Showing 15001 words to 18000 words out of 74587 words

Chapter 6 - Duniya Biyu Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

12 Dec 2024

469

"Aby nikazubamin abinci na naci kasan ko I miss abincin gidanmu, abincin school baikai na gidanmu dadi ba, and a Egypt koda yaushe nikadai nakecin abinci kaman mayya, I miss eating abinci cikin yan uwana da babana da Amah, Amah ina Sabeeha?" Amah zatai magana sukaji sahun tafiya hakan yasa duk suka dago kai matar Aby ce tasauko daga stairs rike da dan karamin tray dake dauke da dabino da olives, murmushi ta sakan musu tace "Assalamu Alaykum, ahlan bikum" tai maganan tana ijiye tray agaban Aby, ahankali Aby yace "ahlan bik" murmushi Umm tayi ta zauna kusada Aby tanadan satan kallon Widad data sunnar da kanta kasa tana wasada flowers din kayanta kaman ba itace mai uban surutun nan yanzun nan kafin tazo wajen ba, maganan Aby ne taji akanta yace "yauwa Hibba zoki zubama yarki abinci yunwa takeji dan rigima kuma wai ni zan zubamata" yar dariya Umm tayi tajuya ta kalli Widad din tace "mezan zuba miki yar gatan baban ta?" faduwa gaban Widad yayi hakan yasa ahankali batare data dagokanta ba tace "Umm kibarshi dama wasa nake" ganin yanda tai magana yasa da sauri Aby yace "yaushe za'ai haka, bari nazubamana sai muci tare ko yarinyar babanta" baijira cewanta ba yazuba musu yadebo yashiga bata, shiru duk akayi kowa ya shiga cin abincin, dayake ka'ida ne basa magana in anacin abinci saida suka gamaci tsaf sanan ta tashi zata shiga tattare kayan Aby yace "leave it mamanki da yan aiki zasuyi, Ke magana zanyi dake zoki zauna, Hibba tashi ki gyara wajen nan" ba karamin ciwo maganan yama Umm ba amman saitai kaman bataji su ba yan aiki ta kwalama kira suka shiga kwashe kayayyakin abinci tana ga yamusu inda zasukai saida suka gyara wurin tsaf sanan yadan numfasa yakalli Widad dinda hankalinta yay nisa tanachan tana kallon wayanda ke raye raye a tsakar gidansu yace "Widad" juyowa tayi da sauri ta kallai da dara daran idanunnan nata, ahankali Abby yace "family Ahmad sun zo last week, although nina hana Ahmad karya fadamiki sabida nafison nafada miki dakaina, iyayen Ahmad sunason dansu wato Ahmad yay settling down, yariga yagama karatu dadaddewa so suke amuku aure inyaso shi Ahmad din can follow you chan Egypt din kicigaba da rayuwan ku kina karatu, nima nafison haka Widad so nake kiyi aure hankalina ya kwanta yanzu you are 20 this is just the right time, sai mukai deciding on yau ranan dakika dawo tunda dasafe zaki sauka da daddare sai ai engagement ceremony din in one week time kuma ai biki yakika gani yar albarka?" wani irin kunya ne taji ya lullubeta batasan lokacin data boye fuskarta a bayan Aby ba tanadan murmushi, Amah tahau dariya tana tafi tace "wanan ayanda suke son juna itada Ahmad koyau kace zakai bikin su bazata taba cemaka a'a ba" akunyace ta tashi da gudu tai sama dakinsu ta fada tamaida kofar dakin ta rufe ta daura hannunta kan kirjinta dake bugawa da sauri da sauri, turo baki tayi saikuma ta harari system dinta tace "kojiya da daddare we did video call shine bai fadamin bako" tai kwafa saikuma tace "mun ma bata baran kiraka ba" ta daure fuska tabude kofa tawuce tafita chan rooftop din gidansu tahau babu kowa awajen sai gari dakeke gani ga iska na kadawa tako'ina, ahankali ta zauna tareda tan kwashe kafa ta lumshe ido tana feeling yanda breeze ke dibanta mamaki take dan she never thought of at this stage Aby zai mata aure, tazaci za'a bari tagama school kafin tai aure tunda duka duka saura mata shekara biyu, sosai tai nisa a tunani taji andafa mata kafada, da sauri ta dago kanta Aby ne, ahankali tace "Aby" zama yayi agefenta shima ya ta tankwashe kafa kaman yanda tayi yana kallon garin yanda mutane ke hayaniyan su cikin kwanciyan hankali yace "naje dakinku banganki ba nasan zan ganki anan saisa nabiyoki, Widad" Aby yakira sunanta anatse, dago kanta tayi ta kallai ahankali tace "na'am Aby" dan shiru yayi yana kallonta kafin yamika hannunshi ya shafa lallausan gashin kanta yace "inaso kifada min gaskiya karki ji kunya ta kinji, am your only friend right, inaso kifadamin kinason Ahmad?" shiru tayi tana kallon Aby kafin ahankali ta gyadamai kai, ahankali yace "mesa kike sonshi?" murmushi tadanyi ta dauke kai ta maida hankalinta kan kallon gari da sararin samaniya tace "Aby Ahmad is my best friend and only friend bayan kai, bayan Mama tarasu he was there for me giving me comfort, we use to play different games duddan kawai yaga bana tunani, anytime nafara kuka saiyaga nahakura nai shiru sanan hankalin shi zai kwanta, ko awayane saiya tabbatar daya lallasheni nahakura naidaina kukan sanan zai katse wayan, bayan nafada maka inaso naje karatu wani gari shima nafada mai he supported me, da ina Egypt kullum sai munyi video call, ya koyamin karatu, ya koyamin assignment, komi daya danganci na rayuwana he's there, he is just my everything my best best friend saisa nakeson shi Aby" tai dan murmushi saikuma ta daure fuska tace "but Aby yanzu fushi nikeda shi mun bata ma" da sauri Aby da tuntuni yake sauraronta yace "mesa?" murmushi tayi tace "Aby baifa fadamin his parents came over ba" dan dariya Aby yayi yakama kafadarta yasa hannunshi a aljihu yaciro wani dan karamin box yamika mata karba tayi tace "me aciki Aby?" cikeda jin dadi yace "open it" budewa tayi ahankali wani hadadden zobene na maza mai shegen kyau na gold tace "wow Aby, this is beautiful" tasa yatsanta tana taba ring din, anatse Aby yace "engagement ring dinki ne give it to your Ahmad kisamai a yatsan shi" dago kanta tayi ahankali ta kalli mahaifin nata kaman yanda yake kallonta hawaye ne suka zubo ahankali ta rungume shi bubbuga bayanta yayi yace "shiiii stop crying u are my everything Widad, am working hard in this life because of you if anything happen to you I will die, saisa nafison ayi aurenku ki koma Egypt tareda mijinki banson yanda kike zama a hostel ke kadai, I know Ahmad will always protect you he is a good loving boy" sun dade ahaka tana manne dashi jin ankira azahar yasa yasake ta tareda dagata yace "muje kiyi salla afara shirye shirye" gyadamai kai tayi yadagata suka tafi.







