Showing 9001 words to 12000 words out of 98628 words
nan da wata daya.
Sai Sadiq yaji dadin haka domin a na shi Tsarin ba Tsarin ya zauna a nan gidan Tare da Hasiya.
Karya suka yi ma Hambali da cewa wani dan'uwan Tahir ne ya yi aure shine suke duba masa gida shi kuma bai Damu ba ya na kan sana'ar shi ne Daman shi ya samo musu gida Saboda shi suka sani shi kuma suka bama kudin Hayan gida na Shekara cur.
Sai yamma suka dawo shiyasa Sadiq bai samu damar kiran Adda Fati ba sai da Daddare yace mata ya samu wani waje duk da kudinsa bai kai ba an yi masa ragi.
Sun rabu akan gobe da Safe tunda Tahir CDS zashi kuma sai ya fara biyawa Fada sai Sadiq ya rokesa kan ya raka Adda Fati ta ga gidan ya na masifa ya na komai ya amince shiyasa Sadiq ya fara tafiya ya barshi Tunda shi nan kafin akai kwangila za shi.
Lambar wayar Tahir ya turama Adda Fati shima ya bata na shi ammh Tahir bai kirata ba sai itace ta kirashi duk da taso suje ko ita da Rukayya ko Ramatu sai taga tafiyar ta su ta Safe ce sai ta yanke shawaran in taje taga gidan daga baya sai ta kai su.
Tunda ita ta na Sabongari ne a pizzet suka had'u da Sadiq ya saka complete kayan Bautar kasar sa sama sama suka gaisa suka samu abun hawa sai Hanwa.
Suna zuwa daman already makullin gidan na hannun Tahir shi ya Bude mata sannan ya bata key d'in Dakin lokaci d'aya ya na fad'a mata Shi zai tafi ne kada ya makara ganin saurin da ya ke yi yasa ta yi masa uzuri ammh ba tun yau ba ta Lura da Tahir din ya na da Basar da Mutane.
Alhamdulillah ta duba daki babu abunda babu ga shi sabon waje gidan ma ya burgeta sosai ganin ba su da yawa ta kuma san in dai zama ne na gidan Haya Hasiya tasan kalubalensa zata kiyaye in sha Allahu.
Ta jima ta na duba Dakunan sai da ta kirga kofa saboda Labule tun kuma ta na gidan ta kira Adda Rukkaya ta fad'ama ita kuma tace sai gobe zata zo su yi mgana.
Cikin Farinciki Adda Fati ta dawo duk da bata gayamin inda taje ba ammh ta na cemin zata fita da Sassafen nan jikina ya ba ni wani abu.
sai ko ga shi ta na waye waye ta na ba da Labarin Tsarin wajen da zan zauna tabbacin chan taje da Safe kenan.
Ina jinsu da Rana suna mgana da Adda sai kuma aka bama Amma suka cigaba da mganarsu.
Tashi na yi na shige ciki domin maganar sam bata burgeni meye amfanin bad'i ba rai? Suna rawan jikin tarewar da ina da tabbacin bazai Daure ba sai wani abu ya Biyo baya.
Ai ni ina ganin abu ganin idona wajen su Adda Fati bayan hidimar kayan Dakina sai kuma suka Turomin Ramatu da magungunar gyara akan sai na sha sai suka bani dariya.
Auren Abubakar na farko ne na yi wannan rawan jiki ammh ko na Salisu Fargaba bata barni na saki jiki na yi wannan Shaye shayen ba.
Wannan ma na Tubure nace bazan yi ba da naga sun fara matsamin kawai sai na fashe musu da kuka ina fad'in"Nace ba na so ko? Haba ku kyaleni mana duk abunda ku ke yi ina sane ban yi muku mgana ba meyasa ni ku ke so ku tursasani aikata abunda ban yi ra'ayi ba. Wlh kuka matsamin zan yi tafiyata in da har Abada bazaku kara ganina ba."
Jin kalamaina yasa suka shafamin Lafiya suka cigaba da Shirinsu duk azatona Amma zata zo tariyata saboda nayi kewarta sosai Fushin Abunda tayi min yasa ko a waya ban yarda na yi mgana da ita ba.
