Showing 6001 words to 9000 words out of 98628 words
cigaba da yi masa da ta tambayi Tahir yace ga shi a gabansa.
Ya mika ma Tahir suka cigaba da shan Hira suna shan Dariyan Innani da wayar ta dawo hannun Sadiq ne Innani tace"ka ganni yanzu wajen mamanka na ke yi ni Shashena ba kowa sulsana ta fara zuwa boko ba mai d'ebemin kewa."
Sadiq yace"Ki zauna da Umman sai ku rika yin hira."
Innnani ta tabe baki kamar ya na ganinta batace komai ba daga gani akwai mgana a bakinta.
Sanin haka yasa Sadiq yace"Yaushe ki ka dawo? Na dauka chan zaki mutu sai dai muje jana'iza."
Innani ta saki baki kafin tace"Kaji wani mugun baki kuma? Ni da mutuwa ai sai na aurar da ya'yan ku kai da Sulsana."
Sadiq ya kyakyace da dariya kafin yace"Kina da son duniya Innani ina Laifin ki ga auran namu na ya'yan mu kuma kina kabari za'ayi."
Innani ta yi gum Magajin gida ne ba Halin ta yi masa masifa.
Jin yadda ta yi shuru yasa yasan gabda ta ke da fashewa da kuka, yasa cikin barkwanci yace"Ya kika baro su Mallam zakarin?
Jin haka yasa Innani ta gyara zama ta na bashi labaran abunda ya faru achan ta karishe da fad'in"Kai dai bari magajin gida kamar kar in dawo. Ammh ya na iya sulaimanu da matansa sai kira suke wai yaushe zan dawo? Saboda ma a nuna min iyakata aikamin akayi da mota akace in ni bazan dawo ba na turo su sulsana zasu fara zuwa makaranta abunan ya yi min ciwo matuka ni fa saboda Salamatu naje kamar ya' na Dauketa ita kuma kaga a uwa ta Daukeni ko ba Haka ba.?
Sadiq yace"Hakane Innani kin Sada zumunci Allah ya baki lada"
Innani ta washe baki ta na fad'in"Ameen Magajin gida, ai da na dawo sun sha masifa nace ina Dalili kun dameni na dawo sai kace Nono zan ba ma shi Sulaimanu din mutum ya girma da iyalansa ammh baza'a bar ran Tsohu ya huta ba, chan wlh ana kula da ni naci na sha mai kyau mu yi ni muna Hira da Zakari gwanin ban sha'awa nan ko sai zama a katon gida kamar mayya Sulsanar da ke tayani zama an yi min nunafunci itama Sulaimanu yace Boko zata yi ai shikenan maji dai ma gani wai an Tura uwar amarya biko."
Sadiq duk halin da ya ke ciki sai da ya Biye ma Innani ya na ta cin dariya daga karshe suka fara Diraman sai ta zo zariya daman bata taba zuwa ba Dakyar ya lallasheta akan zai zo ya tafi da ita sannan ta Hakura.
Sun fi awa biyu suna Hira sai da kudin wayar Umma suka kare shi kuma yaki kira daman ya gaji Innani ce fa Lamarinta sai Allah.
Suna gama wayar alwala suka yi zuwa masallaci ba su dawo ba sai da suka yi isha'i.
Bayan sun dawo ba su nemi abinci ba Ruwan zafi Tahir ya dafa musu suka sha Tea saboda ya warware musu ciki.
Sadiq dai ya shiga uku da Tahir sai ya yi kamar yana goyon bayansa sai kuma ya Turje har ya gaji da basa mgana ya kyalesa duk da ya na da kyakyawan yakinin Tahir bazai iya Tona masa wannan Sirrin ba.
Washegari kuma da wuri kowannen su ya isa inda ya ke Hidimar kasarsa Sai dai ba Sadiq kad'ai ba hatta Tahir kowa ya fahimci wani abu na Damunsa ya rage kazar kazar.
Shi ko Sadiq duk da daman ba shi da Hayaniya sosai shima an Fahimci ya na cikin Damuwa.
