Showing 42001 words to 45000 words out of 74587 words

Chapter 15 - Duniya Biyu Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

12 Dec 2024

476

wane madara sukai ido da ido da ita, wani irin kallonshi take kaman yanda shima yake kallonta gabanshi nafaduwa sosai, kasa jure kallon datakemai yayi hakan yasa ya runtse idanunshi da sauri yana karanto addu'o'i aranshi, an tsinci yara manya da kanana da dama agidan marayun nan wasu ma har amasai aka tsince su amman baitaba jin tsoronsu kojin wani abuba sai akan yarinyar nan shi yana rasa takamaimam miyakeji, ko tsoron dasu Dr Kemi suka haddasamai natane a zuciyanshi oho all he knows is yana shakkan ta.
"aaaahhsshh, aashh, auuuccchh, a hhhhh....." yaji wata irin siriruwan murya, sassanya maidan gardi dake ratsa zukata na furta kalaman nan irin kalaman nan da ake furtawa idan kana jin zafi ko wani abu namaka zafi, ahankali yashiga bude idanunshi kaman wani mara gaskiya kafin yabude su tarr, zaune yaganta kan gadon tadaura hannunta akan saman kanta tana shafa inda ya aske mata a keya yamata stitches tana bata fuska tana making those sounds alamun zafi hawaye yacika idanunta gam, ahankali yake daga kafa yafara tafiya yana binta da kallo harya zagayo ta inda kafafuwanta suke ya tsaya awajen sanan yakama karfen gadon da duka hannayenshi guda biyu ya tsaya chak yana kallonta kaman ba zaiyi magana ba saikuma yace "sannu zafi yakemiki?" ko kallonshi batayiba sai cigaba da tatttaba wajen datayi daidai hawaye ya zararo zirr daga idon haggunta takai bayan hannunta tashare idanunta, tasake maida hannunta wajen tana tattabawa, ganin yanda take tabawan yay yawa zata iya warware dinkin dayay jiyan nan yasa yazagayo ta bangaren datake hannunshi yakai ahankali yakama hannunta dake kan wajen dinkin da sauri, dago idanunta dasuke akarkace tayi ta kallai, sakon hannun nata yayi da sauri yace "kul kidena tabawa, hannunki zai iya yuwa da germs ko bacteria akai bai kamata kina kai hannun kina taba fresh stitches dashi ba, so kidena" zaro ido tayi kaman irin wacce tadan haukacen nan saikuma tadan duko da kanta tana leka bakinshi kaman irin tanaso taga yay magana kuma, ganin yay shiru yana kallonta kaman yanda take kallonshi yasa ahankali takai yatsanta zata daura kan lips dinshi da sauri yakoma baya, komawa baya itama tayi da sauri saikuma tadaga hannayenta tana kallo, shiru yayi yana kallonta ganin da gaske ne lallai wanan blood yay affecting brain nata, ajiyan zuciya yasauke yana tunanin what exactly ma yakamata yamata yanzu, kujeran plastic yajawo yazauna yace "kalleni kina jina inaso nadam miki tambayoyi duk wani abu dakike ji yanzu ki gayamin" yay maganan yana kallonta still ganin har yanzu ba shi take kallo ba hannunta take kallo, ahankali yace "meke miki ciwo yanzu?" kaman ma batasan Allah yayo mutum awajen ba, wani irin kallon hannunta take tana kallon yan zane zanen lallen hannunta dasuka fara fading, jim yayi yana kallonta ganin kaman ma batasan magana yakeba yasa yakai hannunshi kusada kafarta ya bubbuga katifan yace "ke kallen dawo da hankalin ki nan" tsayar da kallon hannunta take ta kalli hannunshi da sauri daya buga akan katifa kaman irin Abun ya mugun jan hankalinta dinan, hannunta tasada sauri takai kusada tashi hannun itama ta bubbuga tana kallon nashi kaman taga wani irin film, safe gaban goshin shi yayi irin na yadamu dinan, ganin mouth conversion bazai musu aikiba dan bamata gane maiyake cewa yasanya yatashi daga kan kujeran kawai da zumin yafita sai yakira mata nurses azo a mata brush amata wanka ashiryata inyaso bayan sun gama sai akirashi yazo yay mata proper check up, tunanin hakan yasa yajuya ahankali yay