Showing 51001 words to 54000 words out of 74587 words
sanan tana tausayin Arham sosai saisa take sonshi ko menene oho ita tama rasa, all she knows is takasa tsanan Waleed, and duk in zata kalleshi saitaji wutar sonshi nakara ruruwa aranta to kodai kyanshi da kudinshi ke dibanta ne? Or is it possible kaso MAZA BIYU KUMA ABOKANAN JUNA? Ta tambayi kanta. "Tunanin5 me kike"? Waleed yamata tambayan yana karasowa gabanta a dinning din ya rungume hannayenshi akirji. "wai ni?" ta tambayi kanta tana kallonshi, daga mata gira yayi alamun yes you, murmushi tasake mai tace "kawai tunanin gidan mu nike inaso naje zaka barni?" yana kallonta eyes to eyes ya girgixa mata kai, sanan yace "matar Waleed bata zuwa ganin gida sai bayan ta shekara da aure, I am a well cultured man you know" yasake daga mata gira, samun kanta tayi da kasacemai kala saima wata shegiyar kasala da sha'awan shi dataji ya diran mata all of a sudden, he was so close to her yana mata magana ciki ciki sanan yana wani kashe mata sexy idanun nan nashi yana daga mata gira, ganin ta shagala da kallonshi yasa yajuya kawai yafice daga dakin yace "tashi kije kiyi salla, ankira magrib".
Sai wuraren 9 bayan anyi isha'i yamayi magana da wasu naroka yan anguwanni haka dasukazo neman taimako ya sallame su sanan ya shigo cikin gidan, maida kofar falo yayi yarufe yana kallon Ammi data zauna kan kujera tana aiki da laptop dinta duba sales din da aka mata a campanonin ta take, is a normal thing kullum around that time zata saka fararen glasses sanan ta zauna tana aikin sai wajen 11 na dare sanan zata gama taje ta kwanta, zama kusada ita yayi ahankali yace "sannu da aiki Ammi" kanshi ta shafa tace "kadawo son" gyada mata kai yayi ya jingina da kujera yana zaro wayanshi daga aljihu yarike wayan yana kallo saikuma ya shiga daddanna wayan yanemo number Dr Kemi yay dialing, ringing daya kaman wayan na hannunta ne daman ta dauka.
"Hello Dr Warbai, good evening" kafin ma yay magana yaji karan kuka sosai a background din wayan, ahankali yace "who is crying?" "your patient" tabashi amsa da sauri, tashi yayi yazauna dukya damu, ahankali yace "what about medication dinta danace a dinga bata dakesata bacci" cikeda damuwa tace "Sir wlh na bata tun bayan ta farka da magrib dinan but taki bacci, daidai da ruwa takisha, inta ganmu ma ihu take, taki yarda damu kwata kwata jikinta ma yadau zafi, tun dazu ina kanta sai yanzu nafito daman nazo nakira kane saigashi kiranka ya shigo kaman kaji ajikinta tana kuka" shiru yayi yana rasa mezaiyi saikuma ya kalli Ammi dake aikinta hankali kwance gabanshi nafaduwa yasan yanzu yana fadimata orphanage zashi saita balbaleshi da bala'i, katse wayan yayi yamaida wayan aljihu ya ijiye yay shiru gabaki daya jin karan kukanta yasa yakasa natsuwa mikewa yayi zumbur kaman an dagashi yazuri key motar Ammi dake Centre table da sauri Ammi ta kallai tace "ina zaka?" "orphanage Ammi, emergency case gareni, I have to go" shiru Ammi tayi tana kallonshi kaman zaiyi kuka yace "please Ammi dazaran nagama zan dawo" yanda yayi yasa tace "saika dawo" da sauri yafita daga gidan, motar Ammi ya shiga yay horn gateman yabudemai gate yawuce yafita ya shiga titi yaba sharara gudu, wani super market yawuce akan hanya hakanan saiya sami kanshi dayin reverse back yadawo parking yayi agaban super market din ya shiga, yau kusan 3days kenan bata sakashi a ido ba, wata Teddy babba yasaya, saikuma yasai su snacks da chocolate da ice-cream yabiya kudi yafito ya shiga motar yaja, ko