Abokansa na wajen ne da sukaje masa Daurin aure suka so su fasa mgana ya rokesu da Allah kada wani yaji Labarin ya yi aure ba su nemi sanin ba'asi ba sukace in sha Allahu sun bar mganar a tsakaninsu.
Ya dauka al'amarin wasa ne sai da ya Faru sannan yasan abun ya wuce Tunaninsa.
*******
Yau na kwana daya a gidan Adda Fati kwana ba irin wanda na saba ba Tunda achan baya in bata da lafiya na kan je har na kwana da ita.
Ammh yau kwanan da na yi ya bambamta da sauran tunda na kwana ne a matsayin matar aure wacce igiya uku kwarara ke kanta.
Tun bayan tafiyar su Amma mu ma mu taho gidan Adda Fati gabadaya har da su Ramatu.
Ni dai ban samu damar sallama da matan gidanmu ba saboda kukan da na ke yi a Lokacin, ammh ina jin sanda Su ke ta fad'in in na tashi tarewa a gayamusu zumunci bazai taba yankewa ba.
Tunda muka zo na shige dayan dakin nata na cigaba da kukana Ramatu ta ba ni baki har ta gaji Inna Talatu ma ta gaji tace su rabu da ni har da zafin tafiyar Amma kamar kuma ta sani duk shi ya dameni a baya itace karfin gwiwana yanzu ta yi nesa da ni wa zai Tsayamin in dan na kasa?
Abunda na ke tunawa kenan ina Tunanin wazai tareni in wata guguwar ta tunkaro ni, su ba zasu gane ba ne ina gujema kaina wani abun da zai iya zuwa ya Dawo ne an yi daya ba'a ji da dad'i ba an sake yi nan ba'a rabu cikin mutumci ba meyasa baza'a hakura ba?
Ko abinci ban iya sakama cikina ba ina jin da su Ramatu za su tafi suka shigo suka min sallama ban amsa su ba kuma dukkansu sai dare suka tafi suka barni gidan Adda Fati ni da Habiba.
Inaga da mijinta ya dawo ne ta warware masa komai shine ya biyoni har dakin ya na ta bani baki da lallashi mganarsa guda d'aya ta saka jikina ya yi sanyi in da ya ke fad'in"Hasiya ki yi hakuri duk abunda kika ga ya faru ko zai faru da sanin Allah, Sannan ka da ki yi fushi da Amma ita uwa duk abunda zata aikata walau mai kyau ko mara duk saboda d'anta ya kasance cikin Farinciki ne ko da ita zata Dauwama acikin kunci to ina so ki sani Amma ta zabi Farincikinki fiye da nata Hasiya."
Wad'anan maganganun yasa ya hakura da kuka na tashi na je waje na kama Ruwa Adda Fati ta sakamin ruwa a kettle na yi wanka na rama sallolin da kai kaina sannan ta had'amin Tea na sha Sosai domin sai a lokacin naji wata irin mahaukaciyar yunwa ta tasomin hade da ciwon kirji.
Allah yasa cikin kayana da su Adda Fati suka tahomin da shi akwai Omeprazole shi na sha na samu na kwanta sai barci.
Har ina makara Sallar asuba Saboda gajiya shiyasa ko da na tashi Fuskata ya yi jajir sannan ta kumbura saboda kuka ammh kuma na daina kuka sai dai ba Annuri ko kad'an a fuskata.
Ban fita ko Falo ba Adda Fati da Habiba daman tare muka kwana suka Biyoni har ciki da abun karyawata.
Dakyar na bude baki na gaisheta ta amsa lokaci daya ta na zama a gefena.
Habiba ta kallah ta na fadin"Ki yi sauri Baban Hanifa na jiran ki sun fita tare da Hanif"
Ko da ban yi tambaya ba naga amsar Tambayata tunda naga Habiba na saka Uniform din makaranta kenan har sun sanya mata makaranta.
Sai naji dadi a raina ina kallonta ta shirya sannan ta yi mana sallama bayan ta Dauki jakar makarantar ta ta fice.
Koko da kosai ne Adda Fati ta yi kuma nasha kokon da yawa kosan nan naci kad'an saboda maiko.
