahir a sanyaye yace"Allah ya tsare hanya Amma."
Amma ta mike ta na gyara Daurin zaninta Lokaci daya ta na fadin"Ameen nagode sosai Allah ya jikan magabata. Allah ya yi muku albarka."
Tahir ta kallah taga sai wani cin mgani ya ke cikin dan mirmishi tace"Shi wannan abokin naka baya mgana ne?
Sadiq ya kalli Tahir kafin yace"Ya na yi ammh ba sosai ba."
Amma bata damu ba ta jinjina kai ta na fadn"Allah ya taimake ku. Allah baku yarda zaku yi ya kuma rabaku da Sharrin duniya da Mutanen cikinta."
Sadiq ne kadai ya amsa da Ameen banda Tahir duk tare suka fito daga Dakin Amma na ta ce ma su Maman Boy tafiya ta tashi fa.
Sadiq da Tahir kofar gida suka tafi suka Tsaya Sadiq na son ganin Tafiyar Amma shi kuma Tahir tsoro ya ke ji kada ya tafi ya bar Sadiq shi kad'ai domin ya fara jin Tsoron mutanen nan shiyasa bai tafi ba ammh ba domin haka ba Tuni bai san inda dare ya yi mishi ba Allah dai ya isa ba kowa ya Cucesu ba sai Sadiq haka kurum yau ya hanasu su kwanta su huta ya kawosu inda kwata kwata ko a Tsari Rayuwarsu bata yi daidai ba.
Har Dakin Maman Boy Amma ta biyoni ta dafa kaina ta yi min addu'a daga karshe ta mike ta na fad'in"Allah yaga kyakyawan niyyata Hasiya. ina miki Fatan alheri da samun ingantattaciyar rayuwa a gidan auran ki in kin huce ki ka nemi sai na yi miki nasihan da uwa kan yi ma yarta a lokacin da zata je gidan mijinta."
Daga haka ta fice ina jin Ramatu ma ta fita tasan ko tace na tashi bazan tashi ba jin irin kukan da na ke yi.
Yan gidanmu da makota na kusa da na nesa duk sunzo sallama da Amma Allah Sarki Sabo suna ta kuka itama ta na kuka Adda Rukayya kuka Adda Fati ma haka, Habiba ko ta makale Amma ta na ta kuka Dakyar aka Rabasu sai cigiyata ake yi ana fad'in Ina Hasiya?
Maman Boye ke ta fad'in"Ta na chan ta nata kukan a daki ita kad'ai"
Maman Salihi ta karbe da fad'in"Abu biyu ne ya had'e mata ga Aure ga tafiyar Amma."
Su kadai dai suke kid'an su suna rawan su Adda na ta kuka ba su bi ta kansu ba.
Gaba Amma ta shiga ita da Hamma jama'a na ta daga musu Hannu.
Motar na wucewa Tahir ya fizge Hannun Sadiq suka nufi hanyar dakin su Sadiq na binsa a baya ya na mirmishi ya ke fad'in"Sake ni ba guduwa zan yi ba Tahir Yusuf Daura."
Tahir yace"Tunda ka iya aure batare da sanin kowa ba to shima ka gudun abu ne mai sauki a wajen ka"
Sadiq sai da ya yi dariya har Fararan Hakoransa suka bayyana.
Cikin kwarin gwiwa yace"Ba inda zan gudu Tahir.
Tahir bai sake masa hannu ba sai da suka Danganta da Dakinsu ya saka hannu daya ya bude kwadon dakin ya tusa kansa da Sadiq ciki ya maida koda ya Rufe.
Ya cire riga da wando ya bar kanshi Dagashi sai gajeren wando.
Wayarsa ya Dauko ya na Fadin"Sadiq ko ka saki yarinyar nan yanzu ko Billahillazi na kira Umma na fad'a mata duk abunda ke faruwa."
Ya fad'a ya na kallon Sadiq ido cikin ido Tunda ya zare bakin gilashin da ya sanya.
Sadiq ya yi zuru ya na kallon Tahir yanzu in yace zai yi wata mgana Tahir ba burga ya ke yi ba, zai iya aikata abunda yace din.
Kuma hakan daidai ya ke da ruguza duka Tsarinsa lallaba Tahir yanzu shine a gabansa kafin yaji da Hasiya Daga baya.
Mikewa ya yi shima ya zare Rigan jikinsa daga shi sai Farar Vest.