minti 15 baidauka ahanya yakai orphanage din, parking motarshi yayi agaban clinic din yafito lokacin 10 harda kusan minti 15 but yana iyajin ihunta daga wajen, daukan Teddy din yayi da sauri yama manta da sauran abubuwan saya sayo tsabagen yanda kukanta ke rudeshi ya shige cikin, ward din datake ciki yayi agaban dakin datake yaga Dr Kemi da nurses dukansu tsaye sunyi charko charko, babu wanda kukanta the bai dagawa hankali ba, Dr Kemi na ganinshi ta sauke ajiyan zuciya tace "thank God you are here, bari naje nahuta ba'a taba kawo mana patient data taba bamu wuyaba irin wanan yarinyar" wucewa suma nurses din sukayi suka tafi bayan sun gaidashi, ahankali yake daga kafanshi haryakai gaban dakin, kukanta dake tsuma zuciya nakara tashi yana kururuwa, daura hannunshi yayi kan door handle din kafin ya murda yatura kofan ahankali yana kallon dakin, tana zaune akasa kusada kofan ta tankwashe kafa kanta sauke tana rusa uban kuka dakowani gaba na jikinta ke amsawa, bama tadago kaiba balle tasan waye yashigo ba, maida kofan yayi yarufe ahankali, sanan yadago kafanshi yazo har gabanta, ijiye mata Teddy yayi akasa agabanta sanan ya zaga ta gefenta ya tsugunna ahankali yana kallon yanda tsabagen bala'in kuka kandaya kulle mata ta wargajeshi yama rufe mata fuska da baya, cikin wata irin karaman tattausan murya yace "Sabeeha" har kasan kwakwalwanta taji kiran sunanta dayayi dawani irin sauri ta dago kanta takai hannayenta ta gyara gashin gaban fuskarta ta hanyar waresu kyakkyawar fuskarta ya bayyana ta kallai suka hada ido, wani irin fashewa da kuka tayi saikuma tasa hannayenta biyu ta tureshi tana ihu da kuka. "ahhhhh ammmm" saikuma tajuya da sauri ganin Teddy daya ijiye mata awurin yasa tai grabbing nashi da sauri ta daga ta shiga kwadamai tana mugun kuka jikinta na rawa ranta ya bala'in baci, saida ta kwalamai Teddy iya son ranta sanan ta jefar dashi akasa ta tattaka tana kuka saikuma ta dauka ta mike tsaye tana tafiya tana dingishi tai wajen gadonta tahau ahankali ta kwanta ta rungume Teddy tana sauke ijiyan zuciya.
[10/18, 1:04 PM] +234 703 278 9649: ✍️ M SHAKUR
2️⃣3️⃣
Yadade atsugunne yanda ta barshi, zai iya cewa tunda Allah ya halltoshi duniya da dai wayanshi aka bai taba ganin mutumin daya daga hannu da sunan zai dakeshi ba aduniyan nan ballema har ya dakan sai akan yarinyar nan, bude idanunshi da tuntuni suke alumshe yayi yadan juya ya kalleta, sai ajiyan zuciya take irin na wanda yay kuka dinan ta kankame Teddy tana jikinta har bari bari yake, ahankali ya furta zuciya! Mikewa tsaye yayi ahankali yafara tafiya batare daya waigo ya kalleta ba yay kofa, hannunshi yadaura zai bude kofan yaji tawani irin fasheda kuka da sauri yajuyo, ganin yayi ta tashi daga kan gadon tana kokarin saukowa daga gadon, saukowa tayi tana kuka ta taho har gabanshi tana dingishi, rungume hannayenshi yayi yanabin gashinta dake lilo da kallo yace "you just finshi beating me, why are you crying again? Ba bakison ganina ba?" yay maganan gabaki dayanta cikin harshen turenci, cigaba da kukan tayi batare data cemai kalaba, sosai yaje yanason yay training nata yabata tarbiya mai kyau, ahankali yace "you don't beat your elder koma mesuka miki, is wrong, now say sorry" dago jajayen kumburarrun rinannun idanunta tayi ta kallai kaman yanda shima ya tsare mata ido, ahankali cikin dishashiyar muryanta dabata fita sosai tace "so...rry" yanda tafadi sorry was so cute da saida yasashi murmushi, handky aljihunshi yaciro yazo har gabanta ya tsaya sanan