wurin kofa wani irin wawan kuka yaji tasaki cikin yar muryanta dayaji har gangan jikinshi ta ratsa tashiga kiciniyar saukowa daga gadon, da sauri yajuyo ya tsaya chak yana kallonta, bare baki tayi tana kuka tana nunashi da hannu tana shirin saukowa yarinyar da tun dazu tai kaman bamatasan yana wajenba shine yanzu danya juya zai fita take wani dan iskan kuka hawaye sun wanke mata ido kaman sune abu mafi saukin fitowa ajikinta, ganin takasa saukowa kaman ma kafarta daya tarike ne dan takasa motsi dashi yasa da sauri yadawo dakin, komawa tayi ta zauna tajuyo tana kallonshi ahankali yabi kafar haggun nata da kallo sanan yamika hannunshi yazaro handglove cikin kwalin shi dake jikin windon dakin ya zura sanan yace "muga kafar" yakai hannunshi ahankali kan kafar yadaura duka hannunshi kai, mugun firgita tayi kaman irin firgita nan nacikin mafarki da sauri yasaki kafan yakoma baya yana kallon fuskarta yama kasa magana, dago kanta itama tayi ta kallai tana turo baki kaman mai shirin yin kuka kaman ba ita bace ta firgita yanzun nan ba, shiru yayi jim yama kasa cemata komi kawai saiya kara jawo kujera ya zauna ya rungume hannayenshi akirji, ganin har lokacin kallonshi take yasa yace "kalla baki magana ne ke kuma ce"? Yay maganan kaman yanda akema kurma magana yana hadawa da yatsa, yanda yay da yatsa tamai itama batare datai magana ba, ijiyan zuciya ya sauke ganin da gaske bata gane maganan shi ne, dagokai yayi ya kalleta ido cikin ido yace "what is your name"? Da sauri tanuna mai kanta cikin yar muryanta tace "name"? Abun ya mugun bashi mamaki ganin tagane turenci rass harda nuna kanta alamun da gaske tagane sunanta ya tambaya, samun kanshi yayi da murmushi dan he call this nasara dan tunda yafara magana da ita sai yanzu yaji tace wani abu, gyadamata kai yayi yace "yes, your name, tell me what is your name" kaman yanda taga ya sakin mata murmushi itama tasakin mai murmushin daya lobar da dimples dinta duka biyun tana leka fuskarshi tace "my name is" tai shiru kaman maison tuno wani abu kaman irin da gaske tanason ta tuno sunanta dinan, saikuma tace "my name issss......name" tai maganan tana lumshe mai idanu, shiru yayi kawai yana kallonta ganin ita karan kanta batasan wacece itaba yasa yace "listen to me, as from today, your name is......" yay shiru yana kallon yanda take kallon bakinshi kaman takosa yafadi mata sunan, dan ijiyan zuciya ya sauke yace "your name is Saheeba" da mugun sauri ta nuna kanta tace "ana Saheeba?" ta tambaye shi, wani irin mugun mamaki ne ya kasheshi jin tamai larabci ahankali ya gyadamata kai yace "anti Saheeba" sanan yace "Saheeba I want you to make my work easy for me, allow me to examine your leg, eye and head, my name is Dr Waleed Warbai, your Dr" yay maganan yana tashi tsaye daga kan kujera, binshi tayi da kallo kaman mai koyon magana tace "a Doctor, injection" tai maganan tana kallon alluran dake ijiye kan table din dakin, kallon alluran yayi kafin yasami kanshi dayin murmushi yace "no injection I promise, now lemme see the leg" yay maganan yana mikamata hannu alamun yabashi kafar, ahankali tadan matsomai da kafar, matsowa yayi shima yakai hannunshi ahankali yadaura kan kafar, firgita tayi sosai da saida yasa yarike kafan gam, ajiyan zuciya ta sauke yace "relax am not gonna hurt you, kidena firgita Inna tabaki" duba kafan yayi ta hanyar mamkatsawa take yagano buge kafan tai dawani abu, probably acikin ruwan nema halan ta buge, sanan yadau torchlight yazo tagaban ta Ahankali yakai hannunshi zai taduba idanunta, firgita tyi takai hannunta da sauri tarike hannun nashi tana kallonshi kaman yanda shima yake kallonta kirjinsu na bugawa atare.
