Showing 12001 words to 15000 words out of 98628 words
na mirmishi tace'Shine Addan mu"
Sadiq ta kallah kafin tace"Abubakar ga Addammu yaya ta ke a wajen Amma."
Sai a lokacin ya dago ya kara kallonta sai kuma ya ga tsantsan kamarsu da Amma cikin sanyin murya yace"Sannu da zuwa. Amma na lafiya?
Adda tace"Ta na lafiya bata zo ba ammh tace sakon fatan alherinta na tare da ku a koda yaushe in sha Allahu."
Da kai ya amsa mata Tahir kan kiris ya rage bai tashi ya zauna ba tunda yaji kafafunsa sun gaji da Tsayawa.
Adda ce ta fara yi ma Sadiq tambayoyin sana'ar da ya ke yi.
Su ka kalli juna shi da Tahir kafin yace"Ina bautar kasa ne da d'an alawun da suke bamu na ke buga bugata namu dai irin na talakawa."
Adda ta jinjina kai kafin tace"Allah ya tallafa Naji suna fad'in kai d'an shinkafi ne nan ta zamfara ko?
Sadiq ya gyada mata kai alamun hakane ya Dauka nan Adda zata tsaya ammh sai ta cigaba da fadin"To bayan iyayenka sun rasu a hannun wa ka ke a chan shinkafin?
Sadiq ya kalli Tahir karo na biyu shima ya kallesa.
Adda na ganin haka tace"Ina fatan ba damuwa ko? Kasan aure na bukatar haka an yi abun cikin gaggawa akwai bukatar ka gabatar ma da Ahalinka Hasiya."
Sadiq ya had'iye wani miyau kafin yace"Eh eh zan kaita in sha Allahu."
Adda tace"Baka amsa min tambayata ba? Wajen wa ye ka girma bayan ka rasa iyayen ka?
Kamar Subutan baki Sadiq yace"Hannun kakata. Eh hannun kakata na girma."
Adda ta murmusa kafin tace"Dakyau. allah ya baku zaman lafiya bayan an kwana biyu sai ka kaita taga Dangin ka. Allah ya baku zuru'a masu albarka nasihata itace ka rike Hasiya da Amana don girman Allah kada ka bari rayuwar Hasiya ta shafi zaman Lafiyan ku. Canfi ba gaskiya ba ne komai kaga ya faru daga Allah ne."
Sadiq ya dago ya na fad'in"Wannan bazai taba zama matsala ba in sha Allahu. Kowa yasan ba bu mai yi sai Allah.".
Adda taji dadin jin haka sai ta yi hamdala itama ta aminta da zabin jari yaron akwai hankali.
Ramatu ta kallah kafin tace"Ki je ki taho da Hasiya. Dare na yi"
Da Sauri ta mike zuwa Dakin Habiba na ciki da tashigo daga baya.
Ban jira tamin magana ba na mike Ramatu ta saka Habiba ta Dauki karamin akwatina ita kuma ta rike Babban.
Ina gaba suna bi na a baya muka fito falon ban kalli kowa ba gaban Adda na Durkusa.
Ta Dafa kaina ta na sakamin albarka kafin ta mike ta na fad'in su tashi su rakani.
Allah yasa ba su sallami mai adaidaitan da ya kawo su ba, har kofar gida suka rakani Adda da Inna Talattu suka sanya cikin adaidaita Sadiq na gefe Tahir kuma ya shiga gidan gaba.
Adda ta kallemu lokaci daya zuciyarta ta aminta wannan ne mijin Hasiya wad'anda ta aura daga Farko suna cikin Kaddaranta ne.
Cike da kwarin gwiwa tace"Hasiya ki yi hakuri da mijinki ki yi masa biyayya iya karfin ki, ki zauna da shi ki lallaba yanayin da ku ke ciki. Ina miki Fatan samun ingatttaciyar Rayuwar da mahaifiyarki ta ke miki Fata ina kuma rokon Allah ya barki a gidan auran ki sai mutuwa."
Kaina na kasa ban yi mgana ba ina ta wasa da hannuna acikin Hijabina.
Inna talatu ce ta jaddamin na yi addu'a kafin na shiga dakina.
Da kaina na amsa musu Ramatu da su Adda na ta daga mana hannu muka bar kofar gidan Adda Fati.