Suna saukowa falo daidai shigowan wata yarinya fara itama tarr doguwa tana sanye da bakin doguwan riga tadaura gyalen rigan akanta batare datai rolling ba ana ganin blonde gashinta hannunta rike da jakan makaranta, Widad na ganin ta washe baki tai wajenta da gudu tai kissing checks dinta starting from the left one taima right din sanan ta rungume ta tace "marhaba Sabeeha" hada ido Sabeeha tayi da Aby daya tsaya yana kallonsu murmushi tayi ta dago Widad din daga jikinta itama tai kissing din kumatun ta sanan ta shafa fuskarta cikin harshen larabci tace "iyye Widad kin kara kyau abinki, kin kara girma kaman bakeba, ya makaranta?" gyadamata kai Widad tayi tana murmushi tace "kema kinyi kyau Sabeeha" "Sabeeha" sukaji muryan Umm daga sama ta kwaloma Sabeeha kira hakan yasa ahankali Widad tasaketa duk suka dagokai harda Aby suka kalli Umm din dake gaban bene, dan murmushi tayi tace "abu zatamin ne sorry na katse musu hira, bari taci abinci saita sauka afara shirye shiryen da ita" gyadakai Aby yayi cikeda gamsuwa yace "hakane, wuce kije kiyi salla Widad bari naje masallacin nima" juyawa Widad tayi kaman yanda mahaifin nata ya umarceta tai dakin Amah itakuma Sabeeha ta gaida Aby ya amsata cikeda fara'a yanai mata barka da zuwa sanan yawuce yafita dan zuwa gabatar da salla a masallaci.