[10/18, 1:05 PM] +234 703 278 9649: ✍️ M SHAKUR





1️⃣8️⃣






Tasowa tayi ahankali taleka fuskarshi tana kallon soft gemunshi da sajenshi har lokacin tana rikeda yatsunshi ta matso da fuskarta daidai saitin fuskarshi takai dayan hannunta ahankali tadaura kan soft gemunshi takama tana zaro ido kabarda hannunta yayi da sauri yakoma baya yana kwalama nurse kira. "Nurse! Nurse, Ramlat" ya kwalama nurse kira da sauri nurse ta taho dakin, cikeda girmamawa tace "gani Dr" anatse ya nuna mata Widad yace "ki kira wata nurse kuzo brush her teeth sanan anata wanka a chanza mata kayan nan be careful kar ruwa yaje kanta in anyway" gyadamai kai tayi tace "to sir" juyawa yayi zai fita Widad takwara wani uban ihu da saida yasa yajuyo da sauri kokarin saukowa take daga gado kota damke shi amman kafanta yahanata sabida ciwon dayike mata, sosai yaji tabashi tausayi saikuma yadawo yace "listen babu abinda zata miki I will be back soon okay" sanan ya kalli nurse din yace "make sure an bata abinci taci, go to the orphanage kitche......" saikuma yay shiru bai karasa maganan ba yace "just tafida ita bayin kimata all abubuwan danace, zan aiko da abinci dazaki bata da drugs kuma, zan fita yanzu zanje wani hospital acikin gadi nataho mata da glasses dazai gyara eye balls dinan nata in tana kallon ka" gyadamai kai nurse din tayi tace "saika dawo Sir" tsugunnawa yayi yadauki dan kunen ta daya cire dazu tai ihun dayasa yasaki dan kunen akasa, juyawa yayi yafita yana jiyota tana rangada shegen ihu da kuka, fita yayi daga asibitin yana dannama Mom dinshi kira ringing daya ta dauka yace "Mom ki aikomin da mota yanzu please" kaman zata tambayeshi saikuma tace "to bari na aiko direba" dan tare take da mai gidan ta, wucewa yayi ya shiga office dinshi basket din abincin rana da Mom ta aiko mai dashi yasa aka karba aka ijiyemai a office yadauka yafito, wani staff dinshi yakira yabashi basket din yace "kai this basket ICU kabama nurse din dake wurin" gyadamai kai staff din yayi yajuya yatafi shikuma yashiga cikin office, wanka yayi ya shirya cikin wasu fararen yadi yafeshe turare yay shegen kyau zama yayi abakin gado yabude wayanshi yay dialing number Ilham but har lokacin akashe tabe baki yayi yamike tsaye jin dayayi ana knocking kofar office dinshi, fitowa yayi direban Mom ne yace "barka da fitowa yallabai" gyadamai kai yayi direban ya mikamai key mota yace "Hajiya tace nakawoma mota gatanan nai parking dinta awaje" karban key yayi da murmushi yace "nagode" murmushi shima direban yayi yace "bari ni nakoma" da sauri Waleed yace "no muje na rage maka hanya ai fita zanyi nima" gyadamai kai Direban yayi ba karamin dadin hakan yajiba, fitowa Waleed yay daga office din yamaida kofan yarufe sanan yay wurin motan shiga sukayi ciki yaja motan sukabar gidan marayun, cikin gari suka shigo akan wata babban Junction ya sauke shi yazaro kudade masu yawa yamikamai yace "gashinan sai kahau abin hawa ni zan dauki wanan hanyar ne" sauka yayi yace "nagode, nagode Allah ikara taimakawa" murmushi kawai Waleed yamai yadauki wata titi daban, agaban wata babban super market yayi parking ya shiga siyayyan abubuwa yayi tundaga kan kayan abinci su buhun shinkafa, semi, wake jarkan manja da man gyada dasu madara da ovaltine sanan yakoma wajen supplement yasai irin supplements dinan na 30+ matan dasuka wuce shekaru talatin above yakamata suna sha, yawuce yabiya kudi ma'aikatan wajen sukamai packaging kayan sanan suka fitomai dashi, bude boot yayi suka zubamai kayan suka rufe yakoma cikin mota abinci yatayar yawuce