Adda Fati ta fita ta bani waje ni ce da nagama na kwashe komai zuwa tsakar gida na isketa ta na wanke wanke kunya da kuma ba Halina ba ne ganin ana aiki ina zaune yasa na Tsugunna ina tayata da Dauraya.
Ta yi ta yi na barshi nace mata ta bari zan yi sai ta kyaleni.
Tunda muka fara batamin mgana ba nima ban yi mata ba ga shi ina so na tambayaeta na kasa Dakyar nace"Amma su sauka lafiya?
Adda Fati ta juyo ta na kallona kafin tace"Lafiya lau suka sauka jiya da Daddare mun yi mgana ta wayar Adda. Da safe ma ta sake kira tace na gaisheki."
Mirmishi na yi ban ce komai ba ganin haka yasa Adda Fati tace"Hasiya ki yi hakuri ki yi ma Amma uzuri ta na cikin Halin da bata da wani zabi ne."
Idanuwana sun tara kwallah nace"Shine zata amince ma wanda bata san komai a kanshi ba ya aureni?
Ni ba ma wannan ba nafi Tunanin makomar tasa Rayuwar"
Adda Fati tace"Allah zai tsare Hasiya sannan ina da kyakyawan yakinin Abubakar zai bambamta da Sauran in sha Allahu."
Daganan ban kara mgana ba har muka gama wanke wanken.
Ni na share wajen na had'a da Tsakar gidan na share tas sannan ta ce ga ruwan wanka nan a gawayi in zan yi wanka ba musu na juye na yi wanka.
Na sauya kaya sai na kara jin dadin jikina.
Tare muka yi ni da ita, na dai tayata da sauran aikace aikace sai la'asar Adda Rukayya tazo sannan ne Adda Fati ta kirani ta na min bayanin Amma ta bar wasu kudi a hannunta tace a karamin da duk abunda na ke so. Kai tsaye yace"Adda ku siya duk abunda kuka ga ya kamata. Ammh ku sani ko kun siya kun kaini da su haka zaku je ku dauko su."
Kalamai na suka kara sanyaya musu jikin da har Adda Rukayya ta tafi ba su karamin mganar Tarewa ba.
Sai ga shi a hankali na sake a gidan Adda Fati Amma ce dai ban bari mun yi mgana ba sai dai Adda Fati na shaidamin ta na gaisheni a bakinta na ke jin Adda ma ta yi ta fad'a wannan gaggawa na Amma bai yi ba sam.
Nima abunda na gani kenan so ta ke a fara kirgamin aure daga biyu zuwa uku har sama ammh in ba haka ba meyasa ta matsa ma kanta da sai na yi aure a Lokacin da ban shirya ba?
Ni ba kaina na ke ji ba domin ni na riga na fidda rai da wata rayuwar jin dadi ASSADIQ na ke ji shine Bakuwar Rayuwarsa zata shiga gagari tunda ya had'u da tawa Rayuwar.
Sai da na kwana biyar a gidan Adda Fati sannan Ramatu ta dawo wannan karon ita da Nura ne shima ta gama gayamasa komai duk maganganunsa Nasiho ne da ban baki to me zan ce? Baza su taba hango abunda na ke hangowa ne tunanina ya tafi kuma shi wannan auran ko ta ya ya zai kare? Na zura ido dai ina son ganin ta ina komai zai fara kuma ta ina zai kare.
Ranar ma ina jin su na mganar Tariyan tawa ita da Adda Fati abunda ke bani mamaki ina su ka ga Assadiq din? Mutumin da tun ranar bamu kara jin Labarinsa.
Bansani ba har Adda Fati ta yi ma Jummai Dillaliya magana Sannan ta bama Adda Rukayya wasu kudaden zata siyamin kula da sauran su Filet da ba na su sosai.
Sai da na yi sati gidan Adda Fati sannan Hankalinta ya fara tashin jin Abubakar shuru.
Ko yau da Safe da suka yi waya da Amma sai da tace ko ta kirasa ne? Amma tace kada ta kirashi ta bari zai nemata da kansa in ya shirya.