ahankali yadaura left hand dinshi kanta sanan yakai right hand dinshi dake rike da hanky din kan fuskarta wani irin wawan ajiyan zuciya ta sauke da saida yasa ya kalli fuskarta kafin ahankali yashiga goge mata hawayen dayay chaba chaba a fuskarta, sanan ya share mata hancin daya baci da majina, sanan yawuce cikin dakin zuwa gaban gadonta, pink bathroom slippers din da aka bata na sawanta yadauko ya ijiye agabanta yace "put on the slippers" sakawa tayi da sauri tana kallonshi shikuma ya tsaya yana kallon cute yatsun kafarta fararen da zai iya cewa baitaba ganin yatsun kafan mace kai kyau hakaba kodan baya kallon yatsun ne oho, dago kanshi yayi ya kalleta yace "let's go" yay maganan yana bude kofa yafito yajuyo ya kalleta, da sauri itama tafito tana kara rungume Teddy dinta ta tsaya kusadashi, hannunshi yasa yajawo kofar yarufe sanan yafara tafiya ahankali sabida ita, kallonsu nurses din suka tsaya sunayi da mamaki yarinyar daketa uban kuka, tana ganinsu tadaga Teddy ta sama tai gaban counter dinsu da gudu zata rafka musu da sauri Waleed ya daka mata tsawa. "Saheeba" tsayawa chak tayi bata rafka musu ba tajuyo kaman zatai kuka ta kallai, daure fuska yayi tamau yace "come here" tahowa tayi ahankali sukuma nurses din na dariya kasa kasa, hannunta yakama yarike sanan yay wajen kofar fita daga clinic din da ita, security yabude musu kofan suka fito, tunda aka kawota bata taba fitowa ga wuta ko ina a premises din kaman ba dare ba, ga hadaddun flowers ga few cars dake pake a filin, tsalle tahau yi tana kara kankame Teddy ta kana ganinta kasan she's very very happy, tai wajen flowers tana tattabawa saikuma ta daura Teddy ta akan flower tana tsalle, murmushi yayi yawuce ta yace "lets go" daga Teddy ta tayi ta dauka tabishi da sauri tana dingishi har zuwa inda yay parking motarshi, bude mata gidan gaba yayi yace "seat" shiga tayi ta zauna ahankali sanan yazaga mazaunin direba tana binshi da kallo kaman zai gudu saida yabude motan ya shigo sanan ta sauke ajiyan zuciya ta shiga tattaba motan tana yan surutai kaman yanda yara keyi in sukaga kayan barna, wajen radio mota ta shiga tattabawa da sauri yace "stop" denawa tayi ta hade hannayen takai dukansu baki tana kallonshi da kwala kwalan idanunta, dan ajiyan zuciya yayi yahanata wanan takoma wanan, ahankali yamika hannunshi baya yadauko jakan desert da snacks din daya siyo mata ya daura kan jikinshi ice cream yaciro yabude yasaka spoon yamika mata yace "ice cream" tsayawa tayi tana kallon ice cream din dabai wani narkeba da kallo dan da kankaramshi aka bashi, kwanto da kanta tayi tana leka ice cream din kaman wata matsoraciya spoon din yazaro ya lakato ice cream din yakai bakinshi yasha ya lumshe ido yace "is sweet, ice cream" karban duka ice cream din tayi daga hannunshi zata sha saikuma ta dago takai hannunta ta fizge spoon dinta shiga shan ice cream din kaman zata hada da roban cikin 2min ta shanye tass tamikamai spoon da roban ice cream din, murmushi yayi yaciro muffin daga ledan yabata kaiwa baki tayi taci taci ye tasake mikamai hannu alamun yakara mata saida tacinye duka guda biyar din dayasa yo sanan yabata ruwan sanyi ba sosai ba tasha tai gyatsa da karfi dayasa yatabe fuska yana kallonta yace "yanyanyaa, don't do that again" gyadamai kai tayi hankalinta yakoma kan yan littatafai data gani kan saman motan, da sauri tamika hannu zata dauka kafin ta dauka ya dauke yace "stop is not mine na Ammi ne" ahankali tana kallon fuskarshi tace "Am....mi?" gyadamata kai yayi