Tunda muka dauki hanya ba wanda ya yi mgana Tahir ne aka kira a waya ya yi mgana sai da ya gama sannan ya juya ya na kallon Sadiq da ke zaune gefe daya hankalinsa na wajen kallon Hanya nima ina gefe a rabuke.
Karamin tsaki yaja bai yi mgana ba shi ya rika yi ma mai adaidaitan kwatance har gidan.
Daman Ramatu ta sakamin key din gidan a hannuna muna sauka na mikama Sadiq yasa ka hannu ya karba"
SShaf mun manta da kaya sai da mai adaidaitan yace ga kaya sannan ya sauke mana.
Ban tsaya jiran komai ba na sunkunci babban akawatin Tahir shi ya yi gaba ya na bud'e gidan.
Sadiq ya kalleni cikin Duhun anguwan ammh hasken Fatata ta Haske masa fuskarsa.
Cikin sanyinsa ya mika hannu ya Dauki karamin akwatin Lokaci daya ya na fad'in"bani akwatin ta yi miki girma."
A hankali ya fad'a wanda ina da tabbacin Tahir bai jisa ba.
Ba musu na mika masa ya dauka daidai Lokacin da Tahir ya Bude get din gidan
Tahir na gaba ina bin bayansa shi kuma Assadiq na bayanmu.
Wannan karon ma Tahir ne ya Bud'e dakin sai da ya dawo daga baya ni na fara shiga da kafar dama tare da Bismillah.
Sannan Sadiq yabi yo bayana Tahir dai a waje ya tsaya bai shigo ba.
Kamar anguwan ba wuta dakin ya yi duhu sai da ya sauke kayan hannunshi sannan ya yi amfani da Fitilar wayarsa ya haska mana Dakin.
Saman kujeruna tun na auran Abubakar na zauna saboda sai naji duk na gaji.
Sadiq yasan Tahir na jiransa bai Tsaya kallon Dakin ba yace"Zan tafi sai zuwa gobe ko?
Ai sai na ware ido ina kallonsa ina kuma ya ke nufin zai tafi ya barni a wannan gidan ni kadai ko'ina Duhu ga shi bani da waya ballatana Fitilar hannu.
Bai ga razanan da na yi ba ne yasa ya jiya zai fice ya na fad'in"Gobe zan zo in sha Allahu."
Ai bai gama fita ba nayi saurin biyo bayansa bai ankara ba sai ji ya yi kirjina ya bangaji bayansa.
Lokaci d'aya na rirrike masa sagalen hannunsa ina fad'in"Don Allah kada ka tafi ka barni, Ina. Ina jin tsoro bazan iya kwana ni kad'ai ba."
Da dan hasken Fitilar wayarsa ya ke kallon Fuskata, ko'ina na jikinsa na wani amsawa da yadda Hasiya ta rikeshi gam ta na rawan jiki.
*Janafty*
*TMWB2K004*
*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*
https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj
Mai_Dambu Candy world's and more. Zaa iya samun Tuwon madara da iloka, gullisuwa, aya mai sugar, gyada mai gishiri, sannan muna bada sari, muna kuma karban oda da aikin biki ko suna. Muna karban aikin donut da cincin..08130269641
Da sauri ya matsa baya saboda kaucema rikon da Hasiya ta yi masa.
Cikin yanayinsa yace"Me zai same ki?
Ba komai kada ki damu"
Nayi kwalkwal da ido cikin bayyana tsoro na nace"Wlh ina jin tsoro."
Sai ya yi tsaye kawai ya na kallon Fuskata ta cikin duhun dakin
Tunanin mafita ya ke yi mganar gaskiya bazata iya kwana ita kad'ai ba shima da fari ya yi tunanin haka.
Kuma zaman shi tare da ita baya cikin Tsarinsa.
Gyaran murya ya yi kafin yace"Kin ga ne? Gobe zan zo yau din ma saboda ina da wani uzuri ne yasa bazan kwana anan ba."
Kai tsaye nace"To ka tafi da ni in da zaka kwana don Allah."
Sadiq ya ware ido ya na kallon Hasiya ya na shirin mgana yaji muryan Tahir daga waje na fad'in"Kasan fa mai adaidaita na jiran mu a waje. Ga shi dare ya yi."
Jin haka yasa batare da ya yi magana ya kama hanya zai fice ina ganin haka na yi zaraf na bi bayanshi.
Ya na fita sai yaji ni a bayansa Tahir ko kallon mu ya yi cikin mamaki kafin ya samu zarafin mgana Sadiq ya juya ya na kallona.