Ashe bansani ba tace bata zo ba Adda ce zata zo kad'ai.
Ina da labulai na tun na gidan Abubakar na kofofi da yawa Shiyasa a auran Salisu ban siya ba wannan karon ma wankesu a sake yi aka goge sai dai sun karamin kayan kitchen da abubuwan da baza'a rasa ba.
Adda Rukayya kuma ta yi mana Atamfa mu h'udu da zamu ci yinin Tarewa da shi, Ramatu kuma ta yi min kayan maggi da sauran kayan Dake dake.
Sannan mijinta Nura ya aikomin da Dubu talatin ban rikesu a hannuna ba na mikama su Adda da su suka yi amfani suka siyamin less da material sai Hijabai da takalmi sai dan kunne, tunda kayan nawa duk sun ji jiki.
Salisu bai yi min kaya ba daman da Niyar in muka yi aure zamu je kano da ni da shi na zabi kayan da na ke so.
Bansan ko shi Sadiq din ne ya saka musu rana ba naji suna fad'in Ranar jumma'a za su yi bikin Tariyar nawa ni har mamaki na ke yi su har wani Tunanin yin biki suke a auran da ba su da kyakyawan tabbaci a kan shi.
Inna Talatu ita ta zame mana uwa a lokacin Tunda ba Amma Adda kuma bata zo ba tukunna.
Adda Fati ta kira Baaba Ta lagos suka yi mgana sai tace Baba tanko ya yi mata mganar an d'auramin aure.
Sai kame kame ta ke yi ta na fad'in ta jima bata zo garin ba ne ammh in ta zo zata zo su gaisa da Amma, nan ne ma Adda Fati ke sanar da ita komawar Amma wajen Adda Sai kunya duk ta kama Baaba ta kasa mgana.
to gwara ita ta na yi mana sako in muka kirata mukace ga wani abu ya taso.
Ba wai mganar sako ba dukkansu suna da karfin da bayan rasuwar Baba zasu duba bayanmu ammh ina ba su yi ba wasu ma cikin su sukan manta damu gabadaya.
Irin su Baba Jibril na kaduna shi kila in na ganshi sai naga kamarsa ne da Dangin Babammu kila na ganeshi ammh daga matansa har ya'yansa ban ko san ko d'aya bani da masaniya ko su Adda sun san su barin ma Adda Fati da tafi mu bin su da son zumumci da su.
Goggon kona fa ta na kusa ita da Baba Tanko ammh har ina manta rabon da na gansu da idanuwana ballatana iyalansa har gwara Baba Saminu ya na zuwa duba Amma duk da ba na duban da ya kamata ba ne na zuwa da ganin ya muka kare ne kuma ya gama mganganunsa ya shuru takalminsa ya kara gaba ko sisi bazai iya taimaka mana da shi ba.
Adda Fati da kanta taje gidan Baba Tanko ta kai masa minti bikin Tariyar da ita da Adda Rukayya da Ramatu suka had'a hannu za su yi taron bikin.
Sannan taje har gidan Goggon kona itama ta kaimata ita sai ta fara fad'an Laifin Amma ce itace ta yanke zumumci da su sai anan ma ne Adda ke Sanar da ita Amma bata garin nan ta koma Wajen Adda da zama gabadaya.
Ni in da duk sun yi shawara da ni baza su yi min wannan gayyar ba. gayyar da bata da wani amfani illah ma daga baya ta zame min Tozarci.
Har yan gidanmu da muka taso Adda Fati ta aika Habiba ta kai musu suna ta murna daman sun rasa ina zasu samu cikon Labarin.
Habiba tace ta na zuwa suka Rufeta da Tambayoyin ina angon? Ya na nan lafiya? Sun gama Ammana aure na ba Alheri ba ne ni kaina tun ina sauraran jin ta ina kuma wannan karon kaddaran zata kwankwansamin ammh har lokacin ya gabato ban ji wata mgana sabanin shirin da suke yi ba.
Ranar laraba suka je suka yi min jere sai dare suka dawo Ramatu ce ta isheni da Labarin kyan gidan kai Tsaye na kalleta kafin nace"Me kyan gidan zai kare min acikin rayuwata Ramatu? Haka gidan Abubukar ma kuka ce ya na da kyau na Salisu ma ammh kuma karshen mai ya faru?