yace "yes Ammi Saheeba" saita shiru ta tsaya kallonshi, murya chan kasa yace "now listen kinsan me yasa nakawo kinsan nabaki kayan dadi"? Yay maganan da turenci dan turenci kadai ya lura tanaji inya mata hausa bata ganewa, turencin ma yawanci bata cikamai reply ba, badaita wani maganan kirki dan baitabajin tamai full sentence da turenci ba, ahankali yace "you see am a very busy person, I work in this orphanage, and I am a Dr, bakoda yaushe zaki dinga ganina ba, kinsan menene banso inhar kinayi zanyi fushi dake?" da sauri ta girgiza mai kai yace "banso kina kuka, kobaki ganni ba karki kara kuka do you know why? Because am going to make you a promise now" yay dan shiru yana kallonta ganin gabaki daya ta natsu shi take kallo yace "duk ranan duniya zaki ganni in sha Allah, zanzo naduba ki dan nine Dr ki, but ba lallai ki ganni dawuri ba sabida ina aiki dayawa, bawai dan baki ganni ba kiyita kuka, no banso kina kuka sabida in kina kuka bazaki warke ba, kidena kuka, be a good girl kome kikeso za'amiki, kidinga shan maganin ki in anbaki kinji" gyadamai kai tayi yay murmushi yace "muje nabaki wasu magani saikiyi bacci saikuma gobe u will see me okay, zan sayo miki ribbon and other hair stuff kidinga kama gashin nan" gyadamai kai tayi yabude kofa yafito yazaga yabude mata side dinta tafito ahankali rikeda Teddy dinta yamaida kofan yarufe sanan yamaida ita dakinta, wasu magani yabata sanan yasa ta kwanta, kwanciya tayi rikeda Teddy tana kallonshi shima yana kallonta kaman wayanda fuskokinsu ke magana da juna harta fara lumlumshe ido, saida bacci ya Kwasheta sanan yatashi bargo yaja yarufa mata sanan yatofa mata addu'an bacci yajuya yafita daga dakin, Dr Kemi yama sallama yawuce yatafi, koda ya isa gida wuraren 12, kulle kofa yay yay upstairs, Ilham yasamu tai bacci abinta bayi yashiga yay wanka yafito saida yay sha'fa'i da wuturi sanan yazo ya kwanta sai bacci.
*******
Da asuba yatashi as usual yatafi masallaci, itama yana fita ta shiga bayi dan maganan Arham ne aranta dayace mata ta tabbatar yakaita gida, salla tayi bayan tafito sanan tai kwalliya cikin doguwan riga baki mai kyau.
Wuraren 7 tafito jin muryan Ammi akasa, ahankali take sauka daga stairs daidai Waleed shima ya shigo gidan, a stairs suka hadu, murya chan ciki tace "good morning baby" "morning" ya amsata yay gaba saikuma ya tsaya yace "kinyi arranging kayan ki ko am dropping you off at home kafin na wuce aiki" gyadamai kai tayi tace "to yallabai bari na gaida Ammi nadawo nayi" gyadamata kai yayi yawuce itakuma ta sauka, a kitchen tasami Ammi dayan aikinta suna breakfast, har kasa ta tsugunna ta gaitada, dda murmushi Ammi tace "Khadija harkin tashi, to barkanmu da asuba Mike tsaye kidena tsugunnawa kina gaidani dan Allah" tashi tayi ahankali tace "Ammi bari nai breakfast din kije kihuta" da sauri Ammi tace "kul, matar d'ana bata wahala, wuce kikoma wajen mijinki ki taimakamai ya shirya aiki, saiku sauko kuyi breakfast kan kuwuce, wuce wuce" Ammi tai maganan tana cigaba da aikinta wucewa tayi tafice tanajin dadi inhar haka Ammi take ai tafita masifan ta ko ajikinta, duk masifar matarnan jibi yanda takeji da ita, sama ta koma Waleed na bayi hada kayanta tayi tsaf sanan tai kwanciyan ta kan gado tadau wayanta ta shiga message ta turama Arham sako.
" _barka da asuba mijin Khadija, dafatan katashi lpy_ "
Kaman wayan na hannunshi da sakon yashiga yamata reply.
_"hey lawyer, couldn't sleep wlh, kin hana wanan fine Hausa Fulanin yaron bacci, wai me kikamin ne_?