Rashin ji daga barayin Abubakar ya sa sai gwowiyinsu ya yi sanyi daga shirin Tarewata.
Ni dai yadda ba su gayamin ba haka na nuna ban gane komai ba.
A cikin raina ina fatan Allah yasa ya tseratar da Rayuwarsa ne daga Rayuwata.
Ko acikin raina bazan damu ba domin ya tafi ya barni ba zan fi son hakan na fi damuwa da tashi Rayuwar fiye da tawa Rayuwar da ta riga ta Gurbace.
Wasa wasa sai ga shi ina son kwashe Sati biyu a gidan Adda Fati ba wani labari daga Abubakar ni kuma jin Shuru yasa har na fara maida jikina tunda na fara samun natsuwar zuciya.
Ramatu ma ta damu bata kwana bata kira Adda Fati suna kuskus dai nasan kan mganar ne ni ko acikin raina Fata na ke yi Allah yasa ya yi nesa da Rayuwata. Har acikin sallata ina rokon sa Allah yasa Assadiq ya yi nesa da Rayuwata kada ya dawo cikin Duniyata balle wani abu ya sameshi sai naji na fi Tsausayinsa fiye da Abubakar da Salisu.
Adda Rukayya da Ramatu suna ta sintiri a gidan Adda Fati in ba su zo ba za su kira waya har acikin zuciyata na ji dadin chanjin da nagani a tare da Adda Rukayya.
Akwai wani al'amarin da mutane suka kasa ganewa shine in mace ta auri mugum miji ya kan rab'a mata wasu daga cikin Hallayansa.
Halin mijin Adda Rukayya ba shi da kyau ya tsani asara sannan ga daukan zuga tunda ya nuna baya son muna zuwa gidansa ita kuma ta na son shi sai ta ke ganin a irin rayuwar da muke ciki shine Rufin asirinta sai daga baya ta gane bayan shi mu ma rufin asirinta ne, shiyasa ta zabi da ta kamashi mu ma kuma ta rikemu gam in bai so mu rab'esa ita da ta ke Dolenmu ita zata zo in da mu ke.
Ranar da na cika kwana ashirin a gidan Adda Fati suka yanke shawaran Kiran Abubakar ita da Adda Rukayya ta kira Ramatu ma suka yi shawara.
Bata gayama Amma ba ammh sun yi mgana da Adda sai Fada ta ke yi ta na fad'in"In auran bazai yuyu ba ya saketa mana Hasiyan ta dawo gabansu ta zauna."
Da wannan Tunanin Adda Fati ta kwala masa kira da yammah.
Lokacin suna Daki tare da Tahir suna shawaran yadda za'ayi.
Bai gane lambar ba tunda ranar ya manta bai yi saving ba sai da ya dauka suka gaisa ta yi masa bayani sannan ya gane da sauri ya saka wayar a amsa kuwwa yadda Tahir zai ji komai.
Adda Fati cikin sanyin murya tace"Abubakar Lafiya ko mu ka jika Shuru ba kira ba wani bayani?
Sadiq ya kalli Tahir shima ya kallesa ya na yarfa masa hannun alamun ina Ruwana sai kaji da su kai da ka kira ruwa.
Da sauri Sadiq yace"Lafiya lau ina ta wani shiri daga bangarena ne kinsan abunka ga talaka."
Adda Fati tace"Mun sani wlh daman mun ji shuru ya yi yawa ne, sai nace bari na kira naji ko lafiya sannan mu ji yaushe ne Tarewwar? Ko nace ka samu in da zaka ijiyetan?
Sadiq ya sauke numfashi kafin yace"Zan kira ki zuwa gobe abunda ake ciki zan sanar da ke."
Adda Fati tace shikenan sai ta jisa da haka suka rabu.
Ta na kashewa Tahir yace"Af daman zaka auri yar mutane ne kazo ka kwanta a gida?
Sadiq yace"ba kai ne kace zaka sama min mafitan inda zata zauna ba."
Tahir ya yi shuru kafin yace"Eh yanzu mafita itace gida zaka siya ko?