yafita daga premises din, wata hanyar ya dauka kafin yay parking agaban wani dan madaidaicin gida mai kyau, kashe motar yayi yafito ya tsaya yana addu'an Allah ya jefo wasu yaran ko almajirai bai gama tunanin ba saiga yaran layin sun keto dagudu daga gani dana kwallo suke, dayake sun sanshi sosai kodan duk randa zaizo saiya musu kyautane yasa suka kwaso da gudu kafin ma yakirasu. "Yaya Waleed, Yaya Waleed, ina wuni, ina wuni, ina wuni" haka duk suka shiga gaidashi ajejjere harya rasa nawane zai fara amsawa murmushi kawai ya sakan musu da sauri kafinma yay magana sukace "me za'a shigan maka dashi cikin gidan Ya Waleed?" remote din motan ya danna hakan yasa boot din motar ya bude, kafinma yay magana suka shiga sunkutan kayan suna cikin gidansu Arham dashi saida suka gama shiga dashi tatas sanan suka dawo wajenshi sukace "munkai Yaya Waleed" kudi yaciro daga aljihunshi yakirga 20k yabasu karba sukayi suna ihu sunamai godiya murmushi kawai yayi yawuce ya shige cikin gidan daidai Maman su Arham nafitowa daga dakin tana tafi da hannu cikeda mamaki, ganin Arham yasa takama habanta tace "ai tunda naga kaya niki niki nasan sai Waleed, waikai Waleed baka gajiya da kashemana kudi dagakai har mahaifiyarka baku gajiya, ai yakamata yanzu duk kubar abubuwan nan tunda kunbama Arham aiki ana biyanshi, eh Waleed" ta karashe maganan da mugun mamaki, murmushi kawai Waleed yayi adan kunyace ya tsugunna yace "ina yini Mama, ya karin karfin jiki" dan dariyan farin ciki tayi takai hannu ta dagoshi a rayuwa tanason Waleed, so dashi kanshi Waleed baisan iyakan son datakemai ba, bala'in sonshi take sabida yama danta komi a rayuwa sanan yaso danta tsakani ga Allah, sanan ya fifita shi sama da kowa nashi aduniyan nan, shafa kanshi tayi tace "Waleed ai jiki kam Alhamdulillah, wayan nan magungunan daka bawa Arham yakawo min tunda nasha yanda kasan tsafi shikenan, muje ciki kaji nacika da surutu kahuta" tai maganan tana janshi ciki, ciki suka shiga, zama yayi akan kujera itama tazauna kujeran dake kallonshi tana washe baki bala'in dadi takeji tace "sannu dazuwa kaji Waleed ubangiji Allah yamaka albarka, Allah kuma yabarka da matarka lafiya" ahankali yace "Ameen Mama nagode" "madallah, madallah, yanzu me za'a kawo maka kaci? Dambu mukai da ranan nan bama adade da sauke ta ba, akawo maka da soyayyan naman talo talo" gyada mata kai yayi yace "Mama kin yanka tala talon kine" "uhmm" ta sauke ajiyan zuciya tana tabe baki tace "ai tunda dan uwanka yatasa yan tala talolina agaba waishi ihunsu na hanashi bacci zai yankasu nace a'a karya sake yatabamin kayana nasan wani abu zai samesu, kasan Arham da shegen bakin hali, ingayama shine fa jiya suka fara zazzabi fa nako gille kayana, nida Salma saici muke, ai bangayamaka ba dayake shekaran jiya tazo ko Arham ma ban gayamishi ba yar wajen kanwata Salma tazo daga kauye, kawai na karbeta koya kagani Waleed, kaga abokin ka bawani zama yakeba kullum ni kadai awanan tangamemen gida daka siyamin Waleed wlh nagaji bansaba rayuwa ni kadaiba, ko kanwar tawama dan mijinta yaki yardane da sonayi su dawo nan kawai tunda gidan gawuri koba komi ai nasami masu debemin kewa" gyadamata kai yayi yace "hakane Mama" tabe baki tayi saikuma ta nisa ta kwalama Salma kira. "Salameme, Salameme, ke Ummu Salama" amsawa yarinyar tayi daga kitchen tace "na'am gani nan zuwa Mama" maida kanta tayi ta kalli Waleed tace "danan bari yarinyar nan tazo kaganta" ki 2min ba'a dauka ba wata doguwan yarinya da tamafi Widad tsayi tana sanye da doguwan rigan atampa ja yarinyar kyakkyawa gata