Cikin kwantar da Murya yace"Tahir na fad'a maka taimakonta zan yi. Da zarar na inganta mata rayuwa Zan SAKETA da gaske."
Tahir ya kallesa cikin shakku kafin yace"Zaka saketa ka ce ko?
Sadiq ya jinjina kai kafin yace"Eh zan saketa Ammh ba yanzu ba?
Tahir ya katse shi da cewa"Har na tsawon wani Lokaci?
Sadiq ya yi shuru kafin ya sauke ajiyar rai ya na fad'in"Ban sani ba ammh dai nasan auranta ba kamar Sauran aure ba ne Tahir tabbas zan rabu da ita ko saboda Ahalina."
Tahir yace"Me yasa ba yanzu ba?
Sadiq yace"Haba baka ganin halin Tsaka mai wuyar da na shiga ne? So ka ke na saketa yanzu na karya zuciyar Uwa mahaifiya ka duba mana Tahir."
Tahir ya yi dariyan Takaici kafin yace"ka faranta ma uwar wata rai kai kuma ka bakanta ma taka uwar kenan?
Sadiq ya girgiza kai ya na Fadin"Tahir zauna mu yi mgana"
Tahir nace ka zauna don Allah."
*Janafty*
*17/01/2024*
*TMWB2K002*
*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*
https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj
K'in zama Tahir ya yi sai da Sadiq da kansa ya saka hannu ya ja shi da karfi ya zaunar da shi.
Shima ya zauna a gabansa ya tankwashe kafa suna Kallon junansu.
Sadiq ya kalli Tahir ya na warware hannunsa lokaci d'aya ya na fad'in"me ka ke son sani yanzu? Me kuma ka ke bukatar a yi?
Tahir ya shaki iskan Takaici kafin yace"Abunda na so ayi lokaci ya riga ya kuremin. Abunda na ke bukata kuma na riga na sanar da kai tun farko"
Ya fad'a cikin cin mgani, Sadiq ya murmusa Allah kad'ai yasan Halin da zuciyarsa ta ke ciki ammh bai rasa kwarin gwiwa ba niyarsa ta Alheri bata bar shi ya ji ya yi Nadama ba.
Cikin sanyin murya yace"Me ka ke bukata Tahir?
Wata uwar Harara Tahir ya sakar masa kafin yace"Bansani ba. Ka fi kowa sanin abunda na ke bukata. Ka sake yarinyar nan domin kasancewata abokinka kamar yan'uwa muka dauki juna. Bazan jure ina ji ina gani ka jefa rayuwarka cikin Halaka ba."
Sadiq ya yi saurin cewa"Ba Halaka ba ne Tahir taimako na yi."
Cikin kufuluwa Tahir yace"Wai ka na ta cewa taimako, hala dole kai Allah ya wajabta ka taimaka musu? Meyasa sai kai? Mazaje nawa ne a gari ba'a neme su ba sai kai?
Sadiq sai ya kasa mgana ganin haka yasa Tahir ya cigaba da zazzaga masifa da kuma alwashin ko Sadiq ya saki Hasiya ko ya kira Umma ya Shaida mata komai tundaga fari.
Sadiq ya yi shuru bai yi mgana ba illah agogon hannunsa da ya kallah kafin yace"Mu yi sallah sai mu cigaba da mganar"
Ya yunkura zai mike cikin zafin Nama Tahir ya maida shi zaune lokaci d'aya ya na fadin"Ba inda zaka je sai mun gama mgana Mallam"
Sadiq ya kallesa cikin mamaki kafin yace"Tahir sallah na gaba da mganarmu."
Shuru Tahir ya yi jin ya fisa gaskiya ganin haka yasa Sadiq ya mike ya na fad'in"Mu yi sallah yau ina da Lokacin ka kaji."
Ya fad'a ya na yar dariya, Dariya ya girgiza kai bai kara mgana ba.
Sun riga sun makara shiyasa a gida suka yi sallar su abinci ma ba wanda ya nema hatta ko Tahir da baya wasa da abinci, suna idar da salla ko Addu'a Tahir bai bari Sadiq ya yi ba yace su cigaba da maganar da suka fara.
Sadiq ya koma ya gyara zama yasan ai yau sai Allah tunda ya shiga Hannun Tahir ya bani wai barawo a hannun mata.
Cikin Sarewa yace"Fad'i abunda ka ke so ayi Tahir."