Har daki Sabeeha tabi mahaifiyarta jakan makarantan ta tacire ta ijiye ranta adan bace tace "Umm maisa baki gayamin yarinyar nan zata dawo ba yau?" kofi Umm tadauka ta tittila mata madara a cup din sanan tajuyo ta mikama Sabeeha tace "nima uban nata bai gayamin ba nadaiga anata saka flowers ana gyara gidan nazaci ko yauma iyayen yaron nan zasu sake dawowa ne ashe itace shine dazu dasafe wai na shirya zamuje mu tarbo yar gaban goshinshi daga Airport" cikin fushi Sabeeha tace "shine ke kikawani je, ni wlh Umm bazan yarda Aby nawani treating naki kaman wata nani ba, ke nani yarshi ce kema ai matarshi ce mai matsayin da daraja, ni wlh bazan yarda ana wulakanta min keb....." da sauri Umm tace "ke jinan inhar zai mallaka miki dukiyarshi all his property yakoma naki ai zan iya komi, kinga daga Widad sai ke ku kadaine y'a y'a agidan nan, banda haka ke accounting ma kika karanta kuma yanzu ma final exams dinki kikeyi ke kikafi chanchanta da zama in charge of dukiyoyin shi ba yarshiba" dan murmushi Sabeeha tayi ta mikama maman tata Cup din milk din data shanye tace "Umm inabadai yau Widad zata fadi ta mutuba ta ina Aby zai mallakamin dukiyarrshi nida ba yarshi ba" murmushi kawai Umm tayi ta ijiye cup din tace "leave everything to me, tashi kije kiyi wanka kici abinci saiki sauka kasa wajenta, so nike kiyi amfani da ita hakan zaisa Babanta yakara miki wata daraja na musamman a fadanshi" dan yatsine fuska Sabeeha tayi tace "I can't stand that gurl Umm am so jealous of her wlh, I wish nikeda mahaifin mai sona irin Aby, I wish nikeda all abubuwan data mallaka" tai maganan tana bude dakinta tana shiga ta maida kofar ta rufe cike da rashin jin dadi, yayinda Umm tabi bayanta da kallo, wasu hawaye ne taji sun tarun mata a ido, tarasa maisa Aby baison yarinyarta kaman yanda yakeson Widad, kome Sabeeha take bukata yana mata, shike biya mata kudin makaranta ya ijiye mota na musamman da ita kadai ake kaiwa duk inda zata dashi, babu abinda Sabeeha ta nema tarasa kawai dai wanan son da kaunar da affection dayakema Widad baima yarta shi dudda Sabeeha ce kullum agidan but baitaba jinta kaman Widad ba, baima janta jiki, daukan tray din madaran tayi tawuce ta shiga kitchen din dake falon ta dashi ta ijiye.



Shirye shirye akahau yi sosan gaske abunku da babban gida, ma'aikata ne daban daban kowa na aikinshi, shidai Aby na zaune a falo kan tattausan kujeranshi yana kallon Widad yanda take murmushi dimples dinta na lotsawa duka biyun tana kallon hannayenta da ake mata hadaddun lalle akai, kowani hannu da wanda ke mata lalle akai, itakuma Sabeeha ganin idanun Abba na kansu yasa ta shiga gyara mata dogon gashinta tana applying hair treatment din da aka gama hadamata na gashinta tana shafawa tana bama Widad labarin yanda take fitsari ajiki datana yarinyar Widad sai dariya take kaman cikinta zai kulle.