Cikin sanyin murya yace"Ba tafiya zan yi ba"
Jikina na rawa nace"Don Allah kada ku tafi barni a gidan nan ni kada'i. Bazan iya zama ba ina jin tsoro."
Na fad'a ina kara kallon wagegen gidan na saba da kwana a daki falle daya tare da Amma da Habiba.
Sannan na saba rayuwa cikin mutane bazan iya kwana a gidan ni kad'ai ba.
Tahir da Sadiq suka kalli juna kafin Sadiq ya sauke numfashi cikin sigan lallashi yace"Kinga Hasiya koma ciki magana zan yi da Tahir."
Sai naji kamar ban yarda da shi ba.
Kada na shiga ciki kuma su tafi su barni na shiga uku.
Kif kif ta idanuwana na rika yi na kasa shiga ciki kamar yadda yace.
Ganin haka yasa Tahir yaja Hannunsa suka koma daga bakin get din ina hangensu.
Sai na samu salama ganin ba tafiyar za su yi ba.
Ammh na kasa komawa cikin dakin tunda akwai Duhu ko Tafin hannunka baka iya gani.
Suna dagachan nesa da ya ke kuma ban kasa kunnuwana ba shiyasa ban jiyo mganganun na su ba.
Kuma dai sun yi kasa da murya kamar wasu munafukai.
Cikin rage sautin murya Tahir yace"Me ye wannan zabiyar matar ta ka ta ke nufi? Bazata iya kwana ita kada'i ba to so ta ke ka taya ta kwanan kenan?
Sadiq ya yi shuru ya na wani nazari akwai hakkin kula da komai na Hasiya a kanshi yanzu aurensa sunan shi aure ko da wani Tunani a ka yi sa.
In ya barta a cikin gidan nan wani abu ya sameta me zai ce ma mahaifiyarta da yan'uwanta?
Har a wajen Ubangiji ma ba shi da abunda zai kare kansa hakkinta zai kamashi.
Shiyasa ya kalli Tahir kafin yace"Tahir ba ni da mafita. kaga dai yanayin anguwan nan sannan ita kadai ce kuma macece akwai hatsari mu tafi mu barta ita kad'ai"
Tahir ya dage hanci kafin yace"I see. to yanzu me ka ke so a yi?
Sadiq yace"Zan tsaya na kwana kai ka tafi sai mu had'u gobe in Allah ya kaimu."
Tahir ya kalli Sadiq a cikin Duhu baya ganinsa sosai ammh ya na ganin Duhun Fuskarsa.
Cikin mamaki yace"Kace me? nan zaka kwana tare da wannan yarinyar?
Tahir ya fad'a ya na nuno Hasiya.
Da Dauri Sadiq ya rike hannunsa ya na fad'in"Ka yi a hankali mana. So ka ke taji abunda mu ke fad'a?
Ya fad'a ya na juyawa ya na kallona sai dai bai fahimci ko naji ko ban ji ba tunda a lokacin Tahir ya daga Sautinsa.
Ni kuma ban ji su ba, na ga dai kamar an nuna ni tunda akwai hasken farin wata da ya raba tsakiya da kwata shiyasa sai duhu ya mamaye hasken farin watan.
Tahir ya rausayar da Murya kafin yace"ammh kasan kwana a tare da yarinyar nan baka saka shi cikin Tsari ba ko?
Sadiq yace"Na sani ba shi cikin Tsarin mu. Ya zama dole ne shiyasa ammh ai daga yau ne zan san abunda zan fad'a mata da zai saka na yi nesa da kwana tare da ita."
Tahir ya yi shuru kamar bazai yi mgana ba. Ganin haka yasa Sadiq ya dafa kafad'ansa ya na fad'in"Da gaske na ke yi maka bazan bari a samu wata matsala ba."
Tahir ya sauke ajiyar zuciya kafin yace"Shikenan bari na tafi."
Sadiq yace"Ok sai da safe kenan?
Tahir ya kallesa kafin yace"Abubakar."
Cikin mamaki Sadiq yace"Na'am Attahir."
Tahir ya had'a hannayensa ya na fad'in"ban da Kusanta, Ban da kusanta Abubakar."
Sadiq ya yi saurin cewa"Kusanta?
Cikin Sigar tambaya.