Sadiq yace"Gida kuma? Ai sai ace ina da kudi haya dai ko zamu kama mata?
Tahir yace"Oh hakane to a kama mata hayan ammh ba a inda aka santa ko aka sanka ba wani waje Dabam da muhallin ku."
Sadiq ya kalli Tahir cikin karin bayani shi kuma ya gyara zama ya cigaba da fadin"Hikimar haka shine Rayuwar da zata yi kafin wata shidda itama kanta Sirri ce Sadiq."
Sadiq ya yi shuru kafin ya jinjina kai yace"Na aminta da mganarka. Tunda har na sallameta ba na so ta san wani abu ko kad'an a kaina Tahir."
Tahir yace"Shine mganata ka ga ko dole mu samo wani waje na Dabam"
Sadiq ya yi shuru ya na nazari Tahir yace"Ka bar komai a hannuna a malaman makarantar da na ke Hidimar kasa akawai wani da ya ke Dillancin gidaje da Filaye zan yi masa mgana gobe naji yadda za'a yi."
Sadiq ya sauke Numfashi kafin yace"Komai ka yi sa a goben tunda ka na ji sanda nace gobe zan kirata."
Tahir yace"Kada ka damu in dai da kudi a hannunka za'a samu ko ciki da Falo ne ina Laifi."
Sadiq yace"Kudina sun yi kasa ammh zan yi ma Abba waya.'"
Da haka suka bar mganar akan gobe Tahir zai bincika musu gidan da Hasiya zata zauna nesa da inda aka santa ko aka san su saboda suna son komai ya kasance cikin Sirri ne kamar yadda Sadiq ya tsara tun farko.
*Janafty*
*TMWB2K003*
*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*
Mai_Dambu Candy world's and more. Zaa iya samun Tuwon madara da iloka, gullisuwa, aya mai sugar, gyada mai gishiri, sannan muna bada sari, muna kuma karban oda da aikin biki ko suna. Muna karban aikin donut da cincin..08130269641
Washegari kan mganar suka rabu da Tahir ya na ko zuwa makaranta ya nemi Hambali ya yi masa mganar, nan da nan yace kada ya daamu za'a samu duk da ya sanar da shi ba sa bukata a nan samaru sai dai wani waje na daban.
To an samu kafin mu su tashi daga makaranta sai dai ciki da falon da ya nema ne ba'a samu ba, sai dai Safecanten mai daki da kitchen a had'e kuma a Hanwa ne aka samu gidan.
Sabon gida ne ma yanzu ne ake son a fara ba da hayan gidan mai dauke da Dakuna hud'u a shekara dubu dari da Hamsin
Da Tahir ya nace sai mai ciki da Falo kad'ai Hambali ya gayamasa gaskiya yace irin d'akunan nan na Haya suna Wahala ga irin wanda aka fi saurin kamawa a irin anguwan waje wajen gari gwara kawai su karb'a.
Bai ce masa komai ba sai dai yace masa in za su karb'an zai kirasa a waya sai da ya dawo gida ya jira Sadiq ya Dawo sannan ya sanar da shi Halin da ake ciki.
Nan take Sadiq yace ba komai su kama wannan d'in.
Tahir ya kallesa shekesheke kafin yace"Ka na da dubu dari da hamsin din ne yanzu?
Sadiq yace"Akwai kudi a hannuna mana da na so na yi ma Abba magana sai kuma na fasa kasan akwai kudin alawuna na ba duka nake amfani da su ba, Tunda koda yaushe Abba na Turamun kudi sai na yi amfani da shi."
Jin haka yasa Tahir ya yi shuru bayan ya kira Hambali yace su same shi a bakin Titi tare suka dumguma suka tafi ganin gida kuma Alhamdulillah Tsarin ya yi ma Sadiq sosai sai dai ya so da wasu a gidan Tunda shi kam ba zuwa zai yi ya zauna a inda ta ke ba ko Saboda Halin rayuwar nan da muke ciki.
Da ya yi ma Hambalin mgana shi kuma yace kada su damu duka d'akunan uku an kama daman wannan ne kad'ai ya rage kuma amare za'a saka