Sosai Abba ke murmushi yana kallonta deep down jiyake kaman karyama aurar da itan wlh baisan ya ai iya rayuwa ba itaba amman abu daya ke kwantarmao da hankali inya tuna shine yanda yaga tanason Ahmad din shima kuma Ahmad din na sonta, dafa kanshi dayaji anyi yasa yadago kanshi ganin Amah ce da sauri yatashi yazaunar da ita zama tayida kyau sanan ta kalli tsakar gidan dayake kallo tai murmushi tace "Widad kake kallo ko?" murmushi yayi yasake kallon inda Widad din take ya zubamata idanu yana murmushi yace "Amah she smiled just like her mother, Widad dina is so happy Amah" murmushi Amah tayi tana kallon Widad din da Saheeba ke saka mata gashinta cikin shower cap tace "nasan duk inda mahaifiyar ta take she's happy yarta is getting married" murmushi dukansu sukayi atare suka cigaba da kallonsu.
Gama zana mata lallen akayi sanan ta mike tsaye tana murmushi tahau rawa irin na yan mata dinan su Sabeeha namata tafi tana juyawa blouse dinta nasake zama umbrella, sosai Aby ke kallonta suna murmushi mawakan nasake rera mata waka duk wanda zai ganta sai yaji kaman ya saceta ya gudu she looks so adorable and so sweet and happy, ta gefen ido Sabeeha ta lura har yanzu Aby kallonsu yake hakan yasa ta tashi itama ta shiga filin sukahau rawa itada Widad din sosai Aby da Amah nata dariya.