Tahir yace"Eh kusanta nace kada ta ribace ka tab'ata kasan an ce in namiji da mace su ka keb'e su kadai to shed'an ne a tsakanin su."
Sadiq sai a lokacin ya fahimci in da Tahir ya dosa baki ya hangame kafin ya rike Haba yace"Haba mana Tahir. Me yasa zaka yi irin wannan Tunanin fisabillahi?
Tahir yace"Dole na yi tunda komai naka ya na zuwa ne batare da sanar da ni ba gwara na ja maka kunni yin haka tamkar ka fallasa sirrin da ka ke son Rufewa ne."
Sadiq yace"Na sani ni har ga Allah saboda taimako na auri Hasiya ba domin wani abu daga jikinta ya na Burgeni ko ni sha'awa ba.
Ba bu wannan tunanin kwata kwata a raina."
Tahir yace"Uhm!
Irin ban yarda ba jin haka yasa Sadiq yace"Ko zaka zo mu kwana tare ne sai ka cire shakku a kaina?
Tahir ya juya ya na fad'in"A dakin mata da mijin ne zan kwana?
Sadiq ya yi dariya har sai da tayi sauti.
Shi ya raka Tahir har kofar gida ya na daga jikin Gate din ya shiga adaidaitan suka wuce.
Sannan ya dawo cikin gida da kansa ya sakama get d'in sakata.
Sannan ya dawo in da na ke tsaye duk sauro sun cijemin kafa ammh tsoro ya hanani komawa daki.
Gaba ya shiga ya na kunna Fililar wayarsa lokaci d'aya ya na fadin"Mu shiga ciki"
Jin haka yasa na bi bayanshi har zuwa cikin Daki muna shiga ya juya ya Rufe kofar da sakatan sama da kasa.
Mun tsaya dukkanmu a tsakiyar falon kowa na saka wani acikin ransa.
Ni sai alokacin nake nazarin dakin shi kuma tunanin me ye abu na gaba da zai yi ya ke yi? Bai kuma sani ba gashi ya manta bai tambayi Tahir ba.
Kallona ya yi kafin yace"Ki na jin yunwa?
Kai tsaye na girgiza masa kai alamun a'a ina ji ya sauke numfashi kafin yace"ke ki kwana aciki ni zan kwanta a falo."
Ban yi mgana ba ya duka ya dauki akwatina babba ya shiga ciki ni kuma sai na dauki karamar na bi bayansa.
Shima cikin an gyareshi da Gado da wardrope duk da dai karami ne sai madubi kawai aciki.
Gefe ya saukemin akwatin batare da ya kalleni ba ya juya ya na fad'in"Sai da safe."
Gani nayi zai fita ya barni cikin Dubu sai jin takuna ya yi a bayansa da Sauri ya juyo ya na kallona.
Kai na kasa nace"Duhu ba filita a nan."
Wayar hannunsa ya kallah karamar wayarsa ne kuma layinsa ne na gida babban wayar tasa ba ya wani abu da ita ya barota a gida.
Wayar ma ba chaji sai buga battery low take yi don ma yar alkwari ce sai ta mutu sau nawa da ya kunna zata kawo sai kuma ta jima bata mutu ba.
Gudun matsala yasa ya kashe Sim din a cikin wayar sannan ya mikamin ya na fad'in"Ki yi amfani da ita."
Ba musu na saka hannu na karb'a ina Fad'in"Nagode.'
Ficewa ya yi zuwa falo ni kuma ya bar ni nan tsaye ina tunanin mafita.
Daman ban tsammaci zamu kwana waje d'aya ba tunda ga yadda auran namu ya kasance.
Dole na nemi mafita hijabin jikina na cire marata ta daure shiyasa na tura kofar da na gani a cikin bedroom din.
Ina tunanin nan ne bayi ina shiga ko naga Tioler ne mai kyau.
Sai dai ba ruwa kad'an ne bai wuce na alwala ba.
Sai da na yi tsarki sannan na fito Allah yasa na yi sallolina a gidan Adda Fati da na shiga uku ina zan samu ruwa a daren nan?
Ko kakkabe gadon ban yi ba, na hau daga gefe na kwanta ina maida numfashi bayan na rufi da Hijabina
Saboda halin da na ke ciki ban yi ma Tunanin sauya kayan jikina ba.
Fililar wayar a kunne na barta ni wayar ma ban da riketa da na yi a hannuna ko latsata ban yi ba Tunda ba tawa ba ce.