Dan dariya tayi tashiga typamai sako
" _nidai karka manta da alkawarin dakamin, kace nakoma gida yanzu kuma zan koma gidan, Waleed zai ijiyeni kafin yatafi aiki_"
_"you will definitely see me, worry not"_
Murmushi tayi zata sakemai reply taji muryan Waleed akanta. "who is making you smile like that"? Awani irin birkice tadago kai ta kalli saman kanta taga bashi akanta yanama gaban wardrobe din dakin yana kokarin ciro kaya, juyowa yayi rikeda hanger da suit kejiki ya kalleta saikuma yay murmushi yace "I guess is that your friend ko, yana sunanta" yay shiru kaman mai tunani da sauri tace "Salima, eh Salima ce tamace na gaisheka" murmushi yayi baice mata komiba ya shiga shiryawa idanunta akanshi kaman zata cinyeshi, tsaf ya shirya sanan suka sauka kasa breakfast sukayi mairai da lpy Ammi tasa aka sauko musu da akwatinan su aka loda a mota sanan tarakasu har wajen mota suka tafi.
Acikin gidansu Waleed yay parking, suka fito akwatin su yaja musu Ilham biyedashi sukai cikin gidan, ga mamakinta taga ko'ina agyare tsaf yana kamshi ba kura hakan yasa tace "naga dakin ba datti" tabe baki yayi yahau stairs yace "Ammi ta aika aka gyara ko'ina" murmushi tayi dan dama tanata tunanin aikin gyaran gidan dazata yi inta dawo har dakinta ya shiga ya ijiye mata akwatin ta sanan yawuce nashi dakin ya ijiye nashi bude akwatin yayi yaciro wandon ranan nan dayake jikinshi daya shiga rafin nan bayan an jefo coffin ciki, zura hannunshi yayi acikin aljihun wandon nan exactly irin dan kunnen Widad yafito, faduwa gabanshi yayi yace "so is true, this girl is in danger, serious danger, someone is trying to kill her I need to protect her" maida dan kunnen yayi yasa a aljihun wandon jikinshi sanan yafito dan dayan dan kunnen na office dinshi a orphanage, sallama yama Ilham yawjce compound ya shiga mota gateman yabudemai Gate yawuce yabar gidan.
A parking lot din gidan marayun yayi parking yabude motan ahankali yafito, as usual Arham yafito daga office dinshi yana sanyeda suit da pad a hannunshi yasauka daga matattakalan yataho yace "welcome boss" hararanshi Waleed yayi yace "yau yan mutuncin na kusa, tell me wat we've got yau?" shiga to do list dinshi Arham yayi yace "the first thing dakace zakayi bayan kadawo daga excursion is meeting da Nora, by 9, already ma he's around, yana jiranka, sai the second thing is meeting da staff dakai shifting, sai na uku, clinic round, hostels round dats all" gyadamai kai Waleed yayi daidai yabude kofar office dinshi ya shiga Arham biyeda shi, jacket dinshi yacire yay hanging a mahanga sanan yazauna akan kujera, yadaga hannunshi ya kalli agogon rolex dake daure a wrist dinshi yaga 1min after 9 hakan yasa, yace "kira Nora din" fita Arham yayi daga office din baiwani jimaba ya shigo tareda wani guy da zaiyi 25yrs, maraya ne tun 14yrs aka kawoshi wajen Waleed, yacigaba da rayuwa gidan marayun harya gama secondary school, Waleed yatambaye shi yanason yacigaba dan wasu basuso yace ceh yasashi a University, yanzu haka yana final year Waleed ke biyamai everything, daman normally insun gama University in aiki zasuyi sun samu Waleed zai barsu sune suyi wasu kuma suna nunamai sunfiso suyi aiki gidan marayun dan sunyi rayuwan maraita suma sunaso su taimakama wasu marayun, haka zasu fara aikin kuma duk watan duniya saiya biyasu albashi mai kyau, shigowa cikin office din yaron yayi cikeda murmushi Waleed yace "Nora" ya mikamai hannu zagawa Nora yayi harta gaban inda Waleed din ke zaune ya tsugunna har kasa yace "ina kwana Mai gida" ko kadan Waleed baijin dadin abinda bama Nora kadai ba yawancin yaran gidan marayun suke hakan yasa yace