Sai ta kasa mgana ni kuma har cikin zuciyata na kalleta nace"To shima haka wannan zai kare a banza. Shiyasa ki ka ga ban tusa kaina ba nayi baya ina ta kallon ku Uhm.! Ku nafi Tsausayi saboda halin da zaku shiga in kuka ga kun kaini cike da Fata na sake dawo muku a karo na uku."
Sai Ramatu ta kasa magana kawai sai ta tsaya ta na kallona cikin mutuwar jiki.
Tayi kokarin kalaman bakinta su yi tasiri sai na dakatar da ita cikin mirnishi nace"Ramatu wannan karon kalaman ki baza su iya tasiri a gareni ba, me jiya ya yi ballatana yau?
Ba bu abunda ya sauya ko da yaushe abu d'aya ya ke faruwa.'
Tunda na fad'amata haka sai bakinta ya mutu ammh duk da haka sai da tamin mganar Kitso da kunshi Tsaraban Harara ta samu.
Sai dai ban tsira ba domin washegari Alhamis Adda ta Dira ganinta ita kadai yasa sai da na tambayeta ina Amma sai ta harareni kafin tace"Daman kin damu da ita ne tunda ta tafi ko a waya baki taba gaisheta ba?
Sai na kasa magana sanin ban kyauta ba, Adda ta gyad'a kai kafin tace"Aisha ba saboda komai ta aikata haka ba sai Saboda Rayuwarki ta inganta Hasiya. Kila yanzu bazaki gane hakan ba sai nan gaba ammh ina miki Fatan ki gane da wuri kafin Lokaci ya kure miki."
Duk sai ta kashemin jiki zuwanta yasa ban kara gaddama ba saboda ta na da Zafi tace sai ta min dukan Tsiya ita ba irin Jari ba ne ballatana ta rika lallabani.
Dole kanwar naki na Tsife kaina Ramatu ta rakani aka yi min wankin kai Kunshi kuma wata makociyar Adda Fari tazo ta min tamin na salatif na kwana da shi wayewar garin juma'a kuma ta yi min baki a hannuna na zane.
Adda tazo min da Gumba wanda za'a sha da madara ban yi musu ba na karba da ta damamin na sha.
Habibu mijin Adda ya yi kokari shi ya bada abincin Sha'anin wanda suka siya kuma sai Adda tace su bar min na gara tunda bazasu kaini haka ba.
Na dauka na gama tara mutane Lokacin aurena ashe na manta cewa wasu ko don tafiya da abunda ya faru suna zuwa.
Duk yadda na so kada na nuna Ina Farinciki da wannan auren su Adda Fati ba su barni ba sai da suka saka na yi wanka na shirya Ramatu ta min kwalliya.
Abun mamaki duka matan Baba Tanko da na Baba Saminu sun zo su gambo da wuri suka iso saboda kada a yi wani sin din basa wajen.
Goggon kona sai da yammah ta zo ammh wasu cikin ya'yanta sun zo da Rana.
Bata ji kunyar yima Adda Mganar Amma ta raba zumunci da su ba ita kuma Adda ta same su ta yi musu wankin babban bargo ta rufe da fad'in"Aisha ta bi ku gajiya ta yi ta kyaleku. kuma har a wajen Allah ba ta da wani laifi ku ne kuka ki ta ku ka k'i ya'yanta duk da su d'in Dolen ku ne. Yau an wayi gari Zumunci ya lalace d'a sai wanda na Haifa ya'yan dan'uwa ba D'a na ba ne, Kwata kwata baku kula da su ba a banzace ku ka bar su suna wahala saboda canfin ku na karya da ba ku da tabbaci."
Kasa mgana suka yi tunda ba su da gaskiya barin ma Goggon kona daman ance gaskiya ai sunanta gaskiya kuma daga kinta sai bata.
Kunya suka ji? Ko kuwa daman suna son ganin abunda zai faru ne yasa suka tsaya har yamma.