Tahir yace"Meyasa ka ke so ka nuna kamar bakaji me na fad'a tun farko ba ne? Sakin ta na ce ka yi ko?
Sadiq ya yi shuru ya na kallon Adon Darduman gabanshi kafin ya dago ya na kallon Tahir cikin muryan Kaushi ya ce"A'a Tahir nace maka zan saketa ammh ba yanzu ba."
Tahir yace"Me ye hujjar ka?
Sadiq yace"Ba na sanar da kai ba, na tausayama rayuwarsu ba su da kowa sai Allah ka na fa gani kuma kaji me dan'uwan mahaifinta ya ke gayamin su kansu sun gujesu in na saketa a wannan Lokacin zan kara fasa gurbin bakinciki a rayuwarsu"
Tahir ya yi saurin taran shi da cewa"Dangin mahaifinsu sun gujesu kai kuma waye na su da zaka Rumgume su Sadiq?
Sadiq ya sauke numfashi kafin yace"Tahir kuka fa matar nan ta rika yi mini. Bazan iya juran ganin Uwa ta na kuka saboda matsalan da zan iya mata mganinta ba, Ita bukatar ta Rayuwar Hasiya ta inganta shiyasa na amince da bukatar ta ammh ni kaina ina da nawa tsarin akan haka."
Tahir ya kura masa ido bai basa damar mgana ba ya cigaba da fad'in"Ba son raina ba ne na yi wani abu batare da sanin iyayena ba Tahir. Da farko na so na sanar da su sai na fasa sanin ba wanda zai goyamin baya shiyasa na yanke wannan hukuncin."
Tahir yace"Naji ka yanke hukunci mafitar da zata bulle da kai fa batare da auran nan ya je kunnen su Umma ba?
Sadiq yace"Kai zaka ba ni wannan Mafitan Tahir"
Tahir ya ware ido kafin yace"Ni kuma? Sadiq ya jinjina kai kafin yace"Eh Tahir saboda kai kad'ai ne na kusa danin da yasan da Labarin auran nan mafitan bangaranka shine ka yi Shuru da bakin ka har Abada ka da wani yasan da wannan mganar.".
Tahir ya yi shuru bai ce komai ba ganin haka yasa Sadiq ya dafa kafad'ansa ya na fad'in"Don Allah Tahir in ka yi min wannan taimakon ka gama sama min dukkan mafitan da na ke hange."
Tahir ya sauke Numfashi kafin yace"Kasan dai abunda zaka sani na aikata ko?
Sadiq yace"Na sani mana, niyyata zaka duba kai ma sai ka dubi ta ka niyar na taimakon abokin ka."
Tahir yace"Naji kai kuma mafitan bangaran ka fa?
Sadiq ya gyara zama ya na Fad'in"Mafitan bangarena shi ne har lokacin da zai cika na saketa ba wanda zai sani nan da zuwa wata shidda lokacin mun gama Hidimar kasarmu nan zariya ne dagani har kai ba Tushen mu ba ne tafiya zamu yi mu koma Mahaifarmu."
Tahir ya kura masa ido ya na neman karin bayani Ganin haka yasa Sadiq ya cigaba da fad'in"Sai dai kafin nan nayi alkwarin inganta rayuwarta da ilimi tare da jari mai karfin da ko bayan na saketa abun bazai dameta ba sosai."
Shuru suka yi dukkansu kamar masu nazari kafin Tahir yace"Har yanzu baka samar ma kanka wata mafitar ba" Sadiq cikin mamaki ya kallesa kafin yace"Kamar wacce mafita kenan?
Tahir ya gyara zama ya na fad'in"Ka manta kace ta zauna gidan yar'uwata kafin ka sama mata Muhalli? mafitan in da zaka ijiyeta batare da kowa ya sani ba na ke mgana."
Sai gabad'ayansu suka kalli juna cikin nazari na wani Lokaci kafin Sadiq yace"Zamu samo wannan mafitar daga baya."
Tahir ya ciji lebensa kafin yace"Na kasa aminta da wannan al'amarin Sadiq. Kai ne ka auri bazawara wace auranta biyu fa ka sani."
Sadiq cikin Halin ko in kula yace"Kada ka fara duba wannan Tahir, Annabin mu da bazawara ya fara ya auri Nana Khadija ya na Saurayi dan Shekara ashirin da Biyar a duniya ita kuma ta na da Shekarun arba'in a lokacin. Ka ga da ba'a auran bazawara da Allah bai umarci Annabin Rahma salallahu alaihi wasallam da ya auri Nana Khadija ba.'