Black beauty, karasowa gaban Mama tayi da sauri tace "Mama gani" baki Mama ta kama tace "nifa dadi na dake haka kike abu kaman makauniya Salma, bakiga yayanki bane Yaya Waleed" tamata pointing Waleed dake zaune a kujeran data juyama baya, juyowa tayi ahankali ta kalli Waleed, jitayi kunya yakamata batasan lokacin data kara duka hannayenta biyuba tarufe fuskarta cikeda kunyan yaran kauyen nan tana washe baki tace "ina kwana" da sauri Mama tace "kwana kuma Salma, oh ni Bilkisu wanga yarinyar wanga yarinya dai to, Allah nagode maka" dan murmushi Waleed yayi yanabin yarinyar dakeda kunyan bala'i da kallo, Mama tace "tashi kije ki zuboma yayanki abinci kihado komi a tray kaman yanda nakoyamiki jiya ki kawomai" tashi tayi tawuce kitchen Mama tabita da kallo tana girgiza kai sanan ta kalli Waleed tace "Waleed kaga Salman ko ya kaganta, yar kanwata ce a kauye suke, ta taba aure sau daya amman ko sati hudu ba'ayi da bakin ba mijin yarasu maciji ya sareshi a gona, ingayamaka shikenan yarasu, yabarta da cikin sati biyu, cikin shima watanshi biyu jikinta yafice da kanshi, na daukota ne musamman sabida nahada aurenta dana dan uwanka" wani irin mahaukacin dariya ne Waleed yaji yazomai da kyar yarike dariyan yadan zaro ido yana kallon Mama, zata sake magana daidai lokacin Salma ta shigo.








Shigowa tayi rikeda tray mai kyau da flask ke kai da plate da serving spoon da cup dakuma juice da ruwa, tun kafin takaraso gaban falon Mama kebinta da kallo sabida taga kotai shirme ganin takawo komi daidai kaman yanda ta koyanata yasa ta sauke ijiyan zuciya, karasowa gaban Waleed yayi daya saukar da kanshi kasa dariya na neman kwasheshi shiba yarinyar kebashi dariya ba Arham kebashi dariya danhar yafara hango bura'uban da Arham zeyi idan Mama tagabatar mai da maganan, harta ijiye ta juya takoma ciki baima saniba sai maganan Mama yaji tace "ya kaganta fisabilillahi Waleed batayi ba"? Gyadama Mama kai yayi yakai kololuwa wajen damke dariyan shi amman saida yar murmushi ta subuce mai yace "tayi Mama" washe baki Mama tayi tace "Allah sarki Waleed wlh kai dan Albarka ne, yaro maijin maganan iyayenshi, jibi fa kai Ammi ka tacemin tana gabatar maka da zancen auren kai na'am inama ace haka dan uwan naka Arham yake, amman ina Arham baida wanan kawaicin" dan shiru tayi tana kallonshi sosai take farin cikin ganinshi ko Allah yasan tanajin Waleed har ranta sosai, ajiyan zuciya ta sauke tace "Waleed daman inaso nakawo maka karan dan uwanka" shidai kanshi nakasa baice komiba tace "kasan menene dan Albarka abokin ka baya kyautamin, tunda yay tafiyan nan bai kirani ba sai jiya, kasan bani iya fito da sunanshi awayan nan daka siyamin, amman ai shi yanada number ta, saida nafita na shiga nan gidan makotan nawa na nemo danta Aliyu inma karike maka zance har jiran Aliyun nayi yadawo daga gantalinshi dan kawai na ganshi na bashi wayan nace yanemo min Arham shinefa yaciro number yakira nasamu nai magana dashi, wai ina mishi korafin bayi wani kirani shine yahau cewa waini nacika fada abu kadan fada kome yayi fada, wai naje naga yanda akema ba'a maka fada kome zakayi agidan ku" ta karashe maganan ahankali alamun kalman yamata ciwo, bata cika kawomai karan Arham ba amman tunda yaga wanan karan takawo mai karan abun yay mata ciwone, ahankali yadago kanshi ya kalleta yace "Mama kiyakuri, ba lallai yanda kikadau zancen haka yake nufiba, kinsan aiki yake sosai achan ko hayaniyan yara zai iyasa yaji baya hayyacinshi, kimai uzuri aiba haka yakeba...." da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login