Na saka kaya kala uku a ranar ina cirewa gabda mangariba Adda Rukayya ta saka na sake wanka na saka less din da Farin Hijabi naji ana ta mganar ya kamata azo a tafi dani kada dare ya yi.
Nayi ta kallon al'amarin ina mamakin ko motoci goma aka kawo sai sun cika wasu ba su samu waje ba.
Saboda duka matan gidanmu da muka taso sun zo har da makota kuma suma sun ce da su za'a je kai Amarya.
Har sai da nayi sallar mangariba ban ji wata mgana ba ina kan sallaya ina nirmishi ni kad'ai mirmishin da yafi kuka ciwo a cikin raina ina Tunanin kamar na Salisu za'ayi kila ma kafin na kai ga tarewan komai zai iya faruwa.
Wayar Sadiq Adda Fati ta yi ta kira a kashe hankalinsu gabadaya sai da ya tashi sun rasa mafita Kuma bai kamata su je su kaini batare da susan wani Hali Shi mijin nawa ya ke ciki ba.
Mutane nata zaman jira shuru ga Duhu ya shiga Adda Rukayyace ta fita ta na ce musu kowa ya tafi gida Amarya angonta yace zai zo ya Dauketa da kansa sai gwiwa duk ya yi sanyi.
Su gambo dole suka tafi ba'a samu an karisa ganin abunda zai wakana ba matan gidanmu ma ba'a son rai suka tafi ba Ammh sunce daga baya zasu kaimin ziyara.
Zuwa karfe 8 na dare kowa ya watse daga su Adda sai Inna Talatu sai Ramatu har Goggon kona ta kwashi Tsufanta ta kara gaba.
Ni ina ciki ban fito su kuma suna falo suna fama da tararradi.
Ramatu ta kalli Adda Fati da ta ke ta faman kiran wayar Sadiq a kashe cikin mutuwar jiki tace"Har yanzu baki same shi ba?
Adda Fati tace"Wayarsa a kashe."
Adda Ta numfasa kafin tace"Ina sha Allahu lafiya lau. Ku yi tunani ba ku da ko Lambar abokinsa ne?
Sai a Lokacin Adda Fati ta tuna da lambar Tahir da Sauri ta mike ta na fad'in"Na tuna ina da lambar wannan abokin na shi."
Da sauri kowa ya washe baki Inna Talatu tace"Maza ki kirashi."
Da Sauri ko Adda fati ta kira lambar Tahir ta shiga har ta kusa katsewa sannan ya daga kiran.
******
Lokacin Da kiran Adda Fati ya shigo wayae Tahir ya na kishingid'e ya na chart ne Sadiq na kwance gefensa barci ya kwashe shi yau yini ya yi a wajen aiki ya dawo a gajiye da yasa barci ya kwashe da wuri suna Hira ne ma shi da Tahir.
Har ga Allah sun ma sha'afa da mganar Tariyan Hasiya Basu san kan al'amarin ba sun zata ma basai ma an kira su ba Shiyasa ba su yi tunanin wani abu ba.
Tahir ba shi da lambar Adda domin ba shi da alaqa da ita ballatana ya adanata shiyasa har ya daga wayarsa suka gaisa bai gane wacce ke mgana ba.
Cikin Muryansa yace"Bangane wa ke magana ba?
Adda Fati tace"Fati ce yayar Hasiya."
Har ga Allah kwana biyu nan Tahir ya fara dawowa cikin Hayyacinsa da Halin Tsaka mai wuyar da Sadiq ya saka su ya fara mantawa da wata Hasiya tunda Sadiq baya masa mganarta shima ba ya yi masa.
Kai tsaye yace"Na'am bangane ba wata Hasiya?
Ya fad'a kai tsaye sai Adda ta kasa mgana su kuma su Ramatu sun Tsorata sun zata wani abu ne ya faru suka fara tambayanta ko lafiya Hankali ta she.
Ba su kadai ba ni kaina ina makale a jikin kofar dakin gabana na fad'uwa.
Bana son wani abu ya samu Assadiq in hakan ta faru ta sanadina bazan tab'a yafe ma kaina ba.