Wuraren magrib aka gama raye raye aka wanke mata gashin ana wake akai drying gashin aka gyarashi tsaf bayan yasha maiyuka akamata parking sanan akasata taje tai wanka, wanka tayo sanan aka shiryata cikin wasu ubansu kaya long kaftan ne milk color dake dauke da stones da bids ta ko'ina masu shining kaman na diamond, djellaba (kaftan mai long lose robe) da aka daure mata igiyan ta wajen waist yay kaman belt, kayan kaman kayan yan India, aka yafamata gyalen kayan aka bayan an gyaramata gashi anyi parking ansaka mata wata sarka ta gaban gashin anmata makeup mai kyau lips dinan anshafa mata red janbaki dayasa tai kyau kaman ita takera kanta, gusan sarewa da wakoki dasukaji yana tashi na welcoming groom's family yasa Sabeeha tace "Ahmad and his family are here, iyye ta Ahmad kinyi kyau" akunyace ta lullube fuskarta tana kara daure fuska ita adole Sabeeha tadena tskonar ta, Sabeeha tai dariya tace "ina platan dake dauke da zoben sa ranan?" ahankali tace "yana wajen Amah" gyadamata kai Sabeeha tayi tace "tom bari naje naga ya ake ciki awajen" fita tayi daga dakin tai dankareren compound dinsu ta tsaya tana kallon kowa, iyayene aketa gaishe gaishe family su Ahmad ne da taasu tawagar yayinda wani kyakkyawan balaraben guy yana sanye da sherwani hadadden gaske milk color kaman kalan na Widad, sai fararen kafanshi sanye da Babouche (traditional morrocan shoes) hadadden gaske shima milk, fuskarshi na kyalli bakin sajenshi da gemunshi a kwance yana murmushi yana kallon kowa kanshi ya kafa wata yar karaman hula milk color dake dauke da bids design tsayamai a tsakiyan kanshi, dan tabe baki tayi ta tsaya daga inda take tana satan kallonshi kaman yaune tafara ganinshi. "Sabeeha" Aby ya kwalamata kira da sauri ta waigo Aby ne da Umm tareda iyayen Ahmad, cikeda fara'a kana ganinshi kasan yau cikin farin ciki yake yace "jeki kawo yar uwanki afara lokaci natafiya" gyadama Aby kai tayi tajuya takoma ciki, bude dakin tayi ta shiga ta tarar da Amah ma natare da Widad din tana kara gyaramata fuska, ganin yanda Amah ke kallonta yasa tace "Aby yace afito da itane Amah za'a fara" dago Widad din Amah tayi tana gyara mata zaman gyalen sanan ta kalli Sabeeha ta nuna mata farantin da jajayen flowers ke cike aciki sai akwatin zoben tace "biyomu da wanan, muje Widad" ahankali Widad ke tafiya idanuwanta akasa har suka fita tsakar gidan inda wakokin larabawa ke tashi taresu maman Ahmad tayi ta rungume Widad din da takasa daga ido ta kalleta tamata kiss akumata tace "masha Allah Widad kinyi kyau" mahaifin shi ma haka yamata kiss akumatu sanan Amah tawuce da ita har zuwa inda Ahmad yake azaune wanda nanne aka tanada dan zaman Amarya da ango Amah ta zaunar da ita akan kujeran gefen Ahmad sanan ta cupping face din Ahmad tace "dan saurayina kai kyau" dan dariya yayi yace "Amah nifa nagayamiki bani sonki jikanki nakeso" dariya tayi tamai kiss akumatu tace "ko kaki ko kaso yaro soyayyan mu ba fashi" tai dariya tareda wucewa tabarsu awajen shiru sukayi Widad taki juyowa ta kallai dudda takosa ta kallai dan tasan yay kyau jikinta na bata hakan. Yana kallon masuyin rawa kaman hankalin shi na wajen yace "tayaya zan fara bawa wacce zuciyata ke bugamawa hakuri?" yadanyi shiru yace "nasan Ahmad mai laifi ne amman da ace Widad zata dan juyo ta kalli Ahmad koda sau dayane da Ahmad yasami natsuwa dan zuciyarshi dab take data buga" dan juyowa tayi ahankali ta kallai saida kirjinshi yabuga baitaba ganin tamai kyau irin na yauba kasa daina kallonta yayi hakan yasa ta dauke kai abinta tanadan murmushi zaiyi magana yaji muryan Aby nabada izini akashe wakan dan zasu fara ceremony din, wani ne yazo yabude taron da addu'a sanan akasa Ahmad da Widad din sufito fili, dan wake aka fara yi ana zubamusu flower kafin abokin Ahmad din dake gefenshi yamika mai farantin zoben daukan akwatin zoben yayi yabude yaciro wani hadadden diamond ring ya kalli fuskar Widad din kaman yanda take kallonshi yace "inason ki Widad and I will love to spend the rest of my life with you, kin yarda muyi taking this relationship a step forward ta hanyar engagement?" ahankali ta gyadamai kai, hannunshi yasa yakamo hannunta ahankali yana kallon fuskarta ya zuramata zoben a yatsa ihu aka dauka da tafi ana jefamusu fulawowi, ahankali Widad ta juya tadau akwatin zoben ta daga farantin da Sabeeha tarike tabude ta ciro zoben sanan ta kalleshi cikin tattausan sweet muryanta tace "Ahmad you've been the source of my happiness and joy inhar ban aureka na zauna akarkashinka ba Menai achieving a rayuwan nan, yes I love you also and I don't have any greater wish daya wuce yin rayuwa dakai" ahankali ta ziramai zoben a yatsunshi hawaye ya cika idanunta saikuma tajuya ta rungume Aby da gudu dake gefen ta yana kallonta tahau kuka, watsa musu fulawowi akahau yi Aby na jijjigata dan tai shiru shikuma Ahmad na satan kallonta Widad is so soft, abu kadan kesata kuka, kaman ma a daura musu auren yau yakeji yahuta da wanan wutan son nata dake cinshi amman ya zaiyi nanda 7days ne tazama tashi halak malak, da kyar Aby yasamu tai shiru sanan yadagota tareda sharemata fuska duk yabi yadamu danshi ko inane ko agaban uban waye baida kunyan nunama yarshi so, cikeda lallashi dakuma damuwa yace "me haka kike kuka so kike kitadamin hankali? Eh" girgizamai kai tayi hakan yasa yace "to menene? Bakida lpy ne?" girgiza mai kai kawai tayi dan batason ta tadamai da hankali zai sake magana Ahmad dayakasa hakura yadan matsi kusadashi cikeda girmamawa yace "ahhh Aby please can I have a moment with her" gyadamai kai Abba yayi yana kara kallon fuskarta cikeda damuwa yace "kuje falona watakila tai shiru, please tafada maka meke damunta" gyadama Aby kai yayi ya kalli Widad din dake share fuska yace "muje" juyawa tayi ahankali sukai ciki yayinda iyayen su suka bisu da kallo cikeda so, instead of yaje falon Aby saiya kaita rooftop her fevorite place in the house, zaunar da ita yayi ahankali kafin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login