Tahir ya tare shi da fad'in"Yanzu sunna na wa kaga mutane na takewa Sadiq?
Sadiq yace"Wannan na su tsarin ne ina so na gayamaka auran bazawara ba Haramun ba ne, Kuma ka sani Annabi shine Jagoranmu abunda ya zo mana da shi ko ya aikata ko Sahabansa suka aikata shine abun koyin mu."
Tahir sai ya kasa mgana ya koma ya na kallon Sadiq kafin yace"Ko ka fara son yarinyar nan ne Sadiq?
A kaikace Sadiq yace"Wata yarinyar?
Tahir na gatsine yace"Zabiyar ka ko nace yar bazawarar amaryan ka."
Sadiq ya jinjina kai ya na mirmishi kafin yace"Sunanta Hasiya Tahir."
Tahir ya dage gira ya na fad'in"Ni kuma ban san sunanta ba."
Sadiq ya kallesa batare da ya yi mgana ba Tahir yace"in ka fara sonta ne ka fad'amin domin naga akan lamarinta kafi kowa zakewa ne"
Sadiq ya yace"In na fara son nata zan gayamaka Tahir ammh yanzu na gayamaka ba mganar so a tsakanina da wannan yarinyar ka gane?
Tahir yace"Zan gane nan da wata shidda in sha Allahu."
Sadiq ya bi Tahir da kallo mai ya Daukesa ya na Tunanin zai karya alkwari ne?zai ko ba shi mamaki in sha Allahu.
Sun yi shuru kenan wayar Sadiq da ke gefen Tahir saman gado ta hau Ruru da sauri ya dauko masa ya duba mai kira cikin zaro ido yace"Umma. umma ce ke kiran ka."
Sadiq cikin natsuwa ya mika hannu ya karbi wayar ya na fadin"To sai me in Umma na kira? Daman ta saba kirana."
Daga haka ya daga kiran lokaci d'aya da sallama bayan ya saka wayar a amsa kuwwa yadda Tahir zai ji.
Dagachan bangaran Umma ta amsa sallamarsa cikin fara'a kafin tace"Auta ka na lafiya ko? Jiya ba mu yi mgana ba yau ma haka."
Sadiq na shafa kanshi yace"Na yi uzurori ne jiya da yau Umma kuna lafiya?
Umma tace"Lafiya lau ya aiki? Ina Attahiru?
Sadiq na kallon Tahir da ya kafesa da ido yace"Ya na nan lafiya Umma ina Abba.?
Umma na mgana yaji Muryan Innani ta na fad'a sai cewa ta ke yi"Kaji min kisisina wajen salamatu ni fa na Dauko kafata nazo nace ta kiramin Magajin gida mu gaisa ammh ta tsaya ta na wani uban labari da shi, don Allah ni dai kin ga ba ni shi mu yi mgana."
Ta fad'a ta na kokarin warce wayar Hannun Umma daidai Lokacin da Umma ke fad'in"Auta ga Innani."
Kai ya dafe sanda Innani ta amshi wayar ta na fad'in"Ina kwana Magajin gida? Shikenan ka manta da ni ko mema na baka yi ba?
Cikin mirmishi yace"A ina zan neme ki? Kina da waya ne?
Innani tace"Wani bakin Munafukin ne yace ba ni da waya? Kaji mutane da son had'a fad'a in sulaimanu yaji ai ransa bazai yi masa dadi ba yaga ya siyamin waya ammh ana chan ana yamad'id'i da ni ba ni da waya"
Sadiq na kunshe Dariyarsa yace"To ai ke kikace an Dauke miki waya ki ka yi ta tsine tsine."
Innani ta Rafka dogon Salati kafin tace"Ni kuma? Yaushe na ce an sace min waya? Oh ni duniya da tsufana ammh har yanzu ba'a daina bi da kulli ba to ta Allah ba ta mutum ba, Ni dije dashen Allah ne na gagara wlh."
Sadiq ya kwashe da dariya kafin yace"Kedai ki ka sani. Sai ki fad'i mgana ki ce baki fad'a ba."
Innani ta sassauta murya ta na fadin"Allah dai ya rabamu da yan Uba kaji Magajin gida.'
Cikin Annushuwa ya amsa da Ameen zencen Innani ta