Adda Fati ta hadiye miyau kafin tace"Sadiq na lafiya kuwa? Na yi kiran wayarsa a kashe ko ya manta yau ne nace masa Hasiya zata tare."
Sai da ta fad'i haka ya tuna da gagurumin tarnakin Bala'in da Sadiq ya jefa rayuwarsu a ciki.
Cikin mamaki yace"Ta na chan gidan ne yanzu?
Adda Fati tace"A'a ina dai tambayan Sadiq ya na lafiya?
Tahir yace"lafiyansa kalau ya kwanta ne bari na yi masa mgana."
Daga haka ya yanke kiran Lokaci daya ya na shurun Sadiq da kafa.
Fad'i ya ke yi"Mallam ai sai ka tashi Shigen Tausayi ya sa ka jefamu a masifa ba ka ga ta barci ba Sadiq."
Sadiq ya motsa lokaci daya ya Bude idanuwansa ya na kallon Tahir kafin yace"A gajiye na ke Tahir ka bar ni na Huta don Allah.".
Tahir ya kwashe da dariya kafin yace"Ina kaga ta wani Hutu? Amaryan ka Hasiya na chan na jiran ka."
Kamar bai jisa ba sai kuma ya mike Zumbur ya na fad'in"Me ka ce?
Tahir yace"Yanzu wannan yayar nata ta min waya suna tambayan ka ko lafiya ka ke kuma da sakon Amarya na chan na jiranka"
Sadiq ya dafe kansa kafin yace"Na manta daman yau jumma'a ne?.
Tahir baka tuna min ba."
Tahir ya balla masa Harara kafin yace"Ni kuma a suwa da zan tuna maka? Kai da abun ya shafa ka manta sai ni karan kad'a miya."
Mikewa zaune Sadiq ya yi cikin kasala ya na fad'in"Duk dai ba wannan ba yanzu ta na ina?
Tahir yace"Oho ina na sani sai dai ka kirata kaji."
Sai alokacin ya duba karamar wayarsa yaga ta mutu daman ya kwana Biyu bai sakata a chaji ba.
Wayar Tahir ya amsa ya kira Adda Fati daidai Lokacin da zukata suka samu natsuwa jin Babu abunda ya faru da Sadiq.
Ta zata ma Tahir ne sai taji muryan Sadiq tambayanta ya yi sun kai Hasiyan chan gidan ne? Adda Fati tace a'a ai ba su yi da shi zasu kaita ba.
Kansa ya dafe kafin yace"Ku yi hakuri na Shafa'a ne sannan wayata ta mutu ba chaji. ina ne in da ku ke sai mu zo mu dauketa?
Nan Adda ta rarrataba masa kwatance tace in ba su gane ba su kirata.
Suna yin sallama ta kalli su Ramatu ta na fadin"Alhamdulillah ba abunda ya same shi yace mu yi hakuri ya sha'afa ne wayarsa ce ta mace ba chaji ammh yace gasu nan zuwa."
Gabadaya suka sauke ajiyar zuciya ni kaina da na ke labe sai da na sauke Numfaashi ina jin gudun zuciyata na Daidaita.
Sad'af Sad'af na koma daki na zauna ina maida numfashi.
Sadiq ya sha fama da Tahir domin da Farko yace shi ba mai sake fitar da shi da Daddaran nan ya gaji.
Sai da Sadiq ya yi ta rokonsa sannan ya tashi ya Shirya suka Rufe daki suka tafi.
Ba yan gari ba ne kuma basa yawo shiyasa suka sha wahala kafin su gane gidan Adda Fati sai da Mijinta ya fita bakin hanya ya tarosu.
Saboda Sauri kananun kaya ne dukkansu a jikinsu gwarama Sadiq ya Dora Jaket a saman riga da wandon jikinsa.
Har Falon Adda Fati Habibu ya yi nusu Jagora in da su Adda ke zaune suna jiransu.
Dukawa suka yi suna gaishesu Sadiq yafi nuna jin kunya Tahir ko aransa cewa ya yi kunyar me tunda ba surukansa ba ne.
Adda ta jima ta na nazarinsu kafin ta yi mirmishi tace"Duk da bansan surukin namu ba ina da tabbacin mai kunyar nan ne"
Adda Fati