Ko add'an barci ban yi ba Gajiya ce ta da rashin barcin da ban samu ba kwana biyu suka taru suka min Rubdugun da yasa wani barci mai nauyi ya kwasheni.
Ban farka ba sai da gari ya waye tangararan.
Bansan meyasa shi bai tasheni ba ammh ko da na farka haske ya cika Dakin wayarsa kuma ta mutu cikin dare ina chan ina barci ban sani ba.
Na kwanta ko motsawa ban yi ba yasa wuyana ya kage ina kallon gefe na mike na shiga makewayin da sauran ruwan da na gani abotiki na da ya zama kankara saboda sanyi na yi amfani da shi.
Ruwan ma bansan dad'ewarsa ba saboda ina tunanin tun na wanda su Adda Fati suka yi amfani da shi ne da suka zo danki.
Hakanan na fito bansan ina ne gabas ba daidaitawa kawai nayi lokaci d'aya na saka Hijabi bayan na shimfid'a d'an kwali na tada sallah ammh a karkace tunda wuyana ya kage.
Na jima bayan na gama sallah na kasa fita falo sai na fara tunanin ko ya tafi ne? Tunda ban ji ko motsinsa afalon nan ba.
Tashi na yi da Hijabin jiya da kayan jiya na leka falon ta labule sai na ganshi kwance saman kujera ya na barci ya hard'e duka hannayensa saman kirjinsa.
Fitowa na yi a sannu sannu gabansa na tsaya ina kallonsa barcinsa cikin natsuwa numfashinsa na sauka Daya bayan Daya.
Fuskarsa na ke kallo kamar ya na mirmishi bansan ma yaushe ya bude ido ba sai gani nayi kawai ya mike zaune Lokaci d'aya ya na fad'in"Da damuwa ne?
Cikin muryan barci, Da sauri na matsa baya naji kunya sai dai na juya kaina azaban wuyana ya isheni bansan Lokacin da na dafe wuya na ina fad'in"Wash."
Da Sauri ya mike ya na fad'in"Lafiya? Me ya faru?
Ina rike da wuya na nace"Na kwanta kan wuya na ne da na tashi kuma sai ya ke min ciwo."
Kallona ya yi kafin yace"Oh sannu ki bar tabawa zai bari"
Da toh na amsa masa kafin na rankwafa ina gaishesa.
Ya amsa cikin dan kamewa hasken garin ya leka ta window ya gani kafin ya juyo ya na fadin"Rana ta yi karfe nawa?
Na jujjuya naga babu agogon falon ganin haka yasa yace"Waya ta."
Ina jin haka na gane da Sauri nace"Ta mutu inaga ba chaji ne."
Kafin ya sake mgana na juya da sauri ammh sai da na rike wuyana saboda zafi
Ciki na koma na Dauko masa wayarsa na basa shi kuma ya karb'a ya kunnata sai ga shi ta kawo.
Ya na kallon wayar yace"Karfe 8 saura. Me ki ke bukata ina so na tafi ne."
Sai na rasa ta cewa ni me zan ce ina Bukata?
Bansan me da me suka kawo ba tunda tare muka zo ko kitchen d'in ban leka ba.
Ganin ina tsaye yasa tunanin ya Duba kitchen saboda kada ya tafi ya barni da yunwa wani abu ya faru ya shiga uku.
Kitchen din ya shige batare da ya yi min mgana ba nima ban bi bayansa ba.
Ina nan tsaye ya fito ya na fad'in"gas din ba Refilling zan je da shi a yi miki Relling ina dawowa yanzu."
Sai da ya yi mgana sannan na juya ina kallonsa har ya Dauko gas din.
A dawo lafiya na yi masa shi kuma ya kimkima ya fita da yake ma karami ne 5kg ne.
Bayan fitan sa na jima tsaye ina ta jujjuya wuyana sai daga baya na koma ciki na dauki akwatina na sauya musu muhalli na kakkabe gadon duk da bai yi datti ba na gyara dakin na Share tare da falo.
Sai alokacin na shiga kitchen din naga Har da kayan abinci rabin buhun shinkafa da taliya da macaroni duka kwali. Sai magyada da manja,garin tuwo da shinkafar tuwo.
Kayan maggi da kayan dage dage irin su kuka da kubewa sai manshanu da Adda Ta zo min da shi da zata zo.
Sai sabbin kololin da Adda Rukkaya ta siyamin sun